PAGE 7
by @1239900
Sosa kai tayi sannan tace,
"Baba na jima ina so in gyara dik wani halayen da nake yi marasa kyau malamin mu ya yi mana wa'azin daya shigi jikina kuma ya tsoratar dani, sannan Allah ya amsa addu'ar ka akan nema mana shiriya da ka ke yi a kullum ba ka gajiyawa,ana haka shine na nemi izinin Ramai na je gidan wata qawata dan muyi karatun qur'ani ina so na gyara hadda ta,dayake ita qawar tawa tana da hadda sosai dan kuwa ita ke yin na ɗaya cikin mu arba'in da wani abu a ajin mu, muna zuwa sai na ga ashe masu kuɗi ne, shine mukai karatu da zan tafi iyayen ta da ita kan ta suka haɗa min abin arziqi, na qi Karb'a maman ta tace ai dik abokiyar d'iyar ta d'iyar ta ce, shine na amsa yayan ta ya dawo dani gida, kuma maman ta ta qara mana k'warin guiwar yin karatu tare"
Nazari sosai Baban nata yayi ma maganar ta, amma sam bai gano qarya a ciki ba, dan haka fara'a ta bayyana a kyakkyawar fuskar dattijon har ya samu kan shi da fad'in,
"Alhamdu lilLAAH, na gode Allah dana ga wannan rana,Allah ya shirya min dan uwan ki shima ya gyara rayuwar daya tsindima kan shi a ciki yaro qarami amma haka za ki ga yana layi a titi dan lalacewa, Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki da kuma shiriya,"
"Ameeen Babana,"
A haka suka kashe bakin shi, ta dage ta dinga yin duk wani abu da zai tabbatar masa da cewa ta shiryu da gaske kamar yanda ta ce ɗin, shi kuwa baba haka ya saka mata ido dan ya ga ko wani makircin suke qullawa amma har dare bai ga ta je zance ba, dik kuwa da naci irin na Babawo da ya zo har leqawa tsakar gidan ya yi ya hau kiran ta, tana nan rungume da qur'ani ta na jin shi amma ta qi fita.
Washegari da assuba bayan tayi sallahta sai ta d'auki qur'anin ta ta hau karatunta ta nata muraji'a, Baba kam daɗi kamar ya d'aga shi sama haka ya dinga sakin murmushi.
Bayan ta gama karatun ta ta shirya dan zuwa wanka sai ta saka hijab daya rufe mata jiki gaba ɗaya taje tayi yi wankan ta ta dawo tayi shirin zuwa makaranta,a hanya suka hadu da Mamalo,cikin ɗauke kai irin na masu kishin qawancen nan Mamalo ta ce,
"Wai ina ki ka shiga jiya daga zuwa gidan su Umaimah kamar wadda ta yi tafiya wani gari?"
"Ba zaki gane baaa yarinya,nace ba zaki gane baaaaa, amma nan da wani lokaci kaɗan zaki gane komai, yah kin tara kud'in anko muje mu siyo ko ki na nan ba ki da ko sisi?"
"Eh na tara dubu uku da dari biyu,"
"Ba laifi in an tashi muje.mu siya,ke ni har na sai takalmin da zan saka ma jiya,"
"Habaa dai ! lallai ke babba ce qawata,"
Murmushi tayi saboda ita wannan yabon da take samu daga qawayen ta na lungun su yana mugun d'aga mata aji ainun, sai ta dinga jin kamar ita ɗin wata Zahrah Buhari ce.
Bayan sun isa makaranta ne ta samu waje ta zauna a nutse, yi tayi kamar bata ga Umaimah ba ma dan kar ace ita take manne mata, Umaimah bata damu ba ita sai ta zira hannu ta tabo ta, murmushi suka sakar ma juna, sanan suka miqawa muna hannu suka gaisa a mutunce, Umaimah ta ce,
"Ya ki ka je gida jiya? Dik da na san lafiya qlou zaki isa tunda Yah Umar ne ya maida ki,"
"Kwarai kuwa, lafiya qlou na isa gida, dan kuwa Yah umar akwai mutunci,"
"Sosai ma kuwa, sai ma kun saba zaki ga hakan,"
Jameelah murna ce ta kama ta da jin kalmar sabo a tsakanin ta da Umar a ranta ta ke ayyana,
'Wayyyoo Allah ka matso da ranar sabawar mu nan kusa'
A zahiri kuwa sai ta dafe qirji ta zaro idanu waje ta ce,
"Ni Jameelah ni me zai kaini sabawa da namiji kamar Yah Umar? Ai ni din ba ajin shi bace, ko ke ɗin ma dan kina qanwar shi ne amma da sai nace yafi qarfin kula ki bare ni 'yar talaka jikar talakawa"
Murmushi Umaimah ta yi sannan ta ce,
"Mu ba haka muka dauki rayuwar mu ba Jameelah, kuma na tabbata a jiya kin gane hakan da idanun ki,ko Mum sai da tace na gaida ki da safen nan kafin na taho saboda kin burge su, kin shiga ran Mum sosai"
A cikin zuciyar ta ta buga ihu tare da murna ta ayyana,
'Alhamdu lilLAAH uwar mijina na sona'
A zahiri kuwa sai ta ce,
"Allah sarki Mum ba ruwan ta itama, ki gaidan ita sosai in kin koma, kinga karbi haddata kiji min,"
Mamaki ne ya kama Umaimah da Mamalo dake manne da su tana jin tattaunawar tasu,amma dole suka shanye mamakin su dan kuwa gimbiya Jameelah ko a jikin ta sai ta fara zubo karatun qur'anin da ya sake tsunduma duk wani mai sauraron ta a cikin duniyar mamaki,daga qarshe dole Umaimah ta shanye nata mamakin ta kasa kunne ta na sauraran haddar Jameelah wadda ke zubo karatun da murya mai dadin sauraro, sabon malamin su da ya shigo ya ji karatun da take zubawa nan take ya kira ta ya tambayi sunan ta saboda ta burge shi sosai.
Bayan ta sanar da shi ne ya ce ta je ta zauna sannan ya gabatar masu da kanshi a matsayin Malam Haroon, sannan ya nad'a ta matsayin Monitan ajin,nan da nan 'yan aji kuwa akai ta ihu suna kiran ba sa so, wasu daga qawayen ta gudun kar ta ce harda su aka ce ba a son ta su kai ta cewa suna so.
Ko bi ta kan su baiyi ba aka fara karatu, ganin haka yasa Jameela dagewa sosai dan kar ta ji kunya.
Malam Haroon baqi ne kyakkyawa kuma Ustaz dan kuwa wandon shi ma a dage yake ga gemu mai kyau daya kwanta a fuskar shi, yana da gira cikakkiya kamar an zana ta, yana da tsananin tsafta, da kuma ilimin addini, yayi boko amma iyakar shi secondary, daga nan ya ci gaba da maida hankali akan kasuwanci da neman ilimin islama.
Iyayen shi sun rasu daga shi sai yayan shi mai suna Ishaq,Haroon yana zaune ne a gidan yayan na shi wanda ke da mata guda ɗaya, Yah Ishaq yana da kuɗi sosai shi ɗin babban ɗan kasuwa ne, ana saida manyan laces, dogayen riguna, atampopi shaddodi da mayafai a shagunan shi, matar shi Hauwa'u mace ce irin 'yan duniyan nan masu yin abinda suka so a gidan miji ba tare da ya sani ba, Haroon ya san dik wani iskancin da take aikatawa na zuwa wajen bokaye dan mallake ɗan uwan na shi,Hauwa'u na matuqar son Haroon fiye da yanda take son mijin ta Ishaq, a cewar ta Haroon ne mai jini a jika yayan shi dik ya zama sauran basir, yanzu haka Haroon a cikin matsalar matar Yayan nashi Hauwa'u yake, dan kuwa ta ɗana masa tarko akan dole sai ya kusance ta, in ba haka ba zata masa sharrin da sai yayan shi ya kore shi daga gidan, dan haka zaɓi ya na wajen shi yanzu.
Bayan kammala karatu sai ya sa yaran su yi masa addu'a akan Allah ya tseratar da shi daga sharrin dikkan mai sharri ya bashi nasarar tsallake dikkan tarkon maqiya, suna kammala addu'ar Haroon ya raba masu sweet, da zai fita ne ya kira Jameela.
Cikin yanga irin ta ta wadda ta zame mata jiki ta durqusa a gaban shi, kallon ta yake daga tsayen gashin idon ta sun kwanta a fuskar ta, ga wani kwantaccen gashi a saman girar ta mai kyau,cikin muryar shi mai daɗin sauraro ya ce mata,
"Jameela ko?"
"Eh malam,"
"Ko zaki faɗan me yasa 'yan ajin ku basu son a nad'a ki monita?"
Wata a jiyar zuciya ta sauke tare da dafe kan ta, alamar ciwo yake yi mata, ganin haka yasa shi cikin kulawa yace ta miqe tsaye, da sauri kuwa ta miqe, dan durquso ba dabi'ar ta bane.
"Kan ki na ciwo ne,"
"Eh malam"
"Subhanallah, maza to je ki amshi magani a office din malamai, sai ki koma aji, mayi maganar watarana,"
Ta bayan shi ta wuce dafe da goshi, kamar mai tsananin jin ciwon kai,
A ranta kuwa sai masifa take yi...
'Kaji min mutum, kawai dan dai hauka akaina ya qare sai na hau faɗa masa ni ɗin ba marajin magana a kaf makarantar sama dani? ka ji a bakin wasu ni kuma na qarya ta su da aiki na,'
Murmushin mugunta tayi, ta zagaye office din malamai ta koma ajin su, zaman ta tayi bata sake kula kowa ba dan kuwa a qufule take da kowa, 'yan zuwa surutu wajen zaman su sun taru,suna jiran su ji me zata ce game da wannan sabon salon da suka gani a wajen ta,banza tai da su ta d'au qur'ani ta fara hadda,dan kuwa Jameelah bata da aikin yi sai hadda yanzu, tana fatan ta kamo 'yan ajin,lokacin shashashanci ya qare.
**********************
A cikin wata shida Jameela ta gama haddace dik inda aka barta abaya, a yanzu ta iya karatun ta sosai da sosai duk inda aka tab'o a qur'ani da hadith da duk wasu littafan da ake yi masu zata karanto wa mutum tsaf ba kuskure,data zauna a waje sai dai kaji karatu na zuba kamar ruwa, daɗin muryar ta ke qara ma mutane qaimin sauraron ta, gidan su Umaimah kuwa ta je shi yafi ba iyaka.
Yau ma sun gama shiri akan zasu je gidan su umaimah yin karatu,driver na zuwa ta faɗa motar kamar tasu,suna ta hira a haka har suka isa gidan.
Da sallama ta shiga, bakin ta ta washe data ga Mum.
"Mum din mu ina wuni? ya aiki?"
"Lafiya qlou Jameelan Mum, ya maman ki da Baba da Bukar"
"Suna Lafiya qlou alhamdulillahi, Mum akwai wani aikin da zan taya ki ne? Ina Dad?"
Umaimah dake murmushi ta wuce su zuwa d'akin ta dan sabon da Jameela tayi da mum ɗin ta na bata mamaki.
"Daddyn ku ya fita, amma na san suna hanyar dawowa yanzu,"
'Anzo wajen, na tabbata da Yah Umar aka fita yau,'
Abinci ta taya ta suka qarasa dafawa, umaimah ma bayan tayi wanka ta sauya kaya suka qarasa shirya table tare, suna kammalawa kuwa su yah Umar na dawowa,a gajiye suka shiga gidan direct kujera ya samu ya zauna ya na qarewa yarinyar da ke yawan faɗo masa a rai a kome yake yi.
Sake kallon Jameela ya yi wadda kullum yake kasa gane a uniform tafi yin kyau ko kuma a kayan gida ne tafi kyau, itama shi ta ke kallo tana masa murmushin da ta kula yana matuqar qayatar da shi.
"Yaahh Umarr ina yini?"
Sai da ya ji tsigar jikin shi ta miqe, tsabar yanda ta karya murya wajen kiran sunan nashi,
"Lafiya Qanwa ta,"
Wucewa tayi ta koma d'akin su Umaimah, kamar yanda take yi in tazo ta taya Mum aiki sai ta shige ta d'auki karatun ta tayi tayi,hakan ke qara mata babban matsayi a wajen su dika mutanen gidan dan kuwa ko abinci bata ci sai ta kammala haddar ta, dik da mugun kwad'ayin da takan ji dan ganin ta ci abinci kan ta yi karatun, amma tinda akwai motive din yin hakan bata damuwa.
A bakin qofar dakin ya tsaya yana bin ta da kallo, yanda ta cire hijab ta rufe kan ta da shi, ta gaba a bude hakan ya yi masa kyau, Umar kasa ɗauke kan shi yayi daga kallon qirjin ta yana mamakin cikar su, Umaimah ko bra bata sawa saboda ba su da wani girma, amma ita sun cika bra din ta sannan sun cika rigar ta har ana ganin su ta saman V neck din ta,
Wani abu ke masa yawo a jinin jikin shi game da ita, dan haka komawa baya yayi yana sauke numfashi da sauri da sauri.
Sai yamma Jameelah ta kammala isar da saqon zuciyar ta a gidan su Umaimah sannan tace zata tafi, kamar kullum Mum ta bata dubu biyu kudin mota suka yi sallama ta fito dan tafiya gida.
A waje ta gan shi cikin motar shi yana zaune kamar mai jiran wani, yana ganin ta ya fita ya buɗe mata gefen mai zaman banza.
Kallo ta bishi da shi mai matuqar daukan hankalin mai kallon ta, shagala yayi da kallon ta ta shagwabe fuska sannan ta ce,
"Yahhhh Umarrr kallon fa?ko dama dan kayi ta kallona ya sa zaka taimaka ka maida ni?"
Murmushi yayi ya sosa qeyar shi ya zauna a mazaunin driver sannan ya tada motar suka fice daga gidan, a hanya ya samu wani wajen bishiya mai iska ya tsaya, juyawa yayi yana fuskantar ta sannan yace,
"Ina son na maki wata tambaya, tsakani da Allah nake son ki bani amsoshin su,"
"Inshaa Allahu zaka sameni mai gaskiya a dikkn abinda zan amsa maka,"
Umar gyaran murya yayi fuskar shi ba wasa a cikin ta, sannan yace............................
*Allah ya maimaita mana Sallah ta badi mai albarka, Hppy sallah to u all,amin hakuri aikin sallah kun san yanda yake akwai wahala, a ajen naman sallah na zan zo na amsa, sai muyi hakuri da wannan gobe ko dik sanda dai na samu dama mun ji me Yah umar zai tambayaq* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH