PAGE 2
by @1239900
Jameelah ce ke tafe tana ta surutu dan kuwa bata son abinda Umaimah take yi mata sam,cikin quluwa take fad'in ,
"Ita da an zauna da ita sai ta dinga yi wa mutum nasiha kamar ta maida mutum jahili, a qalla dai nafi wasu sanin Allah karatun nan in dai qur'ani aka ban ba inda ba zan kawo ba indai an yi mana wajen, hadda ce kawai matsalata,kuma itama haddar in an min uziri ai kai na ne baya ja, ita da take ja ba gashi har boko take zuwa ba, haba malam, ni bana san kinibibi a bi a ishe ka."
Ji ta yi an bangaji kafad'ar ta da qarfi,cikin sauri ta dafe wajen tare da ayyano wadda zata yi mata wannan ɗanyen aikin a saman titi,cikin masifa ta juya suka yi ido huɗu da Mamalo kuwa nan take ta ce,
"Mamalo kina da hankali kuwa? A fa kan hanya muke, shi yasa fa wataran bana son jerawa da ke sai a dinga ganin mutum mara aji, ki bari muje gida, ɗazu ina gani harda ke akai min dariya a aji da malam na duka na, kin san ai zan rama ne indai ni ce baki yi dariya a banza ba sai ta zame maki kuka watarana,"
Magana take yi cike da yanga, ba mai gane masifa take yi saboda yanda take kare ajin ta wajen samarin unguwar su,jikin Mamalo ne ya yi sanyi saboda tsoron abinda Jameelar zata aikata mata dan ɗaukan fansa,sarai ta san halin Jameela ba a yi mata bata rama ba, sannan bata ɗaukan rainin wayo.
Mazan qofar gidan su dake zaune zaman jiran dawowar ta daga makaranta na nan zaune ana ta hira,sun riga da sun san halin ta bata zama har a tashi da ta yi wani laifin ko ta ga za a bada hadda sai ta gudo gida abinta, wasan banza suka tsaya yi kamar ba ita ta gama d'agun kai ba a hanya ta na jan aji,cikin yanga ta ce,
"Dan Allah kayi hakuri Babawo, yau na maka alqawarin kai zan fara kawo wa abinci, na ji ma qamshin girkin kamar an gama, kasan girkin Ramai daban ne dana kowa a gidan nan,"
Wata sabuwar rarumar ya sake kaiwa hannun ta,ita ko tana ta dariya tare da sakar masa hannun yana ta latsawa.
"Allah in ki ka min irin na jiya na kama ki zaki san dani ki kayi ,"
Wani kallo suka yi wa junan su wanda ban gama gane wanne iri bane, dan a iya sani na mata da miji ko wasu masoyan da suka shaqu matuqa ne kawai ke yi ma junan su irin shi.
"To ka sakar min hannu na manaaa,"
"Na sake ki yanzu amma anjima bayan magariba zan zo idan na kama ki ba zan sake ki ba sai na maki hukuncin hana ni zubin farko da ki ka yi jiya sannan na kyale ki, yanzu ki je in an gama ki kawon naci na koma wajen aiki, baban ki daya duba yaga bai ganni ba kamar makaho haka zai hau kirana,"
"Kaga abinda ke haɗa ni da kai ko Babawo? ka mugun raina baba na,"
Murgud'a bakin ta ta d'anyi sannan ta fizge hannun ta ta shige gida.
Tin daga soron farko masu ɗaukan talla ne ana ta jera abinci a babban faranti da kwali, matan gidan suna zazzaune a qananan kujeru su na taya su lissafi da jerawa, wasu sun kunna kid'a a wayar su ana saurara ana ayyuka, wasu nata hira da shewa tare da 'yan gulmammaki irin na gidan haya,wata waqa dake tashe a wannan lokaci ta mutanen kudu Jameelah ta ji an kunna, nan take kuwa ta d'age hijabin ta ta baya ta yab'a shi a kafad'a ta hau rawar zamanin da ake yayi, yanayin yanda take rawar sai ya ba wa mai karatu mamaki da tsoron ko aljanu ke motsa mata sassan jikin ta, ihu wajen ya ɗauka da tafi,ita ko sai tiqar rawa take tana bin waqar cike da nishadi da jin daɗi.
Sai da waqar ta qare sannan ta faɗa gidan babu ko sallama, buta ta ɗauka ta yi band'aki babu ko addu'a a bakin ta, haka tayi abinda zata yi ta fito.Bayan ta ajiye butar ne ta kalli Lantai dake dafa nata abincin, tace,
"Lantai, Mamalo tayi wanka kuwa?"
Wani kallo ta bi ta dashi na qasqanci sannan ta ce,
"Ina na sani ina nan ina aiki na ni, ki duba mana da kan ki,"
Ganin irin kallo da amsar da ta samu ne daga Lantai yasa ta saki tsaki mai qarfi cike da rashin kunya ta doka qafa ta d'age labulen d'akin su babu ko sallama ta shige, tana masifar Lantai na yi mata abinda ta ga dama a gidan nan dan ma ta samu ta na neman 'yar ta? Ita fa ke d'aga ajin ta a dik fad'in layin nasu,to daga yau ta daina suje can su qarata da 'yar ta su zata ga kalar qawayen da za ta yi a unguwar, ta na gama masifa ta kalli kwanon da ke gaban ta ta sa qafa ta tura shi gefe sannan ta ce,
"Ramai wannan abinci na ne? In dai nawa ne na qoshi ni nan da ki ka ganni sai da nayi nak sannan na dawo gida, baki ga dukan dana sha ba yau a makaranta, amma yayi ta banzar tinda na ci abincn gidan masu kuɗi, ya Allah ka nuna min na shiga daula irin ta su Umaimah,"
"Ameeen yarinyar kirki in Allah ya yarda maqiyan ki sai sun zama fadawan ki, har shi malam Isyakun dake dukar min ke kamar nace masa jaka na aika masa, ko kallon kalar fatar jikin ki ba zai yi ba ya san ke ba kalar duka bace,so ya ke wataran na wanke qafa na je na masa rashin mutunci, amma ya ci gaba kar ya fasa, watarana ko da miliyoyi aka bashi bulala aka ce ya dungure maki kai ma ba zai iya ba, wuce ki shirya abin ki,"
Ɗan qaramin towel ɗin ta ta dakko ta daura sannan ta saka wani dan qaramin hijab daya manne mata a jiki, ta dauki soson wankan ta da ruwa a bokiti ta fito tsakar gida nan ta wuce mazan dake diban abinci da abubuwan da suke saidawa a kasuwanni sai bin ta suke yi da kallo wasu ma har leqowa suke yi dan su qare mata kallo da kyau.
Ba ta wani dad'e ba a band'akin ta fito, tana ta mita da surutu akan qazantar bandakin nasu na gidan yawa tare da roqon Allah ya nuna mata ta bar wannan gidan gandun ta huta da bala'i.Tana addu'ar Ramai na amsa mata da Ameen.
Kwalliyar da ake yayi a wannan zamani ta sheqa ta yi masifar kyau kamar ba 'yar talla ba, daga bisani ta samu wani riga da skirt masu kyau na wani yadin material kalar sky blue, ta daura dankwalin ta a gaban goshi ya zauna dasss kamar hula,skirt d'in da ta sanya kuwa ya matse mata qugu da kyau irin yanda take so ya zauna das a jikin ta ko alamar space babu, ga rigar qarama ce sosai itama a d'ame da fatar jikin ta,qirjin ta kamar zasu fasa ihu su fashe saboda yanda ta matso su, turaren ta ta dauka ta hau fesawa kamar bata so,sai tauna cingam take yi yana qara, yar qaramar lalitar ta ta d'aura wadda ta samo a gwanjo mai hoton biri a jiki mai laushi ta na kammala shirin ta ta fito tsakar gida ta na hura hanci sai ka rantse wani wajen zata mai mahimmanci ba wai tallan abinci ba, ta na fitowa kuwa nan da nan kallo ya dawo kan ta, tin tana fesa turare kowa ke Allah-Allah ta fito, mazan zauren can waje har leqowa suke saboda sun san ta kusan fitowa.
Da wani irin taku dai-dai ta qarasa fitowa tsakiyar tsakar gidan, sabon takalmin roba daya dace da kayan ta Ramai ta cire a leda ta watsa mata gaban ta ta na murmushin jin daɗi tare da alfaharin wannan kyakkyawar 'yar ta ta ce, aiko cike da murna Jameelah ta saka takalman tana murmushi Itama.
Abincin da take saidawa a soro na biyu an riga an girke mata shi ita kawai ake jira, maza kuwa sai layi suke yi suna ta yi wa junan su rashin mutunci duk saboda ita, masu hankalin su wanda da gaske siyan abinci ke kawo su ci su tafi ne ke masu nasiha akan su bar yin faɗa kowa zai samu tunda ba su kaɗai ke saida abinci a gidan ba.
Tana zuwa ta wani d'aure fuska ta zauna a kujerar da in ta zauna akai take jin kan ta kamar a office take, nan take ta kalli Babawo ta sakar masa murmushi, shima murmushi ya sakar mata da kyakkyawan haqoran shi da suka rine da hayaqin sigari,gira ya daga mata ta sake sakin wani sabon murmushin.
Nan da nan ta fara zuba masa abincin sa, wanda baya bata kud'in a wajen sai da dare in ya zo zance a nan ya cake mata kudin ta,banza tayi ma masu kiran sunan ta ta je har gaban shi ta aje masa, sannan ta juya tana kad'a mazaunan ta Babawo ji yayi kamar ya ture mutanen dake wajen ya riqe ta tsam a jikin shi,wani ihu ya kurma sannan ya ce,
"Allah ya kaimu dare,bu.....ub....nan kayyasa"
Abincin ya ja gaban shi ya dau spoon yana ci yana santi tare da kallon ta, haka tai ta zuba abinci tare da masu taimaka mata tana masifa kamar wadda take basu kyauta,wasu kuma da ta san suna bar mata canji in sun sai abinci sai ta washe masu baki har da fari, su na sane suke bada dubu ɗaya su ce a yi masu had'in ɗari biyu ko uku su bar mata canji, wasu ma dubu biyu zasu dunqule su bayar ta zuba masu na dari uku suce ta riqe sauran tsabar rashin sanin ciwon kai dan kuwa da damar su ma masu aure ne sun baro gida ba na cefane amma suna kashe wa wadda bata da lokacin su kuɗi.
(Sun baro halal din su sun taho su na yaba haramun,matan su da yara a gida kuwa ko za su wanke kan su a inji ba sa burge su, wannan ta wajen da ba halalin su bace shaid'an ya qawata masu ita su na ganin ta ma fi matan su na aure kyau,sannan ita ta fi cancanta su yi wa kyautar kud'in da zai iya ci da iyalan su.)
Baban ta ne ya zo zai shige gida yana takaicin yanda d'iyar cikin shi ke wannan sana'a da ya hana ya hana amma anqi ji, ya tabbata tinda ya ganta da wuri haka, ko dai bata je makaranta ba ko kuma ta gudo, dole dai akwai dalilin dawowar ta ta da wuri.
Rasa hanyar wucewa ya yi dan kuwa cikin gidan ma kan shi maza da mata ne a cakud'e ana ta hada-hada, ji yayi ba zai iya zaman awa ɗaya bama a gidan, dan haka sai ya fidda dubu ɗaya ya bawa Ramai yace ta qulle masa abincin sa a leda zai koma can wajen aikin shi yaci, aiko ba godi bare na gode ta amshe,haka rayuwar ta take sam bata san meye godiya ba ita, dan haka baya ganewa idan ya kyautata mata shin ta ji daɗin abu ko akasin hakan
Zuba masa tayi a ledar ko arziqin kwano bai samu ba a matsayin sa na mai gidan ta miqa masa, ya ko sa kai ya bar gidan yana zuwa soron ya jiyo muryar Jameelah ta na ihun sai an cake mata kudin ta casss ba za ta yarda ba,sai wani fari take yi tana zaro idanu waje.
Ganin yanda ta cukuikuye ɗan barno yasa Baban ta daka mata tsawa, sannan yace masa ya tafi ba tare da ya biya kuɗin ba, Cike da rashin kunya haɗe da tsoro-tsoro tace wa Ɗan borno,
"Zaka dawo zaka ga ni indai a waje na ne ba zaka sake cin abinci ba, kuma dik inda na ga kuɗi a wajen ka sai na k'wace,"
"Allah ya shirya min ke jameela,"
Shi ne kawai abinda Malam Jameel ya iya furtawa cikin takaici ya wuce wajen sana'ar shi, ita kuwa haka ta ci gaba da banbamin faɗa tana bada abincin ta.
Sai wajen huɗu na yamma suka tashi daga wajen saida abincin, da wuri abincin ta ya ke qarewa amma bata shiga gida da wuri anan zata zauna har huɗun ko biyar na yamma,zama take su yi ta wasa da mazan wajen da ita da Mamalo da sauran yaran matan gidan da sunan amso kwanuka da kud'in abincin su.
Wata ma direct a mazaunan ta namiji zai d'aka mata duka sannan a bata kud'in tana dariya tana fad'in "kaaabaaariiii" wanda bai kai zuci ba.
Bayan sun gama sai su ka shiga wajen iyayen nasu suka miqa kudin da su ka yo a ranar,gidan ya yi dan dama duk an tattafi sai masu naci da masu siyan kwantan abinci wajen wanda suka yi kwantai, Mamalo da Jameela ne zaune suna tatauna yanda za su yi wankan yau.
"Kin san me? Yau mu qure wa wanka laya, yaran layin can wai har damu suke takara, atampar da kika saka rannan ta wajen Babawo shi wai Saudatun qasan layi ta sa itama shekaran jiya,ya kamata mu shiga kasuwa fa saboda gaskiya kayan mu sunyi qasa.
"Dan Allah fa? Rabu da 'yan wahala kin ji Mamalo duk abin su ba za su taɓa kamo ni gayu ba sai na wuce su biyo baya na ni ce zan dinga raba wa 'yan hassada aiki ba biyan albashi, amma rabu da ita yau zata sha mamaki ,dan kuwa kayan da zan saka kowa bai sanni da su ba ma, zata san dani take gasa a layin nan, sai na gasa ta sosai kamar aya,"
"Shi yasa kike burgeni tawan, ni kam ko aramin wanda ki ka saka waccan juma'ar kiyi dan Allah, sai na shirya a d'akin ku, kin san Lantai matsala ne da ita ba zata barni ba(kun ji 'yar zamani mai zamammiyar qeya ko?)
"Kar ki damu Mamalo kema leshi zan ara maki ki saka yau,ni wannan da zan saka yau kuɗi na tara na siya na kai ɗinki jiya na amso, yau kuma zan buga abuna na ji shegiyar da zata faɗan maganar banza,"
Su na gama tattaunawa suka sallami juna kowa ta wuce d'akin su, ta na shiga ta cire kayan jikin ta dan ta na so ta huta kafin magariba a yi shirin fita zance kuma,ta na nan kwance ba tare da ta tuna bata yi azahar ko la'asar ba ta hau rera dik wata waqa da ta zo mata a kan ta, (kanta baya ja wajen hadda amma yana ja wajen waqa Jameelah ta daban ce)
A haka bacci mai daɗin gaske ya sace ta, kamar wadda aka kwad'awa mari haka ta miqe a firgice a zato na ma tunawa ta yi da bata yi sallah ba sai na ga ta miqe tsaye ta hau sauya doguwar rigar da ta saka kafin ta kwanta zuwa wani lace ruwan zuma farar saqa mai guntun hannu da fad'in qirji, rigar guntuwa ce dan kuwa da zata ɗan d'aga hannun ta sama ba abinda zai hana a ga cibiyar ta,skirt ɗin rigar ta saka matsattse sosai,sai ta qasa ya bude sosai,ta kafe kan nan da d'auri mai kyau,ga kwalliyar ta nan bata goge ba, Jameelah saboda son gayu na musamman ta sai kayan kwalliya masu tsada irin wanda ake amfani da su a saloon,ta yi hakan ne dan ta nuna wa sa'annin ta ba ɗaya suke ba, da ta yi kwalliya za ka gane da kayan kwalliya masu tsada ta ke amfani, lokuta da dama idan za a yi aure ma har baiwa qawaye aro take yi dan ta nuna masu sune a qasan ta ita ta wuce ajin su.
Mayafi siriri ta yafa a kafad'a ɗaya ta saka takalmin ta kalar mayafin, tana wani shan qamshi tare da tauna mutumin nata wato cingam, kudi ta Karb'a wajen Ramai tace zata siyo abinda zata ci yunwa take ji, cike da washe baki Ramai ta ce,
"Ga shi, mai nemowa ai in baya ci yana qoshi wataran sai an nemo shi, sai kin dawo,"
Jameelah na fita tsakar gida ta ɗauki buta ta kurkure bakin ta sannan ta hau kwala wa Mamalo kira,
"MAMALOOO ! idan baki fito ba zan wucewa ta fa,"
Karkad'a jiki take yi ita a dole ta makara kamar wata wadda zata je wata ma'aikatar.
Can sai ga Mamalo ta fito sanye da wata shadda da ta ɗan sha wanki, amma ta amshe ta ba laifi tayi kyau sosai itama dai-dai kyaun ta,
"Kin ari kaya a waje na me yasa baki saka su ba? ko 'yan baqin cikin iyayen naki sun hana ki sakawa ne? Dama ni dan ki kankaro wa kan ki mutunci ne yasa nake ara maki, ki qure wanka kema a gan mu ba raini amma tunda sun hana sai mu jera kowa ya kalle ki kamar wata mai aiki na,muje ya na iya,"
Mamalo ta muzanta sosai dan bata ji daɗin abinda Jameelah ta yi mata a tsakar gida ba kowa na ji da gani, amma haka suka ɗauki hanyar zuwa shagunan da ake saida kayan kwalama irin su shawarma da gasasshen kifi da meat pie da sauran su.
Su na isa Jameelah ta shiga wani sanannen shago a wajen haka ta hau nuna abinci kala-kala sai ta yi wani fariiii farrrr da idanu tare da lanqwasa harshe tana kad'a qirjin da ba ta gama rufewa dika ba tare da yatsina ta tambayi farashi,a haka suka gama siyayyar su a wajen suka faɗa wani shago da ake saida qananan kaya nan ma ta sai abinda za ta siya suka ɗauki hanyar komawa gida mai nisa, dan bata so su isa gida da wuri,ta hanyar makarantar su suka bi har an tashi yara kowa ya wuce gidan su sai qalilan da ɗaukan su ake yi su na zaune a waje ɗaya su na jiran iyayen su dan kuwa magariba ta gabato, su na isa layin su ta qarasa cire siririn mayafin da ke kafadar ta ta hau jujjuya shi a hannun ta ta na wani juyi da jikin ta ta na lilo da ledar hannun ta,a dai-dai inda suke zama su yi zance ta ga Babawo babu b'ata lokaci kuwa ta tsaya a wajen suka zauna, Baban ta kuwa na tsaye a qofar gida dan bai jima da dawowa ba ya ga qofar gidan da duhu wanda ya san ya saka k'wan fitila shekaran jiya da safe amma gashi yau ma har an samu wanda ya fashe shi, sai duba wajen k'wan lantarkin gidan yake yi yana mamakin kusan koda yaushe in ya saka k'wai a wajen sai an samu mai fashe shi, amma har yau ba a kama me aikatawa ba ya na gama dubawa ya shige gida ba tare da ya san ya baro 'yar shi a bayan shi ba.
Zaune suke su na ta hirar soyayya abun su Mamalo ma na tsaye tana masu hira itama, anan suka cinye abinda suka siyo ta duba sabuwar shimi da panties ɗin da ta siyo a gaban Babawo ko kunya bata ji shi kuwa sai yabawa yake yi tare da fatan watarana ya siyo mata wanda suka fisu kyau ta saka a gaban shi ya gani,suna gama ganin kayan Babawo ya fiddo naman daya siyo mata suka hau ci.
Kafin a kira sallar isha'i naga 'yan mata na ta fitowa cikin wanka da kwalliya kamar ana wani kwarya-kwaryan biki a layin cike da mamaki na buɗe baki ina bin su da kallo.......... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻. MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH