A GARIN MU

PAGE 5

by @1239900

"Ina sauraron ki sarauniyar mata, menene matsalarki yau Kuma?"

"Auuu ni ce matsalar ma ko Ɗanjumma? Tau ya yi na gode."

Ƴabbuga ta faɗa tana wani kakkame jiki tana tura baki tare da harar gefen da Ɗanjuma ke zaune.

"Kin dai san ba haka nake nufi ba ko? Ina so na San damuwar ki da ta sa har zan yi sallama ki ƙi amsa min ki na a matsayin ɗiyar musulmai."

"Suhwa nika so ka siya min"(super na ke so nake so ka siya min)

"Menene hakan kuma Ƴabbuga? Wani sabon abinci ne;gama ke ba a raba ki da shegen kwaɗayi."

"Ni atanhwa suhwa nika so ba abinci ba." (Ni atampa super nake so ba abinci ba)

"Ai ko aiki ya ganki wallah, ni da nake qaramin ma'aikacin da rabo na da albashi yau wata biyu kenan, haka kawai sai ki ɗakko fitinar siyan atampa super dan dai ban da hankali kuma na siya miki?  To idan na sai miki super atampa me za mu ci kenan?"

Kuka Yabbuga ta saka har tana faɗin.

"Na shiga uku na lalace ni Ƴabbuga ina zan saka kai na? Yau ga tsiyar auren talaka jama'a ka kawo buƙatarka amma ba a iya share maka hawaye."

Nan da nan ran Ɗanjumma ya yi mugun ɓaci, wani irin kallo yake jifan ta da shi wanda ko kaɗan bai shige ta ballantana ya sassauta shirmen da take yi masa. Ƙirjinsa ya daka yana kallonta ya ce.

"Ni ki ke kira da talaka yau Kuma Yabbuga? Lallai mace akwai ta da mance alkhairi, kin manta sanda nike da walwala nake siya miki duk abinda kike so da wanda ma baki so sai ki bayar? Kin mance sanda nike da azziqin da kike Shan gatan da babu ya ke a cikin tsarar ki? Ke fa ba qaramar yarinya bace yanzu Ƴabbuga, karki manta bara waccan aka kai Kareema d'akin miji, yanzu haka ciki gare ta kin kusa samun jika, shi ne kika zaune kike aikata wannan baqar ɗabi'ar da ko Karima ba za ta yi irinta ba."

"Ɗanjumma ni kake kira mai aikata ɓakar d'abi'a? Kai yanzu ace ƴar super nan da mata ke yayi ba zaka iya sai min ita ba kuma ka zauna kana zagina? Shin ta Ina ma ka bi ka shigo gidan nan da ka dawo? Ba ka ga su Lamishi a waje bane ko ba ka ga irin suturar da ke jikin su ba ne? Nan Nan Isa da ya gansu sai da ya tsaya ya yabe su har da kiran su manyan mata,ni kuwa matar ka Kuma maqotan shi ko kallo ban ishe shi ba ballantana ya kula da atampar jikina."

Wani irin zabura DanJumma ya yi, tare da kallon Yabbuga a cikin yanayi na tashin hankali,bakinsa na kumfa saboda bala'i ya ce mata

"Me kika ce Ƴabbuga? Isa ya gan ku a waje bai yaba suturar jikin ki ba shine hakan ya ɓata ranki? Ashe dama Isa kike aure ba Dan Jumma ba? To ki tashi ki koma gidan Isa idan ya so sai ya siya maki super Yabbuga ni na Yi masallaci."

A harzuƙe Ƴabbuga ta miƙe ta sha gabansa tare da kama ƙugu tana girgiza jiki ta ce.

"Walle ba ka Isa ka juya min magana ka tafi ba, ka San ba haka nika nufi ba ai, super kuwa dole sai ka siye ta a gidan nan kafin ka ga fari na."

Zagaye ta ya yi tare da ɗage labule ya yi tsakar gida domin gabatar da alwala. Ransa a ɓace ya ce.

"Irin wannan halin da kike yi shi Kareema ta koya,shi yasa daga yin aure mijin ta ya kawo qararta ya fi sau bakwai, kwanaki ba koro ta ya yi ba da ya gaji da bani bani da sai min? Da girman ki amma ki dinga irin wannan mummunan hali. Amma ba laifinki bane Ƴabbuga, laifina ne da na shagwaɓa ki a baya na gatanta rayuwarki na ɓata ki da siya miki duk wani abu da ake yayi a gari, maimakon yanzu da banda shi ki hakura ki San na kyautata maki a baya, shi ne kike hango na sama da ke,to yanzu sai ki fada min da su Lamishin basu aiki gidan Gwamna a ina zasu samu kwancen tsohuwar super ma balle sabuwa? Sannan  da ki ke gasa da su Lamishi, ai Lamishi ta ciri tuta tunda ta iya zama da kishiya, me ya sa baki yi gasa da ita ta nan ba? Sai gasar abinci,sutura,takalmi da jaka da duk wani abun duniya,amma kin kasa yin gasa da ita ki bari kema a kawo miki abokiyar zaman da zaku zama kamar yaya da ƙanwarta."

Wani irin kwalmaɗe jiki Ƴabbuga ta yi ta ja baya tana aikawa Ɗanjumma wata kafirar harara kafin ta ce.

"Babbar batasin nan kayyasa! Yau ni kake kallon tsabar idona kake yi min maganar kishiya Dan Jumma? Ashe ka daina so na ban sani na? Su ɗin ka San ya aka yi Suka fara zaman lafiyar ne har kake alfahari da su? Ai zaman lafiyar da ka ga suna yi na dole ne, tunda Ɗantalo ya auri Mai Buruji ya kai ga gidan ta fara rashin mutunci ta ga bata diban komai jikin Lamishi, shi ne ta yada makamanta suke zaune lafiya, Kuma indai akan maganar suhwa ne Dan Jumma yasa ka min batun kishiya riqe suhwar ka bana so, amma ka sani kai da ka samu kwaciyar hankali a gidan nan sai na huce haushin da ka ƙunsa min."

Tana gama magana ta hau matsar hawaye ta kutsa cikin ɗakinta tana gunjin kuka kamar wadda ya yi wa laifi. Ɗanjumma kuwa dariya ya saki a hankali,dan kuwa ya san an gama maganar super a gidan tinda ya shigar da maganar kishiya a lamarin. Cike da shaƙiyanci ya ce mata.

"Ga leda nan na shigo maki da ita,maza jeki ki huce haushin ki a kanta"

Alwala ya ɗaura ya fita waje dan tafiya masallaci, gani yayi qofar gidan nasa babu kowa dik sun tafi nasu gidajen. Abinda su Ƴabbuga basu sani ba shine,su Lamishi basu tafi ba sai da suka gama jin dramar da akai a gidan nasu,dan haka da dariyar abun suka tafi gida suna gulmar Ƴabbuga.

Hansatu kuwa bayan ta gama dafa wake ta soya man ja babu ko albasa,sai ta zuba ita da yaran a mazubi ɗaya ta aje ma Isa na shi da ruwan sha a shimfidar shi da yake zama. Yaran na dawowa ta saka su a gaba suka wanke hannuwansu sannan suka zauna suka hau cin abincin a tare da yaranta,sai da ta tabbatar kowa ya ƙoshi ya Sha ruwa sannan suka zauna suna godewa Allah tare da fatan Allah ya hore musu abinda za su ci a gaba. Nan da nan walwala da annashuwa ta fara wanzuwa a tsakaninsu,wanda ta rage musu zuwa safiya ta ɗauke ta adana saboda kada ya lalace kafin safiyar. Alwala ta yi tana sake godewa Allah akan kyautar da ya yi musu ta samun abinda za su ci. Sallah ta shiga ɗaki ta yi ta sake yin addu'o'inta kafin ta fito tsakar gida ta hau wankin Lamishi,tinda ta fara bata tashi ba sai da ta gama shi tsaf ta ɗauraye ta shanya,da yake lokaci ne na iska bata kwanta ba sai da ta ninke su irin ninkin guga ta daure ta ajiye. Hamma ta dinga saki saboda tsananin gajiya,agogo ta kalla ta ga ƙarfe sha ɗaya na dare ya yi Isa bai dawo ba,a ƙa'ida da dokarsa kuwa ko zai kwana a waje ne bai yarda ba,bai amince mata ta rintsa ba har sai yadawo gida. Wata iriyar suka ta ji ƙirjinta na yi mata,nan take ta ɗebi ruwa ta hau sha,dan bata da maganin da ya wuce ruwan. Ta riga ta san dole haka za ta faru,duba da cewa tana da ulcer ga shi kuma ta ci wake,shi yasa ta tanadi ruwan sha a babban jug mai yawa take ta korawa. Dan kishingid'a ta yi a tsakiyar yaran ta da ke kwance a parlour , Nan da Nan kuwa bacci Mai dadi ya share ta.

Ba tare da ta san tsawon lokacin da ta ɗauka tana baccin ba ta ji wata iriyar azaba ta ziyarci ƙwaƙwalwarta,a firgice ta farka sai dai har a wannan lokacin ƙafar isa da ya yi amfani da ita wajen take tata ƙafar na nan a jikinta bai ɗaga ba. Da sauri ta janye qafarta a tashi tare da miqewa tsaye ta na yi masa sannu da zuwa.

Amsawa ya yi ciki-ciki kamar baya so,kallonta ya yi daga sama har ƙasa yana sakar mata wani shu'umin murmushin da ya Sanya gaban Hansatu faduwa da qarfi, dan kuwa sarai ta San ma'anar shi, taba wuyan ta tayi ta ji shi zafi rau, ta San ba komai ya ja ba sai aikin da ta Sha da baƙar yunwar da ta yi dako ta kwana da kwanaki. Ƙirjinta ta dafe da ya sake sukanta a karo na babu adadi ta hau karanto addu'o'i a cikin bakinta. Rufe yaranta ta yi ta musu addu'a sannan juya tana kallonsa.

Kwallar da ta cika mata ido ta mayar, ta raka shi waje tare da zuba masa ruwa ya wanke hannunsa sai kace ƙaramin yaron da bai san hanya ba. Ɗaki suka koma ya zauna ya hau cin abinci babu ƙaƙƙautawa har sai da ya qoshi, nan take ya zabga wata gyatsa me ɗan banzan wari yana yashe baki kamar tsohuwar shaddar gidan haya. Kauda kai Hansatu ta yi gefe tana jin kamar ta yi amai, Isa kuwa ko a jikin shi ya na tashi ta tattare komai sannan ta je ta wanke bakin ta da ruwa da dan gishiri ta bi shi daki, (ita ta iya ta wanke bakin ta saboda Kar a ji warin shi, Amma shi ya wuni zubur da baki bawanki, sannan ya ci abinci, ko kurkurewa bai ba ya tafi ya kwanta a haka)

A duk romance ɗin da mata da miji ke yi Isa ya fi ƙaunar kiss, tsananin warin da bakinsa ke yi shi ne ya ɗarsawa Hansatu tsanar sumbatarsa a ranta,sai dai bata isa ta nuna hakan ba, duk wani qoqarin ta na Sanya shi ya dinga wanke bakin ta yi tun tana amarya amma abun ya gagari tunaninta. A baya ta gwada ajiye masa hodar wanke baki da suke amfani da shi, ya yi fatali da ita ya ƙi wanke bakin,daga qarshe ma sai da yajibge ta ya ce ta raina shi, shi zata kalla ta ce bakin shi na wari? Hansatu ta gwada Yi masa magana direct,nan ma bata tsira ba Isa ya sa hannu jibge ta sannan ya kamata da ƙarfin tsiya ya yi mata kiss ɗin ya ce in mutuwa zata yi sai dai ta mutu amma yanzu ya fara sumbatarta tinda shi yake aurenta ba ita ke aurensa ba.

Gani ta Yi tunani ba zai kai ta ba dan ya na iya fizgar ta da qarfi, da kan ta ta cire kayan ta ta kwanta a saman qaton gadon nasu, Wanda kyawunsa ya yi matuqar bani mamaki, ace kamar Hansatu masu ci da da sha da kyar ta na da irin wanna gadon.

Addu'a kawai take a ran ta har ya gama abinda zai ya tashi, fatan ta Allah ya raba ta da daukan wani cikin dan ba za ta iya da lalurarsa ba sannan ya bawa Isa ikon dinga wanke bakin shi, tunda ta Yi dik wani qoqari ya dan ya dinga yi ya ƙiya,dan haka ta sa a ranta Allah ne kawai zai sauya masa ra'ayi ya fara yi.

Cikin daren Isa na ta sharar barci jikin Hansatu ya dau zafi Mai tsanani, ga wani irin sanyi da take ji, bargonta ta ja ta lullube jikin ta da kyau, Amma dik da haka sanyi take ji, Isa bai ma San tana Yi ba, Kuma in ta tashe shi ta San sauran, tunda naquda ma ya yi fada da ta tashe shi ballantana zazzabi. Da zafin jikin ta ya dame shi ma sauka ya yi daga gadon, ya sa pillow a qasa ya kwanta ya na ta mitar ta hana shi bacci ta daɗin rai. Hawayen baqin ciki ne suke kwaranya a idanunta har aka Kira asuba ta na Nan kwance, ta kasa tashi.

Hansatu na nan kwance duk sonta da yin sallah akan lokaci tana ji tana gani gari ya waye tarwai ba tare da ta yi sallah ba,kan dole ta tashi da kyar ta hura wuta ta sa musu ruwan wanka, Amina da Bilkisu ne Suka shiga gidan Yabbuga duka samo ruwa a ƙananan bokitai,sai masifa ta ke yi masu ta na cewa.

"Kai wannan wace iriyar jaraba ce ta ɗiban ruwa babu ko gajiyawa? Na ga alama fa watarana sai kun ƙafar min da rijiyar nan za ku huta."

Hansatu na gama wanka ta Yi sallah, Isa kuaa ya fita tun tini, ya na can wajen Mai soya masa ya ce ta bashi ta dari biyu. Hansatu kuwa kayan da ta daure jiya ta kunce ta raba biyu, ta ɗora ma yaranta aka ta ce,

"Maza ku kai wa mama Lamishi, ku ce mata Ina godiya,in ta na da ra'ayi ta na iya kawon wani wankin Nan gaba, ku Yi sauri kafin su fita, sun kusan tafiya gidan Gwauna maza ku dawo."

Da sauri kuwa yaran suka ɗauji kayan suka nufi gidan Ɗantalo suka isar da saqon Mahaifiyar su. Sai da Lamishi ta buɗe kayan ta duba ta ga wankin ya yi mata kyau,sai ta ce zata kawo wani in ya taru,Mai Buruji ma ta ce za ta kai nata idan sun dawo daga aiki. A hanyar su ta komawa ne Bilkisu ta ce,

"Amina mu je ta wajen Mai masa, na San baba na can,"

A tsorace Amina ta ce.

"Kin san dai idan ya gammu a wajen muna leƙensa dukan tsiya zai yi mana a banza ko?"

"Ni dai don Allah mu je ko yawu na hadiya daga nesa mu dawo."

Da sauri ta kama hannun yayar ta da ke son guduwa gida suka nufi rumfar me Masa.

Da yake Isa na da jarabar wanke hannu, ana zuba masa ya ja gefe shi kad'ai ya ajiye masar shi ya tafi wanke hannu. Bilkisu kuwa na ganin haka sai ta lallaba ta dauke kwanon Masa, ta ja hannun Amina Suka gudu zuwa gida. Su na zuwa suka miqawa Mamansu suka ce mata,

"Gashi baba ne yace a kawo maki."

Cikin matsanancin jin dadi Hansatu ta amsa, ta sa yara a gaba Suka fara dukan waina da ci, su na ci ta na murmushin jin dadi.

A can rumfar me Masa kuwa wasu matasa da Suka San Isan da yaran shi sun ga sanda Suka dauka, Dan haka dariya kawai Suka dinga Yi.

Isa na zuwa bega Masa ba sai ya hau matasa da duka da zagi ya na faɗin sai sun biya shi masar shi, da kyar aka raba fadan, Nan suke sanar da Isa su ba su bane suka ɗauki masar shi, yaransa su Amina ne suka ɗauki masar suka gudu. Da jin haka sai ran Isa ya yi mugun ɓaci,cikin kumfar baki da masifa ya hau sakin ashar,a harzuƙe ya Sanya takalminsa guda ɗaya da ya faɗi wajen dambe ya nufi gida......... [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU.

RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️