PAGE 10
by @1239900
Jiƙaƙun tissue paper ne a ƙasan parlourn da ke tashin sautin kukan Sultana, jikinta babu abinda yake yi sai rawa kamar mazari,idanuwanta da fuskar ta kuwa sun yi ja-jawur. Videon da take kallo a YouTube ta wayar hannunta ta sake playing kamar wadda ke ƙoƙarin haddace kowanne bayani akan abinda take kallo. Matasa ne ɗauke da manyan makamai wanda bata taɓa ganin irinsu ba a ƙasashen Africa sai dai a fina-finan ƙasashen,fuskar su sanye take da hulunan sanyi irin na sojoji kamar yanda jikinsu ke sanye da riguna ko wandunan sojojin,wasu kuma complete kayan soja ne a jikinsu tin daga sama har ƙasa. Idanuwanta ne suka sauka a wani ƙonannen ƙauyen dake tashin hayaƙi da kururuwar mata da ƙananan yara wanda yake a cikin garin Zamfara. Babban abinda ke bata tausayi bai wuce yanda ta ga an karkashe mata da ƙananan yara tare da mazajen garin ba, kisa irin na rashin imani domin kuwa bayan yanka su da aka yi da wuƙaƙe sai da aka bi su da harbi domin tabbatar da cewa babu wanda ya rayu sai wanda suka so bari a rayen. Gungun ƴanmatan da za su kai goma suka tasa a gaba kuccensu an ɗaureta da igiya an kaɗa kansu zuwa daji. Matar dake ɗaukan videon kanta kuka take yi saboda tsananin tausayin matan da aka kashewa mazaje da yara,sannan aka tafi da yaransu mata. Wata mata ce ta yi ƙarfin halin tsayawa a gaban matar dake ɗaukan videon tana gunjin kuka ta ce.
'A gabana ya kashe min jaririyata da wuƙa sannan ya bita ya harbe da bakin bindiga.....kafin kuma ya ɗauki Asabe ya yi mata fyaɗe akan idona da na sauran mutanen gari... Sun kashe uban da ya tafi ceton ƴarsa da ake wulaƙantawa a gaban dubban mutane...bani da ƴaƴa bani da miji bani da kowa sun kashe au sun barni a raye baƙin cikin rashin dangi da iyali ya yi ajalina....shin ina gwamnati take ne? Ana kashe mu da yaranmu, ana ƙone mana gidaje da dukiyoyinmu, yanzu ki duba gidajen can da aka bankawa wuta a ina zamu kwana? Wa zai karɓe mu a dangi ko cikin mutanen gari a matsayin ƴan gudun hijira idan mun bar garinmu? Rayuwar nan kowa fama yake yi da kansa,ku ji tausayinmu ku dena kashe mu,mu ma bayi ne na Allah kamar ku. Shin gwamnati me yake faruwa A GARINMU na zamfara da kewaye?'
Kuka ne ya ci qarfin matar da ke magana, wanda da dukkan alamu ita kan ta 'yar jaridar kuka take yi, Sultana kuwa kamar ta sume saboda tausayi,Lamishi ce ta shiga parlourn ta duƙa tana tattare tissue ɗin da Sultana ta ke zubarwa ta na hawaye. Jikinta a sanyaye ta kalli Sultana dake wani irin kuka mai ciccira ta ce.
"Uwar daki na ki yi haƙuri ki dena kukan haka kada ki jawo wa kan ki zazzaɓi,na tabbata masu aikata wannan laifukan ba mutane ba ne,ba kuma za mu kira su da dabbobi ba,domin ko dabba mai cin nama bata kashe ƴar'uwarta haka kawai face tana jin yunwa. Dan haka ki yi haƙuri mu bi su da addu'a Allah Ya kawo mana sauƙin waɗannan abubuwan dake faruwa A GARIMU."
Cikin tsananin kuka Sultana ta ce,
"Baba Lamishi Ina za su tafi bayan an rushe musu gidajensu, wa za su kalla su ji daɗi an kashe musu yaran da Allah ya basu su zamo musu sanyin idaniya? Wa za su jingina da shi bayan an kashe musu mazajen da za su fita su nemo musu abinci su kuma basu kariya? Yanzu idan aka tinzirasu suma suka ɗauki makami ba fa su san wanda suka zalunce su ba ballantana su je wajensu su ɗauki fansa, al'ummar gari za su farwa su yi musu kwatankwacin abinda aka yi musu ko sama da haka."
Kukan ta ne ya qaru da ta ga wata mata ta fita da gudu, ana ta tare-tare, ashe a gaban ta aka yanka mijin ta da matashin yaron ta, aka tafi da yan matan yaranta guda uku,shi yasa kanta ya kwance take surutai mara kan gado tare da bazama cikin mutane tana kiran sunansu. Babu zato babu tsammani suka ji muryar Hajiya Ikee na faɗin.
"Ke Lamishi ! amshe wayar nan ki kashe ta gaba ɗaya sanan ki tashi ki tafi waje"
Jiki na rawa Lamishi ta karɓi wayar Sultana dake rusa kuka kamar wadda ake zanewa da bulalai,ta kashe sannan ta ajiye a center table ta ɗauki ƙaramin dust bin ɗin da ta zuba tissue paper ta kama hanyar fita waje ta ƙofar baya.
Cike da ɓacin rai Sultana ta miƙe za ta hau sama dan bata son ganin iyayen nata da ta gama tabbatarwa kanta duk abinda yake faruwa a garin da saninsu. Jiri ne ya ɗebe ta tafi luuu za ta fadi, Hajiya Ikee da Lamishi ne suka yi kan Sultana da gudu dan su kamata,kafin su isa har ta faɗi ƙasa,da sauri Lamishi da ta riga Hajiya Ikee isa gareta ta ɗagata ta rungumeta a jikinta tana tsiyayar da hawayen tausayin yarinyar da ke da farar zuciya kamar ba daga tsatson Hajiya Ikee ta fito ba. Da ƙyar Lamishi ta iya kai Sultana ɗakinta ta kwantar da ita a gado sannan ta rufe ta. Kallon fuskarta da ke sauke ajiyar zuciya ta yi idanuwanta na zubar ruwan hawaye Lamishi ta yi. Cike da tausayawa ta kaɗa kai ta fita tare da ja mata ƙofar ta rufe. Tana karasawa step ɗin ƙarshe ta ji Hajiya Ikee na yi wa Daddy bayanin zubewar tissue mai datti a tsakiyar parlour.
"Sultana ce fa your Excellency, daga ganin abinda ya faru a wannan qauyen da ake ta haskawa a gidajen talabijin da kafafen sada zumunta shi ne duk ta daga hankalin ta, yanzu haka ta na daki kwance babu lafiya."
Ran gwamna a matuƙar ɓace ya nuna Hajiya Ikee ya ce.
"Wai me ya sa ba ki jin magana ne Iklima? Ban hana ki barinta kallon irin wadannan shiraruwa shirmen ba? Sanin kanki ne da ta samu kanta za ta saka ni a gaba da tambayoyi kamar ni ne na je na kashe mutane da hannuna." Ransa a matuƙar ɓace ya hau sama yana baza babbar rigarsa kamar zai tashi sama. Lamishi dake rakuɓe kamar munafuka ce ta bankawa bayansa harara a cikin ranta ta ce.
'Dan butar uba mai suffar tumakin DanTalo, wannan mutumi mara tausayi Allah ka yi mana maganinsa.'
Duƙawa ta yi tana kwashe tissue ɗin tana jiyo Gwamna na ci gaba da zazzagawa Hajiya Ikee masifa ita kuwa ta bishi tana ta faman bashi haƙuri kamar za ta yo aron baki.
Tinda Lamishi ta koma sashen masu aiki jiki a mace har suka gama aikin su bata sake yin walwala da barkwancin da takan yi ba idan suna aikinsu.
Lokacin da Lamishi ta yi shigar qarshe dakin Sultana dan ta ji ko da abinda za a yi mata kafin su tafi,sai ta gan ta zaune ta na tunani mai zurfi. Cikin sanyin murya ta ce.
"Uwar daki na lafiya? Ko na kawo maki abinci ne ki dan taba kadan? Saboda ke na tsaya har yanzu ban tafi gida ba,"
Gaba ɗaya hankalinta Sultana ta tattare ta mayar kan Lamishi ta ce.
"Ni kam na tambahe ki mana Baba Lamishi."
Da sauri Lamishi ta zauna a gefen Sultana tare da bata dikkan hankalinta tace.
"Ina jinki uqar ɗakina,ki tambaye ni,ni kuma na yi alƙawari zan baki duk wata amsa da na sani."
Ƙasa Sultana ta yi da muryarta sannan ta ce.
"Dan Allah ya yanayin gidanku yake? Ina nufin akwai sirri ta yanda wani zai iya zama ba tare da an sani ba?"
Haɓa Lamishi ta kama tana jinjina kai,kafin ta ce.
"Tab gidan mu yanda ki ka san bakin kasuwa haka yake ,matan unguwa kaf shiga suke yi,maza kuma na qofar gida, dan kawai a ci abincin da muke tafiya da shi daga nan, da an gama ci ne dai ba za ki sake ganin kowa ba sai kuma wanshegari"
"Ok na gane, amma kuma ba ki san ko ina ba da mutum zai iya zuwa na sirri ba haka ya zauna ba tare da kowa ya san yana rayuwa a wajen ba?"
"Gaskiya ban sani ba,idan hasashena ya yi daidai, ke ce ke son fita daga gidan nan ki samarwa kanki mafaka ko?"
Shiru Sultana ta yi ta juyar da kanta gefe hawaye na tsiyaya a idanunta, jin ta take yi kamar a gidan kurkuku. Lamishi ce ta ci gaba da magana ta ce mata.
"Idan haka kike tunani a ran ki to ki saki wannan tunanin ki kama wani, domin zaman ki anan shi ne rufin asirin ki da samun kariya a gare ki, kinga duniyar da ke a wajen gidan nan? Duniya ce ta azzalumai, duniya ce ta daukan rai ,duniya ce ta shan jini, da kwace muhalli, duniya ce azzaluma,duniya ce cike da miyagu masu raba Mata da maza da mutuncin su, zaman ki a inda iyayen ki suka killace ki shi kad'ai ne kwanciyar hankalin ki da kariya a gare ki"
Cikin kuka Sultana ta ce,
"Su kuma bayin Allah'n da ake kashewa fa? Haka za su ci gaba da rayuwa?"
Tashi ta yi da gudu ta fita daga dakin tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Lamishi kuwa komawa ta yi wajen Mai Buruji, ta ce su tafi kawai, dan bata ga alamar Sultana za ta ci wani abu ba ballantana ta tursasata ta ci ɗin.
Sultana kuwa ɗakin mahaifanta ta nufa ta dinga buga qofar da qarfi, Hajiya Ikee ce ta fito ita da Sultan ,Sultan na ganin yanayin Sultana ya san babu lafiya, cikin hanzari ya nufe ta, tare da qoqarin kama ta ta kwace ta yi gefe tana tsura musu idanuwa ta ce.
"Ina daddy? "
"Yanzun Nan ya fita, za su fita government house mene ne ya same ki sultyna?"
Da gudu ta fita waje babu ko takalmi a qafar ta ta bi bayan mahaifinta . Gwamna ya shiga motar da zata kai shi gidan gwamnati kenan, bayan shi da gaban shi kuwa motoci ne masu bashi kariya, duk sun yi shirin tafiya ya hango Sultana ta fito a birkice cikin kuka da hargowar kiran sunansa,nan take ya dakatar da motar ya leƙa kansa waje yana faɗin.
"Sulty baby me ke faruwa? Ina za ki je a haka?"
Cikin sauri tare da haki ta kalli Gwamna ta ce.
"Daddy Ina zaka je? Za ka je wajen mutanen can ne da aka qonawa garin su? Daddy pls help them they really need ur help, daddy su ma fa mutane ne, Kuma a qarqashin kulawar ka suke, me ya sa haka take faruwa da su ko su ɗin ba ƴan ƙasa masu ƴancin rayuwa a duk inda suka so bane?"
Dan kallon gefe da gefen shi ya yi, ya ga kan mutanen da ke wajen a dan duqe, wasu kuma sun qura musu ido dan son jin irin amsar da zai bayar, dan kama kafadun ta ya yi, ya goge mata hawayen idan ta, wanda ba su daina zuba ba duk da gogewar da yake ta yi,
"Sulty baby calm down please yanzu haka can wajen zan je,ki koma ciki ki ci gaba da yi musu addu'a kin ji? Guards ku tsananta tsaro, a cikin gidan nan kar a bar kowa ya shiga ko ya fita,"
Ya kalli idanun Sultana a lokacin da yake fadin hakan, saboda ba yau ta saba satar jiki ta fice ba daga gidan,musamman idan ta ga irin wannan tashin hankalin,sai dai ya ji labarin ta kai taimako wajen Wanda ibtila'i ya fadawa. Datse haƙoransa ya yi ya sake maimaita abinda ya faɗa.
".....ina nufin kar a bar kowa ya fita, a tsananta tsaro"
Ture hannunsa Sultana ta yi daga kafadun ta, cikin hawaye ta ce,
"Me ya sa ba za a ba wa mutanen can tsaro ba kamar yanda ake ba wa wannan gidan? Shin masu gadinmu a gidannan nawa ne? Yawan su bai isa ya kare wani qaramin garin ba? Me ya sa ba za a kai taimako wajen da ya dace ba?.."
"Keep quiet sultana and go inside kafin na saba maki,"
Mota ya bude cikin fushi ya shige, nan da nan kuwa aka kunna jiniya, motocin da ke bashi kariya na biye da shi.
Qoqarin durqusawa take yi a wajen Sultan ya tallabe ta,ƙwacewa ta hau yi tana wutsil wutsil a hannunsa ya kama ta za su shige gida. Motar su Lawwali ce ta shiga gidan bayan gwamna da muƙarrabansa sun fita, Lawwali ne a gaba gefen mai zaman banza, yau ce rana ta farko da ya fara dora idanun shi a kan Sultana, yau ce rana ta farko da ya taba jin wani abu mai nauyin gaske wanda bai taba jin kalar shi ba a gaba daya rayuwar shi ya soki zuciyar shi, wani irin yanayi ne mai dad'i cike da shauki da wani dandano wanda bai san yanda zai fassara shi ba ya kai wa ƙwaƙwalwarsa ziyara, har motar ta tsaya,yaran shi suka fara fitar da wasu buhuna da aka nannade aka yi wa wani irin dauri mai tsanani ta yanda komai kwakkwafin mutum bai isa ya gane meye a cikin daurin ba, Lawwali na zaune a mota, har Sultan ya yi nasarar dauke Sultana a wajen. Suna shigewa ciki Lawwali ya ɗauke kansa daga kallon bakin ƙofar shiga gidan yana sakin wani irin shu'umin murmushin da ya bayyana tsantsar kyawun da yake da shi. No 1 ne ya ɗan duƙar da kai a saitin Lawwalin ya ce.
"Oga an gama,"
A dan daburce ya kalli No 1 ya ce.
"To to shikenan shiga mu tafi. Kun tabbata kun ajiye kayan a inda Excellency yace ko?"
"Eh oga,"
"Tau ya yi, muje"
Kallon inda ya ga Sultana a duqe ana fama da ita ya sake yi,fuskarsa ya shafa sannan ya saki murmushi, cikin ransa ya ce.
'shege Excellency, dole ya dinga kaffa-kaffa da zuwanmu, ashe ya aje kadara mai tsada a cikin gidan shi,'
Har suka fita daga gidan suka dauki hanyar dajin su bai magana ba, No 1 yana ta yi masa magana bai san yana yi ba saboda gaba daya hankalin shi ya tafi wajen tunanin sultana.
*********************
Isa ne ya ke bin Hansatu da wani irin mugun kallo ya ce mata.
"Ki na nufin har yanzu ba su dawo daga makarantar ba kuma kike zaune a gida kina kukan banza ba zaki tafi Nemo su ba? Bari ki ji Hansatu,idan wani abu ya samu yara na sai na yi maki abinda ya fi qarfin mutuwa azaba, ..ba Zaki tashi ki tafi makarantar tasu ki binciki inda suke ba?"
A tsawace ya Yi maganar yana muzurai kamar wani kumurcin maciji. Cikin rashin kwarin jiki, da ciwon da qirjin ta yake yi Mata ta miqe ta nabin bango ta shuri takalminta tare da zarar mayafinta dake kan igiya ta yafa. A daidai wannan lokacin duhun magariba ya fara yi,gashi ko yar touch light dinnan ba ta da shi, ga uban rashin wutar lantarki da suke fama da shi a unguwar,a haka ta isa soron gidan tana layin yunwa ta nufi makarantar yaran.
Dama can tana da niyyar zuwa nemo su,tinda ta riga ta sani duk abinda ya samu yaranta mai kyau ko mara kyau ita ke da asara Isa bashi da lokacinsu balle ya damu da rashin ganinsu,sai dai Isa ya bata mamaki da ya nuna damuwarsa akan yaran duk da ya dace ace sun fita neman yaran ne tare da shi. Cikin ranta take ayyana.
'Hansatu yau ne kike tare da Isa? Ai ko kece Kika Bata ba zai je Nemo ki ba sai dai ki gaji ki dawo da kanki, ballantana kuma yaran da ya tsana ya ke ganin su na daga cikin silar talaucin ku'
Hawaye ne masu tsananin zafi ke sauka a fuskar ta, a cikin zuciyar ta kuwa wani irin quna ta ke ji, qirjinta ne ya sake Yi Mata suka har sai da ta damqi saitin zuciyar ta, ta durqusa a tsakiyar hanyar da wasu maza ke wucewa dan dawowa daga masallaci za su koma gidajensu da harkokinsu na yau da gobe. Kamar daga sama ta jiyo muryar Isa na faɗa mata
"Tsayuwar uban me kike yi anan?"
Daga Kai ta Yi a wahale ta ce masa.
"Ƙirjina ne ke yi min ciwo, Amma yanzu zan tafi"
Ƙwafa Isa ya yi ya ce mata.
"Hummmm"
Ya wuce ta cikin sauri kamar zai tashi sama. Hansatu kuwa da kyar take tafiya, ko da ta isa makarantar sai ta ganta a rufe alamu sun nuna babu kowa a cikinta. Mai gadin wajen ta tambaya tare da yi masa kwatancen yaran, cike da jimami ya ce mata bai gan su sun je makaranta ba a ranar,saboda ya san su Aminatu yara ne nutsattsu masu hankali, ga kuma uwa uba qoqari, malaman makarantar kan su na yaba qoqarin su. Dan ya kwantar mata da hankali sai ya ce mata.
"Hajiya to ko za ki duba gidan ƴan'uwa ko can suka je?"
Idanun Hansatu ne suka ci gaba da zubar da ruwa tana tambayar kanta inda yaranta za su je a wannan rana su ƙi zuwa makaranta tinda su ba masu yawo bane. A hankali ta furta.
"To ko gidan mu Suka tafi?....kaii inaa ba nan suka je ba, tun da suka je sau uku na Hana su ba su sake zuwa ba, yau shekara biyu kenan, to Ina suka tafi?"
Yawo Hansatu ta fara yi lungu da saqo na unguwar amma bata ga yaranta ba ko ta ji Wanda ya ga yaran. Kanta ne ya yi wani irin sarawa ta hau roƙon Allah Ya sa ba sace mata yara har uku aka yi ba,fatanta bai wuce ace yawo suka je ba a wannan rana duk da ta san hakan ba halayyarsu bace. Tunani ne ya yi mata yawa,nan take ta faɗi ƙasa ta yanke jiki ta fadi a qofar gidan Asshibi......... [26/03, 9:13 pm] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: A GARINMU
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH