PAGE 3
by @1239900
Allah ya halicci duniyar nan kusan komai guda biyu ne, misali,da ya yi duniya sai kuma ya yi lahira,mace da namiji, mutum da aljan, mai kyau da mara kyau. Unguwar TUDUN FAILA itama ta qunshi mutane kashi-kashi a cikinta, akwai mutanen kirki sannan akwai na banza, a kuma kwai 'yan babu ruwanmu da kowa.
Mutanen kirkin da ke unguwar TUDUN FAILA sun fi na banza yawa sai dai ya na daga cikin d'abi'ar dan Adam bayyana mummuna ya boye kyakkyawa, wannan dalilin ne ya sanya mutanen kirkin unguwar suka ware kan su daga cikin irin su Dan Talo da matan shi,duk da hakan da suka yi baya hana mutane kiran matasan su da ɓata gari a cikin gari. Bahaushe ya ce,wake d'aya ke bata gari.
Lamishi ce ta fito cikin wata atampa mai kyau da hijabi kalar kayan ta, ƙafarta sanye take da baƙin takalmi mai kyau,hannunta na dama kuwa riƙe yake da wayarta shafa-shafa. Cikin isa ta kalli qofar dakin Mai Buruji ta yi tsaki sannan ta ce,
"Ke dai akwai malalaciyar mata, komai saurin da ake yi sai kin bata wa mutane lokaci, Allah ya cece ki kar a tashi tafiya Makka ki makara, walle jirgi tafiyarda zai ya barki, ba ruwansa dan shi ba ya jiran kowa"
Cikin dariya Mai Buruji ta fito sanye da ta ta shigar kamar wadan da za su je biki ko suna. Kallon ta Lamishi ta yi ta miqa mata hannu suka tafa, sannan suka sanya dariya kamar wasu yara. Cike da shaƙiyanci Lamishi ta ce.
"Meye ya baki dariya?"
"Idon mutuniyar na hango,na tabbata idan taga wannan kayan a jikin mu sai hankalin ta ya tashi,kin dai san hali."
Dariya suka yi suka tafa a karo na biyu tare da nufar ƙofar fita daga gidan nasu,suna daf da isa zaure Kamalu dan gidan Mai Buruji ya dawo daga yawo, ƙafarnan tayi fururu kamar manomin da ya wuni a gona. dika-dika Kamalu ba zai wuce shekaru sha uku ba a duniya,idan ya sa kai ya bar gida sai an zaci barin garin ya yi sannan ya dawo.. Saɓanin ɗan'uwansa Jameelu mai shekaru sha biyar a duniya, a koda yaushe Jameelu na kusa da gida,baya nisan kiwo,da ya zaga unguwa ya gaji yunwar cikinsa ta dame shi zai yo gida ya ci abinci ya ƙoshi wataƙila har ma ya kwanta bacci. Kamalu kuwa idan ya fita tun safe yana iya kaiwa sha daya na dare a waje watarana ma har sha biyu yana kaiwa shi ke rufe musu gidan. Ranƙwashi Lamishi ta kai wa sumarsa da ta taru kamar gidan bushiya ta ce.
"Ja'iri na san yunwa ce ta dawo da kai gida, da ace ka samu inda kaci abinci ma na san sai dare za a ganka."
Duqar da kan shi yayi cikin sauri ya kauce wa dukan da Lamishi ta kai masa a karo na biyu ya na dariya. Ciki ya shige su kuma suka fita dandalin hira ko kuma a kira wajen da majalisar matan unguwa. tun daga nesa suka hango wasu mata guda biyu zaune a saman duwatsun dake a qasan bishiyar darbejiya mai yalwar ganye da ni'ima.
Daga nesa 'Yabbuga ke wara ido dan ganin sunan atampar da su Lamishi suka sanya a jikinsu,sai dai duk yanda ta so ganin sunan atampar hakan bai samu ba saboda tazarar dake tsakaninsu.. Suna daf da isowa wajen ta kula da yanda aka kalmashe ƙasan zanin aka dinke shi,ta yanda duk ƙwaƙwar mutum ba zai iya karanta sunan atampar ba. Da isar su sai matan suka hau shewa,cikin dabara Ƴabbuga ta saka hannu ta shafi jikin atampar Mai Buruji da tafi kusa da ita tana yi musu sannu da zuwa,wani mugun kallo Mai Buruji ta yi wa Ƴabbuga sannan ta ce mata.
"To sa'idawa shafa da kyau wallah, super ce dai da kika sani ba komi ba,kuma sabuwar ta mu ka saka ba kwance ba,ko kema zaki siya ki ɗinka ne?"
A hasale Ƴabbuga ta mere baki ta ce.
"Yo in da kudin kuturu alkaki ai sai na qasan kwano ko?"
Lamishi da Mai Buruji sai suka sanya shewa tare da tafawa,cike da shaƙiyanci Lamishi ta kalli Ƴabbuga ta ce.
"Ahayyyyeee Allah gani inji gurguwa, watarana kam kuturu zai hadiyi yawu da quda,dan wani alkakin na sarakai ne,ba na siyan gama garin mutane bane...keni rabu dani da surutun nan naki na banza, bamu labari mene ne ki ke son fada mana dazu ki ka ga dodon ki Lawwali ki ka gudu"
Wadda ake kira da Ta Yahai (Yahya kenan) cikin dariya ta ce,
"'Dana ya shigo gari kenan, dan albarka me maganin munahukan unguwa."
Dariya suka sanya baki ɗaya su ukun suka yi shewa,Yabbuga kuwa ranta a matuƙar ɓace ta karkata kai tana kallonsu, dan ta riga da ta san san ci mata fuska kawai suke yi,tunda babu wanda bai san yanda take tsoron Lawwali ba. Sai da suka gama yi mata ɗan biki sannan Lamishi ta taɓa ta tana dariya ta ce.
"Ke rabu da Ta Yahai, bamu musha kin ji,duk iskancin ɗan nata ai bai isa ya taɓa ƙawar uwassa ba."
Nan take Ƴabbuga ta gyara zama dan jin an sosa mata inda yake yi mata ƙaiƙayi.
"Hummm na taba ku da alheri ƴan'uwa wai kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta....jiya akai dirama a lungunmu, tsakar dare naji ana ta zabga ihu, ana bada haƙuri, kun san halina da son jin gulma,nan take na tashi zaune na tada DanJumma, ko da mun ka saurara, ashe mutuniyar ce ke karɓar duka wajen jaruminta,"
Ran Lamishi ne ya ɓaci,a hasale ta ce.
"Kaiii amma wannan mutumi ba dan Sunnah bane, to me ta yi masa da zafi haka?"
Mai Buruji kuwa tsabar son jin gulma har waje ta yi wa kanta daf da Ƴabbuga ta zauna tana kallon bakinta kamar za ta faɗa ciki. Kyaɓe baki Ƴabbuga ta yi tana jin daɗin gulmar da ta kwaso musu ta ce.
"Yo ai abun ba sabo bane kuma kun sani,ita da yara ne suka yini ba bu ko kwayar hatsi a gidan,dare ya yi dan bashi da kunya ya lallaɓa karɓar lamuran duniya,kun dai gane,to shine fa ta hana shi sauke buƙatarsa, shi ko dake ba haƙuri gare shi ba ya hau bugun abun banza,ya danneta ya amshi haƙƙinsa ta ƙarfin tuwo,yana gamawa ya tsallaketa ya bar ɗakin shine ta ke ta ihu kamar ana zare mata rai."
"Ohhhh wannan abu na Isa shi ake kira da ƙarfin hali ɓarawo da sallama,wai ta yaya za a daki mutum sannan a hana shi kuka? a gaskiya mutunin nan azzalumi ne na ƙarshe"
Lamishi ta ƙarasa magabarta cike da tausayawa. Lokuta da dama idan ana bata labarin Hansatun Isa ji take yi kamar ta je ta koya mata yanda za ta yi masa rashin mutunci,dan shi ba irin mazan da ake yi wa biyayya a zauna lafiya bane. Sai dai duk wanda ya kwana ya tashi a unguwar ya san cewa Hansatu ta kame kan ta bata hulɗa da matan unguwa sai abinda ba a rasa ba na dole dake haɗa su da junansu. Ita ɗin mace ce da take da ƙoƙarin rufe sirrin gidanta tare da kiyaye dik wani abu da zai haɗa ta hulda da su Yabbuga, tunda ta san halin su sarai na gulma da munafurci.
Su na nan a waje suna ta gulmar ta, ita kuma tana cikin gida ta na fama da matsanancin ciwon ƙirji,wanda tsananin yunwa ya haddasa mata shi. Yaranta guda uku ta kalla taga ga yanda suke kai lomar ƙanzon da ta daka ta zuba ruwa da ɗan ƙuli-ƙuli da gishi ko azziƙin mai babu,nan da nan ta ji zuciyarta ta karye. Da rarrafe ta isa gaban kwanon ta damƙi loma daya ta kai bakinta dan lafar da azababbiyar yunwar dake addabarta. Wani irin zafi da murdawa qirjin nata ya yi kamar ta watsa wa ciwo gishiri,nan take ta rintse ido tare da kama ƙirjin nata ta lallaɓa ta koma ta zauna tana mayar da numfashi da ƙyar. wasu hawaye ne masu mugun zafi suka hau zubo mata a kunci da gudu, da sauri ta saka hannuwanta biyu ta share dan kar yaran su gani,sai dai duk saurinta haƙanta bai cimma ruwa ba,karaf suka haɗa ido da ƙaramin yaronta mai shekaru huɗu a duniya,dakatar da cin abincin ya yi ya ce,
"Umma sannu ƙirjin ki ne ke yi miki ciwo?"
Cikin murmushin yaƙe ta ɗaga masa kai tare da cewa,
"Eh shi ne ke yi min ciwo Ahmad, amma yayi sauqi yanzu da ka yi min sannu,tsaya ma ka ga yanda zan tashi cikin kuzari na. Maza ka ci abincin ka yaron kirkin Ummaa,ku tafi makarantar islamiyya."
"To Umma"
Ahmad ya ce cike da murnar ganin Mahaifiyarsa a tsaye da ƙafafuwanta. Nan take Amina da Bilkisu ma suka yi mata sannu sannan suka dauki dan sauran ƙanzon da suka rage suka ajiye a gaban ta suka ce sun qoshi. A raunace Hafsatu ta ce musu.
"Abincin da ba shi da yawa shine har kuke ragewa? Maza ku cinye ku samu ƙarfin yin karatu,idan Allah ya yarda kafin ku dawo zan yi mana girki mai kyau."
Qin ci suka yi kamar yanda ta umarce su,sai kawai suka bar mata kwanon a gaban ta suka tafi da gudu zuwa wanke hannu, suna gama wankewa Amina mai shekara goma ta shirya Ahmad cikin wasu yagaggun uniform din da sun gaji da duniya har sun ɗage masa, ita kuma hijabi kawai ta saka tamiqawa Bilkisu mai shekaru takwas nata hijabin, su na kammala sakawa suka yi wa umman su sallama suka fita, bakin su dauke da addu'ar fiya daga gida.
Ta gaban su Mai Buruji yaran suka wuce suna gaishe su cike da ladabi da biyayyar da mahaifiyarsu ta ɗora su akai. Amsawa suka yi su na bin su da kallo kamar a wannan ranar suka fara ganinsu. Mai Buruji ce ta yi ƙwafa ta ce.
"Dazu da muka dawo daga aiki na hango Babansu a ƙofar gidanmu wajen cin abinci"
"Ba dole ki gan shi a wajen ba Mai Buruji? Ai yanda kika san dan shi muke zuwa aiki,kullum yana nan zauna a ƙofar gida yana dakon zuwanmu,yana gama cin abinci yake tattare rigarsa ya ƙara gaba zuwa yawon bin inuwa."
Yabbuga ce ta karkace zata yanko wata gulmar,sai ta ja baki ta tsuke saboda hango Isa tafe da ta yi zai shige gidansa,sai wani buɗawa yake yi cike da izza da isa da taqama, wanda be san shi ba zai iya rantsuwa da Allah wani namijin azziqin ne.
Cikin sauri matan suka kashe murya har su na rige-rigen gaishesa,juyawa ya yi ya amsa tare da tsokanar su Lamishi ya ce.
"Ah ah ka ga matan Dantalo masu babbar shiga da babbar harka, irin wannan gayu haka kamar wanda za su je gidan biki? Ko dayake masu hidima a gidan Gwauna ai dole ku wataya da sutura son ranku. "
Murmushin jin daɗi suka yi a tare suna kallon junansu, tare da jin kansu kamar zai fashe dan girma. Nan da nan Yabbuga ta saki dogon tsaki ta ce,
"Haramun dai ka aikata da ka tsaya yabon matan wani, ka baro ta gida ba yabo kana kallon na maƙota."
Dariya Isa ya yi ya ce.
"Yabbuga dai kishi take yi da ku wallah, kun San bata iya ganin wani ya yi abu bata yi irinsa ba,yanzu sai a samu matsala da ita."
Dariya suka sanya har da shewa kafin ya shige gida ya bar Yabbuga da mita.
Isa na daf da shiga cikin gidansa ya ɗaure fuskar nan tamau,sai kace ba shi ne ya gama hira da matan wasu a waje ba....... [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH