MAZAUNA GIDA

PAGE 10

by @1239900

Tunda ya farka yake ta qoqarin kawar da tinanin mafarkin da yayi akan ta amma ya kasa mantawa, har ya gama shiryawa dan zuwa makaranta bai bar tunanin ta ba, daga qarshe sai ya sakar wa zuciyar shi ragamar ci gaba da tunanin ta dan yin hakan shine kawai mafita a gare shi a wannan lokacin.

Yau Aunty Hauwaa har qarfe takwas na safiya ta yi ta na d'aki bata fito ba,saboda kai ya kumbura mata ya yi him ta gaban goshin ta, ga wani azabbben ciwon kai da take ji ta rasa inda za ta saka kan ta ta ji daɗi a ran ta,cikin ran ta take ayyana,

'Ni yaron nan ya tozarta haka,ai kuwa daga daren jiya yayi na qarshe, ko ya biya min buqata ta ko kuma na rusa masu kyakkyawar alaqar dake tsakanin shi da dan uwan shi dani yake zancen in ya san wata bai san wata ba'

Bangaren Haroon kuwa yana zuwa makaranta da ita ya fara tozali, murmushi tayi masa sannan ta sauke kan ta qasa tana kallon qur'anin ta, kafe ta yayi da ido yana tuno mafarkin da yayi da ita, da sauri ya fara korar shaid'an sannan ya buɗe murya ya fara karatun qur'ani, nan da nan kowa ya nutsu suka bashi hankalin su, Jameela ce take tab'o Umaimah wadda hankalin ta gaba ɗaya na kan karatun da ake yi masu.

"Ke Umaimah, dallah tambayar ki zan yi,"

"Dan Allah ki bari a gama mana qari in ya fita sai muyi maganar,"

"Yana da matuqar amfani a wajena"

"Menene haka da ba zai iya jiran malam ya fita ba?"

"Da wannan surutun da kike yi da amsa ki ka bani tini da an wuce wajen,"

Malam Haroon ne ya ce,

"Jameela fito nan,"

"Me nayi?"

Wasu daga daliban ne da sauri suka riqe baki dan jin tambayar da ta yi ma Malam Haroon, malamin da kowa ke girmamawa saboda ba shi da takura kwata-kwata, cike da Mamaki ya kalle ta ya ce,

"Tambaya ta ma me ki ke yi meyasa? OK fito nan in yaso sai na maki bayani,"

Cikin gantsaro girji ta fita gaba ɗaya na shanun ta sai kad'awa suke yi dan ta nuna masa ita fa ta girma tafi qarfin a na wani kiran ta gaban aji ana dizga ta, ɗauke kai yayi daga kallon ta, shaid'an na sake maida idon shi wajen kallon qirjin nata, da sauri ya ɗauke kan shi tare da a'uziyya a cikin ran shi,cikin ranshi yake ayyana,

'Tin jiya na fara jin wannan baqon lamarin akan mata, meke damuna ne haka?'

Ganin ta zo kan shi ta tsaya qerere ne ya sanya shi saurin dakatar da ita ya ce,

"Tsaya can malama, ko kin ji na ce ki zo daf dani kamar zaki fado min akai ne? Ke wai me ya sa baki da tarbiyya ko kaɗan ne? Amma babu komai Zanyi maganin ki yau, faɗa min a wacce sura muke sannan aya ta nawa muka tsaya?"

Tinani ta hau yi ta rasa ina suke kwata-kwata, sai wani qiqqifta ido take ta na d'aga kai sama ita a dole tuna inda suke take son yi,ta kalli wajen su Mamalo da Umaimah dan a taimaka mata da amsa sai motsa baki suke yi ana faɗa mata amma ta kasa ganewa saboda tun asali bata maida hankali ta gane a ina ake ba balle ana faɗa ta gane ta iya furtawa,ganin ta kasa faɗa ne ya sanya ta murgud'a masa baki sannan ta ce,

"To ai ba ni kadai bace nake surutun ai harda Umaimah, ai da ita muke magana sanda ka ganni,"

Umaimah ce ta d'aga kai da sauri tana zaro ido waje jin Jameelah na so ta ja mata duka,dan ita ba a taɓa ma fidda ta gaban allo ba da sunan laifi, tasan ta yi surutu amma bata fatan a hukunta ta akan hakan dan ba da niyya ta yi ba,malam Haroon da ya kalli sashen Umaimah ya ganta a tsorace sannan ya gane Jameelah so take kawai a yi mutuwar kasko dan haka sai ya ce mata,

"Ban gan ta ba ke na gani, ki karanta min surar da muke yanzu ko na saɓa maki,"

In-ina ta fara yi kawai daga qarshe ta hau yi masa wata surar daban, sai da ya bari ta kai qarshe sannan yace a mata kabbara, ya yafe mata tinda a qalla ta iya karatu in yaso sai ya maimaita dan ta gane wajen da suke, sannan ya yi mata warning akan surutun daya ga tana yi, Ko irin godiyar nan bata yi masa ba haka tai komawar ta wajen zaman ta,Kad'a kai yayi tare da furta.

"Allah ya shirya ki Jameela"

Da break kuwa Umaimah yau sai ta haɗe fuska sosai, dan kuwa bata ji daɗin yanda Jameela ta tona mata asiri ba, da an dake ta fa?

"Haba qawalliya rabin duwais, me ne ne wai? Ke baki san wasa ba, na san ba zai taɓa fidda ki ba kawai na fada ne amma kiyi hakuri"

"Kin san dai bana son abinda zai zubda mutunci na ko ya yake,ke kika fara magana bani ba, amma kike son dole sai kin manna min laifin, yanzu to me kike son tambaya ta ɗazu a ajin da ki ke neman ja mana duka a banza?"

"Yauwaaaa, yanzu kuwa zan zayyano maki tambaya ta,"

Zama tayi daf da Umaimah sannan ta ce,

"Dan Allah wace shawara kika ji Mum ta yanke akan komawa ta gidan ku?dan kuwa ina da tsananin sha'awar karatun boko yanzu musamman ma ina so na ji ni ina turanci, kyau na ba zai taɓa haskawa ba in ban waye ba, ba mai kud'in da zai auren a haka na san ga talauci ga jahilci ,habaaa abun sai yayi yawa kuma,"

Baki sake Umaimah ke sauraren ta sai da ta kai aya sannan Umaimah ta ce mata,

"Yan zu ke Jameela har hango ki ki ke yi da aure a wannan shekarun namu? Har hango wanda zaki aura ma kike a idanun ki? Ikon Allah ni kuwa kin ganni ban taɓa hango ni da saurayi ba ma balle aure, ni ban san me ta yanke ba akan maganar gaskiya, sai in na je na tambayar maki ita,"

"Yauwa Ta'umancyna na gode sosai, ke in banda abinki ma yanzu fa muna kusan shekara ta 16 ne fa, sannan ace ba zamuyi tinanin aure ba? ki kalli zubina ki kalli naki mana, kina nan qirji a manne a bra kanar allo ki duba cika ta kin san........"

"In ki naiwa Allah mu bar wannan maganar, shekarun mu basu kai ba,"

Dariya mai qarfi Jameela ke yi wa Umaimah, Mamalo ce ta iso gaban su da awara a leda tana dame ta, zama tayi tare da yi masu bismillah, dan ta san ba me ci a cikin su,musamman Jameela data raina ta.

Cikin dariya Jameela ke yi wa Mamalo bayani, aiko dariya su kai ta yi mata suna nuna mata ita din bata waye ba kuma muguwar baqauyi ya ce sannan yarinya ce qarama, wasu manyan kalamai sukai ta fitowa da su daga bakin su suna faɗi, Umaimah tsoro da mamakin me suke faɗa dik ya kama ta, dan ta kula ba abin alkhairi suke faɗi ba, duba da yanayin da suke yi in zasu faɗa ɗin su maqale murya su kare baki da hijab.

Tashi tayi ta bar masu wajen tana mamakin su, anya ba zasu tabka kuskure ba kuwa ta hanyar gayyatar Jameelah zuwa gidan su? Kaiii da sakel.

***********************

Kusan wata biyu kenan da zuwan Mum dan roqon Baba akan yabar Jameela ta koma wajen su da zama, har yanzu ba su gajiya ba wajen roqon Baban, Jameelah na yi Mum nayi har ma da Dad ɗin su Umaimahn,kowa ya yi amma Baba ya qi amincewa.

Ramai ma tayi masifar har ta gaji tayi lallashin nan ma ya kafe, Jameelah ma ta yi fushi har ta gaji ta sauko, har da yajin cin abinci ta yi a gidan, Baba ko a jikin shi bai ma san ta na yi ba, hakan da take yi ma shi ke qara nesanta zuciyar shi da amince mata ta koma gidan su Umaimahn da zama tunda ba dangin iya balle na baba,kuma shi ba bokon ne baya so ba, ah ah komawar ta can ta ci jar miya anjima tace ba sune iyayen ta ba shine matsalar shi.

"Gaskiya ina ganin Daddyn su Umar ya kamata kawai a gudanar da gabatarwar aure a tsakanin Jameela da Umar, tinda ya nuna min yana tsananin son ta shima, amma bai furta mata kalmar so ba har yanzu saboda ganin makaranta yake yi ita kuma kamar ta yi qanqanta da soyayya, kaga shikenan ya hutar da mu tunanin kar mu tursasa shi yin abinda bai da niyya akai"

"Kwarai da gaske, ina jin ba sai an wani jira Umar ya kammala karatu ba, a auro masa ita kawai  mun sa masu ido mu kula da su, in yaso sai ta fara makaranta kawai anan ai shi ma ba zai bar karatun shi da yake matuqar so ba akan mace,"

Dariya Mum tayi ta shafa qirjin shi,tare da kafe shi da kallon qauna ta ce,

"Daddyn Umar kenan, shin soyayyar ka raina ko macen?"

Shima cikin nishad'i ya kalle ta tare da murmusawa ya ce,

"Ni na isa na raina ɗaya a cikin su, bayan ina amfana da kowaccen su,"

Dariya suka yi cikin jin daɗin yanda dik da girman su suna nuna ma juna soyayya mai kyau da tsafta.

*****************

Mata ne dattijai masu shiga ta alfarma suka nufi gidan su Jameelaah dan kai dukiyar auren ta,sai kuma maza guda uku wanda sune a matsayin wakilan mahaifin Umar, tafe suke motocin su jere da na juna sun yi layi suna  ta hirar su ta zumunci, Umar dake tuqa mazan bakin shi yaqi rufuwa saboda ya san auren gata za a yi masa.

Yamma ce liss matan layin su Jameelaa an firfito ana ta zance da samari, kun dai san ya zancen na su yake gudana.

Jameelaa na manne mattt da Babawo ko masaka tsinke babu a tsakanin su hannun shi na cikin rigar ta,yana yin abinda ya saba a cikin rigar ta ta idan ya shiga, motar su Umar ce ta yanko ta shiga layin ta haske gaban gidan, nan da nan samari da 'yan mata suka h[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻

WRITTEN BY HAERMMAERH