Chapter 7
*RIKICIN DUNIYA...*
©️ Meenat A. 'Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
CHAPTER 07
...Gudu suke tamkar zasu tashi sama. Kayoyi duk sun shige mata kafa, duk sa'in data waiwayo sai ta ga matar da bata san wacece ba ta kusa cimmata. Kara kaimi take tana gudu iyakar karfinta, sai dai kafin ta ankara ta ji anyi jifa da ita ta afka ciki wani rami.
A gigice Nadiya ta mike ilahirin jikinta duk ta haɗa gumi. Wayarta ta lalubo. Karfe shida na safiya, ajiyar zuciya ta sauke tana mai mikewa ilahirin jikinta duk ya mutu.
Wanka tayo ba ita tayi sallar asuba ba sai karfe bakwai na safiya.
Saurin da take su tafi exam Shi ya hana ta sanar da Inna irin mafarkin da tayi, saboda ita dai kam ta tsorata ba kadan ba.
A hanyarta ta zuwa gidansu Wasila nan ta fahimci kudin da ke hannunta sun dauko gangara, ga Kasim ya bullo mata da wata sabuwar ɗabi'a. "Anya yau ba zasu biya gidan Malam bawa ba kuwa?"
Maganar zucin da take yi ce ta kawo karshe sakamakon shiga gidansu Wasila da ta yi.
Nama ta hango anyi farfesun shi ga uban biredi sai faman badago suke yi.
Da yake sai karfe takwas zasu shiga exam, zaunawa ta yi aka zuba mata nata ita da Wasila suka hau ci. Suna ganawa suka fito Nadiya so take ta tambayi Wasila duk wannan abin arzikin daga ina, sai dai yau ita ce rana ta farko da taki tana shakkar tunkararta da wannan maganar. Uwa uba ma kwarjini take yi mata.
"Wasila! Wannan abun arzikin daga ina?"
Dariya Wasila ta yi
"Jiya Baba ya yima wani mutum aikin ɗora dansa daya karye, shi ne fa da kudin da aka sallamesa ya siyo mana abinda kika taras."
"Ko da naji, don nasan baƙin talaucin da kuke ciki ina ku ina cin naman ai sai dai idan wani ne ya siya maku”
Nadiya ta karasa maganar a cikin zuciyarta.
“Hmm! Yaro man kaza. Wato kinga mun fara dangwalar arziki shi ne har kin fara tambaya ko, to kadan kika gani sai ma na shige a gidan Kasim sannan zaki gane Allah da girma ya ke”
Wasila tana karasa maganar zucin tare da tsayar masu da Napep.
Tunda suia shiga lokaci bayan lokaci sai Nadiya ta duba screen din wayarta ko Kasim ya kira amma shuru.
Murmushin mugunta Wasila ta yi a cikin zuciyarta.
“Saboda ke nayi waya da Kasim na sanar da shi bazan fita da waya ba saboda exam, idan na dawo gida zan kirashi. Nadiya a cikin makirci da tuggun da muka shirya miki baki ga komai ba. Ba dai ni kike kira diyar matsiyata ba? Har kina ikirarin in yi duk yadda zanyi in samu mai kudi in aura. Ba tare da sanin mijinki shi ne wanda zan aura ba, dama har can baya zuba miki ido nayi lokaci na baki kiyi ki gama. Kuma kin gama yanzu lokacina ne Nadiya”
Haka aka gama exam din Sam hankalin Nadiya ba a makarantar ya ke ba. Bayan sun fito zasu tafi gida suna tsaye bakin hanya suna jiran Napep, Nadiya so take ta sanar da Wasila halin da ake ciki amma wani tsagi na zuciyarta na gargadinta.
Karfin halin fara magana tayi.
"Kinsan wani abu Wasila?"
"Me ya faru Nadiya?"
"Hmm! Anya aikin Malam Bawa ya ci kuwa?"
"ban gane abin da kuke nufi ba, fada mini me ya faru?"
"Kasim ne duk ya canza mini na rasa gane kansa"
"To! Ikon Allah. Amma kin tabbatar kinyi duk abubuwan da Malam ya ce ayi?"
"Wasila nayi babu abinda banyi ba. Shi ne nake tunanin ko dai daga nan a wuce damu gidan Malam bawa?"
Gaban Wasila faduwa yayi ji da tayi Nadiya na neman ɓallo mata ruwa.
"Aa mu je dai gidanku sai mu yanke shawara a tsanake."
"To shikenan muje"
Kai tsaye gidansu Nadiya aka sauke su. Inna ce kadai cikin gidan Jamila tana makaranta.
Dakinsu Nadiya suka shiga Nadiyar ta fito waje domin nema masu abin da zasu ci.
Wannan ita ce damar da Wasila ta samu ta daukar ɗan kamfam Nafiya. Boye shi tayi cikin jikka zuciyarta cike da farin ciki.
Wake da shinkafa ne ta shigo da shi.
A tare suka ci da Wasila bayan sun gama suka hau tattauna yadda zasu shawo kan matsalar Kasim.
"Gani nake kamar muyi hakuri mu kara bada lokaci ko aikin zai ci nan gaba. Kinsan aikin Malamai ba yankan wuka bane sai a hankali ya ke ci, da dai wani hatsabibin boka ne tsaf sai mu ce to akwai damuwa In aikin bai ci ba kawo yanzu"
"Yanzu kina nufi mu zauna har zuwa wani lokaci sannan in komai bai daidaita ba sai a dauki mataki?"
"kwarai kuwa Nadiya. "
"To shi kenan. Ba damuwa Allah ya shige mana gaba"
Da Amin Wasila ta amsa tana mai mikewa tsaye.
"Ba dai tun yanzu za ki tafi ba?"
"Eh Nadiya ina da wani uzuri ne wallahi"
"Ko sai mun hade gobe kome kenan"
"Ba damuwa Allah ya kai mu" har bakin kofa tayi mata rakiya yau izgili da habaici Nadiya sam babu.
Jikin Inna har ciri ya ke tana jiran dawowar Nadiya. Motsinta da taji ya saka ta kama hannunta tana mai zaunar da ita.
"Shalelen Inna! Me kika aikata haka?"
Da mamaki Nadiya ta kalli Inna "me nayi ni kam?"
"Wauta mana. Ina ji fa kina sanar da waccan shashashar abin da ke faruwa tsakaninki da Kasim, hakan fa tamkar burmawa cikinki wuka ne a kasuwa"
"Inna kin manta ita ce abokiyar zuwa wurin malamin? Banga amfanin boye mata ba."
"Ke yarinya ce, ai babu amfanin fada mata aiki ya ci ko bai ci ba. Idan tana da wani nufi cikin zuciyarta fa"
"Inna kenan. Ni har gobe ban dauki cewa Wasila zata iya zamar mini abokiyar gaba ba. Suna fama da kansu ina ta ga lokacin kulla makirci"
"Haka dai kike gani. Amma ni yau sam na kasa yarda da yarinyar nan gani nake kamar akwai abin da take boyewa a cikin jikkarta, amma ke na ga sam baki fahimta ba. Sakaci da rena allura da kika yi ya saka kin kasa gane ita ma karfe ce. Ina so ki shirya gobe kafata ƙafarki zamu je wurin Malam Bawa, ke yau nake so muke ma In an jima"
"To babu damuwa Allah ya kaimu"
Da haka suka wasar da zancen amma sam hankalin Inna ya kasa kwanciya.
Gidansu Wasila
Da farin cikinta ta shiga gidan "tunda na hangoki na tabbatar da anyi nasara" Umma ta karasa maganar tana murmushi
"Sosai kuwa. Na samoshi yaushe zamu kai masa saboda ya ce da wuri yake son shi."
"da kinci abinci zamu je saboda ba a bori da sanyin guiwa"
Malam Ɗayyabu daya gama jin labarin abinda ya faru a bakin matarsa washe baki ya yi. "Kaga haihuwa mai rana, jikina ya jima ya na bani ke din nan hannun jari ce Allah ya bani. Hausawa suka ce da haihuwar yuyu ƙara ɗa ɗaya kwakkwara"
Dariya Wasila ta yi. "Nasha fada maku zamu yi arziki. Yanzu dai Umma jeki shirya mu tafi"
"Nima fa tafiyar nan kamar dani za kuyi ta. Kara in je in genewa idona abinda ke faruwa"
Wasila da Umma kallon juna suka yi. "Malam! Wace irin lalacewa ce zaka bimu wurin Malamin tsubbu. Ni dai ka rufa mana asiri."
"To naji yanzu dai ku je ku dawo ina nan ba inda zan fita ina dakinku"
Sama-sama ta ci abincin suka nufi gidan Malam Bawa.
Wando ya amsa yana jujjuya shi tare da babbakewa da dariyar mugunta...
Meenat A. 'Yandoma
***