PAGE 2
by @1239900
Babu zuciya haka Dan Talo ya durqusa a gaban matan nasa yawu na qoqarin zubowa daga bakinsa, sai surutu ya ke zubawa mara ma'ana,ganin basu da niyyar sallamarsa ne ya sanya shi yin magana cike da kosawa ya sake wage baki yana surutu. A hasale Mai Buruji ta kalli Lamishi ta ce
"Ni dai don Allah yi sauri ki sallame shi ya tafi,gaba ɗaya ya cika min kunne da surutun banza"
Ta ƙarasa maganarta tare da wurgawa Ɗantalo harara. A hasale ya zaburo kanta yana faɗin.
"Wa kike cewa yana yin surutun banza? Na ga alama Mai Buruji ta gama raina ni a gidan nan,ke tsaya ki ji ni da kyau,idan taƙamar iskanci da rashin kunya ki ke ji na dame ki na shanye, kin dai san hakan ko?"
"Ahayyyee washhhh ! Ƙwarai ni ko na san ka dame ni ka shanye a rashin kunya,tunda ga ƙarshen rashin kunya nan ka zauna a gida ba za ka fita biɗar na kanka ba,ka zauna sai dai mata su biɗo su kawo gida ka cinye tare da goge baki,kana gamawa kuma ka dasa wa mutane mita da faɗan banza."
Har Ɗantalo ya buɗe baki zai yi magana Lamishi ta miƙa masa kwano cike da abinci, tini ya rufe bakin shi ya karbi kwanon ya yi waje ya na fadin,
"Ina zuwa ki jira ni kin ci bashi. Ki jira har na gama cin abinci za ki maimaita abinda ki ka fada da babban baƙi."
"Haka nan ka iya dama,namijin hotiho kawai."
Lamishi kuwa da ta dawo daga ajiye abincin yaran su sai ta dangwara kwanon nasu abincin a gaban Mai Buruji ta zauna tana faɗin.
"Ke dai ba ki gajiya da jayo mana wancan dan na gaji mitar ya zo ya yi ta yiwa mutane cin mutunci, sarai kin san ni ba haƙuri na cika ba a zo gida ya rike rai ya yi ta ɓaci"
Dariya Mai Buruji ta fara yi ta na kai lomar shinkafa bakin ta. Suna tsaka da cin abinci wata mata sirirya baƙa ta shiga gidan ta rangaɗa sallama tare da cewa
"Mutanen gidan na nan kuwa?"
"Me zai hana su zama a gida a daidai wannan lokaci kuwa uwar kwaɗayi? Kin san sarai muna nan,shigo ciki mu ci abinci idan zaki shigo."
Washe baki ta yi tana lasar harshe ta ce.
"Kai bawa ai ba ka ƙi ta mutune ba,shi abinci abokin kowa ne dama."
Babu Bismillah matar nan mai suna 'Yabbuga ta danna hannun ta a kwano ta fara yanka lomar shinkafa bakinta,sai da ta ci loma biyar sannan ta hau ƙoƙarin basu labari. Cikin sauri Lamishi ta ce mata.
"Dan Allah dai ki bar surutun nan haka,dan gaba ɗaya mayar mana da na baki kike yi cikin abincinmu."
Wata sabuwar lomar ta kai bakinta,tare da lumshe ido ta ce.
"Akwai labari"
A tare suka haɗa baki suka ce.
"Ai mun san ba a rasa nono a riga"
A shagiɗe ya shiga gidan yana zuƙar sigari,ba tare da sun ga zuwansa ba sai ji suka yi ya yi fatali da butar da ke saman hanyar shiga cikin gidan. Kansa yake yi wa kirari kamar mai shirin shiga daji farauta, daga qarshe sai ya taƙarƙare ya zabga wani uban ihun da ya sanya 'Yabbuga kwarewa da shinkafa tsabar tsoro. Tarin da ya taso mata take ta ƙoƙarin maƙalewa amma abun ya ci tura. Idanuwanta na zubar da hawaye ta hau zuba tari tana yarfe hannu. A hasale Lamishi ta kalle shi cikin ɓacin rai ta ce.
"Lawwali yanzu tsakanin ka da Allah fashe min buta zakai ka tafi ka barni da sayen sabuwa? Ka..."
Kafin ta ƙarasa magana ya kalleta yana tangaɗi kamar zai faɗa kanta ya ce.
"Ina abinci naaa...yunwa nake ji...ciki na ba komai kamar tekun da ta qafe haka nake ji na"
"Yana can kitchen tafi ka dauka lalataccen banza da wofi kawai."
Wata zabura ya yi kamar ba shi ne ya shiga a bige ba ya zaro wata sharbebiyar wuƙa a ƙugunsa ya goga ta a ƙasa tare da zuba irin wani uban ihun da ya fi na da, nan take 'Yabbuga ta zabura ta runtuma dakin Lamishi a guje ta na fadin.
"Tsautsayin halaka ne ya kawo ni gidan nan yau Lawwali na gari, da na san ya na gari da ban zo kwadayi ba,yau na shiga uku na lalace Allah ka taimake ni na fita daga gidan nan lafiya."
Jikinta banda rawa babu abinda yake yi,ga wata uwar zufa na karyo mata kamar wadda kunama ta ɗalleta. Ƴabbuga na bala'in tsoron Lawwali, irin tsoron da ko Allahn da ya halicce ta bata yi masa irinsa,Ƴabbuga a rayuwarta ko salloli biyar basu dame ta ta tsaida su ba, yanda take tsaida gulma da munafurci a unguwar. Shi kuwa Lawwali dan ya farke mutum ya ɓace a neme shi sama ko ƙasa a rasa ba wani abu bane a wajen shi , ko da an kama shi ma ba ya kwana a cell, a ranar ake fito da shi,daga ƙarshe wanda ya sa aka kama shi ya jawa kan shi masifa da bala'i,dan ba zai barsa ba sai ya ɗauki fansa. Saboda sanin halinsa sai mutane suka hakura da kai shi ƙara wajen hukuma suka taru suka zuba masa ido.
A shagiɗe ya wuce kitchen ya ɗauki abincinsa ya fita zuwa dakin shi da ke zauren gidan ya na fito cike da ƙwarewa,wata ajiyar zuciya 'Yabbuga ta sauke, tare da ƙarasa sude hannunta da ta ci abinci. Leƙe ta hau yi ta window dan ganin shin ya tafi ko yana nan? Ta na ganin fitar shi ta yi wuf ta fito itama kwashe takalmanta tayi a hannu ta fara bin bango cike da sanɗa, Lamishi na yi mata magana akan ta tsaya ta fesa masu me ya faru a unguwa da basa nan, ta ce su same ta a gida,tana kaiwa soro ta zura da gudu ta yanki kwanar gidanta,sai da ta yi nisa da gidan ta zube takalmanta a ƙasa tana haki ta nufi gidanta tana tsinewa Lawwali a cikin ranta. Ƴabbuga Kwata-kwata bata son duk wani abu da zai haɗa ta da Lawwali, saboda ya na da ɗaurin gindi sosai a wajen manyan mutanen garin. Lawwali matashi ne da bai san me ake kira da tsoron ba, yana da juriya,dauriya tare da jajircewa a duk wani aiki da aka saka shi,basu taɓa saka shi aiki ya koma bai cika musu shi ba,duk wahala da hatsarin aiki baya hutawa sai ya biya wa shugabannisa buƙatarsu.
Shi yasa suka dauke shi a matsayin wata kadara tasu mai amfani da mahimmanci,wadda suke kula da ita da dukiya, da ƙarfin mulki da ikonsu, gudun kar wani abu ya same shi.
Lawwali shi ne babban d'an Lamishi wadda ita ce uwar gidan Dan Talo, masu bi mashi mata ne guda uku, Rakiya, Ashibi, da Lami, dikkanin su suna dakin mazan su, sai autar Lamishi mai suna Mubaraka. Mai Buruji na da yara biyu maza, Kamilu da Jamilu. Duk yaran gidan Ɗantalo babu wanda ya yi makarantar islamiyya ballantana kuma boko sai Mubaraka. Ita kadai ce ta ke zuwa islamiyya da kuma boko,wanda da kyar ta samu Lamishi ta amince tare da sanya bakin Lawwali. Lawwali na mutuwar son ƙanwarsa Mubaraka kamar ransa, ba ya son duk wani abu da zai ɓata mata rai,ko ya taɓa lafiyarta. A ɓangare guda kuma Lamishi babu wanda take takurawa a gidan sama da Mubaraka,Mubaraka yarinya ce mai tsananin biyayya,hankali,nutsuwa,riƙo da addini,son tsayar da gaskiya tare da kore ƙarya. Sai dai waɗannan halayen nata na yawan haɗata faɗa da mahaifiyarta,dan gani take yi Mubaraka na yi mata rashin kunya da nuna musu ta fi su tsoron Allah da bin dokokinSa. Wannan dalilin ne ya sa duk abinda Mubaraka ta ke so sai ta bi ta hannun Yayanta Lawwali kafin ta same shi.
Shekarar Mubaraka sha shida, a duniya amma ta matsu ta yi aure itama kamar sauran yayunta, ta bar ma su Lamishi gidan ko ta huta da tsana da tsangwama da ake yi mata a gidan.
Kusan kowanne gida akan sami irin wannan, yaron da ya fi yin biyayya tare da sanin ya kamata da ciwon kan shi ya fi shan wahala da samun tsangwamar iyaye da ƴan'uwa. Sannan duk wani aiki da wahalhalun gidan a kansa suke ƙarewa,baya taɓa samun yabawa ballantana kulawa daga iyayensa da ƴan'uwansa a koda yaushe. Yana ji yana gani za a dinga fifita marasa amfanin gidan shi ana ture shi gefe.
Irin haka ne ke faruwa da rayuwar Mubaraka a cikin gidan su, wajen Lawwali kawai take samun yabo, da soyayya har ma da kyauta, lokuta da dama har mamaki take yi tare da zargin anya Lamishi ce mahaifiyarta kuwa? Amma kamanninsu da juna kad'ai na share mata tantamarta akan hakan.
Mubaraka irin yaran nan ne baƙaƙe masu matsakaicin kyau,amma saboda kyaun hali da d'abi'un ta mutum ba zai gaji da zama da ita ba. Sallama ta yi a tsakar gidan nasu fuskarta ɗauke da murmushi mai annuri. Ba komai ne ya saka ta yin murmushi ba, sai ganin alamun yayanta na gida.
Kai tsaye ɗakinsa ta shiga ta same shi suka gaisa ya ɗauki tsarabarta ya bata. Littattafai ne da biskit, da alawowi. Lawwali na gama bata tsarabarta ya kulle ɗakin nasa ya bar gidan,dama zaman jiranta yake yi shi yasa da ya ɗan cakali abincin ya zauna har sai da ta dawo.
Ba tare da sun amsa sallamar ta ba, Lamishi ta kalli sabuwar ledar da ke hannunta ta ce,
"Ke ! Menene wannan a hannun ki?"
Cikin ɗoki da murna Mubaraka ta ce,
"Tsaraba ta ce da Yah Auwal ya kawo min"
"Kawo ta nan in gani,ai bake kaɗai bace ƴa a cikin gidan,Lawwali ne ke bata yarinyar nan take yin abinda take so. Shi dai bashi da aiki sai na bannar kuɗinsa a harkar banza, ayi ta siyan takardun da ba su da wani amfani ana cika su da jagwalgwalo ana kimewa a ɗaki."
Da fari ko kadan Mubaraka ranta bai ɓaci ba da Lamishi ta ce ta kai tsarabar, dan dama ko bata ce ba, ba zata ci komai ita daya ba sai ta raba da su, amma zagar mata takardu da karatun ta anan ake samun matsala da ita, nan da nan kuwa ta tura baki, alamar ran ta ya baci.
"Za ma ki bar turo min shegen goshin nan naki gaba ne sai kace jinjirar jaka. Maza ki zo ki bani abinda ya kawo miki nan."
Mubaraka na matsawa kusa da Lamishi ta sa hannu ta amshe ledar ta hau bubbuɗa cikinta, tana yin karo da littatafai sai ta hau yin wurgi da su a ƙasa,cikin sauri Yarinyar ta bisu tana kwashe abinta cikin ƙunar rai, ko biskit din bata tsaya amsa ba ta shige dakinsu tana jin hawaye na ƙoƙarin zubo mata.
A nan take su Lamishi suka rabe kayan ƙwalamar har da ƙawayen su da suke nunawa kalar azziqin da suke da shi a unguwa, yamma kawai suke jira ta qarasa yi su fita dabarsu ta unguwa a sha hira, kafin nan sai kowaccen su ta nufi dakinta ta kwanta babu sallah babu salati.......... [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: *A GARINMU*
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH