PAGE 6
by @1239900
Da qafar shi ya daki qofar gidan, gaba dayan su zabura Suka Yi a tsorace, Hansatu ce ta Dan Yi murmushi da ta ga shi ne, godiya ta ke da niyyar Yi kafin ta buɗe bakinta ta furta kalma ɗaya ta ji ya haɗa yatsun shi biyar da fuskar ta.
A kidime ta kalle shi domin neman sanin laifin da ta aikata masa, Amina da Bilkisu ne suka shiga tsakanin su da gudu suna ƙwalla ƙara, a zuciye ya ja hannun Amina ya kife ta da mari, zai qara mata Bilkisu ta riqe shi ta na kuka ta ce.
"Baba ka bar dukan su ni ce na ɗakko maka abincinka ni zaka daka, Kuma ni ni na ce Kai ka bayar mu zo gida mu ci shi yasa Mama ta karɓa tana yi maka addu'a."
Wurgar da ita ya yi gefe ta fadi ta dauje guiwar hannu, kuka ta Sanya Mai qarfi saboda azaba, tuni Hansatu ta durqusa a gaban yarinyar ta na duba hannun nata, cikin sanyin murya da mamakin halin mijin nata ta ce
"Yanzu akan wainar jaka biyu ka fiddawa diyar ka jini sannan Ka daki matar ka Wadda ta sadaukar da millions of nera saboda Kai? Anya Isa Kai ne Wanda na fada son shi shekaru Sha uku da Suka wuce kuwa? Anya Isa Kai ne Wanda ka min alqawurran kyautatawa kala-kala na jin daɗin rayuwa? Haqqin ka ne fa ciyar da mu Amma ba ka Yi ba, da na san ba Kai ka Basu ba dakkowa suka Yi ba za mu ci ba, ka Yi hakuri In sha Allahu baza mu kuma tambayar ka kudin abinci ba ko Kuma mu dau abun ka domin mu ci mu kawar da yunwarmu, tashi Mu je na wanke maki jikin ki sannu kin ji."
Kalaman ta Basu ratsa fatar Isa ba ballantana tsokar jikin shi, hasalima wata fassarar ya Yi mata ta daban, rai a ɓace ya ke kallonta ya ce.
"Auu abun gori Kuma ya koma Hansatu? To da ni da ke wa ya fara furta ya na son wani? Sannan wa ye ya kafe ya guji kowa na shi saboda masoyi? Kar ki dakko maganar baya akan haramun din da ki ka ci ke da yaran ki, duk Wanda ya sake yi min irin wannan gangacin zai ga ganganci"
Kamar ta sanar da shi ba su ci haram ba, sai ta kama bakin ta ta tsuke, saboda ta San duka zata sha a banza. Har Isa ya shiga daki ba Wanda ya sake motsawa a cikinsu, sai sautin shassheqar kuka kawai ke tashi a tsakar gidan. Ya na shiga daki ya laluba ko Ina bai samu ko sisi ba,fitowa ya sake yi tsakar gidan ya bi su da kallo ɗaya bayan ɗaya yana zaro ido waje ya ce musu.
"Ba kuci banza ba, ki tabbata kin nemo min dari ta biyu na dan ba yafe muku zan yi ba."
Daga Kai ta yi ta na bin shi da wani irin kallon mamaki. Nan take zuciyarta ta hasko mata rayuwarsu ta baya. Shekara goma Sha uku da Suka wuce, shi din yaron mahaifinta ne,Isa mutumin Kano ne,ita Kuma mutuniyar zamfara, a gidansu yake da zama ya na ma mahaifin ta tuqin mota, ta haka suka fara soyayya, mahaifin ta na da lalurar hawan jini, kafin ya rasu soyayyar su batai qarfi ba, Amma dik da haka ya fuskanci suna son junansu, Dan haka ya ce ya bawa Isa ita, Yan Uwan ta da dangin ta kaf aka dinga surutu, Dan me zai dauki Yar shi mace tilo ya aura mata yaron shi,Hansatu kuwa sai ta kafe kai da fata ta ce ita fa ta na son Isa a haka.
Ba a ɗauki wani lokaci ba aka saka ranar bikinsu da zarar ta gama candy. A cikin satin da aka saka ranar auren su Mahaifin Hansatu ya rasu,Iyalan gidan da ƴan'uwa tare da abokan arziƙi sun shiga damuwa sosai na rashin Alhaji, saboda shi din mutumin kirki ne me son dangi da taimakonsu,hatta da mutan unguwa da abokan aikin shi sun koka rashin shi saboda duk wanda ya raɓu da shi sai ya dangwali arziƙinsa. A cikin iyalansa Hansatu ta fi kowa shiga damuwa da kiɗimar rashin mahaifinsu,rashin lafiya ta dinga yi har sai da aka kaita asibiti aka ɗaura mata ruwa. Da ƙyar aka samu ta dawo hayyacinta aka ci gaba da zaman makoki tare da alhinin rashin Alhaji.
Bayan rasuwar mahaifinsu Hansatu da wata bakwai ƴan'uwanta suka yanke shawarar a raba gado sannan a aura mata Dan abokin mahaifin ta Wanda ke riqe da kampanin Baban su, Dan ya ci gaba da kula da ita da dukiyar ta, Amma Hansatu sai ta dage ta nace ta ce sai Isa ,a lokacin nan Isa kan shi ji yake in aka raba su zai iya shiga mawuyacin hali saboda yana sonta.
Rashin lafiyar da ta dinga Yi bai bawa dangin ta tausayin komai ba ballantana su sauya ƙudirinsu na raba ta da Isa, daga ƙarshe har korar shi akai daga wajen aiki suka ɗauki wani dattijo a madadinsa.
Hansatu da ya ga danginta ba za su sakko daga dokin naƙin a suka hau ba sai ta tattara kayanta da daddare ta gudu wajen Isa, a dakin da ya kama suka kwana a takure,saboda ba ƙaramin kai zuciya nesa Isa ya yi ba ya danne zuciyarsa har gari ya waye bai taɓa Hansatu ba, da safe bayan sun yi sallah suna zaune jigum-jigum Hansatu ta roqi Isa akan su je wani masallacin a Daura masu aure, in yaso sun koma a matsayin mata da miji ta haka ne babu wanda zai raba su.
Sai da suka sha wahala sosai kafin su samu limamin da ya amince zai aura musu junansu. Washegari Juma'a a masallacin unguwar da Isa yake haya aka ɗaura musu aure akan sadaki naira dubu goma wanda Hansatu ce ta bawa Isa ya biya sadakin nata. A wannan ranar suka koma wajen dangin Hansatu a matsayin ma'aurata,mahaifiyarta ta ji takaicin abinda ta aikata sosai, Yayan ta babba kuwa sai ya ce ba za su bata ko sisi ba a gaban mahaifiyar ta kuma bata sanya baki ba ballantana ta hana, Hansatu kuwa yarinta da Giyar soyayya ne suka ɗebe ta ta yi abinda bata taɓa yi ba a gidan nasu,wato rashin biyayya akan abinda magabatanta suke so,nan take ta shige dakin ta cikin fushi ta hau tattara duk wani abu mai amfani da muhimmanci nata ta fito. Ganinta dauke da akwati ne ya sanyaya jikin Hajiyanta ta bita da kallon mamaki,Hansatu na zuwa gaban Isa sai ta kama hannun sa suka bar gidan ba tare da ta kula kowa ba.
Da kudin sarqoqinta na zinare da ta kwaso suka sayi gidan da suke ciki aka sanya sunan Isa a takardar tinda shine namiji a cewarsa,daga nan suka shiga kasuwa suka siyo kayan gado da kujeru tare da duk wani abun buƙatar yau da gobe.
Lokacin da kudi suka qare ne Isa ya fara fito wa da Hansatu asalin kalar shi, rashin mutuncin yau daban na gobe daban, da ciki ko ba ciki in ya ga damar dukan ta zai daka, da ya ji kawai ta bata masa rai zai yi mata rashin mutuncin da za dasa mata mamaki da taraddadin anya wannan Isan da ya furta mata kalmar so ne?
Wani irin kuka ne mai tsanani ya turniqe Hansatu a daidai lokacin da ta dawo daga duniyar tunanin rayuwarsu ta baya, Bilkisu ce ta fada jikin ta ta na kuka ta ce,
"Mama dan Allah ki dena kukan haka ya isa,laifina ne da na ɗakko masa abincinsa amma na yi miki alƙawarin bazan sake ba."
Dan shafa bayan yarinyar kawai ta yi saboda sanin cewa ba laifin ɗaukar masa abinci ne ke bibiyarta ba,illa laifin bijirewa magabatanta da ta yi ne ya saka ta a cikin wannan tashin hankalin da juyawar bayan mutumin da ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗora masa........ [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH