MAZAUNA GIDA

PAGE 5

by @1239900

Da sauri Jameelah ta ja Umaimah baya cike da in-ina take magana tare da yin nuni da yatsan hannun ta tana Kyafkyafta ido tace,

"Wwaaa... nnee... ne wan can???"

Murmushi Umaimah tayi mai kyau kafin ta bata amsa da cewa,

"Yah Umar kenan dama ina son na nuna masa babbar qawa ta, muje na gabatar dake wajen shi,"

Cikin sauri Jameelah ta hau goge fuskar ta da bayan hijab dinta ta gyara sosai dik Umaimah na kallon ta bata ce komai ba sai murmushi da take yi,cikin wani sabon ladabi daya matuqar bawa Umaimah mamaki suka jera suna tafiya.

"Me yasa kuka koma ne? Ku fa ake jira"

"Mum wai...."

"Na yi fitsari ne,"

Jameelah ta yi saurin katse Umaimah dan kar ta faɗi gaskiyar abinda ya faru,kallon Jameela Umaimah ta yi da sauri itama dan kuwa a gidan nan ba ta tab'a tina sanda taji wani ya yi qarya  ba, waje suka samu a saman jerin kujerun dinning table ɗin nasu, kan Jameela a qasa ta sake gaida iyayen Umaimah, cikin jin daɗin tarbiyyar da take da ita suka amsa, Umar sai zabgawa qanwarshi murmushi yake yi, tare da langab'ar da kai gefe irin na masu shagwab'a Umar ya ce,

"Lallai ma Umynaa wato kin yi sabuwar qawa ne ashe shi yasa ki ka dai na so na ko? Ta kwace min ke,"

Sunkuyar da kai Jameela tayi tare da lumshe kyawawan idon ta dan jin daɗin muryar Umar,cikin ran ta ta ayyana,

'Wayyooo Allah na yau gani ga jarumin maza kenan,Allah kasa sanadin haduwa da wannan gwarzon ne ya kawo ni gidannan'

Ɗan taba ta Umaimah tayi dan kwata-kwata bama ta san me ake yi ba ta tafi duniyar tinani.

"Nanna'am"

"Yah Umr na yi miki magana,"

Kallon shi tayi ta sunkuyar da kai qasa, wani iri yaji azuciyar shi game da ita dan kuwa ta yi matuqar yi masa kyau ba kaɗan ba, a zuciyar shi ya furta,

'Masha'Allah'

Shine abinda Umar yace, a zahiri kuma ya sake maimaita mata tambayar shi inda ya ce mata,

"Cewa nayi meye sunan ki,Umaimah na son riga ki sanar dani sunan naki,"

"Jameelaahhh"

Cikin salo mai ɗaukan hankali tayi magnar, a zahiri ta nuna kamar bata san ma ta yi magana dan jan ra'ayinsa ba.

"Wooow masha Allah Jameelaah nice name, u deserve to be called Jameelaah, naji tace ajin ku daya ko? ashe kema hafiza ce kamar Umynaa....naji daɗin haɗuwa da babbar qawar Umynaa Allah ya sanya albarka a qawancen ku,"

"Ameen"

Itace kalmar da kowa ya fada a wajen, bismilla suka yi kowa ya fara cin abinci, Jameelaa a ran ta sai surutu take yi cikin mita take ayyana.

'Matsalar masu kudi kenan a tashi a hada ku cin abinci a babban teburi tsabar rowa, in ba rowa ba dan kar naci na qoshi da ba sai a bamu mu je can d'akin mu ci hankali kwance ba? ji kaji ma malam yanzu a banza zan barsu'

Ɗan juya ido tayi ta d'ibi shinkafa kadan a spoon ta kai bakin ta, tana taunawa a hankali, kowa a tinanin shi tsabar kamun kai ne ya sa take yin hakan,ganin haka sai Mum ta kiran mai aikin gidan ta ce,

"Kin ga haɗa masu abinci ki kai masu d'akin Umaimah su ci a can, baquwar tamu ta kasa sakewa ta ci abinci da mu"

'Alhamdu lilLAAH kaiii babar su Umaimah na da hangen nesa,yanzu ba sai na ci kaji acan na gyatse abuna ba? habaa da an wani hadani da wannan mai kalar mutanen boyen ta ya abinci zai shigen'

Bayan an kammala haɗa masu abincin an kai masu Umaimah ta kama hannun ta akan su shiga daki su ci, cikin jin kunya ta miqe  basu qarasa shiga ba taji Umar na cewa,

"Gaskiya na ji daɗin ganin qawar Umynaa, tana da hankali da nutsuwa ga kuma kunya, "

"Gaskiya nima na yaba da hankalin yarinyar, ana fadin yaran unguwar basu da tarbiyya gaskiya naga sab'anin hakan akan ta, yarinya kintsattsiya haka? Lallai iyayen ta sun bata kykkyawar tarbiyya,"

"Kwarai kuwa, Allah ya musu albarka to,"

"Ameen dai"

Ai wato suna shiga d'akin Jameela ta yi arba da abincin nan ga lemuka kala biyu kowa da nashi ga nama ga shinkafa da miya da salad, wayyooo ji ta yi kamar bata taba cin kowanne a cikin su ba, zama ta yi ta aje hijabin ta a gefe ta duma hannu ta hau yagar naman tana ci tana santi, tasss ta tashi da abincin bayan Umaimah tace ta qoshi, wata gyatsa ta sake ta hau yi wa Umaimah surutu,

"A gaskiya kuna jin daɗin ku Umaimah, kullum wai haka kuke cin abinci mai daɗi a gidan nan?"

Murmushi kawai Umaimah tayi wa Jameelah,kafin ta yi magana kawai sai Jameela ta fara share hawaye cikin kuka ta ce,

"Allah sarki Ramai na da Babana, na zauna na cika cikina da mai daɗi irin wannan, ko su me suka samu suka ci da rana? Wataqila abincin siyarwar da Ramai ke dan dorawa dan siyarwa shi zasu ci yau, Allah kenan mai yarda ya so, mu muna nema ku kuma kun gama samu,"

Tausayin ta ne mai qarfin gaske ya kama Umaimah da sauri ta rungume ta tana lallashin ta, tare da yi mata alqawarin zata ɗebar mata abincin da taci ta kaiwa iyayen ta,

"In aka gani a gidan ku fa ba za a maki faɗa ba? ai sai su ce na zama makwadaiciya Umaimah,basshi kawai kin san soyayyar dake tsakani na da su ne ya sa na ji sha'awar na gan mu muna ci tare, amma ban fada maki dan ki debar min ba,"

"Na sani kar ki damu, inshaa Allah sai sunci nima hankali na zai kwanta, tashi muje parlour,"

"To ai ni tafiya zan yi ma, da kin barshi kawai,"

A hanyar su ta tafiya parlour suka rabu, Jameelah ta yi parlour Umaimah ta yi hanyar kitchen sanye da zumbulelen hijabi......

*A yi hakuri da wannan na yi busy ne thank you mutanen kwarai da hakuri da ni.* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH