A GARIN MU

PAGE 4

by @1239900

Jin motsin shi ne ya san ya ta miqe wa da kyar hankalin ta tashe, domin shi din kamar wani dan aiken mutuwa ne a gare ta,ta sani sarai rashin fitar ta tsakar gida zai iya ja mata masifa a wajen mijin nata da take tsananin so da qauna.

Murmushin yaqe ta sanya a labban ta tare da yi masa sannu da zuwa, bai amsa ba sai ma shura buta da ya yi da qafar shi ta hagu, cikin wani irin mummunan yanayi ya juya ya kalle ta, yawu ta hadiya da kyar cike da tsoro bakin ta na rawa ta ce,

"Ka yi haƙuri su Amina ne suka wanke hannu, Na....naaa manta ban sake zuba ruwa a ciki ba."

A hasale Isa ya ce mata.

"Zaki debo min ruwa ko surutun banza za ki tsaya yi min?"

Da sauri ta tafi daukan butar,sai dai kafin ta kai ga dauka har ya tura mata da qafarsa,baya ta ɗan ja saboda kar ta bige ta sannan ta duqa ta dauka, wajen diban ruwan bashi da nisa da inda Isa yake a tsaye,madadin ya ɗiba ya yi lalurarsa amma ba zai yi hakan ba sai ya wahalar da ita.

Ta na gama zubawa a butar ta duqa ta fara zuba masa a hannuwansa,nan take qamshin miya ya daki hancinta. Murmushi ta saki mai ciwo, ta tabbata yau ma ya ci abinci a waje ba tare da ya damu da ita ko yara sun ci ko basu ci ba. Murya na rawa ta ce.

"Baban Amina, don Allah ko akwai dan kuɗi a wajen ka na samu na dafa mana abinci kafin yara su dawo daga makaranta?  Yau kwana uku kenan ba mu ci abincin kirki ba a gidan nan, ɗazu ma qanzo na samo gidan Yabbuga na dafa muka ci, kuma da alama yaran nan basu qoshi ba."

Hannayen shi ya sanya a qugun shi ya na yi mata irin kallon nan mai kidimar da wanda ake yiwa shi,nan take ta yi matuƙar gigicewa,dan ta san tana gaf da karɓar hukunci mai tsanani a wajensa. Gyara tsayuwarta ta yi kanta a ƙasa tana jiran abinda zai je ya zo,tinda bata da zabi dole ta tambaye shi,ko babu komai shine wanda haƙƙin kula da su ya rataya a kanshi. A hasale Isa ya kalle ta ya na nuna ta da yatsansa manuni ya ce.

"Wato kin raina ni ko Hafsatu? Na ce kin raina ni ko? Kin raina ni mana tinda kika fara yi min tambayar titsiye. To ina da kudi bari ma ki gan su, ba zan bayar ba sai ki yi duk abinda za ki yi."

Hannu ya sanya a aljihun shi ya zaro dari bakwai ya nuna mata, sannan ya miqa su daidai fuskar ta yana kaɗawa ya ci gaba da cewa.

"Ko zaki kwata ne tunda na ga kin yi qarfin halin yi min magana yanzu, so ban sani ba ko kin yi qarfin duka na ki amshi abu a hannu na."

Kaɗa kai take ta yi kamar ƙadangaruwa tare da fadin,

"Ah ah ka yi haƙuri ba haka na ke nufi ba"

"Hansatu , Hansatu, Hansatu ki kiyayeni kar ki bari na juyo kan ki ba zaki ji daɗi ba"

Duqar da kan ta tayi, tare da share majinar da ke diga daga hancin ta, saboda kukan zucin da take yi. Daki ya shige ran shi a matuqar bace. Cike da isa da taƙama irin ta namijin da ya isa da gidansa Isa ya ja kwanon da Hafsatu ta ajiye masa a shimfiɗa mai kyau da tsafta gabansa ya zauna, yana buɗewa sai ga irin abincin da ta bawa yara suka ci a kwanon, duk uwar yunwar da suke ji bata juye musu da yara sun cinye ba sai da ta aje masa.

Dan mugunta irin ta Isa duk da cewa a ƙoshe yake bai hana shi danna hannu a ciki ba ya fara kai loma zuwa bakinsa. Tinda ya fara ci bai ajiye ba sai da ya cinye tass ya sude kwanon ya yi fatali da shi sannan ya kora ruwan da ta ajiye masa a jug,yana gamawa ya kaɗe jikinsa ya bar gidan.

Qarfe biyar da rabi na yamma na bugawa gabanta ya yanke ya faɗi, kaiwa da komowa ta dinga yi a tsakar gidan tana tunanin mafita akan yanda zata samawa yaranta abinda za su ci. Duk da tana gudun wulaƙanci da tonon asiri babu yanda ta iya kan dole ta yafa mayafinta,sannan ta saka takalmin ta silifa da ya sude ya ke qoqarin bulewa ta ƙasa. Jan qofar gidan ta yi jiki a sanyaye ta nufi dandalin gulmar su Lamishi, duk wanda ya kalle ta da kyau zai tabbatar da ta sha kuka. Babu yanda ta iya haka ta tinkare su tunda mai rufa mata asirin ya tone shi kowa ya san halin da suke ciki,  (ba mai rufa asiri sai Allah).

Ta na zuwa ta gaishe su cike da girmamawa dikkan su amsa wa sukai cikin zumudin son jin me ya faru take kuka.

Shiru ta yi kamar ba zata ce komai ba,sai da ta nisa sannan ta gyara tsayuwarta,ganin ta ƙi magana sai kawai suka ci gaba da hirar su hankulansu na kan ta, gani ta yi lokaci na tafiya,sai ya aro jarumta cikin sanyin murya ta ce,

"Uhmmm... Nicce ko akwai wadda ke da wanki cikin ku? Ku kawo na hwara na kuddi, amma za a haɗa min da kuɗɗin wanki da klin da toka(sabulu) "

Kusan a tare suka haɗa baki suka ce babu. Kallon su ta yi a razane tana jin kamar sun daki zuciyar ta, nan take zuciyarta ta hau raua mata to da me za su ci abincin dare? A sanyaye ta sake cewa.

"To ko wani aiki ba ku da shi Wanda zan yi ku biya ni?"

Lamishi ce ta ja ta  gefe ta ce mata,

"Ina da wankau amma fa na yau ne kawai zan baki, ba wai kullum zaki dinga yi min wanki ba"

Wani irin farinciki ne ya lulluɓe Hafsatu ta ji kamar ta taka rawa. Kamar ta durqusa a qasa haka ta yi wa Lamishi godiya. Nan take suka koma gidan Ɗantalo Lamishi ta bata wankin,sannan ta bata kudin omo da sabulu tare da biyanta ladan wanki dari uku, godiya Hafsatu ta dinga yi har da kwallar ta.

Ɗaukan wankin ta yi a ka ta yi shago ta auni wake, dan ya fi arha,sannan ko babu komai idan sun ci za su yi ta kora ruwa saboda riƙon cikin da yake da shi, man ja da maggi ta siya,tare da ta omo da sabulun wanki daga nan ta wuce gida da azama. A hanyar ta ta komawa gida ne, ta ga dandalin su Lamishi suna nan suna hira, kafin ta qarasa ta ji Lamishi na basu labarin irin taimakon da ta yi mata,ranta ya sosu da jin hakan,amma ba yanda ta iya, sai ta ɗora laifin duka akan wanda ya ajiye ta wato Isa, ta na yin kusa da su suka yi shiru kamar ba su ne ke maganarta ba.

Gida ta shige ta ajiye kayan,sa sauri ta haɗa wuta da guntun itacen da take da shi ta wanke wake ta zuba a tukunya tare da jiƙa tokar murhu kadan ta zuba dan ya dahu da wuri, fatan ta Allah ya sa ya dahu da wuri kafin itacen ya ƙare, ba dan yaran sun kusan dawowa ba ma da jiqa waken zata fara yi dan ta rage asarar ice.

Bokiti ta dauka ta je majalisar su Ƴabbuga ta roƙe ta ruwa,kasancewar tana da rijiya a gidanta shi yasa Hafsatu ke zuwa gidan ɗiban ruwa lokaci zuwa lokaci. Cike da daure fuska ta ce ta je ta ɗiba amma kar ta jiƙe mata bakin rijiya, godiya ta yi ta shiga ta dinga jidar ruwa qirjin ta na yi mata matsanancin ciwo, amma ba yanda za ta yi, dole ta yi hakuri ta yi abinda zai sama musu abinci a kwanon su da yaranta. Sai da ta yi kai uku tana fitowa daga gidan Yabbuga ta ji ta na bawa su Lamishi labari.

"Kuuu ban baku labari ba kun kuwa san an yi baquwa a unguwarnan tamu? Humm in kuka ganta kamar baƙar tukunyar miya tsabar baƙi. Mijinta kuwa fari tas kyakkyawa da shi gwanin burgewa,nan take na ce wannan bawan Allah ko me ya gani har ya kwaso mace da muni haka sai kace wanda kuɗinsa basu cika ba"

Dariya suka sanya da shewa sannan suka tafa,

Ta Yahai ce ta kai wa Ƴabbuga duka a kafaɗa ta ce.

"Yabbuga idon duniya kenan, ta wanne bangare gidan yake gobe in su Lamishi sun taso aiki mu je ganin gida ?"

"Can bayan gidan su Lamishin ne ai, sai kun ga gidan,wayyooo aljannar duniya kenan, gida ne irin wanda nake mafarkin samun irinsa a koda yaushe,ina gani na ce babu komai su ci anan mu kuma mu su ci can."

Mai Buruji ce ta gyara zamanta ta ce.

"Ke na gane gidan, gidan nan me dan banzan kyau na bayan layinmu take nufi, ashe har an tare bamu sani ba?"

"Shi fa nake nufi."

Lamishi na qoqarin yin magana Yabbuga ta jiyo qarar machine din DanJumma mijinta, da wata iriyar alkafura ta hantsila ta fada gidan ta ta banke ƙofa ta tura dutse, dariya suka fara yi suna fadin.

"Shegiyar za ta yi tsiya kenan,dan duk ka ga Yabbuga ta shiga gida bata son Dan Jumma ya ganta a nan, to akwai tsiyar da take shirin shukawa."

Yana ƙarasawa wajen nasu ya kalle su cike da takaici,su kuwa a tare suka haɗa baki suka ce masa.

"Ina yini Dan Jumma ?"

Cikin daure fuska ya amsa ya shige da machine ɗinsa cikin gidan ba tare da ya jira jin me za su sake fada ba,cike da ƙunar zuciya ya jingine machine ɗinsa ya sauka dan ya san dole Yabbuga ma na wajen a zaune a wajen,da ta ji dawowarsa ne ya gudu,tinda ba yau ta saba yin hakan ba.

Sallama ya rangada a cikin gidan tare da zare makullin babur ɗin ya cire yar ledar da ke jikin hannunsa ya riƙe a hannu. A hankaki ya taka zuwa bakin qofar dakin nasu, kwance take abun ta ta na jin shi ya na sallama ta qi amsawa.

Murmushi ya yi dan kuwa ya san halin kayan shi, ajiye ledar ya yi a gabanta ya zauna tare da bude kwanon abincin da ke gaban shi, shinkafa ce dai da miya, kullum abincin kenan, in har ta sauya girki kuwa to baya wuce tuwo, in ya kawo taliya ko wani kalar abincin sai ta dafe lokaci daya ta raba wa qawaye dan ta nuna masu itama ana cin dadi a gidan ta, ba wai dan ta samu lada ba.

Budewa ya yi ya fara ci bayan ya yi Bismillah,

"Au ka na gani ina hushi ba za ka kula Ni ba ko? Tauu ya yi, ci abincin ka ka qoshi da kyau kar ka kula ni ɗin."

Ƴabbuga ta faɗa tare da juya masa baya ta na zumbura baki wai ita a dole fushi take yi.

Dan Jumma bai kula ta ba, sai da ya ci abincin shi ya ƙoshi sanan ya tattara hankalin shi zuwa gare ta...... [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH