A GARIN MU

PAGE 8

by @1239900

Da yamma liss su Yabbuga suka Yi qungiya dan zuwa gidan sabuwar maqociyar su Lamishi dake a bayan gidansu. Yabbuga ita ce a gaba a dole ta kowa sanin matar gidan. Sun jima su na buga gidan ba a buɗe ba, har Lamishi ta fara jin haushi ta ce su tafi da gani matar gidan yar wulakanci ce. Nan da nan Yabbuga ta hau basu hakuri tana rokom su tsaya watakila wani abun take yi,da ta ga Lamishi na son botsarewa sai ta kada baki ta ce.

"Ke wataqila fa bacci take yi, ko kuma ta zaga bayan gida, mu yi hakuri mu jira kadan,kun dai san ba zai yu daga buga gida sau uku a zo a bude mana ba kamar dama a bakin kofa take tana juran zuwan mu,"

Suna tsaka da jayayya matar gidan ta bude qofa. Cikin sauri Yabbuga ta shige gaba tana washe baki, ba tare da neman izini ko jiran a basu izinin shiga ba ta kutsa Kai ciki, su Lamishi na ganin haka sai suma suka bi bayan ta,baki sake matar gidan ta bi su da kallo,bata da zaɓin da ya wuce ta bisu,jiki a sanyaye ta shiga parlourn ta gansu tsaye suna bin kowanne lungu da saƙo da kallo,sai da ta fara zama sannan suma suka zauna.

Gaisawa Suka Yi cikin mutunci,Yabbuga uwar tafiya ta gabatar da su baki daya a wajen matar gida,murmushi ta yi sannan ta ce,

"Allah sarki ni kuma suna na Asshibi, ai na so na shiga wajen naku, sai na ce bari har a gama gyara wajen,tinda har yanzu wajen bai kammalu ba, gashi ban shiga gaishe ku ba har kun riga ni zuwa, to na gode sosai da baku biye ni ba kuka shigo aka sada zumunci."

Budar bakin Mai Buruji da ta kalli matar ta ga Yar babba ce dan za ta kai sa'anninsu sai ta ce,

"Ina Yan yaran ko har sun fara zuwa islamiyyar unguwa?"

Cikin jin nauyi matar ta ce,

"Babu yara, ai da yake ni din amarya ce,sati na biyu da tarewa."

"Amaryaaa"

Suka haɗa baki suka fada a tare, sai Kuma Suka yi shiru suna kallon juna kowa da abinda ya ƙunshe a bakinsa,tashi ta yi ta shiga wani ɗaki dan ta ɗebo musu abin Sha da na motsa baki,kasa jure gulmar dake mintsininsu suka yi,kafin ta fito daga ɗakin har har sun fara gulmarta, ta na dawowa Suka Yi shiru.

Lamishi ce ta fara daukan cincin ta Kai bakin ta tana zuba surutu,a hankali kowaccen su ta fara ɗauka tana kai wa baki suna ta zuba kamar wanda aka saka su aikin.bada labarin mutanen unguwa,abu kamar wasa sai ga plate babu ko ɓurɓushin cincin a cikinsa, lemo kuwa sai da suka shanye tas suka riƙe gorunan a hannu da niyyar za su ɗura ruwa a ciki. Ganin sun cinye komai ne ya sanya su miƙewa suna hamdala suka yi mata sallama sannan Suka tafi,har bakin ƙofa ta raka su tana yi musu godiya sannan ta koma ciki ta rufe gidanta.Tun a qofar gidan Suka hau gulmar ta,cike da dariyar shaƙiyanci Lamishi ta ce.

"Kee ni dai yau na ga duniya, kin gan ta kuwa jibgegiya kamar basamudiya? Ga fuskar nan baqa qirin kamar bayan tallen miya(tukunyar miya),Wai a haka take iya buɗar baki ta faɗa mana amarya ce ita."

Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayansu suna ƙyaƙyatawa kamar wasu ƙananan yara. Lamishi ce ta sake katse musu dariyar tasu ta ce.

"Kee Yabbuga Ina kyautata zaton ƙawar nan taki bazawarace."

Cike da dariyar shaƙiyanci Ƴabbuga ta daki kafaɗar Lamishi ta ce.

"Kai Lamishi baki da dama wallah, wai bazawara, yo baku ga hoton mijin nata ba a jikin gini ta rataye kyakkyawanda shi kamar ya haɗa dangi da fulani?"

Mai Buruji ce ta kama haɓa tana matsar ido ta ce.

"Ohhh wannan haɗin aure nasu shi ake kira da haɗin Allah, in ba Allah ba wa ya isa ya yi wannan haɗin?"

Dariya Suka dinga suna faɗin albarkacin bakinsu har suka isa ƙasan bishiyar su suka zauna Suka dora da hirar gidan Asshibi.

Hansatu na jin sun fara hira ta San an kafa dandalin munafurcin kenan, tagumin da ta zabga ta gyara domin ba ta da lokacin ma saurararsu abinda ya isheta shi ya dame ta. Duniyar tunani ta faɗa game da abinda za ta ganganɗa ta dafa ko ta kwadanta masu su ci da daren ita da yaranta.

Babbar damuwarta ta duba kaff cikin gidan babu wani abun kaiwa baka, sai wani ragowar tsakin masara da ya jima a ajiye har ya yi qwari, tunani take ta yi akan yanda zata sarrafa shi kafin yaran su dawo, ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce.

"Mara shi ba ya fushi dole na tashi na je na nemo abinda zan ciyar da yarana."

Mayafi ta zara ta duba qafarta, takalmin ta da ya gaji da murzarsa da take yi ta kalla ta yi murmushi,nan take ta tuna baya lokacin da tana gidan su bata saka kowanne takalmi sai wanda ta zaɓa,wani lokacin ma daga qasashen turawa Babanta ko yayunta ke siyo mata takalmin da zata saka,sai gashi yanzu ita ke saka wannan takalmin da ko mai aikin gidan su ya fi qarfin shi.

Tun daga zaure sukai ido huɗu da Yabbuga, cikin magana qasa-qasa ta sanar da su Lamishi ga Hansatu Nan zuwa, shiru Suka Yi kamar ba su ke gulmar Ta Yahai ba da bata samu damar zuwa majalisar ba a wannan ranar,sakamakon rashin lafiyar da Yahai ɗin nata ke yi,kuma yana gida bai fita ko ina ba. Cikin sanyin muryar ta ce musu.

"Assalamu alaikum, mun wuni lafiya,Ya yara?"

A tare suka ce,

"Lafiya ƙalau Hansatu ya su Amina,"

Kai ta sadda ƙasa kafin ta ce.

"Lafiya ƙalau suke,....na ji ku na hira ne shine nace bari in zo na roƙi alfarma, don Allah taimakon Nan dai da kuka Saba yi min shi nika nema a wajeku, mai nake so ku ɗan sammin da d'an gishiri ina so na dafawa yara abinci kafin su dawo daga makaranta, da yake tun safe basu ci komai ba shi yasa nake ƙoƙarin sama musu abinda za su ci ko babu yawa."

"Toohh ikon Allah! Isa baya gari ne da kike roƙon mai da gishiri Hansatu? Idan kuwa yana nan ya barku da yunwa bai kyauta ba,dan me zai bar mace da yara har uku basu ci abinci ba tun safe? Kai Allah Ya wadaran halin Isa."

A hasale Ƴabbuga ta ce.

"Ke Lamishi Ina ruwan ki da kike irin wannan maganar? Ba ita taga tana zata iya zama da shi a haka ba? Ai duk wacce ta maida namiji uba watarana za ta mutu a marainiya, gashi Nan ta na ɗanɗanar azabar namiji saboda mafisar son da take yi masa. Irin biyayyar da take yi wa mijin ta,ni bana yi wa nawa haka,kuma gashi kowa ya shaida lafiya ƙalaou muke zaune da junanmu sai ɗan abinda ba a rasa ba na yau da gobe. Bakin gwargwadon iko Ɗanjumma ya ɗauke min ci da Sha,sutura kuwa yanda kowacce mace me ji da kanta za ta saka haka nima nake sakawa a jikina. Yanzu haka jiya ya kawo min naman sa saboda bana son aiki na bar masa abunsa, shi ya zauna ya gyara ya yi mana abinci mu ka ci dazu, komi ya aje min dan kar na je roƙo maƙota,babu kuma wanda bai san cewa Ɗanjumma qaramin ma'aikaci bane,kun ga kenan abun zuciya ne ba wai karfin samu ba,Hansatu ya kamata ki miƙe tsaye ki nuna wa Isa kurensa,dan kuwa su maza Zuma ne sai da wuta, wa ke ragawa namiji yanzu?"

Mai Buruji ce ta taɓa Ƴabbuga dake ta zuba kamar an kunna tsohuwar radio ta ce mata.

"Keee Yabbugaaa raba kan ki da bawa matar mutane irin Wannan shawarar, idan za ki bata abinda take nema ki bata ta tafi, in zaki bata ba ta kama gabanta,dan mu mun yi nisa da gida."

Bata rai Yabbuga ta Yi tana kame-kame,Dan ita ma kayan abincin nasu sun Yi qasa duk burga ce ta watsa dan ta shashantar da zancen Hansatu abun ya koma hira,sai dai yanda ta gama yabon mijinta a gabansu ta tabbatar da ya kawo mata kayan abinci har da nama bai kamata ta kunyatar da kanta ba. Tashi ta yi tsaye ranta a matuƙar ɓace tace wa Hansatu ta bita ciki.

Ko da suka je cikin gidan sai Ƴabbuga ta ɗakkowa Hansatu wata tsohuwar jarkar manja ta Bata,ɗagawa Hansatu tayi sama tana kallon robar da idan an narka be fi a samu dan kadan ba a ciki. A hasale ta shiga kitchen ta ɗebar Mata uban gishiri mai yawan tsiya ta haɗa da debar Mata barkonon da ba a daka ba, sannan ta Bata Maggi guda biyu. Cike da ƙunci da harare-harare ta ce wa Hansatu.

"Tauu ga su Nan ki boye dai ba sai sun ga me na baki ba su Yi ta tsegumi akai,tunda kin San dai abin magana baya yi musu kadan a unguwarnan."

Durqusawa Hansatu ta Yi ta na ta yi mata godiya, saboda a wajenta hakan babban taimako ne ta samu.

Zata fita kenan ta ga zogalen Ƴabbuga ya Yi fala fala gwanin sha'awa, roqar zogalen ta yi dan ta ƙara a tsakin ko ya ƙara auki. Cike da ɓacin rai Yabbuga ta tsinkar mata kadan ta bata,a tare suka fita Hansatu na boye abubuwan da ta samo a mayafi kamar yanda Yabbuga ta umarceta, Yabbuga na qara kare wa har sai da Hansatu ta shige gidan ta, sannan ta koma wajen zamansu.

Ta na zama ta dinga lissafin qarya na abinda ta bawa Hansatu, harda cewa ta bata busasshen kifi yara sun ji galmi-galmi a bakinsu. Nan fa su Lamishi suka yi ta mata jinjina, ta na basarwa ita a dole ta yi abun kirki. Suna tsaka da jinjina mata ta tuno da Asshibi sai ta kece da dariya , sannan ta kalli Lamishi ta ce,

"Hummm walle duk na tuna matar nan se dariya ta kama ni, kun ga shegiya baki kamar ta'adin Wuqa."

Dariya sosai su Lamishi suka dinga yi suna tofa nasu albarkacin bakin akan halittar Asshibi da mijinta.

A daidai wannan lokacin Hansatu kuwa na can na sarrafa tsakin masara domin yaranta kada su dawo babu abinda za su kai bakinsu.

Cikin ikon Allah kuwa sai ga faten tsaki ya samu wanda za su ci su dan maida yunwarsu ta wuni guda, cikin murnar samuwar wannan abincin Hansatu ke yin kamar wadda ke dafa naman zabbi ko kaji, a fili take ta zabga hamdala zuwa ga Allah,ta na kammalawa ta zubawa kowa na shi ta shiga wanka,ta so ci kafin su dawo,sai ta tuna su da suke yara ma suka hakura da yunwa ballantana ita?

Da misalin shida na yamma su Amina suka koma gida, tinda Ahmad ya ƙyalla ido ya ga murhunsu da sauran garwashi da toka ya fara murna.

Cike da so da qaunar yaranta tare da kulawa ta zuba masu ruwa suka wanke hannayen su, sannan ta yi musu jagora har ciki suka zauna suka hau cin abincin suna yabawa qoqarinta,dan sun san ita ce cinsu da shan su,dan ta Mahaifinsu ko za su kwana basu ci ba ba damuwarsa bane.

Bayan sun gama sun sha ruwa, Hansatu ta fara koya masu karatun boko, Amina ta iya rubuta Hausa, turanci kuma ta na ji amma bata iya mayarwa dika, Hansatu ta ga tunda ita ta iya, yaran ta basu samu damar zuwa makarantar boko ba mai zai hana ta koyawa musu a gida?

Basu jima suna karatun ba bacci ya ɗauke su tsabar gajiya. A haka Isa ya koma gida fuska a cunkushe da ɓacin rai kamar ko wanne lokaci. Ko gaisuwarta bai amsa ba ballantana ta Ahmad ya ya farka dan jin bugun ƙofarsa.

Wajen zamansa ya isa ya ja bincinsa gabansa,sai ya zura hannu a aljihun shi ya zaro ledar kifi dan dari biyu ya juye ciki ya cinye. A wajen ya bar kwanon abincin da bai san daga inda aka samo shi ba,shi dai buƙatarsa ta biya ya tsallake ya wuce ya wanke hannu ya koma ɗaki ya zauna yana latsa ƙaramar wayarsa.

Ahmad ne ya je wajen shi cike da tsoro da kuma son ya nuna mahaifinsa sabuwar kalmar da ya koya ta Father wato Baba a wajen Hansatu.Cike da Bata Rai Isa ya ce,

"Wato Hansatu kin rantse da Allah sai raina ya baci ko? Ban hana ki koyawa yarana karatun nasara ba? Ni da na yi zuwa Sakandire uwar me ya tsinana min in ba tuqin motar uban ki ba? Ke da ki ka yi zuwa Sakandire ta ina kike amfana da shi? Kai zo nan kawo littafin nan."

A tsorace yaron ya isa gaban Isa ya miƙa masa littafin hannunsa na rawa,babu tausayi ko tunanin yanda zai karyar zuciyar yaronsa Isa ya karɓa ya keta littafin zuwa gida biyu,nan take yaron ya tsanyare da kuka.

Korar shi waje Isa ya yi yana masifa kamar zai ari baki,a guje Ahmad ya fita ya koma wajen Mahaifiyarsa dake share hawayen nadamar auren Isa da ta yi a rayuwarta,jin kukansa ne ya tada su Bilkisu dake bacci suka hau tambayarsa abinda ke faruwa? Lallaɓasu Hansatu ta yi har Ahmad ɗin suka koma bacci. Shi kuwa Isa daga nesa yake kallon yaran da mahaifiyarsu,wani irin shu'umin murmushi ya yi, sannan ya furta,

"Allah ya kai damo ga harawa....."

Sannan ya gyara kwanciyarsa yana danna wayarsa nokia raka ni kashi......... [26/03, 9:12 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH