A GARIN MU

PAGE 7

by @1239900

Lawwali ne da yaran shi zaune a wani tsohon kamfani na gwamnati,waje ne da ya qunshi sashe sashe, da dikkan alamu ofishin ma'aikatan wajenne, Lawwali kuwa ya maida shi matsayin ma'aikatar shi ta yin garkuwa da dik Wanda aka bashi umarni, ko Kuma ra'ayin kan shi ya bashi da ya Yi hakan,waje ne da ya ke a cikin wani surquqin daji, da dikkan alamu gina shi aka fara yi domin wani aikin na gwamnati kuma aka bari ba tare da an kammala ba ko an waiwaye shi, Lawwali da yaran shi sai qoqarin Neman network suke yi saboda suna son su yi waya amma abun ya ci tura. Zaune yake rai a ɓace saboda ya fi awa uku ya na abu d'aya. Cikin nasara kuwa ya samu wayar da ya ke son Yi ta shiga, da hanzari ya fara magana.

"Hello Excellency  ba waku, yunwa ta addabe ni da yarana, ga shi ba ruwan sha,kuma mu na buqatar kayan caji,...hello...hello"

Wayar ce ta sake katsewa,cikin fushi ya buga ta da qasa tare da dakan jikin ginin wajen da yake tsaye sai da dattijo dake ɗaure a jikin ginshiqin da ke a tsakiyar faffadan wajen ya tsorata. Bakin sa ya bushe kamar wanda ya sha farar ƙasa irin ta masu juna biyun nan, tsananin yunwa da qishirwa tare da ciwon jiki da zafin zuciya ne suka haɗu suka dabaibaye rayuwarsa. Wani baƙin ƙyalle suka sa suka rufe masa ido dan haka baya ganin kowa a wajen sai sauraron muryoyinsu. Cikin wahalalliyar muryar da ta shaƙe saboda azaba ya ce.

"Yanzu Lawwali duk irin amanar ka da na dauka na riqe haka zaka saka min da shi? Kada ka manta fa babu irin taimakon da ban yi maka ba a rayuwa, amma saboda wancan dan adawar ya biya ku kudi qalilan kuke wulaqanta ni kamar ka manta mafari."

Cikin fushi Lawwali ya kalli dattijon ya shure shi da qafa, sannan ya dunƙule hannunsa na dama ya hau naushinsa;har sai da wani daga yaran shi ya riqe shi ya ce masa.

"Oga ka Yi hakuri Kar ya mutu, in ya mutu Excellency ba ze Mana da kyau ba,kar ka manta ajiya kawai ya ce muyi ba kisa ba, ya faɗa ya kuma jaddada Mana hakan, sai bayan zabe mu sake shi."

Bangaje yaron nashi ya Yi ya duqa a gaban dattijon cike da ɗacin rai ya ce.

"Ka ce ka riqe ni amana ?Wace iriyar amana ka riqe mini? Amanar shaye-shaye Ko ta Neman mata da kisan kan mutane? Ko kuma amanar fyade da garkuwa da mutane Dan neman kudin fansa? Kai Bari ka ji na taƙaita maka dogon sharhi,Yau ace Excellency ze sauka daga mulkin garinnan, Wanda ya sake Hawa ya bani irin wannan kwangilar ba zan yi ƙasa a guiwa ba wajen qaddamar Masa, taimako d'aya ka min a duniya wanda nake mora har yanzu, shi ne Iyayena Dake aiki a gidan gwamnati har yanzu,da wannan aikin gidan mu suke ci su qoshi su Yi sutura."

A kiɗime babban yaron Lawwali ya kallesa ya ce.

"Oga ya suma fa,gashi ba ruwan yayyafa Masa a nan."

Murmushin mugunta Lawwali ya Yi, babu bata lokaci ya kunce wandon shi ya fara tsiyaya ma wannan mutumin fitsari akai, sai kuwa gashi ya farfado. Kula da abinda Lawwali ke Yi masa ne ya Sanya wannan bawan Allah'n qoqarin kaucewa, Amma dake ya na a daddaure ne, sai ya kasa matsawa. Dariya Lawwali da yaran shi Suka dinga Yi masa cike da shaƙiyanci.

Har magariba ba wani bayani daga wajen gwamna suna nan zaune yunwa da qishirwa ta addabe su, daga ƙarshe ma wayoyinsu mace wa suka yi ba caji, sai torch lights suka kukkuna suke haska waje, su na Nan zaune har isha'i ta Yi, Lawwali ne ya tada mutane uku ya ce su dau mota su shiga gari,su sama masu abinda za su ci,Dan ya na ta jiyo kukan yaran da ke killace a ɗaya daga cikin sashen dake wajen, ya kuwa tabbata yunwa ke damun su. Daga nan ya basu umarni su tabbata sun samu ganin Gwamna a daren ko Kuma su Yi magana da shi ta waya, a Kai masu abinci da ruwa. Har za su tafi Lawwali ya dakatar da su ya ce.

"Yauwa ga waya ta ku tafi da ita, a sama min caji"

"To Oga," suka haɗa baki wajen faɗa.

Mota suka tada Suka dauki hanyar shiga gari. Suna fita saƙon da suke ta jira ya isa cikin dajin. Wata ƙatuwar mota aka lodo da abinci tare da ruwan sha da duk abinda suke da buƙata.

Babu bata lokaci yaran Lawwali da za su Kai su goma suka dirar wa abincin suka dinga shigar wa wani daki ana lodewa, bayan sun kammala shigar da duk wani abu da ya kamata ne suka zauna cin biscuits da juice dan kawar da yunwa kafin matan da ke cikin wajen su dafa abincin, drivern da ya kawo saqon ne ya tsaya ya na bawa Lawwali saqon gwamna.

"Oga Lawwali gwamna ya ce na faɗa maka a cewa dangin Lamido su bayar da kuɗin fansarsa  milliyon dari biyar, kar a rage masu ko sisi, dan ya San ya saci abinda ya fi haka a asusun gwamnati, da zarar sun kawo kun amshe ku qarasa shi, ya gama Yi wa qasa amfani."

Daga Kai kawai Lawwali ya Yi cikin isa da nuna shi ne oga a wajen,dik qoqarin cin binci da kowa ya ke yi a wajen shi bai  je ba ya na gefe yana kallon kowa. Ana gama abinci ya saka ido sosai dan ganin kowa ya ci ya qoshi har da yara da matan da suka kwamushe, Dan haka yaron shi Mai kula da wajen in baya Nan ya aika, ya kwaso Mata uku su raba abinci, haka kuwa aka Yi, kowa ya ci ya qoshi, daga qarshe Lawwali shi ma ya samu ya ci a nitse.

A wajen ba a Kiran kowa da sunan shi saboda tsaro, Lawwali Oga suke ce Masa direct, daga Mai bi Masa zuwa mutum biyar da ke qarqashin shi da Number ake Kiran su.

No 1 shi ne Mai bi ma Lawwali, sai No 2 Mai bi Masa,No 3 mabiyinsa sai No 4 da No 5.

A cikin mutanen da aka kwamushe akwai wadan da iyayensu ko 'yan Uwansu sun zaci sun rasu dan haka har sun haƙura da jiran komawarsu domin an amshi kudin fansar su ba a sake su ba,har sun Saba da rayuwar wajen, wasu Kuma har yanzu ba su Saba ba, a kullum neman duk wata hanya da zata fidda su ta maida su wajen ahalin su suke yi, musamman manya masu hankali.

Wasu Kuma sabbin zuwa ne, bangaren sabbi daban na tsoffin zuwa ma daban, wasu daga yaran Lawwali sun Yi 'yan Mata a wajen, su na dik wani abu da suka so da su cikin sauqi, ba tare da sun takura su ba, Lawwali na sane da hakan,bai taɓa hana su ba tinda da yardar matan ake yin komai ba tursasa su suke yi ba.

Wajen sai ya zama kamar prison ga wasu, wasu Kuma kamar unguwa suka je su na saka ran komawa gida watarana, wasu Kuma kamar gida Suka dauke shi saboda yanda suke rayuwar ƴanci da jin daɗi a dajin babu takurar dangi da kwaɓar ƴan unguwa. In ba an samu akasi kamar na yau ba a koda yaushe cikin wadatar abinci abubuwan sha da kayan maye suke, wutar lantarki ce kawai babu a wajen sai Generator babba,wanda suke kunnawa su ga haske idan dare ya yi,sannan su saka giyarsu da naman miya a babban fridge tare da saka caji.

**********************

A gajiye Mubaraka ta dawo daga makaranta ta shiga gida tana hamma saboda yunwa da ƙishirwar da ke addabarta. Ɗakinta ta shiga ta hau cire Kayanta sannan ta fita tsakar gida ta ɗebi ruwa a bokiti ta shiga bayi ta Yi wanka,tana gamawa ta fito ta ɗaura alwala sannan ta shige ɗaki ta shirya ta yi sallar azahar,daga nan sai ta dauki abincin ta ta fara ci. Lawwali ne ya shiga gidan kamar yanda ya saba babu sallama ballantana gaishe da mutanen gidan.

Sanye yake da qananan Kaya kamar ko da yaushe, sun Yi matuqar Masa kyau, zama ya Yi a kusa da ita, suna sakarwa junansu murmushi, hannu ya sa ya amshi spoon din hannunta ya Yi Loma daya, sannan ya sake ɗiba ya Bata a baki,sai da ta karɓa cike da farinciki,sannan ta noƙe kafaɗa tana faɗin.

"Yah Auwal ni fa ba yarinya bace ka dena sangarta ni."

Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce mata.

"A waje na ke jaririya ce har yanzu,shi yasa ba zan dena sangarta ki ba,ke ko tsufa muka yi ba zan dena hango ki a cikin zanin goyo ba."

Murmushi suka Yi a tare ya miƙa mata cokalinta ta ci gaba da cin abincinta. Ledar da ya shiga da ita ya janyo ya buɗe yana duddubawa, wata Yar madaidaiciya ya dakko ya bude masu, sannan ya ja kujera qarama ya zauna da kyau yana kallon ƙanwar tasa da yake tsananin so a rayuwarsa. Nama ne gasasshe a ciki, zuba masu ya yi a saman abinci sannan ya fara kai wa bakinsa yana lumshe ido tare da yin waƙar santi Mubaraka na yi masa dariya. Cike da nishaɗ ta kalle shi ta ce.

"Na Yi kewar cin abinci da Kai Yayana"

Murmushi ya yi sannan ya ce.

"Nima haka qanwa ta"

Kallonsa ta yi sannan ta ce.

"Amma za mu ragewa su Umma ko?"

"Ga nasu can na ajiye musu wannan namu ne, Ina sane na zo yanzu ai,saboda na San yanzu kike dawowa daga makaranta. "

"Gashi kuwa hasashenka ya tabbata na dawo daga makaranta har na yi wanka da sallah ina cin abinci,da ace sai da na ƙoshi ka dawo da babu abinda zai hana ni kuka."

"Ai Ina aiki da lokaci, na san ma baki ci ba"

Sun shagala da hira suka ga an yi sama da kwanon abincin nasu,rai a ɓace Lawwali ya kalli Lamishi dake tsaye akan su tana faɗin.

"Lawwali zaka ci uban ka a gidan nan idan kana nuna rashin adalci a tsakanin ƙannenka,ko ita d'aya ce a gidan da zaka saka mata nama mai yawa a gaba ita kaɗai ta cinye?"

Cikin Bata rai Lawwali ya ja ledar gefen shi ya cire wata Leda ya miqawa Lamishi,

"Aje Mana abincin mu ga naku Nan, Dan tsabar kwaɗayi ya yi maki yawa Lamishi wannan naman da bai da yawa shi ne kike yi wa ƴarki baqin cikin ci. Kar ki manta da wanda kuke samu ku ci a gidan Gwamana mai yawa watarana har maƙota kuke bawa idan kun dawo."

"Ubanka ne yake bamu nama a gidan Gwaunan da kake ikirarin muna cin nama a can?"

"Lamishi na fada maki ki dena zagi na amma ba kya ji."

"Me zaka min Dan uban ka idan na zage kan? A waje ne kake Zaki amma a cikin gida baka fi jaririyar mage ba, ni ce uwarka dan haka ina da ikon zaginka yanda na so."

Dariya Mubaraka ta Yi sosai har da kama ciki, Dan ita dramar Lamishi da yayanya na nishaɗantar da ita sosai. Fuskarta ɗauke da fara'a ta ce.

"Yah Auwal tsaya biyewa Umma na canye naman."

Cike da nishaɗi Shima ya ɗebi naman guda biyu ya sa a bakin shi, Lamishi da ta ga ta na ta masifa Basu kula ta ba sai kawai ta tafi waje tana mita,ta na tafe ta na laluba ledar ta na diban naman ta na watsawa a baki, kafin ta raba masu ta ci da yawa.

Bayan Lawwali ya gama cin abinci da Mubaraka sai ya Kira ta dakin shi, hannu da bakinta ta wanke ta same shi zaune a bakin gadonsa mai kyau kamar na amaryar ƙauye. Waya ya zaro a aljihunsa ya miqa Mata yana murmushi.

"Ga taki wayar kin huta da aron ta Lamishi tana zagin ki mutanen unguwa na ji duk safiya,a yanzu za ki iya Kira na duk sanda kk so, zan dinga saka maki Kati akai akai,ki kula bana so ta hana ki karatun ki ko ki dinga waya da samarinki,ba dan haka na siya miki wayaba."

Murna sosai Mubaraka ta dinga yi tana kumawa. Addu'a ta yi masa tare da yi masa fatan shiriya a cikin ranta,dan babu abinda take so a rayuwarta da ya wuce Yah Auwal ɗinta. Mubaraka bata son harkokin da yake yi yana samun kuɗi dan ta san ba ta hanyar halal yake samo duk wasu kuɗaɗensa ba,sai dai babu yanda za ta yi da shi,tinda iyayensu ma basu isa su saka shi ba ballantana su hana shi. Sosai take tausayawa rayuwarsu da suke zaune kara zube ba tare da cikakkiyar tarbiya da kulawar iyaye ba....... [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH