A GARIN MU

PAGE 9

by @1239900

Yau Lamishi ta tashi ba ta jin dadin jikin ta, zazzaɓi ne mai zafi yake damunta. Mai Buruji na gama shiri za ta tafi aiki sai ta ce babu inda Mubaraka zata je da sunan yawon zuwa makaranta,ta shirya ta bi Mai Buruji ta yi mata aikinta.

Mubaraka bata so hakan ba domin har ta yi shirin makaranta ta saka uniform,kuka ta dinga yi tana yi wa Lamishi magiya akan ta barta ta je makaranta,amma Lamishi ta ƙeƙasa ƙasa ta ce sai ta je,daga ƙarshe da ta ga Mubaraka na son ta yi mata taurin kai sai ta hau zaginta tare da qoqarin kai mata duka. Cikin kuka Mubaraka ta cire uniform ɗinta dan bata da zabin da ya wuce ta bi Mai Buruji, a ranta ta na ta jin haushi rashin Auwal a gida,domin in yana gida duk bala'i da masifar Lamishi sai ta tafi makaranta.

DanTalo ma da ya ji me ke faruwa sai ya bi bayan Lamishi ya tirsasa ta ya ce sai ta je, wa ya sani ko ita ma a ɗauke ta aiki a gidan hanyar samun lsu ta qaru.

A haka suka tafi suka isa gidan da misalin takwas na safiya, sai da suka sha tambayoyi da kuma neman izinin barin Mubaraka shiga gidan. Kai tsaye sashen Hajiya Ikee suka nufa,a parlour suka zauna suka tarar da wajen shiru babu kowa. Har suna shirin barin parlourn suka ji takun takalmi mai tsini na sakkowa daga saman bene,nutsuwa suka yi tare da zubewa a ƙasa cike da ladabi Mai Buruji ta fara miƙa gaisuwa wajen Hajiya dake ta yatsina kamar ta ga kashi. Sai da ta zauna a kujerar da ta saba zama sannan Mai Buruji ta sanar da Hajiyan dalilin zuwa da Mubaraka. Faɗa ta fara yi sosai,daga ƙarshe dai Mai Buruji ta yi nasarar lallashinta har ta amince da Mubaraka ta yi aikin da Lamishi take yi a gida. Zuwan Mubaraka gidan na farko kenan, dan haka sai kalle kalle take yi kamar wata baƙauyiyar da ta shigo birni, direct dakin Sultana Mai Buruji ta kai ta, suna tafe ta na sanar da ita duk binda ya kamata ta yi.

A zaune ta tarar da Sultana ta na karanta qur'ani, sai ta ji wani irin dad'i ya kama ta, durqusa wa ta yi ta gaishe ta cikin girmamawa ,sai da ta kai ƙarshen ayar da take karantawa ta ɗaga kai ta amsa tana binta da kallon rashin sani. Bayanin kanta ta yi mata,nan da nan Sultana ta saki fuska, cike da murmushi ta ce,

"Ai kuwa ga kamannin ku nan sun fito ke da Umman naki, Bismillah in kin wanke toilete zaki gyaran nan, sannan ki dan wanken wadannan kayan,shikenan aikin da za ki yi min."

"To."

Bayi ta je ta wanke tass kamar dama ta saba da aikin, wankewa take yi zuciyarta cike da mamakin irin haduwar wajen,kayan wankin da ta gani a wata roba ta dauka ta duba an aje washing machine da omo da duk abinda za ta buƙata,rashin sanin yanda za ta yi amfani da washing machine ɗin ne ya sanya ta tunanin wankewa da hannayenta,duba da ba wani datti dama kayan suka yi ba.

Ko da ta fita gani ta yi Sultana ta koma saman sallaya ta bar mata gadon dan ta gyara, ai kuwa cikin azama ta fara gyarawa.

Karatun da Sultana ke yi itama ta fara bi, shiru Sultana ta Yi tana sauratonta cike da burgewa tare da sakin murmushi mai sauti,nan take ta ji yarinyar ta shiga ran ta,a hankali ta furta.

"Masha Allah, Mubaraka kike ko? Ashe ke din hafiza ce masha Allah, Muryar ki na da daɗin karatu, izifinki nawa?"

"Na sauke Aunty sultana ,Amma ba a yi Mana bikin sauka ba."

Har ran ta ta ji daɗin yabawar da Sultana ta yi Mata, ta jima tana son samun irin wannan yabon a wajen iyayen ta, amma su ba su san mahimmancin karatun qur'ani ba su ballantana su yaba mata,ƙarshe ma idan ta matsa da zuwa makarantar zagi da cin mutunci ne ke biyowa baya daga wajen Lamishi.

A haka ta gama gyara dakin suna karatu ita da Sultana cikin nishadi, sai Sultana ta ji kamar ta jima da sanin Mubaraka, yarinyar ta shiga ranta cikin lokaci qanqani. Lokacin da Mubaraka ta a gama aikin a ɗakin sai suka hau hira Sultana na yi wa Mubaraka tambayoyi musamman akan abinda ya shafi karatu,ita kuma tana bata amsa daidai saninta. Daga ƙarshe suka gangara kan hirar gari da unguwarsu Mubarakan,anan ne Sultana ta ji wasu labaran da ba su yi mata dad'i ba game da rayuwar Mubaraka,ta kula yarinyar na son karatu, iyayenta kuma ba su damu da shi ba, nan take ta ji kwaɗayin taimaka mata,da kuma son shiga cikin gari ta ga ya mutane ke rayuwa, amma ta san zai yi matuƙar wahala ta samu amincewar iyayenta akan hakan.

Wankin da ta yi wa Sultana ta shiga bayi ta ɗakko za ta je shanya. Girgiza kai kawai Sultana ta yi,dan ganin yanda ta zauna ta wanke mata kaya da hannu bayan ga washing machine nan da za ta sauƙaƙawa kanta aikin.

Kai tsaye wajen Mai Buruji ta je ta nuna mata inda za ta je ta yi shanya. A ranta take jinjina girma da tsaruwar gidan,dan har tsoro take yi kada ta gama shanya ta kasa komawa wajen Sultana. Murmushi ta saki a ranta take ayyana.

'Dole gida ya had'u ya tsaru kamar a turai,yo gidan gwamna ne fa.'

Tunanin ta ya tsaya cak a daidai lokacin da ta shiga farfajiyar da Mai Buruji ta tabbatar mata anan ne za ta yi shanyar. Ƙasa-ƙasa take jiyo kukan qaramin yaro,cikin sanɗa take tafiya har ta kai saitin inda kukan ke fitowa,kunnenta ta kafa a jikin windown ɗakin tana zaro ido waje,cikin kuka ta ji yaron ya na cewa.

"Don Allah ku kyale ni na tafi da zafi, wayyoo na Shiga uku akwai ciwo."

Duk yanda ta so ta leƙa cikin ginin ta ga abinda ke faruwa abun ya ci tura,saboda manyan labulaye masu duhu da ke kewaye da wajen. A haka ta haƙura ba dan ta so ba ta koma wajen shanyar jiki babu ƙwari, Shanya ta fara yi ta rage wasu a bokitin ta zauna tana nazari akan kukan da take jiyowa. Ta rasa dalilin da ya sa zuciyarta ke azalzalarta da son ganin wane yaro ne yake kuka,kuma me ya same shi yake kiran akwai ciwo da zafi? Sabuwar wayarta da earpiece wanda Lawwali ya siya mata ta zaro a ƙugunta ta kunna karatu ta maƙala a kunnenta,sai ta samu waje ta zauna riƙe da bokitinta tana wasa da ƙasar wajen. Ihun yaron ta sake jiyowa da ƙarfi kamar wanda ake zarewa rai,nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa,ji ta yi kamar ta miƙe ta afka cikin ginin da take jiyo kukan yaron ta ga dalilin ihunsa da neman taimakon da yake yi. Zuciyarta ta gama tabbatar mata akwai abinda ke faruwa a cikin wannan ƙaton gidan wanda ba kowa ne ya san da hakan ba.

Cikin sanyi jiki da rashin madafa ta miƙe tana ci gaba da shanya kayan da suka rage,tana tsaka da shanyar ta ji ƙarar buɗe ƙofar wajen,sai ta ƙi juyawa ta ci gaba da abinda take yi,cikin dabara ta kara volume har ƙarar karatun ta fito fili, da gefen Ido ta ke kallon sashen da ta ji kukan yaron, qaramin yaro ta gani yana kuka da ciccira kamar ransa zai fita. Kayan jikinsa ne ya tabbatar mata da cewa almajiri ne, da ƙyar yake taka ƙasa yana tafiya a tattale kamar wanda aka yi wa shayi, dik inda ya wuce jini ke ɗiga a ƙasa. Duƙawa ta yi tana bin karatun da take saurara domin samun sauƙin tashin hankalin da ta shiga,ta na ɗakko rigar Sultana ta yarfe za ta shanya,idanuwanta suka sauka akan Yayanta Lawwali da wani amintaccen yaron shi riqe da yaron suna taimaka masa saboda ya kasa ci gaba da tafiyar. Nan da nan wani irin kuka ya tokare mata maƙoshi,da ƙyar ta mayar da shi ta kammala shanyarta ta fara manne su da clip.

Su Lawwali na wucewa Excellency ya fito daga building ɗin ya na qarasa gyara rigar shi tare da yarfe zufar dake goshinsa,wata takarda Mubaraka ta gani a hannunsa ya na tafe ya na nannade ta kai tsaye ya zagaya bayan ginin wajen, ya bude wani Dan Rami a wajen suck away ya wulla takardar da in ba qarya idanuwanta suka yi mata ba rubutun larabci ne a jiki. Kasancewarta ma'abociyar karatun arabiyya shi yasa ta gane rubutun dake jiki. Wata iriyar zufa ta ji ta karyo Mata,cikin ranta take ayyana

'Ya Allah ka Sa ba abinda nake zargi bane yake faruwa a gidan nan. Me Yah Auwal d'ina yake yi tare da almajirin da ke neman taimako?'

Cikin tashin hankali ta ƙarasa wa rigar ƙarshe clip tare da durƙusawa ta ɗauki bokiti za ta tafi cikin gida. Wurga bokitin ta hau yi tana cafewa kamar babu abinda ke damunta,sai ta ji murya mai kauri da amon sauti ta ce mata.

"Keee !"

Nuna wa ta yi kamar bata ji ba,ta ci gaba da rera karatun qur'anin ta tana sake wurga bokitin sama ta na cafewa. Kula da abinda ke kunnen ta ne ya Sanya Excellency jinkirtawa ya daina motsi ya na son tabbatar da shin ta gan shi ko bata gan shi ba, zuciyarta ce ta fara ayyana mata ta juya, kwakwalwar ta Kuma na yi mata gargaɗi da hani akan hakan. Gargaɗin ƙwaƙwalwarta ta ɗauka ta ci gaba da tafiya, kamar bata san abinda ke faruwa ba.

Bata tsaya ba kuwa se da ta kai qaramar qofar da zata sada ta da cikin babban gidan, hannun ta na tsananin rawa saboda tsoron da ya mamaye zuciyarta ta bude qofa ta yi wuf ta shige.

Ta na isa ɗakin da washing machine ɗin gidan gaba ɗaya yake ta ajiye bokitin ta durƙusa a bayansa ta dinga kuka kamar zuciyarta zata Fado waje.

Ta na tsaka da kuka ta ji dawowar su Lawwali da hayaniyarsu, lallabawa ta Yi ta bi bayansu a hankali, a cikin wani lungu ta laɓe tana hango su, ji ta yi magana qasa-qasa da gwamna,sai ta tsaya tana binsu da kallo ranta na matuƙar ƙuna,Mubaraka na ganin sun fara haramar komawa cikin sauri ta bar wajen da gudu ta koma wajen Mai Buruji ta yi mata sallama ta ce za ta tafi tinda ya gama yi wa Sultana aiki,kuma tana so ta je makaranta ko lokacin break ne ta faɗa aji a yi karatu da ita har zuwa lokacin tashi ya yi. Mai Buruji ta jinjina maitar karatu irin ta Mubaraka,sai ta zaro ɗari biyar ta bata ta ce ta yi abun hawa sai sun haɗu a gida. Jiki a mace ta karɓi kuɗin ta soke a bayan wayarta ta nufi bakin gate. Kai tsaye ta nufi bakin titi tana tafiya a ƙafa tana tunani,ba tare da ta san lokacin da su Lawwali suka fito ba ta ga motarsu ta tsaya a gabanta. Wani irin murmushin yaƙe ta sakar masa tare da murnar ganinsa. Fuska a sake ya bada umarni aka buɗe mata mota ta shiga sannan suka rufe suka ci gaba da tafiya. Fuskarsa da take kallo ce ta sanya hawaye zubowa a idanuwanta sakamakon tunawa da abinda ya faru a gidan Gwamna da ta yi,nan take hankalin Lawwali ya yi bala'in tashi,ransa a mugun ɓace ya kalle ta ya ce.

"Barakana me ya same ki kike kuka? Waye ya taɓa ki lahira ta yi baƙo?"

Kafe shi ta Yi da jajayen idanuwanta,a hankali ta furta.

"Kaina ne yake yi min ciwo"

"Subhanallahi sannu kin ji? Me ya sa na gan ki a nan gidan yau ke da Mai Buruji ina Lamishi?.....Kai mu wuce chemist"

Kasa bashi amsa ta yi sai tsiyayar da hawaye take yi. Suna zuwa chemist a ka haɗa Mata magani kala-kala har da na zazzaɓi,daga nan sai ya siya Mata yagot da lemun roba ya sai Mata snacks suka wuce gidansu. A hanya ne take bashi labarin yanda Lamishi ta hana ta zuwa makaranta ta ce dole ta je ta yi mata aikinta a gidan Gwamna,gashi yanzu ciwon kai da zazzaɓi sun dameta. Ransa a ɓace suka isa gidan,da kanshi ya buɗe mata ƙofa ya kama hannunta suka shige cikin gidan,fatali ya yi da duk wani abu da ya tsaya a gabansa,har suka isa ƙofar ɗakin Lamishi,murya ya ɗaga yana faɗin.

"Uban waye ya aiki Barakana aiki gidan can ? Na ce waye ya aike ta aiki can gidan yau?"

"Uban ka ne ya aike ta aikin ishasshe. Dan uban ka ni ba za ka zo kana wani yi min fad'in banza da fankama anan ba, ni uban ka zan ci na kwana lafiya"

Baya ya ja yana yarfa hannu ya ce.

"Ni ba fad'a nake nema dake ba Lamishi, kin San yarinyar Nan Bata Saba da aikin wahala ba,makaranta take son zuwa,wa yace a aike ta aikatau bayan kin san aikin gidan nan ya fi ƙarfinta ba iyawa za ta yi ba? Na tabbata yanzu ma da ta dawo ba ƙyaleta za ki yi ba,wani aikin za ki saka ta."

"Idan bata je ba ubanka kake so na aika a madadina? Yau tashi na yi da masassara, Shine nace ta je a madadina tinda ba su son fashi,kuma Allah na tuba ma aikin Sultana har wani aiki ne? Yarinyar da idan ta saka kaya ko sun wuni jikinta ta cire ganinsu za ka yi kamar ba a jima da sakawa ba. Kai ne fa kake daure wa yarinyar take yi Mana iskancin da ta ga dama Lawwali."

Ganin sa'insa da musayar yawun da Lawwali ke yi da mahaifiyarsu ya ƙi ƙarewa,sai Mubaraka ta ja hannun Lawwali Suka je dakin ta, ta ce masa.

"Yah ni fa qarya na yi maka ɗazu,Amma ba ciwon Kai nake yi ba"

Cike da mamaki ya kalle ta domin ƙarya bata daga cikin halayyar ƙanwar tasa,hasali ma a rayuwa ta tsani maƙaryaci. Dan haka sai ya samu waje ya tsaya yana binta da kallo ya ce.

"Ke ko me ya faru haka yau kika yi ƙarya da bakin ki da kike hana a yi ƙarya?"

"Yah Auwal ina so ka faɗa min gaskiyar abinda kuka yi wa almajirin nan a gidan gwamna,domin da kunnena na ji yana kuka yana neman taimakon mutane,daga baya kuma naga ya fito ya na zubar da jini ta qafar shi."

Wani irin kuka ne ya ƙwacewa Mubaraka,ta durƙusa a wajen tana yinsa kamar ranta zai fita,da jajayen idanuwanta ta kalli Lawwali ta ce.

"Don Allah kar ka ce min kana daga cikin maza masu aikata ɗabi'ar mutanen Annabi Lu...."

Cikin sauri Lawwali ya saka hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai ya ce.

"Ban taɓa ba Barakana,ba na daga cikin mutanen dake aikata luwadi, na Yi maki alqawari ban aikata ba,kuma ba zan taɓa aikatawa ba,yaro kawai muka samo muka kaiwa Mai Gida bisa umarninsa."

Kukan ta ne ya ƙaru sosai,zama ta yi a ƙasa ta dinga rera shi kamar zata shide,ruwa Lawwali ya bude yana ƙoƙarin bata, hannu ta sa ta Yi wurgi da ruwan cikin kuka ta ce,

"Yah Auwal ka bar aiki da shi bana so,ina jin tsoro idan ka ci gaba da aiki a gidan Gwamna zaka shiga wuta. Yah Auwal ko babu abinci mai daɗi za mu rayu,kai ko da sau ɗaya muke cin abinci a rana ba zamu mutu ba,idan kuma ka ci gaba da aiki a can kana samo kuɗi mu shirya wa kawunan mu wajen zama a cikin wutar Allah,wadda na tabbata ba zamu iya yin second daya cikinta ba, Yah Auwal ka yi min alqawarin baka taba aikata wanan abun da kowa ba, ba kuma za ka bari a yi da Kai ba,"

Cikin tsananin tashin hankali da fargaba Auwal ya ce.

"Na yi maki alqawari Barakana ba a taɓa aikata luwaɗi da ni ba,kuma ba zan aikata da kowa ba,na tsani wannan abun Barakana na kuma tsani masu yinsa,dole ce ta sa nake zaune a gidan nan nake yin aiki. Don Allah ki dena kukan haka ya isa,zuciya ta zafi take yi idan Ina jin kukan ki kin sani,"

Muryar Lamishi suka jiyo a waje tana faɗin.

"Shegiya 'yar bid'ar a Yi bala'i, wato kuka kika saka shi a gaba kina yi masa shi Kuma uban mu ya zo ya Dake mu ko? Ke kin sani ai,idan duk gari ana tsoronsa ni ubansa zan ci na haɗa dake gaba ɗaya babu kuma abinda ya isa ya yi min."

Duk masifar da Lamishi ke yi suna jinta,babu wanda ya tanka ta,sai ma tunawa da takardar arabiyya da ta gani a hannun gwamna ya sama a suck away,cikin tashin hankali ta kalli Lawwali ta ce.

"Yah Auwal in dai kana son farinciki na to ka bar aiki a gidan nan,isan ba haka ba kuma zan kashe kai na."

Wani gigitaccen Mari Lawwali ya sakar Mata idanuwansa na zubar da ruwan bala'i ,cikin tsananin bacin rai ya kalle ta yana zaro ido waje,Mubaraka kuwa wasu taurari ta gani sun gilma a idanuwanta tare da walqiya.

Hannu ya sa ya rungumeta yana jin wani irin matsanancin son ƙanwar tasa na ratsa shi. Cike da nadamar marin da ya zabga mata yake shafa kuncinta a hankali yana taune leɓensa na ƙasa. Mubaraka ta san cewa ita ce rauninsa,tana sane da matsananciyar soyayyar da yake yi mata wanda kaf ƙannensa ya fi sonta. Me yasa za ta furta mummunar kalmar kisan kai akan ta bayan ta san ba zai taɓa iya jure rashinta ba? Cikin wata iriyar murya ya ce.

"Ki yi hakuri Barakana na yi miki alƙawari zan bar aiki a gidan Gwamna,amma kin san ba zai yu na bar aiki kai tsaye ba gudun kada ya gane dalilin barina aikin ya ɗauki tsattsauran mataki akaina da ku baki ɗaya,ki bani lokaci watarana zan bar gidan ba tare da kowa ya gane dalilin barina gidan ba. Don Allah kar ki sake danganta kanki da mutuwa,ke fa malama ce ke kike yi min wa'azi,to me yasa kuma yau kike ikirarin kashe kan ki? Kar ki sake bana so kin ji?

Kai ta ɗaga tana daidaita natsuwarta kafin da ƙyar ta ce.

"Ka yi haƙuri ba zan sake ba,sannan ka yi min alƙawari zaka bar aiki a gidan nan ba da jimawa ba."

"Na Yi alqawari Barakana zan bar aiki a gidan nan kusa. "

Share Mata hawaye ya Yi, sannan ya ce,

"Kinga yanzu dole ki Sha maganin da muka siyo Dan yanzu kan ya fara ciwo da gaske,Malama ta yi ƙarya yanzu gaskiya ta tabbata akanta."

Snacks ya ajiye Mata a gaban ta da magani da lemo,sannan ya ce ta tabbata ta ci abinci sannan ta Sha maganin,daga nan ya fita ya tafi wajen yaransa dake jiransa. Kasa cin abincin ta yi ta ci gaba da aikin kuka.

Har suka isa maboyar su Lawwali bai daina jiyo kukan qanwar tashi da ya ke so sama da kowa da komai ba a kunnuwasa.

Dakin shi ya shige ya kwanta yana nazarin rayuwar da yake ciki ta shagala da gafala. Lawwali ba ya shiga shirgin mutanen da aka sa su kamawa,sai dai yaransa su kula da su,ya fi bawa 'yan siyasa muhimmanci domin su ne silar shigarsa cikin rayuwar da yake yi a yanzu. Dan haka gaba ɗaya mutanen gari da suke kamawa ba su san shi ba, No 1 zuwa No 5 kawai suka sani da sauran yaransa. Kalamanta ne ke yi masa amsa kuwwa a cikin kunnensa musamman inda take ce masa.

'Za mu iya jure rashin abinci,amma ba za mu iya jure wutar Allah ba'

**********************

Da misalin takwas na safiyar asabar Isa ne zaune a majalisar su ta masu zaman banza, labarai ake ta bayarwa da suka ja ra'ayin shi matuqa, shiruuu ya yi ya na sauraron su ba tare da ya tanka musu ba, matashin da ake kira da Idi ne ya ce,

"Yau Malam Isa ya shiga tunanin uwar gida, ko dai gida za ka koma ne kar ka yi laifi?"

Yatsina fuska ya yi,ya gyara zamansa sannan ya ce.

"Habaa Allah ya kiyaye, ai mata bayin mu ne sai yanda muka yi da su, da sassafen nan me zan zauna na yi mata a gida inna koma? Zaman gida ai sai mata."

Dariya suka fashe da ita suka ci gaba da hira,rana na kwallewa Idi ya miƙe tare da yi wa mutanen wajen sallama zai tafi,cikin sauri Isa ya tashi ya bi bayan shi,sai da suka yi tafiya mai nisa Isa ya ce masa.

"Ka na ta sauri Ni fa biyo ka na yi game da maganar da ka yi ɗazu a majalisa, da gaske ka ke sana'ar saida goro a Makka indai an samu ta shiga akwai riba ?

"Kwarai da gaske, kai baka taba jin labarin bane?"

"To a ina zan ji ni da ba wasu yan uwa masu maiqo gare ni ba?"

"Da gaske ne to Malam Isa, yanda ka ji na faɗa haka abun yake,da ka je da goro garin Makka za ka mayar da kuɗin jirginka har ma ka samu ribar da za ka iya komawa wata shekarar."

Zaro ido waje Isa ya yi tare da kama baki,a hankali yake jinjina kai kafin daga bisani ya ce.

"To na gode, zan neme ka inshaa Allahu mu ƙarasa maganar nan da kai."

Dariya Idi ya yi ya kalli Isa sama da qasa, sannan ya tafi ya na dariyar ina Isa zai samu kudin siyan goro ya kai Makka, ballantana uwa uba ya samu na kujerar tafiya makkan?

Isa kuwa gari ya shiga ya dinga yawo, domin neman qarin bayani akan sana'ar saida goro a makka, yanda ya ji ana samun kuɗi ne ya rikita shi har ya ji kwaɗayin son gwada zuwa makka shima ya fara siyar da goro,wataƙila a nan hanyar arziƙinsa take. Daga ranar da ya hau jirgi kuwa ya tafi makka da goro zai yayewa kansa zama da su Ɗantalo masu mutuwar zuciya..... [26/03, 9:13 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH