BELOVED HEARTS

PAGE 33

by @swrites22

Maesha na faɗawa daki bathroom ta wuce da sauri don ta watsa ruwa.

Ameer ne ya shigo ɗakin yana kiran sunanta hakan yasa a gurguje ta ƙarasa wankan ta fito, "Shi ne kika wani shige kika shanya mutane suna ta jiranki ko?".

"Ai whl baka kyauta min ba Ameer ya zaka shigo dasu baka sanar ba, ni fa ban san ma zasu zo ba dan sai yanzu Ummu ta bani wayata".

Yayi dariya yace, "Kuma whl da kyanki fa a lokacin da kika fito ɗin nan sai glowing kike ai da kaya kawai kika canza kika fita".

"Kaci gaba ai zasu tafi ne, zaka sani". Ta faɗa tana karasawa wurin mirror ta hau shiryawa shi kuma ya fice yana dariya.

Buɗe sip ɗin tayi ta shiga neman kayan da zata sa, duk Saida ta fitar da kayan ciki kafin ta dauko wani lace purple me touch din pink ta sanya, sosai dinkin yabi Jikinta haka colour ma kamar dan ita akayita, bata shafa komai a fuskarta ba sai kwalli data zira da lipgloss, ta dauki cumb ta ɗan kwantar da gaban gashinta da ya tashi dan ma kar ta tsaya sabon gyara ta bata lokaci, ta dauki mayafin data ciro dan ita a rayuwa in ana so aga gazawarta a haɗata da daurin dan kwali.

Tana ƙoƙarin fita Ameer ya sake sawo kai sai kuwa ya tsaya tsokanarta, bata kulashi ba ta wuce falon, da sallama ta ƙarasa su Faez suka amsa shi kuwa Moha ya wani kafeta da ido kamar zai dauketa ya mayar ciki.

"Ina wuninku Dr". Maesha ta faɗa tana zama, suka amsa mata shi da Nashed Faez yace, "Da gaske fa har kin fara hasken amarci tun yanzu, muma a bamu sirrin mana". Ta kalli Moha suka haɗa ido ya kashe mata ido sai tayi saurin sunkuyar da kai tana murmushi shi kuwa gyara zama yayi ya kalli Faez yace, "Nine sirrin ai, abun daga mu ne".

"To me kake nufi?".

"Oho kuma". Moha ya faɗa yana maida hankalinsa kan Maesha dan bata taba masa kyau irin na yau ko dan bai taba ganinta da irin wannan shigar bane cox kullum daga hijabi sai abaya saisa yaga kamar canja masa ita akayi.

Ƙasa ƙasa yadda ita kaɗai zataji yace, "Yanzu da kika sake wankan canza kama kikayi".

"Wa yace ma wanka na sake?".

"Na ganki ai kika yi wuqit kika faɗa daki kuma whl kinfi kyau kafin ki sake wanka".

"Shikenan to zageni".

"To nayi shuru tunda ba'a so in fadi gsky".

"Da yafi dai". Ta faɗa tana kallon refreshments ɗin da aka kawo musu wanda ko tabawa basuyi ba tace, "Dr baku sha komai ba ai".

"Gashi nan tambaye shi, shi ya hana mu sha". Ya faɗa yana nuna Moha Sannan ya miqe ya dauki tumbler din ya shiga tsiyaya musu lemo.

Maesha tayi Murmushi a zuciyarta tace lalle Meelah ta samu daidai ita. Shi dai Moha da kallo ya bishi yana jin kamar ya kai masa duka, haka ya zuba musu lemon ya ɗauka musu cake shi da Nashed ya miqa masa.

Nashed yace, "To Moha din fa ".

"Tunda bakaji abinda yace ba sai ka tashi ka zuba masa ". Ya faɗa yana zaro wayarsa dake ringing ya duba sai yaga Meelah ce.

"Helloooo My Apple".

Moha yace, "Allah yasa guava ce ba apple ba". Ya watsa masa Harara yana cigaba da wayar, sai kuma yace, "An gama, yadda kikace haka za'ayi". Ya karashe yana tashi ya Ajje tumbler ɗin sannan ya kalli Moha yace, "To ni Allah ya min tafiya, zan ɗan zagaya in ka fito ka kirani".

Maesha tace, "A'a ina kuma zaka?".

"Ina kuwa za shi, kaudi kaudinsa ce ta kirashi shi ne yake ta rawar ƙafa mana".

Maesha tayi dariya jin sunan da Moha ya bawa Meelah, shi kuwa Faez cewa yayi, "Kanka akeji, Nashed tashi ka rakani ".

Tashi Nashed yayi yana gyara rigarsa, Moha yace, "Au Kai ma tafiyar zakayi?".

"Wai dai kar ganin mu ya ragewa aya zaki, gwara mu ɗan baku waje". Nashed ya faɗa da sigar tsokana.

"Ka cigaba da biye shi in dai Faez ne, Allah ya raka taki gona".

"Ameen". Faez ya amsa suka sa kai suka fice, falon ya rage daga Moha sai Maesha.

"Yanzu da gaske baza ka sha komai ba?".

"Ai ba'a yi niyyar in sha ɗin bane".

"Kamar ya?". Ta tambaya ba tare data fahimta ba.

"To ba'a dauko an bani ba". Ta girgiza kai ta miqe ta zubo masa drink ɗin ta dauko plate ɗin cake ɗin ta janyo side stool ta shiga ƙoƙarin Ajje masa mayafin kanta ya zame, sai da ta ajje abubuwan dake hannunta sannan ta dago dan gyara mayafin, "Me rowa kawai". Moha da ya zuba mata ido ya faɗa.

"Rowar me".

"Naqi in faɗa ɗin". Ya faɗa yana daukan tumbler ɗin ya kai baki ya kurɓa. Hira suka shiga yi cike da so da kauna, suna maida halin da kowannensu ya shiga, a haka Abbah ya dawo ya same su suka gaisa da Moha sannan ya wuce ciki.

Sake gyara zama sukayi suka cigaba da hirarsu ta masoya can sai ga kiran Faez ya shigo wayarsa, dauka yayi ya sa a speaker sannan yace, "Ya akayi ne Malam?"

"Wani irin ya akayi, hala baka duban agogo, dare fa ya fara yi, har yanzu baku gama bane".

"Matata bata sallame ni ba Malam, in kun fito ku jirani a mota".

"Kai nifa ban yarda daku ba wai me kuke cewa ne, Allah yasa ba wanna miskilancin naka ka kai mata ba kuka tsaya kallon juna".

"Kaga malam karka dameni kaji".

"To wai nace zaka fito ne ko kuma a biyoka da kayanka?".

"Hakan ma ba laifi, ku dan bani 5 minutes". Ya kashe yana murmushi.

"Kina ji na da mutumin nan ko?".

"Har kaudi kaudin ta sallame shi kenan".

"Ni dai ba ruwana in taji a bakinki".

"Ai kuwa na riqe, kuma kai ka sakamin sunan a baki". Sai da suka sake shafe 7 minutes kafin ya tashi ta rakoshi har kofar parlourn, ta tsaya riqe da kofar tana kallonsa, shi ma ita yake kallo kamar karsu rabu yace, "Ina zuwa gida zan kiraki ki kula da wayarki kar tayi nesa dake Kinji".

"In sha Allah, Allah ya kaiku lpy ya tsare hanya". Haka sukayi sallama ya tafi ita kuma ta koma, shopping bag ta hango a inda suka zauna, da mamaki ta bita da kallo dan har suka gama zamansu bata lura ba dan haka ta ɗauka ko mantawa yayi, ɗauka tayi ta wuce daki ta ɗauki wayarta ta kira shi.

Kashewa yayi sannan ya kirata kamar yadda ya saba, "Hello Angel! Har an fara missing din nawa ne?".

"Mantuwa kayi a inda muka zauna n......"

Katseta yayi da faɗin, "Shikenan kin maidani tsoho tun ba'aje ko ina ba na fara mantuwa".

"To ai yanzu yaran ma sunfi tsofaffi saurin mantuwa".

"A bakinki dai na fara ji, amma yanzu dai duba kiga miye a ciki?".

Ba musu ta hau dubawa saidai abubuwan data gani yasa ta fahimci ba mantuwa yayi ba ita ya ajjewa amma sai tace, "Naga abubuwan arziki, amma wa za'a ajjewa".

"Ki ajjewa matata, nata ne ita kaɗai".

"To yaushe zata zo ta karba".

Murmushi yayi yace, "Kina gwara kai na da yawa Angel ranar da zan kamaki ko".

Tayi yar dariya tace, "Allah yasa dai bakai kake driving ba".

Moha ya kalli Faez sannan yace, "Mijin kauɗi ne". Suka sa dariya shi da ita.

Faez yace, "Kasan Allah ku fita hanyar mu kai da matar ka tohm".

Moha na dariya yace, "Angel bari sai mun koma gida zan kiraki".

"To shikenan Allah ya maidaku gida lpy, ka gaida Momma". Da haka sukayi sallama ta kashe.

Aikuwa ranar kwana sukayi suna waya, washe gari kuma ta shirya suka wuce makaranta tare da meelah. Haka rayuwa ta cigaba da gangarawa su Maesha kullum ƙara shaquwa suke da juna har sun matsu ma ranar tazo.

HAMEEDAH

Hameeda tunda ta dawo gidansu komai ya sake rikice mata wata irin sabuwar soyayyar moha ce ke sake taso mata, gashi daddy yace indai ta taka gidan nan sai ya mata abinda bata taba zato ba dan zai iya tsameta cikin ya'yan da akan hakan.

Hakan yasa ta rasa damar aiwatar da ɗaya aikinta dan har yanzu tana kan bakarta, ta samu Maryam ta sanar mata ita kuma tace tazo su koma wurin bokanyarsu, haka suka shirya suka koma. Bayan tayi yan tsubbace tsubbacenta ta dago tana kallonsu tace, "kin makaro". Zaro Ido Hameeda tayi kamar zata ɗaura hannu aka.

"Babu makawa sai anyi auren nan dan akwai rabo a tsakanin su kuma ko an musu wani aiki ba lalle ya sake tasiri a kansu ba".

"Bokanya ki temakamin Karna rasa shi, ni ko mu biyu zai haɗa ma na yarda in dai zai aureni". Hameedah ta faɗa da rawar murya.

Itama Maryam sake cewa tayi, "Ki temaka Mata karta rasa shi bokanya".

"Ha ha ha zata rasa shi". Ta sake faɗa tana wata irin dariya marar dadin sauraro.

Miqewa hameeda tayi rai bace tace, "Ai bake bace Allah da zaki fadi abu ya yiwu, makaryaciyar banza makaryaciyar wofi, macuta kawai, ta Allah ba taki ba kuma sai na auri Moha whl ko zanyi yawo tsirara".

"Keeeeeeee". Bokanya ta daka Mata wata uwar tsawa da saida dajin gabaɗaya ya amsa. "Karkimin fitsara yanzu zansa ɗan majnunu ya miki fitsari aka, marar albarka kawai".

Maryam ce takamota ta zaunar tana zungurinta ta shiga bawa bokanya hakuri itakuwa Hameedah sai harararta take.

"Ha ha ha he he he. Za'a mata aiki na karshe albarkacin ki, idan har shima baiyi ba to babu wani aiki da zai sake yiwuwa ko da ba nan kika zo ba duk Inda zaki zagaya ba aikin dazai sake kamawa".

"Eh bokanya mun yarda koma wani iri ne ayi".

"Aiki ne me hatsari sosai kuma idan aikin bai same su ba zai iya komawa kanku Ku duka".

Da sauri Maryam ta kalli hameeda sai kuma tace, "A a gsky bokanya ni ban dani, ai bani bace mai bukatar ba taya za ace abun zai dawo kan mu mu duka, kinga Hameedah tashi mu tafi". Ta faɗa tana riqo Hannunta.

Hameedah ta kwace jin cewa za'a samu mafita, tace, "Haba mana kawata ya zakimin haka, ashe duk son da kikemin na baki ne, saida abu ya rage saura kiris kice zaki gujeni, wanna fa shine aikin karshe kuma zamuyi nasara ni naji hakan a jikina, ki zauna muji sharadin mana". Da haka ta rinjaye ta suka zauna.

Hameedah tace, "Miye sharadin bokanya?".

"Sai kun aminta tukunna zakuji amsarku".

Da sauri Hameedah tace, "Mun amince, itama ta amince". Ta faɗa tana mintsinin Maryam, ba dan tana so ba tace ta amince.

Wata irin hayaniya marar daɗi ta cika ilahirin kunnuwansu ga wani hayaki da ya fara tashi ba tare da sunsan daga ina yake fitowa ba, suka toshe hancinsu da mayafansu can kuma suka ji dif kamar anyi ruwa an dauke.

Idonsu ne ya sauka kan wata kwalba dake gaban Hameeda dauke da wani maciji ya fasa Kansa. "Wannan kwalbar ita zaki binne a gidansu, sharadinta idan har wani ya ganki to aikin bazai tashi a lokacin ba. Ke kuma ". Ta faɗa tana jehowa Maryam wani kullin magani. "A ruwa ko abinci zaku sawa yarinyar ku tabbatar taci wannan abun da kuka zubawa maganin in ba haka ba zaki nakasta".

Maryam tace, "Wai bokanya ni miye nawa ne kike hadawa dani, nifa rakiya kawai nayi ".

Wata muguwar dariya bokanya ta shigayi kafin can kuma ta haɗe rai kamar ba ita ba tace, "Saboda kema kina da naki qudurin akan ta, ba wai dan ki taimakawa kawarki kawai bane kike ta wannan kai kawon".

Hameedah ta juya ta kalleta da mamaki da kuma neman Karin bayani ita kuwa Maryam tsorata tayi dan bata taba tunanin bokanya zata iya bincikenta ba itama. Katsesu tayi da faɗin, "Ku ajjewa melis kuɗin aikinta ku tafi".

Kudi hameedah ta ciro a jakarta masu yawa ta ajje, yana ajjewa kudin ya bace da sauri sukaja baya. "ku ɗauki kayan aikinku ku fice da baya, kuuuuu fice da bayaaaa". Ta ƙarashe da wani irin sauti.

Da sauri suka tashi suka dauki abubuwan suka sa a jaka sannan suka fita da baya har hameeda na wuntsilawa saboda sauri ita takasa sabawa da zuwa irin nan wajen Amma saboda jaraba dole takoyawa kanta.