PAGE 14
by @swrites22
SAHAD STORE
Saida suka gama shopping ɗin zasu je wurin biya Maesha tace ya xeenah tsaya nayi mantuwa, akwai abinda na manta ban duba ba.
"In dai kika sake kwaso wani kayan zaqin saidai ki nemi ne biya miki". Ya Zeenah ta fada tana tsayawa, Maesha kuma ta wuce ta dayan side ɗin, tana zagayowa sukayi clashing da wata yarinya dake kokarin dauko wani drink amma tsayinta bai kai, ganin Maesha yasa tayi saurin faɗin, "Ukty, saaduni fi haza, lau samahaty". Da sauri kuma tace , help me with this please". Ta faɗa da alama wancan Yaren kwace mata yayi.
Murmushi Maesha tayi ta dauko mata guda daya ta bata kana tace, "Hal al amr munasib lak au turid wahdan Akar?". Ta tambaya da Arabic accent kamar bata ji hausa ba.
Riqe baki yarinyar tayi sai kuma ta saki dariya, "Are You from My country?".
Maesha ta shafa kanta dan yarinyar ta burge ta tace, "Which country?".
" UAE!, since moving to Nigeria I haven't had anyone to speak Arabic with outside of my family, until I met you".
Tayi murmushi tare da faɗin, "What's your name?".
"Danin wa inti ?.
"Ismiy AYUSHERH wa laqabni Maesha.
"Lakin min ay daulatun?
"Oman". Maesha ta fada tana daukan drink ɗin data dawo saboda shi, kafin ta wuce tana dagawa danin ɗin hannu.
Da gudu danin ta isa wurin su Moha. "Ya Moh dan Allah muje ka karba min number wancan matar, she's so kind kuma bakaji Arabic accent ɗin ta ba muje kace tayi ma, i wanna be friend with her".
"Really?". Ya faɗa idonsa akan Maesha.
"Wallah ya Moh, muje karta tafi".
"Oya go put the drink in the basket, see Nash there, bari na karba miki number ta ta kinji. Ya fada yana pointing Inda Nash yake, da sauri ta nufeshi shi kuma ya nufi wurin Maesha.
Maesha na tafiya tana sake duba wasu abubuwan taji tafi a wurin kunnenta, a tsorace ta juyo har tana sakin abinda ke a hannunta suka zube a ƙasa, gira ɗaya ya dage mata yana mata wani cool smile, durkushewa tayi a gurin ta rungume hannuwan ta a kirji cikin rawar muryar tace Haba dan Allah moh, whl ka tsoratani da yawa". Ta ƙarashe hawaye na zubo mata.
Zaro Ido yayi da mamaki yace, "Haba sarauniyar shagwaɓabbu mai arhar hawaye, kai na bisa wuyana".
Hararar sa tayi yayi yar dariya kafin ya dan rankwafa ya mika mata hannun sa, hannun tabi da kallo kafin ta mike tana goge hawayenta, dan dage kafadunsa yayi irin I don't care din nan kafin ya daibe mata abubuwan data zubar ya miqa mata tare da faɗin, "I missed something precious!
Kallon sa tayi tare da faɗin, "What?".
Pointing dinta yayi da yatsarsa manuniya sai ta juya tana kallon bayanta. "Menene? Ni banga komai ba".
"Kece ai".
" Ni? "
"Eh ke ɗin A TAFIDA, ke nayi missing.
Sunkuyar da kanta tayi tana ɗan murmushi. " Ina wayarki ?
"Ni kam wai Meysa ko yaushe muka hadu sai ka nemi wayata, me kake min a ciki ne".
" Wani abu nake son dubawa.
Kallon jakar dake saqale a kafadarta tayi sai kuma ta shiga ƙoƙarin riqe kayan dake hannunta a hannu daya, ganin haka yasa Moha dan matsowa, saurin ja baya tayi tana ɗagowa ta buɗe baki zatayi magana ya sanya hannu ya buɗe jakar ya bude ya dauki wayar. Tasa wayar ce tayi ƙara haka yasa shi zarota daga aljihunsa ya kara a kunne banji mai akace daga ciki ba yace just wait for me outside ". Yana fadin haka ya sanya wayar a jaka.
Kunna ta Maesha yayi sai kuma ya dago ya kalleta ta zuba masa ido tana kallo, "Password?".
"Mamuh".
"Mamuh". Ya nanata sunan kamar zai sake tambayarta sai kuma ya taɓe baki ya maida Hankalin sa wayar. A sanyaye ya ɗago tare da dubanta yace, "Meysa ba'a bawa sha ɗaya ta matsayi na har yanzu?".
"Miye sha dayarka?". Ta yi tambayar tsakaninta da ALLAH.
Wayar ya daga mata tare da nuna mata numbersa da bata yi Saving ba har lokacin, shuru tayi ta rasa me zatace masa. "Meye matsayina mamii?". Ya Tambaya still idonsa a kanta yana wurga mata wani kallon data kasa fassara shi. (Mamii yake kiranta sbd sunan Momma ne da ita) shuru ta sake yi gabanta na faduwa .
Ya Xeenah ce ta ƙaraso wurin, hankalinta akan Maesha ta shiga faɗin, "Haba maesha, wannan wani irin wulakanci ne tun dazu mun gama abinda zamuyi, amma kin barmu sai nemanki muke". Ta ƙarashe tana maida kallon ta kan Moha da bai motsa ba bai kuma dauke idonsa akan Maesha ba.
Kallon su tayi sai kuma ta sake maida idon ta a Kan Maesha data sunkuyar dakai, ta sake kallon moha da ya matsa ya sanyawa Maeshan wayarta a jaka, yana ƙoƙarin wucewa ta dago ta kalle shi sai tayi Sa'a shi ma ita yake kallo, Murmushin gefen baki ya mata me tarin ma'anoni kafin ya wuce ya barta da kamshinsa da ya cika mata hanci.
Ya xeena data saki baki tana kallan ikon Allah sai taga kawai maesha ta juye abinda ke a hannunta cikin cart din hannun Ya Zeenah ta bar wurin.
Hannun Nabila ta rike da sauri tabi bayanta zuwa wurin biya, suna zuwa akace masu an biya. Ya Zeenah ce ta kalli Maesha da duk jikinta yayi sanyi tace, "Ke kinsan wa ya biya din ne?".
Girgiza mata kai tayi kawai, ya Zeenah ta juya wurin matar tace, "Madam, ko zamu iya sanin wanda ya biya Please?".
"Wani ne yanzu ya fita da peach colour din T shirt ajikinsa". Maesha na jin haka tayi waje da sauri Ya Zeenah na kiranta amma ko juyowa bata yi ba, ɗaukan kayan nasu tayi tabi ta.
Juye juye ta shiga yi a lokacin data fito amma bata ga ko mai kama dashi ba. "Kinga Maesha muje kawai ya riga ya tafi". Ya zeenah ta fada tana wucewa Wurin mota. A sabule ta bi bayanta, ta buɗe motar ta shiga ta kifa Kanta Kan steering ta shiga raira kuka, Ya Zeenah data gama sa kayan tare da yaran a mota ta shiga, ta buɗe passenger front seat ta shiga Itama, "Maesha". Ya Zeenah ta fada tana dafa kafaɗarta.
Bata ɗago ba sannan bata daina kukan ba, shuru motar ta ɗauka ya Zeenah bata ƙara cewa komai ba, saida ta gama kukan ta dago ta share hawayenta ta daidaita kanta ta kunna motar ta yi reverse suka hau titi.
"Waye shi Maesha?".
"Muhammad sameer Adam jikamshi". Ta fada tana sauke ajiyar zuciya
" Ba sunansa na bukata ba, ai nasan shi ba cousin din safna ba wanda yayi karatu a London, shi ne wanda mukaje gidan su ai ranar".
Dan duban Yayarta ta tayi tana tunani, a London yayi karatu? Ta maimaita, a sanyaye kuma tace, "Me kika sani game dashi ya Zeenah ?".
"Menene alakarku da har dan yayi fishi kike kuka haka".
"Fushi kuma, fushi yayi ya Zeenah?".
Kallanta tayi sannan ta maida kanta titi, "Ki ban amsata tukunna?".
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kwashe komai ta faɗawa yayarta ta sai dai ta boye mata cewa itama ta dade tana dakon sonshi tun farko haduwarsu.
" Ya akayi kika kasa gane abinda ke zuciyarshi Maesha, ko da yake ke yarinya ce har yanzu shiyasa kike wauta. Kallo daya na muku na gane yadda kuke masifar san junanku bance zan faɗawa kowa ba amma ki Kula kinsan halin Abbah.
" To yanzu ya zanyi ya Zeenah kuma gashi kince fishi yayi.
"Ikon Allah, yanzu abinda zakiyin ma sai na faɗa Miki?".
"To ni ai kinga har yanzu baice yana so na ba, ba wai zan yi treating nasa bane kamar masoyi shiyasa.
"Kiransa zakiyi ki bashi hakuri". Shuru tayi har suka iso kofar gidan su ba wanda ya kara Magana sai yaran dake bayan suna wasa.