PAGE 3
by @1239900
Wasu 'yan matan tabarmi na ga suna shimfidawa wasu kuma sallaya, wasu kuwa kujerun zaman gida('yar tsugunno) suka dasa guda biyu su ka zauna da samarin nasu, Mamalo na ɗaya daga cikin wanda suka shimfid'a tabarmi domin kuwa saurayin ta Sadeeq mutumin kirki ne yana matuqar son ta auren ta yake son yi, dan ma iyayen ta sun tsaya masu wala-wala da tini ya turo, daya sako maganar aure sai Lantai tace nawa ma Mamalon take? dika-dika shekarar ta sha biyar, me zai tsinta a wajen ta? Dole haka Sadeeq ke hakura ya bar maganar ya yi ta fata da addu'ar Allah ya kai su lokacin da zata qara girma ta kai aure ya aure ta su yi zaman aure.
Qarfe 9: 45 na dare baka jin maganar kowa sai mutsu-mutsu da 'yan dareraiku sama-sama a wajen 'yan mata da samarin layin su Jameelah, soyayyar shan minti kawai ake zubawa a lungun nasu, Jameela da Babawo kamar zasu shige cikin junan su tsabar mannuwa da suka yi da juna,ba qaramin jin daɗin rigar da tasaka mai faɗi wadda ake kira da ziro hannun ka masoyi Babawo ya ji ba, hannun sa ya zura ya na ta zare idanu kamar ya biya sadakin ta.
Mamalo kuwa ran ta in yayi dubu ya baci saboda Sadeeq ba abinda yake yi mata da ya wuce wa'azi akan abubuwan da ya ke ganin matan layin na su na aikatawa, juya kai tayi ta yi fari farrr da ido sannan ta murguda baki tare da sakin siririn tsaki sannan ta ce,
"Wai kai dan Allah Sadeeq yaushe zaka waye ne? Ka duba fa ka gani kowa sai jin daɗin shi yake yi, amma kai ka wani qame a gefe wai kai ustaz, ka mori quriciyar ka tin kafin tsufa ya riske ka,haba malam ! A yi mutum gaba ɗaya shi bai san mene ne soyayya ba? ko dan kalaman nan na soyayya ni baka jiqa ni da su, ko irin yanda saurayi ke fad'awa budurwa yanda yake ji game da ita da yanda zai mata bayan sunyi aure kai baka iya ba, gaskiya ni da sake,ba zan dauka ba, ka waye kawai mu mori rayuwar mu,"
Sadeeq baki sake yake kallon ta a qalla ya bata kyawawan shekaru takwas amma yarinyar nan bata ji nauyin sa ba ta rufe ido tana fada masa yanda zai gudanar da soyayya, lallai wannan zamanin namu na cikin rud'ani, wa'azi ake yi akan yanda lamura suka tab'arb'are, fadakarwa ake yi amma kamar ba a yi.
"Yanzu dan Allah Fateema abinda kika faɗa bai maki nauyi a bakin ki ba? Ko kunyar faɗa min waɗannan kalaman baki yi ba? Iyayen ki cewa fa suka yi na basu nan da shekara biyu ko uku, ke har yanzu yarinya ce amma shine....."
"A ganin su ba ! ni fa da ka ganni nan ba abinda ban sani ba, in zaka sake jiki muci soyayya ka sake, ba dan ma ina son ka ba ko bi ta kan ka zan yi ne? ina son ka fiye da yanda nake son kaina, kuma bazan iya rayuwa ba kai ba, shi yasa ma kaji ina fada maka me nake so a yanzu, banda haka aje ka zan yi a gefe na nemi wani,"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un ! me kk ce Fateemah ? Kamar ke ki ka iya fad'in zaki aje ni ki nemi wani saboda ba na yi maki muguwar soyayya? Yo muguwar soyayya mana wannan ai ba soyayyar gaskiya ake gudanarwa ba sam,Wai me ki ka dau soyayya ne ma tukunna? Soyayya fa shine na kare maki mutuncin ki ba na zubda maki mutunci ba kafin aure, inna gama tattabe ki a waje me na tanadarwa kai na a gidan? In muka gama soyayya a waje in mun je gidan meye sabo da za mu yi dan debewa kan mu kewar shekarun rayuwar mu da zamu yi a tare? Kiyi tinani, ni kam anyaaaa Fateema.... anyaaaaa?"
"Anyaaa me? Nace Anyaaaa me? Kana kokwanto akaina ne? Bari ka ji ita soyayyar nan dana ke fada maka ba fa wai wani iskanci za mu yi ba,kawai dan simba da runguma ne, ka dubi yanda Jameela suke yi ita da Babawo mana abun nasu gwanin sha'awa, ji dan Allah in muka jera da ita qirjin ta taff da dukiyar fulani, amma ni sai kace allo, gaskiya ni baka kyautamin sai da safe, ba zan zauna in sha sanyin banza da sauro ba ban amfana da komai ba sai shegen wa'azi , sai da safe,"
Cikin fushi ta shige gida bazar bazar, da matuqar mamaki Sadeeq yabi bayan ta da kallo, kanshi yayi mugun d'aurewa da abinda ya faru yanzu, sai tunani yake yi anya sanda bai samu zuwa ba ba wasu samarin dake zuwa su lallatse ta kuwa?
" Aiko da sakel, daga yanzu kullum zan dinga zuwa zance dan ba zan bar wasu banzayen su lalata min ita ba tunda ta na so na kamar yanda nake son ta,"
Tina sanda suka fara haɗuwa da ita yayi, a lokacin sun taso daga islamiyya ita da Jameelah, kula da rashin kamun kai irin na Jameela ne ya sanya bai ce ita yake so ba dik kuwa da kyaun da take dashi, amma yanzu Mamalo na so ta goge masa haddar kan shi, k'wafa ya yi sannan ya ce,
"Dik laifin wannan Jameelan ne, dan komai take yi shi Fateemana take son daukewa, zan yi qoqarin raba su kuwa inshaa Allahu dan na more wa soyayya ta cikin tsafta,"
Muryar Mamalo ya ji cike da tsiwa ta na kad'a qugu a saman kan shi ta ce,
"Wai malam baka tafi bane? Ni to ka tashi zan shiga da tabarma ta,"
Tana wani jijjiga, kallon ta yayi yayi murmushi kawai, hannu ya sa a aljihun shi ya na d'akko abinda zai bata, tana ganin haka jijjigar ta koma rausaya,tana wani abu kamar mai jin kunya, kuɗi ya d'akko a aljihun shi dubu ɗaya sabuwa fill ya miqa mata,cikin sauri kamar zata haɗa da hannun shi ta amshe ta hau godiya,
"Dan Allah ki min alqawarin daina kula dik wani saurayi in ba ni ba,"
"In dai kayi alqawarin kawon kalar wannan kullumm ba wani qato da zan dinga kulawa wannan alqawarin mamalo ne, kasan kuwa bana karya alqawari inna dauke shi,"
"Indai wannan ne kin samu, sai da safe abar qauna ta,"
D'aga masa hannu tayi suka yi sallama ta nad'e tabarmar ta, zata shige gida kenan ta kalli dai-dai inda su Jameelah suke a duhun, dariya ta ji suna yi qasa-qasa, hankalin ta ta tattara gaba ɗaya tare da qura ido qurr, Jameela ce kaɗai take iya hangota, Babawo kam bata ga ina yake ba ma a wajen sai dai tabbas ta san su biyu ne a wajen,haka ta dinga gwale ido ko zata iya ganin shi amma bata gan shi ba, a zaton ta ko ya tafi ma, dan haka kawai sai ta ɗauki hanyar yin wajen Jameelan, da sauri Babawo ya miqe daga qasan Jameela daya shige, ita kuma taja skirt ɗin ta ta rufe qafar ta ta na b'ata rai,cikin masifa ta ce wa Mamalo,
"Meye zaki zo ki wani tsaya mana akai,"
"Wayyoo kuyi hakuri dama da ban ga Babawo ba na zaci ya tafi ne, sai da safe a ci soyayya lafiya, na baki labarin gobe,"
Can qasan maqoshin ta Jameela ta amsa ta, tana tafiya Babawo ya maida kan shi inda ya fito.
Sai da ya kai wajen minti goma sannan ya fito suna ta dariyar jin daɗi, kudi ya debo canji-canji kimanin dubu biyu, ta tsaya tana kallon shi a ranta tace,
'matsiyacin banza kawai kullum sai dai ya zo ya ji daɗi dani amma ba wani kudin arziqi da yake bani'
A zahiri kuwa sai ta kyab'e baki ta ce,
"Nawa ne nan kuma? Kasan na tsani canji-canjin nan ko?"
"Sorry babyna dubu biyu ne fa shine kike bata rai? canjin ne kawai amma ai yafi na kullum yawa yau ko?"
Ɗan sake fuska tayi ta zaci yauma dubun ce, ahhh lallai dole ne ta d'agawa Mamalo kai dan a da kullum ya zo dubu ce ko dubu da dari biyar, to yau gashi an samu ci gaba.
Haske ne ya bayyana ya haske masu idanu daga ita har Babawon,daga baya hasken ya tsaya akan Jameela, mahaifin ta baya son ya daga murya aji yana magana da d'iyar ta shi,dan haka sai ya dinga haska ta yana kada fitilar.
Cike da zumb'ura baki ta tashi tana doka qafa, Babawo kuwa da sauri ya bar wajen yana kare fuskar shi.
Kewaye baban ta tayi ta shige gidan nasu wanda Soron cike yake da yaran gidan samari, suna ta bacci, haskawa yayi ko zai ga Bukar a wajen kwanciyar shi amma ba Bukar ba labarin shi, kad'a kai yayi yana nemawa yaran shi shiriya a wajen Allah, baya taba zagin su ko tsine masu, shi dai fatan shi su shiryu.
Har ya sa qafa zai shige dakin su, yaji hayaniya, ana fad'in,
"Dalla kar ka fad'o min a ka ni, kayi can ga shimfidar ka can Ramai ta yi maka,"
Bukar kuwa sai hayaniya yake yi irin na 'yan shaye-shaye, dan kuwa ba mai gane me yake faɗa, fari tasss aka haife shi kamar Jameela, amma saboda shaye-shaye ya koma baqi, musamman bakin shi da hannayen shi.
Dika-dika shekarar Bukar sha Uku amma ba irin iskanci da dabar su basu saka shi yi, dan yana qarami da shi suke amfani ya je ya masu 'yan qananun sata,sannan ya yi masu aiken siyan kayan maye, daga nan har ya fara sha shima.
Kad'a kai Baban su jameela yayi ya qarasa shigewa d'akin su dan kuwa ba zai je kallon takaici ba, tinda ya dawo gida to Alhamdu lilLAAH.
Ya na shiga ya doki qafar ta ta tashi tana gantsaro girji tare da yin hamma,
"Malam lafiya ka ke tashi na da wannan tsohon daren? Kasan nayi aiki na gaji fa gashi gobe ma zan ci gaba da aiki kamar kullum, in ban bacci da wuri ba kasan bana samun jin daɗin yin aiki na,"
"Yi hakuri dan tashi ki duban lokaci a agogon nan,"
Wani haushi ne ya kama ta, agogon ne bai iya ba ko me?
Cikin fushi ta kalla tace.
"Qarfe sha daya da rabi na dare mana baka iya agogon bane ko me?"
"Yauwaaa alhamdulillah kema kin faɗa da tsohon daren nan, sannan kin ce qarshe 11 na dare,to a tsohon daren sai yanzu yaran ki ke dawowa daga waje daga macen har namijin, ya kamata kenan? Haba Ramai, yarannan fa amana ce Allah ya bamu a hannun mu fa, Allah ya aminta damu fa kenan tunda har ya azurta mu da yara dan mu kula da su mu basu tarbiyya mai kyau, amma shine ke kike sakaci da basu tarbiyyar,ni dai Allah ya sani ina yin iya bakin qoqari na amma ba ki bani had'in kai, kin kyauta min kenan tsakani da Allah,"
Tin da ya fara maganar ta ji farkon amma qarshen bata san me yake faɗa ba, dan kuwa baccin ta ta koma a zaunen, dan indai ta shi ne kar suyi bacci ayi ta magana akan yaran wanda ita kuwa bata ga abinda suke yi mara kyau ba,ba zata iya matsawa yaran ta ba ta hana su sakewa sammm.
Malam Jameel yaji haushi kuwa matuqa amma haka ya danne, ya bi gadon nasu tare da yin addu'ar bacci ya kwanta sannan ya tofa mata itama, dan bai taba gani tayi ba shi kuma baya gajiya wajen yi mata kafin ya kwanta, cikin dakiya da jure ɓacin ran da yake ji ya ce wa Jameelah,
"Ki rama sallolin da ake bin ki kan ki kwanta dan bana jin ko azahar kin yi, in Allah ya so ya amsa, in bai so ba ya barki da abun ki, Allah ya shirye ku, kuma kiyi addu'ar bacci kafin ki kwanta,"
Cike da zumbura baki ta amsa shi.Fita tayi tayo alwala ta yi zaman ta a kan sallaya tana ta tinanin abin da ya faru ɗazu da Babawo yazo sai murmushi ta ke ta zabgawa tanashafo dik wani sashe na jikin ta daya taba.
'Gaskiya Babawo ya iya soyayya sai kace a indiyan fim'
Sai da ta dad'e a wajen sannan ta miqe ta ninke abin sallan, ta sauya kayan jikin ta zuwa na baccin data siyo a gwanjo, dan ita tana son harkar hutu, ta yi kwanciyar ta a dan bargon da take shimfidawa kalar pink, a rayuwar ta tana son ya zamana tana da d'akin ta na kan ta, ta yi masa ado irin yanda take gani a wayar Babawo a films.
Tsaki ta doka ta sake gyara filon ta mai mugun tauri sannan ta juya wa dakin baya, nan da nan kuwa bacci ya dauke ta...... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH