CHAPTER 7
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 7.*
"Samha kin ga abin da nake gaya miki akan yarinyar nan ko ? Wallahi ta fara canza wa. Idanuwanta sun buɗe Ita ma yanzu tana kama manyan kuɗaɗe dole ta fara yin duk abin da ranta yaso kai tsaye ba tare data nemi jin naki ra'ayin ba."
Cikin tsananin fushi Samha tace" Mummy nima tunanin da nake kenan, Jidda ta fara canza min ba kamar da ba. Ada duk wani kamun da tayi sai ta sanar mun, sannan kafin kafarta ya taka wuri sai ta fara neman izini na amma yanzu kai tsaye take yin abubuwan ta yadda kika san zaman kanta take, well in so take in sallameta ayanzu zata iya rik'e kanta ai sai ta gaya min babu dole aciki."
Murmushin takaici Haj. Nafeesa tayi kana tace"Hmm kin manta da halin ɗan adam da ake kira butulu? Sai ka gama jansa daga rana zuwa Inuwa ka rufa masa asiri sannan daga baya kai ya tura ka cikin rana. Ni dai ki bi ahankali da wannan yarinyar naji kina batun ta haɗaki da maneminta kuyi magana. Meye naki na lallai sai kin yi magana dashi ? Shi ya miki laifi ko ita ? To Samha ki taka asannu, na sha faɗa miki ki dinga tuna ke matar aure ce, akwai wasu abubuwa da ya zama dole ki kiyayesu in har kina son zaman lafiya a gidan auren ki. Kar ki kuskura ki ƙure Mijinki don kin ga yana da hakuri kuma ya zuba miki ido kina wataya wa son ran ki."
Samha tace" Shikenan Mummy in sha Allahu Zan kiyaye dama so nake in nuna masa rashin dacewar abunda yake yi, yana shiga haƙƙi na da yawa."
Sosai Haj. Nafeesa ta karanci tsantsar kishin Jidda kwance cikin ƙwayar idanun 'yar tata. Ta lura sam bata k'aunar wani mahaluk'i ya fita samun matsayi da kusanci arayuwar Jidda.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"Ke yanzu baki yi tunanin yana iya bibiyar ki muddin kika sake ya samu lambar ki ba ? Ko kin manta halin ɗan bariki ne ? Babu ruwan shi da auren dake kan ki in har kika kwanta masa arai bibiyar ki zai fara yi musamman in kika samu tantiri na k'arshe kin gama yawo wanda zai iya jawo miki matsala da mijinki."
Samha ta ce"To mummy zan kiyaye in sha Allah."
Haj. Nafeesa ta ci gaba da faɗa"Duk wani abu da zaki yi ki tabbatar kin tsaya iya kan 'MATAN KI, kar ki kuskura ki yarda zuciya ta ɗebe ki ki fara mu'amala da maneman su. Babu ruwan ki dasu naki kawai Matan su su kawo miki kuɗi."
Haj. Nafeesa tayi nisa wajen ingiza 'yar ta ga rayuwar da babu riba. Babu abin da ya dameta duniya kawai tasa gaba.
Basu gama tattaunawa ba tabar gidan babu shiri don masu kai kaya sun addabeta da waya cewa sun isa amma basu samu wanda zai dudduba kayan ba. Daga Jidda har SALA babu wanda aka sama a gida. Hakuri ta basu tace gata nan zuwa da kanta.
Tana cikin mota ne ta sake k'iran Jidda take ce mata tabar batun lamba ba sai ta turo ba amma fa ta kiyaye kar ta kuma tafiya ba tare da saninta ba.
Jidda ta ji wani irin farin ciki ya lulluɓeta. Samha Ke sanar da ita cewa tana hanyar zuwa duba kaya don SALA ma bata nan kuma aikinsu ne.
Jidda ta ce"Uwata ki yi hakuri tabbas na kira SALA ita ma bata gida."
"Ban damu ba tunda na san nema kowanne ya fita yi, kawai haushin dana ji kan mutumin dayake neman sa ki fara min wasa da aiki ne. To, amma ina so ku sani, da ke da SALA zaku rarrashe ni da kaso 20 na cikin alkhairin da kuka samo.
Jidda ta murmusa ta ce" In dai wannan ne baki da matsala da ni."
Samha tayi murmushin jindadi tace" Shiyasa nace ke ALKHAIRI NA ce."
Ta yi furucin nan ne adaidai lokacin da Yallabai ya shigo dakin ɗauke da siririyar sallama fuskan nan a murtuke tamƙar bai tab'a sanin dariya ba. Ya ɗan jima da shigowa amma ganin tana waya yasa ya yi zamansa a falo.
"Wai har yanzu baki gama wayar bane?" Ya faɗa da zafi. Jidda bata san lokacin data jefar da waya saman gado ba tare data katse ba.
Samha nata "hello hello Jidda" amma ina hankalin Jidda ya koma kan Daddy ne, kasancewar dama wayar a hands free yake yasa Daddy saurin shaida mai muryan balle jini fa akace ba wasa ba.
Cikin zafin nama ya nufi inda wayar yake ransa a matuk'ar bace, sai alokacin Jidda ta dawo hayyacin ta. Cikin azama ta matsa kusa da gadon zata kai hannu ta ɗauki wayar amma ta makaro ya riga ta ɗauka wa.
Wuta ne kawai ya ɗauke wa Jidda don ta riga ta sadakar cewa yau asirinsu zai tonu.
Gyaran muryar sa ne ya dawo da ita cikin hayyacin ta. Kuka ta sakar kasa kasa tana masa maqiya" Don girman Allah........."
Sai kuma ta kasa magana tasa hannu ta toshe baki.
Abun ya matuk'ar bashi mamaki ganin jikin ta har ya dauki rawa. Hakan ba karamin kara kufular dashi yayi ba, ya rasa meyasa Jidda take matuk'ar tsoron Samha kamar wata mala'ikan mutuwa.
Kafin yace wani abu Samha ta katse wayar a tunaninta matsala ce ta network. Dire mata wayar ya yi a saman dressing mirror sannan ya bar dakin ko kala bai ce da ita ba.
Yana fita kitchen ya shiga don neman abunda zai sa aciki gashi har sha biyun rana ake nema tunda garin Allah ya waye bai sa komai aciki ba. Haɗaɗɗen Indomie da dafaffen kwai ya dafa wanda ko cikakken minti sha biyar bai yi ba ya kammala ya taho dinning.
kamshi ya cika gidan abun ka da kwararren kuku. Had'a kakkauran shayi yayi sannan ya fara aikawa cikinsa. Jidda na daki tana kwance tayi ruf da ciki, kamshin indomie ya cika mata hanci sai ji tayi duk duniya babu abunda take so ta ci sama da Indomi d'in nan. Ba ta tsaya cutar da kanta ba ta tashi tayi falo, Can dinning ta hange shi yana cin abincinsa hankali kwance ko kallon ta yaki yi alhalin yasan da fitowar ta.
Karasa wa dinning ɗin tayi yawunta har ya tsinke ta jawo kujera ta zauna. Ganin ya cigaba da cin abincinsa ko tayi bai mata ba tace ashagwab'e" Ni fa ina son in ci."
Ita ce hadda zubar k'walla wanda duk cikin shagwab'an ne. Ko kallon ta bai yi ba amma in yace salon ta bai rikita shi ba yayi karya. Ganin bai kulata ba yasa ta danne zuciya takai hannu ta jawo filet ɗin sa zuwa gabanta alokacin yana kan kurban shayi ne.
Da sauri ya dire kofin shayin ya sha mur yace" Ke wai meye haka bani abinci na yunwa nake ji wallahi ban ci komai ba tun safe."
Miƙewa tayi da abincin ahannu don kar ya kwace tace" Ina Nafeesa ko yau rowan girkin ta ta maka ne ?"
Ko kadan bai yi mamakin jin ta ambaci sunan matarsa kai tsaye ba tunda dama sun saba irin wannan wasar In yace ta ma shi kaza sai tace Nafeesa fa ? meya hana ta yi maka ?
" A nan gidan naga damar yin breakfast ɗina, kin ga ban son wasa ki bani abinci na."
Da gaske yake yau ta lura sam babu alamun wargi atattare dashi amma haka take ta k'ok'arin jan sa da wasa, tace ashagwab'e" Kai fa rowa tayi maka yawa kuma ai ba laifi na bane, babyn ka ne keso fa."
Ta furta tana masa nuni da shafaffiyar marar ta. Yin hakan da tayi ba karamin daɗi yaji aransa ba har yake jin tabbas akwai alamun nasara, ga dukkan alamu shi zaiyi nasara akan Samha wajen mallakan JIDDATULKHAIR...
Sake haɗe rai yayi tamk'ar bai tab'a sanin wani abu wai shi dariya ba yace" Wani babyn ? babyn da kike k'ok'arin ganin kin raba shi da mahaifinsa?."
Babu zato babu tsammani sai ji yayi hawaye masu dumi sun fara wanke mishi fuska. A b'angare daya kuma wani irin juyawa kan sa ya shiga yi ga tsananin zafin da zuciyar sa keyi kamar ana hura masa wuta.
Gaskiya baya jin zai iya rayuwa babu Jiddan sa, In ko ya kuskura kaddarar rabuwa ta gifta tsakanin su to tabbas zuciyar sa na iya yin bindiga.
Ko fushin da yake da ita dauriya ce kawai amma ba wai zuciyar sa zata iya jure tsawon lokaci acikin wannan halin bane. Bai jira yaji ta cewar ta ba ya cigaba da magana awannan karon muryar sa tayi bala'in yin k'asa" Jidda don Allah ki taimake ni kar zuciyata tayi bindiga, bazan iya jure tsawon lokaci ina fushi dake ba, ki taimaka ki zab'eni kan Samha wallahi ki sani ni ne masoyin ki na hakika. Bana nufin cutar da rayuwar ki sai dai na inganta shi in kuma zame miki gatan da kika nema kika rasa arayuwa. Alkhairi na please ki rayu dani kin ga yadda na koma kamar ɗan yaro ɗan shekaru goma agaban ki sai sani kuka kike ko tausayi na ma bak'ya ji uhmm matata."
Gaba ɗaya wuta ne ya dauke mata ganin babban mutum kamar Yallabai na kuka akanta, Uban wata kenan fa wanda ahaife ita kanta ya haifeta. Amma wanda bai sani ba In yaga Samha aka ce masa ai shi keda haihuwar ta wallahi atashin farko mutum bazai tab'a yadda ba sabida yanayin jikin sa kamar na matashi mai kan ganiyar sa.
A take taji aranta bata k'yauta ba yadda take ta juya shi son ranta, Ita kanta in tace zata iya rayuwa babu shi to tabbas ta yaudari kanta.
"Na amince zan raini cikin har in haifesa."
Ai bai san lokacin daya tashi daga inda yake zaune ba ya nufi wajen ta ya rungume kana ya Fashe mata da sabon kuka kamar wani karamin yaro yana" Da gaske kike kin amince zaki haifa mun ɗa? Hakan na nufin kina tare dani kenan kuma kin amince zakiyi watsi da duk abunda zai kai ki ga hallaka sannan kin shirya maida hankali wajen bautar ubangijin ki."
" Hakane ina tare dakai amma kamin alfarma bazan iya rabuwa da Samha ba. Samha guɗan jinin ka ce kuma ya zama dole in k'aunaci duk abunda ya fito daga tsatson ka balle Samha wacce ta min rana bai kamata ace in fara tunanin guje mata don kawai tana aikata ba daidai ba."
Ajiyar zuciya ya saukar yace" Duk abunda kike so haka za'ayi Gimbiya ta, Ni dai tunda kin amince zaki haifa min ɗa ai shikenan magana ta kare nasan duk daren daɗewa dole gaskiya zata yi halin ta ta bayyana kanta don ba zamu dawwama acikin wannan rayuwar ba, kina da bukatar 'yanci daga ke har abun da zaki haifa min."
Lamo tayi ajikinsa bata sake cewa komai ba don ta san gaskiya ya faɗa duk guje-gujen da suke dole ya kusa zuwa k'arshe.
Koma wa suka yi zaman cin abinci ayanzu tunda rayukan kowa yayi fari tas, sai shagwab'a take ta zuba masa yana bata abaki itama tana bashi har suka kammala, daga nan kuma sai daki anan suka fara rama baccin da basu same shi awadace ba har na tsawon kwanaki uku.
***GIDAN MATA***
A can Gidan mata kuwa sai rawar jiki matan gidan ke tayi akan Samha kamar wata shugabar k'asa, duk inda tayi suna biye da ita cikin girmamawa, ga bala'in shakkar ta da suke kamar me. Hajiya Sama Hajiya k'asa kamar su goya ta haka suke taji.
Har ta gama dudduba kaya taga dai babu matsala komai ya cika a sannan tasa aka shisshigar dasu cikin store sannan ta sallamesu. Batun rabo kuma sai daga baya don akwai wasu dattijan matan data yi appointing ɗin su awannan matsayin, su ke zuwa duk ƙarshen wata In an kawo kaya su zo su kakkasa kowa ya kwashe nashi wanda ya rage kuma su kwashe rabon su zuwa gida kuma abiyasu ladan aikin su.
Duk Wanda baya gari store ake mayar wa in ya dawo abuɗe abashi nashi kason, Kuma duk wanda aka bawa akan yi ticking sunan shi amatsayin an sallame shi na wannan watan.
Kayan abincin da ake rarraba musu sun haɗa da shinkafa kuma 'yar gwamnati, taliya, indomie, wake hatta da omo da sabulun wanki da pad basa kukan shi. Kayan abincin da babu kuma sai ka siya da kudinka tunda already ita dai tana iyakacin bakin k'ok'arin ta.
To, da wannan salon k'yautatawar ne Samha take samu tana rinjayar Ya'ya mata waƴanda suka rasa gata ko kuma waƴanda suka fito bariki, ko wani dalili na daban.
Duk wanda yaji labarin irin tarin alkhairin da ake Samu a GIDAN MATA ba tare da wani dogon tunani ba yake kawo kansa amma fa iya MATASAN MATA take karba. Sai dai Samha tana fakewa da salon k'yautatawarta tana samun nata riban a jikinsu.
Duk yanda kake jin labarin GIDAN MATA iya k'yautatawar kawai ka sani amma sai ka shigo ciki zaka san dawan garin da kuma makasudin wanzuwarsa. Gashi Samha tana samun tallafi sosai daga manyan mutane masu zuciyar taimako duk da basu san sirrin Gidan ba iya positive sides ɗin sa kawai suke da labari, makusantan ita samhar da kuma mazauna Gidan Matan ne kadai suka san sirrin sa kuma muddin wata tayi gangancin tona musu asiri Samha ta dau alk'awarin ganin bayan ki koda kuwa zata yi yawo tsirara ne.
Shiyasa In ke sabuwar hannu ce bayan kinyi register, dole zakiyi signing kan agreement paper na cewar bazaki tab'a bayyana sirrin gidan ba. Duk da komai na duniya baya b'oyuwa na har abada, mutane dai sun fara jin jita-jita na negative sides ɗin sa amma har yanzu babu wani kwakkwaran hujja da aka kama ahannu. Jami'an tsaro na silent moves sai dai matsalar Samha nada daurin Gindi awajen manyan su.
Sai data zo wucewa ne take tambaya" Wai ina sabuwar yarinyar nan ne da take son jawo mana matsala agidan nan ina son saninta yau."
Ta yi tambaya cike da izza da kuma takama, Kowa ya shaida wacce take nufi wato Saffy. Koda aka duba an ga dakin nata garkame da katon kwaɗo da alamun bata nan.
Kwafa Samha tayi tace" Ba damuwa watarana zamu san juna, ko ta daɗi ko akasin ta, Ta sanni nima In santa."
Adaidai wannan lokacin kuma Saffy tana salon ana mata gyaran gashi. Saffy akwai son ado 'yar gaye ce ta bugawa ajarida. Ko Samha bata isa ta gaya mata ado ba, sai dai ta nuna mata kudi da kuma gogewa na hutu.
Bayan barin Samha Gidan kai tsaye wajen Aminiyar ta Hadiza ta nufa don su sasanta, bata wani sha wahalar shawo kanta ba ta hakura da wulakancin da tayi mata rannan.
A nan take ta bata labarin Gidan abincin da Yallabai yaso mallaka mata. Sosai Hadiza ta sake fusata tace" Haba Samha Ni wallahi wautar ki ba karamin haushi yake ban ba. In banda shashasha asararriya har yaushe zaki tsaya haɗa shahararren GIDAN ABINCI da wani GIDAN MATA ? halal da haram ? Mu makusantan ki mu mukasan irin nakason da kika yi wa rayuwar ya'yan mutane amma kike fakewa da taimakon su, wallahi Samha ki tuba tun kina da sauran dama kafin lokaci ya shige miki, ki sani ita duniya da kike ƙawance da ita ba 'yar amana bace ki rubuta ki ajiye watarana tabbas sai ta ci amanar ki."
A fusace itama Samha tace" A'a malama bana san diban albarka ya zaki tsaya kina wani zagina sai kace wata uwata ? ni fa shiyasa bana son zama kusa da ke sabida maganganunki basu da daɗin ji. Yanzu ma Sulhu nazo yi amma kike kara wa wuta fetur."
Haka suka rabu ana uwaka-ubanka irin faɗan da basu tab'a yi ba suka yi ayau, har makotan Hadiza suka shigo gidan aka shiga tsakani amma ko kadan Hadiza bata bari su san dalilin fadansu ba don ita tana da riƙo da sirrin mutum shiyasa Samha bata tab'a nadamar bud'e mata cikin ta taga sirrin ta ba.
Abunda Samha tayi wa Hadiza ayau yayi bala'in sosa ranta, sai ta kara samun ƙwarin gwiwa kan abunda take da niyyar ƙullawa.
Kwafa tayi bayan komai ya lafa kuma Samha tabar gidan tace" Samha dani kike wasa sai na koya miki darasi."
***
Sai dab da magrib Yallabai yayi shirin barin gidan ba dan yaso ba, Jidda sai kuka take rera masa duk tabi ta d'aga masa hankali, rarrashinta ya shiga yi yana"Sai fa kinyi hakuri don ba laifi na bane, ke kike son muyi rayuwar sirri In ba haka ba naso ki samu 'yancin ki. Ki shimfiɗa rayuwar aure irin yadda kowacce 'ya mace ke yi da mijin ta duniya tasan da su, hakan zai sa mu rika kasancewa da juna amma tsoro bazai bar ki ba. Ina da aiki sosai agaba na don ga dukkan alamu ba ƙaramin yaƙi zan sha wajen ganin na cire tsoron Samha da Nafeesa a ranki ba."
Bai jira ta cewar ta ba ya kwaso takaddun da yazo dasu original copy wanda sai ayanzu itama take ganin su, ga mamakin ta sai gani tayi ya zaunar da ita yana fadad'a murmushin sa, wani irin farin ciki mara misaltuwa kawai yake ji ya cika zuciyar sa kamar wanda akai wa wani d'ad'ad'ar albishir. Miƙa mata takaddun ya yi yana" JIDDATULKHAIR Ni mijin ki JALALUDDEEN AHMAD ALKALERI na mallaka miki shahararren GIDAN ABINCI NA da ake kan kerawa ak'asar birtaniya. Na mallaka miki shi halak-malak sabida nuna godiya ta agare ki da shigo wa rayuwa ta da kika yi, baki duba shekaruna ba kika amince kika aure ni."
Sai daya ja wani dogon nishi sannan ya ci gaba:
"Gashi kina shirin haifa min ɗa, JIDDA ke ɗin alkhairi ne agare ni. Nagode Nagode bazan iya biyan ki ba Allah shi zai biya ki, nawa kawai In k'yautata miki daidai gwargwaɗon iyawa na. Dama nayi alk'awarin baki babban tukwici sakamakon d'ad'ad'ar labarin dana samu na guɗan jini na da kike dauke dashi. Shine na yanke shawaran mallaka miki babban gidan abinci na wanda babu kamarsa wato JAY. ALKALERI'S KITCHEN LONDON. Ki karba takaddu kisa hannu banda korafi kuma banda maida hannun ƙyauta baya, ke nake ganin kin fi cancanta da in mallaka miki gidan abincin nan."
Tunda ya fara magana take kallon sa ta kasa cewa uffan har ya kai aya. Bata iya tantance wani duniya take ba don gaba ɗaya Yallabai ya gama rikitata.
Ganin shirun ya yi yawa yasa Yallabai kamo hannun ta ya shiga murza k'yawawan 'yan yatsun ta ko hakan zai sa ta dawo cikin duniyar mu ta fuskanci Zahiri, yace" Jidda kiyi magana don't be silent ba mafarki kike ba, abunda kika ji kuma kike gani zahiri ne. Our love story is my favorite chapter in life so I'm gifting you my Favourite restaurant under construction to write the next chapter together."
NAGODE ALL❤️