PAGE 4
by @1239900
kamar kullum yauwa da safe haka Jameelah ta tashi ta kammala dik wani shiri data saba yi ta shirya dan zuwa makaranta, tare da qudirin yau zata sai dik abinda take so a lokacin break,idan ya so daga baya sai ta sanar ma da Umaimah tana son ta bita gidan su ranar juma'a, so take dai sai ta ga gidan su Umaimah hankalin ta zai iya kwanciya, babbar motar da ake kawo ta ake ɗaukan ta na matuqar girgiza ma Jameela zuciya, ga irin cimar da take kawo masu makaranta kullum kala-kala na sake tabbatar mata da su Umaimah masu kuɗi ne,dan kuwa haka take zuwa musu da kaji a cikin abincin su suci har su qoshi, sannan wataran ruwan roba take zuwa da su gora biyu zuwa uku, ga kudi da bai gaza dari biyu ba ita ko hamsin in ba ta zara a na abinci ba ba mai bata.
Karatu ake ta zabgawa a ajin nasu ko da ta isa,kowa ya maida hankalin akan abinda ake koyarwa banda Umaimah wadda ta tattara hankalin ta gaba ɗaya akan qirjin Jameela, wanda a ran ta take matuqar mamakin cikar su, a iya tinanin ta shekarun su daya amma ita da tafi Jameelah girman jiki bata da cikar girji irin na Jameelan, ikon Allah kawai take ta kalla.
Kamar daga sama ta ji muryar Jameelan, cikin kare baki dan kar a gan su ta ce;
"Yaushe wai zaki kai ni gidan ku ne? Ko dai baki son naje cin arziqi nima? Lallai Umaimah ban taba sanin ke marowaciya bace sai yau, ashe dik abinda ki ke ban a iya nan ne ba zaki iya gayyata ta gidan ku ba? Himmm duniya kenan, yau da ace nima 'yar wani ce da tini kin gayyace ni, shike nan, na gane irin zaman da zan nayi dake daga yau,"
Cike da mamakin yanke hukuncin da Jameela tayi a kan ta take kallon ta,
"Kinyi kid'an ki kin yi rawar ki,kin taɓa ji nace bana son na kai ki gidan mu, Kawai daga fara magana sai ki qarasa ta da kan ki? Ni ba wai bana son kai ki gidan mu bane,halayen da kike yi ne bana so,haka kawai na je na kai ki gidan mu ki jamin faɗa, gaskiya shine dai matsala ta dake"
"Indai wannan ne matsalar ki an kauda ita,yanzu yaushe zaki kai ni?"
"Ko rannn.... wayyoo Allah malam,"
Saukar bulala ce da ihun Jameelah ya karad'e wajen, nan da nan kuwa Umaimah ta nutsu ta shiga hankalin ta saboda tasan dukan akan ta zai qare daga qarshe, dan kuwa Jameelah ta riga da ta jawo mata duka, shirun da ta ji ne ya tabbatar mata ita ba za a dake ta ba.
Qunquni Jameela take tayi ta na fad'in,
"Yarinya ba dan ina son naje gidan ku ba ko dan na bada labari kuma na ci daɗi nima da sai na fanshe dukan nan a jikin ki yau,"
Bayan an tashi break, Mamalo ta ce ma Jameela,
"Qawa zo muje ki ji, ki yi sauri akwai labari, na jira ki mu taho aka ce ai kin yi gaba,"
"Ban na sha mutuniya ta, nima ki ji nawa,"
Nan kowaccen su ta faɗa ma 'yar uwarta yanda suka yi da saurayin ta, cike da zumud'in jin qarshen yanda Babawo ke ma Jameela wasanni Mamalo ke kallon ta, sai da ta gama ji ta d'akko dubun ta ta nuna wa Jameelah, aiko Jameela na gani ta ce,
"Yauwaaa ya kamata ki fara tarin kudin ankon Furairah, kinga kar azo baki dashi, dan ke ba kullum kike samu ba,"
"Waya fada maki? Ai yanzu Sadeeq yace ina fada masa komai nake so, kuma zai dinga ban dubu daya kullum, amma kin san meke damuna? Ni nafi son muna irin soyayyar ku, amma shi kwata-kwata ya qi ya na abu kamar wani baqauye"
"Wai me kuke ta tattaunawa ne haka? Kunyi shiru, ko kuna bitar karatun dazu ne,"
Wata harara Mamalo ta watsa wa Umaimah da ta matsa kusa da su, Mamalo na jin kishin yanda yanzu Jameela ke qawance da Umaimah sosai,cikin washe baki Jameelah ta ce wa Umaimah,
"Babu komai zauna muyi hirar dake,"
Bayan sun gama hirar su suka hau cin abincin su Umaimah, daga nan suka je wajen yin break suka dinga siye-siyen kayan kwalama da abinci, a wannan ranar sai da suka ci suka yi nak sannan suka koma aji.
Lokacin da aka tashi kowa sai ya tafi gida,cike da zumud'in zuwa gidan su Umaimah Jameelah ta koma gida, dan haka tin a ranar ta ware kayan da zata saka dik randa zata je gidan su Umaimahn, kaya ne masu kyau da tsada ta ɗauka ta ajiye a saman jakar kayan ta,dama ita ta na tanadin irin kayan fita unguwa na ba raini ɗin nan da kud'in talla ko na samari take siyan irin kayayyakin, tare da taimakon Ramai za a mata dinkin na garari dan kuwa watarana ma Ramai ce da kan ta zata kai mata tace wa tela ayi mata dinkin 'yammata da ake yayi dan kuwa 'yar ta ta 'yar zamani ce, haka za a yi mata dinki ko a auna ta dik Ramai na gani, matsattsen dinki daya bayyana kowacce surar ta amma sai Ramai tana jin daɗi har cikin ran ta ta na jin cewar diyar ta kyakkyawa ce da ba kamar ta a layin har ma da layin dake kusa dasu.
Cikin ja da baya ta ke kallon kayan da ta fitar dan zuwa gidan su Umaimah Jameelah ta ce,
"Toooo yanzuuuu ina zan samu hijab babba, mai dan kyau da zai shiga da kayan nan, ina da takalmi da jakar da zan saka 'yar qaramar can dana siyo a gwanjo, kaiii Allah yayiwa gwanjo albarka, gaba daya sai ka siya kai luf a bayan shi, a zaci dama abu na ka ne tin fil azal,Allah dai ya biya masu gwanjoooo, Ramaiiii!"
Ta k'wala wa mahaifiyar ta kira da ke tsakar gida, babu b'ata lokaci kuwa ta amsa kamar ita ce 'yar ba uwa ba.
"Na'ammm 'ya guda ɗaya tamkar zinare ya aka yi?"
Cikin shagwaba da bubbuga qafa da wani yauqi da tasan yana qara mata kyau ta burge dik mai kallon ta take maganar, hakan kuwa na tasiri a zuciyar Ramai sai tana ganin ohhhh ni nake da wannan kyakkyawar d'iya, domin Ramai in ba fari ba gaskiya sai a hankali ce, amma kyau da hasken fata na wajen Baban Jameelah, dik da dai yanayin aikinsa ya sa ya yi duhu.
"Ramaiiii ! kinga wannan qawar tawa Umaimah ce ta gayyacen gidan su ranar juma'a kuma banda hijabin sakawa, dan gidan su gidan Ustazai ne bana son zuwa da mayafi hijabi nake so na saka dan Allah ki ban kuɗi na d'inka hijabiiii, tayi tayi naje gidan su saboda rashin hijabi yasa ban je ba har yau,"
"Me yayi zafi ina da kuɗi kuma kece me nemowar muje ciki na baki"
Da murna a ran ta tabi Ramai suka koma dakin, amma a fuska sai ta nuna kalar shagwab'a da tausayi kar ace dama son amshar kuɗi kawai take yi tunda Ramai ta san halin ta sarai, ba zato babu tsammani suka ji muryar Bukar na fad'in,
"Ni ma Yasin sai an ban wani abu, kullum sai a dinga bata dik abinda take so ni ba me bani, inna sata ace min b'arawo, ai in ba a son yaro ya ɗau abin da ba na shi ba a dinga bashi abu in yace yana so,"
"Sannu ubana, nace sannu ubana, ga ta nan, dube ta daga sama har qasa wa ka taɓa gani me kyau a dik layin nan sama da ita? Amma ba talla take yi ba dan a rufa wa kai asiri? Nan take sai da abinci ta sama mana wannan kud'ad'en da ka sa wa ido, kai ruwan piyawata nace zan dinga baka kaima kana zama qofar gida,da aka yi sau ɗaya ka tattara kud'in kai gaba kasha maro abin ka,to tsoron ka nake yi da zan sake baka kid'i na? Ka fita daga ido na in rufe Bukar, ka iya faɗan min abinda ya zama wajibi iyaye su wa yaran su amma baka iya aikata wanda yara zasu ma iyaye dan suna sama masu kudi ba ko,bar nan kan na ma rotse dan uban ka,"
"Habaa Ramai ko hamsin ki bashi mana ya sai wani abun ko ɗari ce ma haka,"
Dan bata fuska ta yi kafin daga baya ta d'au wata tsohuwar ɗari ta wurga masa, da murna ya dauke yana mata kirari, sai ga baki an washe, ana cewa
"Ja'iri ! sauran a sai sigari kuma, da kudina dai aka sai sigari ban yafe ba,"
Ficewa yayi yana mata dariya, har sholi an sha da kudin ta dan sigari, yafiyar ta ba abinda zata yi masa a ganin shi.
(Ina fatan ko da ban sharhi ba kun fahimci saqon wannan kalaman nata, ta kira shi ja'iri, da damar mutane suna ce ma yara ja'irai wanda ya na nufin 'yan wuta kenan, da wasa ba a sani ba ana kiran yara 'yan wuta, sannan tace ma yaro mara jin magana bata yafe ba, ko sanin amfanin ta bai ba balle yafiyar ta a gare shi, bare har ya kiyaye me tace kar ya halaka,kenan in ya aikata abinda tace masa din Allah zai iya sawa ya qara lalacewa, tinda tace bata yafe ba? Mu kiyaye mu kula da bakunan mu akan yaran mu)
Hijabi mai kyau Jameela ta siyo kalar ja mai shiga sosai, dan kalar atampar ta kenan, so take ta burge sosai, amma dole sai ta nuna ma iyayen Umaimah su talakawa ne dan a tausaya mata, sosai.
******************************
Rana bata qarya sai dai Uwar d'iya taji kunya, yau juma'a kuma yaune ranar da Jameela zata je gidan su Umaimah, da kayan ta ta tafi a jaka, fuskar ta yau ba kwalliya, asalin kyaun ta ya bayyana, sai qamshi take zubawa, haka ta saka uniform ta tafi makaranta sai taunar cingam take yi.
Ta tinama Umaimah zancen binta gidan su da za ta yi yafi sau bakwai, Umaimah dariya tai ta yi mata, daga baya tace,
"Ina sane da wannan ranar Jameela dan kuwa na sanar ma da Mum din mu, ta san da zuwan ki, yau kina da sa'a dan kuwa Dad na nan shi ma, Yah Umar ne ban da tabbas din zaman shi a gida, amma ina fatan ya ga babbar qawa ta shima a yau,"
Tsaki mamalo ta yi dan jin ance ma Jameela itace babbar qawar, cikin jin haushi Jameelah ta kalli Mamalo ta ce,
"Dalla meye na yi wa mutane tsaki? In ba za ki ji hirar mu ba ki bar nan ba wanda ya ajiye ki,"
Washe baki Mamalo tayi ta dafa kafad'ar Jameela, Jameela ta zame hannun Mamalo da ke kafad'ar ta, umaimah kuwa ta gama gano mamalo, dan haka kawai sai ta buɗe Hadith ɗin ta tana bita ta yi masu shiru, Mamalo sai hirar gida take yi masu tana ta zuba qarya, anyi kaza da kaza a d'akin su, Jameela kuwa bata son ai ta bada labarin gida a makaranta yara su gane talaucin su, ana mata kallon babbar yarinya,cikin hasala ta sake cewa Mamalo,
"Dalla ki yi mana shiru, kamar a gidan ku ne kawai ake cin biredi da bota,"
Dariya aka dinga yi wa Mamalo ta yi abin tausayi, ta d'au jakar ta ta koma nesa da su ta fara karatu, Jameela sai kuma ta ji babu daɗi, amma haka ta basar ta ci gaba da manne ma Umaimah.
Drivern su Umaimah ne yazo daukan su ta buɗe mota ta shiga, Jameela data sauya kaya a aji bayan kowa ya fita ta buɗe ɗayan side d'in ta shige, Mamalo na tsaye zuciyar ta baqqirin ji tayi dama ace itama iyayen ta na da kuɗi dan kawai ta burge Jameela, tana son ta da abota sosai, haka ma jameelan amma tafi son umaimah domin kud'in su.
Suna tafe tana ta ganin unguwannin masu kudi tana ta santin gidajen a ran ta, amma a fuska ba zaka taba gane irin son abin duniyar da qaramar yarinya irin ta take ɗauke da shi ba.
Wani qaton gida taga an nufa, iska ta shaqa mai daɗi ba mai warin kwata da sigari da hammata ba na unguwar su, wata kwallar kwad'ayi ce ta taru a idon ta a zuci take roqar Allah daya fito da su daga wancan lungun nasu ya kawo su sarari irin wannan.
"Jameela menene Ko baki son zuwa ne? Ko wani abu ke damun ki,"
Cikin sauri ta buɗe baki tace,
"Ni ce bana son zuwa nan din? Hauka nake da zan ce bana son zuwa irin wannan wajen? Shiga gaba muje ki gani,"
Da sauri ta bi Umaimah, tana sake qarewa kyakkyawan gidan Kallo.
Bayan sun shiga cikin gidan ne Jameelah ta samu qasa gefe da inda Iyayen umaimah suke ta zauna kan ta a qasa take gaida su, sun yi matuqar yabawa da tarbiyyar ta, sun ji daɗi da 'yar su ke da qawa irin Jameelah mai kamun kai da matsuwa, sunyi sunyi ta zauna a kujera amma taqi.
Kayan motsa baki aka kawo mata kala-kala dakin Umaimah saboda ta qi shan ko ruwa a gaban iyayen Umaimahn, tana shiga taga gado babba da kayan alatu irin wanda take mafarkin mallaka a d'akin ta a matsayin ta na budurwa me tashe, ji tayi kamar kar ta koma gidan su, zama ta yi a kan gado, ta yi juyi ta sake juyawa, can kuma ta kwanta ta yi lamooo, daga baya ta miqe da sauri ta sauka qasa ta hau cin abubuwan da aka kawo mata ba qaqqautawa, Umaimah na ta yi mata dariya.
Allah Allah take Umaimah ta dan fita ta kwashi lemukan ta sa a jaka, amma umaimah ta gano ta sai tace,
"Kar ki damu qawata kici wannan, in zaki tafi gida zan baki wasu,"
"Dan Allah? Yanzu kuna da irin wannan da yawa kenan? Ai kuwa zan din ga kawo maku ziyara akai akai,"
Dariya Umaimah ta dinga kwasa wajen Jameela.
Suna zaune mai aiki tayi kiran su akan suje a ci abinci cike da zukud'i Jameelah ta miqe, sai bayan ta yi gaba sai ta tsaya sai da Umaimah ta wuce sannan ta bi bayan ta, a table ta gan su zaune, kasa qarasa wa ta yi saboda sumar da tayi a tsaye a wajen, jiri ne taji yana d'iban ta, hankalin ta ya kai qololuwa wajen karkata wajen table din da abinda ke tattare da shi, Umaimah na taba ta dan su yi gaba taji ta taho mata gaba ɗaya kamar zata faɗi, da kyar ta tsaida kan ta ta samarwa kan ta natsuwa, qafa ta daga zata yi tafiya amma taji ta mata nauyi, idon ta kuwa ko qiftashi bata yi dan gani take kamar da ta qifta shikenan ta daina ganin abinda ke gaban ta da ya fi komai kyau a idanun ta da zuciyar ta............ [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH