Chapter 16
by @maidambu41
16
Faduwar Naanah Asma'u yasa Khamiee fasa ihu da ya janyo hankalin mutanen gidan tare da tawagar Ango shigowa gidan. Da wani irin sassarfa ya isa gabanta tare da saka hannu cak ya rabata da kasa. Ya juya da sauri yana me barin gidan. Waje ya nufi da ita inda motar Fuad yake. Nufo shi Ya Moud. "Kada ka kusanto Matata!" Ya furta yana sakata a cikin motar da fuad ya bude mishi gaban ya kwantar da ita a hankali. Sannan ya kwantar da kujerar. Cire rawanin yayi tare da juyawa ya wurgawa Fuad, bai yi wata wata ba ya cire babban rigar yayi ya dawo gaban motar ya fisge key din motar a hannun Fuad, ya shiga tare da turawa Mahmoud kura ya a guje ya ja motar yana me barin kofar gidan. Sai hankalin mutane ya dawo kan abinda ya faru aka shiga jajjantawa.
A cikin gidan kuwa Maamah ce hankalinta ya tashi, amma saboda ta nuna musu bata damu ba, ta cigaba da zamanta can sai ga Hajiya Turai ta shigo cikin gidan. "Rakiya ita Yarki akanta aka fara auren bazata ne?" Da yake itama Maamah a fusace take tana fitowa ta ce mata. "Idan na ba a fara akanta ba, ai kin ga ba zaa gama a kanta ba. Aure ne ai dole ta firgita."
"Kada ki min rashin kunya don kin ga an auri Yarki!" Inji Hajiya Turai, dariya Maamah tayi tana fadin. "Rashin kunya dai? Haba ai wuce nan, meye abin murna da auren wanda bai cika mutum ba? Hala baki san waye Adamu ba shi yasa har kike tunanin zanyi fari ciki, cab ai ko ita wacce ta hada auren tasan akwai rata tsakanin sama da kasa, haka tsakanin Adamu da Naanah Asma'u yake, har abada wannan shirin naku ba zai taɓa nasara ba, aure kuwa in sha Allah matuƙar ina raye sai na raba shi. Me aka yi aka yi auren mutumin banza! Meye abin farin ciki a wannan auren da bai da wani amfani t
Mtseew" Ai kuwa fadar haka da Maamah tayi ina wutar da za a saka ta, fadar tashin hankali rigima da aka yi ta yi har sai da Hajiya innah ta faɗi. Ta ce Maamah ta bar gidan ko ita ta bar gidan. Haka yasa Maamah ta bar gidan tare da mutanen nan ta da suka zo tayata murna.
***
Asibitin nan dai ya kai ta, don tun s hanya yake kiransu a waya, lokacin da ya isa bai tsaya jiran a kawo gadon marasa lafiya ba, ya dauki Matarshi ya nufi cikin asibitin, yana zuwa ER bai tsaya a bashi gadon ba ya kwantar da ita, likitan da ya zo inda yake ya ce mishi. "Lafiya dai ko?" Kallon cikin idanun likitan yayi ya ce mishi. "Aurenta nayi yau!" Yadda yayi maganar yana kallon yanayin likitan. "Amma kasan akwai hatsari me girma akan haka?" "Meye girman hatsarin?" Ya tambaye shi kiran Nurse likitan yayi ya suka shiga bada taimakon gaggawa. Cikin ikon Allah ba wani babban al'amari ba ne, domin suma tayi sakamakon girgiza da tayi na jin daurin auren wanda bai da alaka da ciwonta, ruwa suka saka mata tare da allura. Likitan ya ce mishi. "Ka same ni a office." Ba musu ya bi bayanshi haka ya bi bayanshi yadda ka san wani giwa saboda yadda yake takunsa.
Shigarshi cikin shadda sky blue, yayi mishi kyau, sai ya fito yanayinsa wato afro-arab, gashin kanshi da yake tarawa ya sauka har gadon bayanshi, yadda ya ja kujerar ofishin likitan ya zauna. Yana kallon likitan. "Da izinin waye ka aure ta? Waye ya gaya maka irin wannan ciwon ana musu auren dole? Kasan hatsarin da yake cike da haka kuwa?"
Wani hade rai yayi yana watsa mishi harara tare da faɗin. "Kai waye da zaka saka ni a gaba kana min faɗa? Idan ban maka rashin mutunci ba! Izinin fa? Amma ka ci uwar rena min hankali, dube ni da kyau nayi kama da wanda zai jira wani ya bashi umarni ne? Ka ga nayi kama da wanda zai bari a huce da rabon wani ne? Mtseew" ya fada yana ƙoƙarin mikewa ya bar office din yana watsawa likitan wani kallon banza da renon hankali.
Cikin sassauta murya likitan ya ce mishi. "Kasan meye?" Wani uwar harara ya kafa watsa mishi kamar idanunsa zasu fado ƙasa ya ce mishi. "Ni akuya ne da zan san meye! Wai me ka mai da ni ne? Sai wani rena min hankali kake to me zaka gaya min" Ya mai da mishi tare da watsa mishi kallon banza. Shi kanshi likitan da yana da hanyar da zai kori Uban kowa a cikin asibitin da yayi amma ba yadda ya iya tunda ƙaddaran asibitinsu ne da uban kowa yasan asibitinsu. Gyara murya yayi ya ce mishi.
"Daga cikin abubuwan da zan gaya maka shine zan fara tambayarka abu biyu!" Ya fada yana kallon Uban kowa da yake wani cika yana batsewa tare da tsare shi da idanunsa masu kaifi da kwarjini. "Tana sonka?" Jin yayi kalmar ya bashi dariya hade da jin kalmar kamar ya kunduma mishi zagi, irin ace maka kaci abu kazan kazanka, "kai da yake matarka auren soyayya kuka yi da ita?" Ya bashi amsa tare da dukar table din. "Shi kenan ya alaƙarka da ita?" " Ba na gaya maka yar Yayar babana ba ne? " Girgiza kai likitan yayi yana faɗin." Ba haka nake nufi ba!" Ya fada yana kallon kwayar idanun Uban kowa ya ce mishi. "Nufina kuna gaisawa ko da yar dariya da fara'a ce?" Mikewa Uban kowa yayi yana nufar hanyar fita. "Kada ka fita Adam yarinyar nan tana da last chance ne na tsawon shekaru uku idan ka iya sarrafa kanka zata yi nisan kwana tsawon shekaru biyar ko shida, ya danganta da yadda ka bi mata. Adam yarinyar nan hatta ciki idan ta dauka zai iya kawo karshen rayuwarta balle kuma idan anyi auren ranta baya so, Adam yarinyar nan idan har kasan bata sonka ka san yadda zaka koya mata sonka ajiye kome domin rayuwarta!" Naushi ya kaiwa kofar da karfin gaske, wanda sai da kofar da yake ta katako ce, sai da ta samu na kasu don kaniyarta.
Juyawa yayi a fusace yana me zuwa gaban likitan ya zuba hannunsa a saman table ɗin ya ce mishi. "Na maka kama da wanda zai ta kwadayin wani abu daga jikin mace ne?" Girgiza kai likitan yayi yana ƙoƙarin fahimtar da shi hatsarin da yake tattare da mu'amala da masu irin laluranta ya ce mishi." Wannan kuma sha'anin aure ne, duk yadda zan gaya maka matsayin da halin da zaka fuskanta nake gaya maka aure yana da wata irin daraja da duk dauke kanka akan mace baka sanin lokacin da zaka biye mata ba ne" hannu uban kowa ya kai keyarshi yana hararan likitan yana niman maganar da zai laftawa likita wanda duk lokacin da ya ganshi sai ya bashi girma na musamman, amma kasancewar watan azumi ne sai ya tsinci kanshi da kurawa likitan ido kafin ya motsa dark lips dinsa ya ce mishi"ka taɓa jin labarin na bi yan mata ba ne?" Yadda Adam yake faɗa da ihu kallo daya likita ya mishi ya ce mishi. "Akwai wasu kwayoyin halitta a tare da ita, daga lokacin da ka fara kusantar lamarinta zasu rabe ka. Daga nan idan ka shirya ka sani akwai hanyoyi da zaka gyara tsakaninku yadda. Idan ta kama ayi rayuwar aure akwai robar kariya.. kada ka sake kayi amfani da maganin tazara don masu ciwo irin nata zai haifar musu da babban matsala!" "Allah ya kare min abina ni ba dan iska ba ne! Kuma ko tsirara mace zata yi yawo a gabana ba zai taɓa damuna ba, kai idan ka ga matan da suke bina kayi karya ka gaya min magana haka." Ya juya zai fita daga office din Likitan ya ce mishi. " Idan ta farka zuwa dare zan sallame ku.. amma Adam kasan me? Kada ka yarda da kiyayya mace tana da saurin riƙe abu a ranta sannan tana da kokarin ɓoye abinda yake ranta kayi kokari ta manta da wanda take so don nasan tabbas tana da shi. Ka mai da ita sarauniyarka bincika me wancan yake mata sai ka ninka sama da haka, ka bata kulawar da ita kanta zata ji kafi kowa."mikewa likitan yayi ya nufe shi yana faɗin. "Duk wutar da kake ji ita aure ruwan sanyi ce dafa moɗa!"
Duk yadda yaso ya fahimtar da shi, sam Uban kowa yaki ya fahimta, haka dai suka fito, an mai da ita ɗakin da zata huta. Dakin ya shiga ya samu tana ta barci, shafa kanshi yayi yana kallon yadda take barci peaceful.
Wayarshi ce tayi kara, ya zaro a cikin aljuhun rigarshi, ya kalli wayar yana jin wani abu a ranshi. Dauka yayi ya saka a kunnenshi. "Hajiya ya dai?" "Ina kake? akanta aka fara auren da baa sani ba ne? Da har zaka wani kwashe ta zuwa asibiti. Ka manta alkawarin da ka ayi min ne?" Ta tambaye shi a wata irin raunanniyar murya. "Hajiya matata ce fa, sannan a yanzu haƙƙin kula da ita lafiyarta da suturanta duk yana kai na, ai kema dai ba zaki ji daɗi ba ace matar da na aura yau ta suma kuma na bar ta cikin wani irin yanayi. Hajiya ni fa bana son ana zuga ki kina wani abinda bai dace ba Fisabiilillahi. Wallahi idan baki daina biye musu ba zan dauke ta mu bar kasar nan sai ranar da kika ganni!"
"Allah ya baka hakuri, shi kenan kayi yadda kake so." Ta fada, murmushi yayi yana soka hannunsa cikin aljuhun wandonsa. Ya sauke wayar yana kallon agogon hannunsa lokacin da aka kira sallah laasar. A hankali ya fito daga dakin ya nufi waje. Masallacin da yake asibitin, yayi alwala tare da shi cikin massalancin ya zauna. Haka haduwa sannan aka gabatar da sallah. Yana fitowa daga masallacin ya haɗu da ƴan sanda biyu. Dauke kai yayi kamar bai gansu ba. "La Mayor!" Juyawa yayi yana kallonsu. "Ya zaka ga mutane amma ka dauke kai kamar ba gansu ba?" Murmushi yayi tare da shafa kanshi sannan ya cigaba da tafiya. " Kana tsoron kada yarinyar da ka aura tasan kaina din ɗan taadda ne?" Cak ya tsaya yana kallon wannan jami'in tsaron da ya je gidansa. Takawa yayi har inda yake ya sakar masa wani devilish smile, ya ce mishi. "Ni bana tsoron kowa, domin na gaya maka idan ka isa ka kama kayan da na fitar da su. Amma ka kasa to me zanyi da ragon maza, ni bani da lokacin irinka."
Ya fada yana murmushi domin yasan ya gama da jami'in tsaron,
Cikin fushi jami'in tsaron ya fito yana kallonshi, cikin rashin mutunci da yake jin zai iyawa kowa musamman El Mayor. "Sai na lalata maka suna a cikin garin nan, sai na hana ka zama a cikin garin nan."
"Karya kake Malam a haife ni a garin nan ka kore ni ai an samu matsala baka san wani ba ne amma ka kira Matarka ina ga kamar an tura mata sako yanzu gidan." Ya faɗa tare da nufar cikin asibitin. Da saurin jami'in tsaron ya ciro wayar tare da kiran Matarshi, "Hafsa an kawo wani abu ne gidan?"
Can ta bashi amsa, bai tsaya ba ya ce.maza su bar asibitin ya nufi gidansa. Tafiyar minti goma ya kai shi yana shiga ya samu an kawo musu wani ƙaton kwali. Daukan kwalin yayi ya fito da shi waje, ya shiga budewa. Kayan wasan yara ya gani.
Wayarshi ce tayi kara ya ɗauka."ka girgiza ko? Me yasa sai ka shiga rayuwata zaka ji ka gamsu? Ni fa ina gaya maka ka kula."
-----
Sai da ya gama wayar ya sake murmushi wanann ba wani abu ba ne, matuƙar mutum ya shiga gonarshi abinda zai iya fuskanta yafi haka ma, shi wani irin mutum ne baya shiga kuma baya son a shiga mishi.
Lokacin da ya shiga ya samu tana motsi jan kujerar dakin yayi ya zauna. Yana me daura daya akan daya, ya zuba mata ido cigaba da barcin tayi har zuwa karfe biyar na yamma. Kiran wayarshi aka yi ya ciro a cikin aljuhun rigarshi. Kurawa Number ido yayi, a hankali ya dauka yana mai sakawa a kunnen. "Wani asibiti ka kai min Y'ata?" Cikin sanyin murya ya ce mata. "Muna hamda!" Ya fada cikin girmamawa, yake bata amsa, kashe wayar tayi. Bayan minti talatin ai kuwa sai ga ta tare da matan yayunta, biyu sai Khamilah. Yana ganinsu ya mike tare da durkusawa ya gaishe su yana tsugunne Maamah ta cewa Khamilah "Kira mana likitan ya dubata, gidanmu zamu wuce." "Wani abu ne ya faru?" Ya tambaye su cikin girmamawa. "Ka je ka tambayi kannen Babanka!" Maamah ta fada da karfi, sunkuyar da kai yayi yana kallon kasa. "Allah ya huci zuciyarki!" "Na gaya maka ka sake min y'a ban yi niyyar amsar auren nan ba, kuma babu me yiwa yarinyata dole." Mikewa yayi ya fita daga dakin, ya nufi can Amarewat domin yasan a can aka kitsa kome.
Lokacin da ya isa ya samu ana ta hidimar bude baki, a yadda ya shiga parlourn Hajiya a fusace, ta zuba masa ido. "Uban kowa ya aka yi ne?" "Bana ce ki fita hanyar Maamah da Yarta ba? Hajiya ki kori kowa wallahi ko kuma idan na shiga na fito na bawa kowa abin da ya dace dasu yadda ba zasu manta da ni ba, yau zaku tabbatar da dalilin da yasa ake kirana Uban kowa!" Ya fita daga cikin parlourn, yana zuwa tsakar gidan ya maimaita abinda ya fadawa Hajiya kafin ya shiga bangaresu , ai kuwa bai rufe baki ba kowacce ta kama gabanta, ai yadda Allah ya daura mishi kwarjinin nan da haiba, babu inda uban kowa zai shigo yayi magana ba tare da an kula shi ba, wannan dole ce a d'aga mishi kafa. Domin wannan kwarjinin da yake da shi, ko kai babba ne dole ka sauke kanka.
Shi yasa a rayuwarshi Mutane ƙalilan yake jin kunyarsu da ganin girmansu, ba ruwansa don yana yawan cewa ya taso tsakanin titi da titi. Babu amfanin ya girmama wanda bai girman kanshi ba. A bakin Fuad yake kin labarin rashin mutuncin da Hajiya Atikah. Yadda ya shiga yayi wanka ya fito tare da nufar bangaren Hajiya. Wani irin bori da rigima, hade da fitina yake yiwa Hajiya, wacce a duniyarta bata jin akwai wanda ya isa ya mata wannan rigimar da Uban kowa yake ta dauka. Cikin fada da mita wanda hada da wani guntun wulakanci ya cewa Hajiya. "Ba an daura aure ba? Kowacce ta koma gidanta babu biki babu kome haka na shirya rayuwata kome ina buƙatar sirri da adanawa ne!"
Sake baki suka yi suna kallon yadda ya hade rai. "Kana nufin babu bikin da za ayi kana jikan da Hajiya take so! Kace ba zaa yi biki ba?"
Hade rai yayi sun san tunda ya ce ba zaa yi ba babu shegen da zai saka shi dole. "Ba za ayi ba haka na gaya muku Hajiya ki gaya musu bana bukatar kome kayan aure zan hada mata ba zan barta tsirara ba." Zuciyar Hajiya rawa yake domin gani take kamar ta rasa tilon jikanta da yake kyautata mata sama da sauran jikokinta. Bakinta cike yake da magana amma tsoron borin da zai mata yasa tayi shiru.
Sai ma lokacin suka kara kallon kayan jikinsa. Duk inda aka ga ango an sanshi da shigar alfarma da nuna yana cikin farin ciki, amma banda Uban kowa da ya saka wasu mahaukatan kaya, takalmin kafarshi kuwa wata tukikiya ce. Amma fa fess yake zuba kamshi saboda gwanin gayu ne da ado. Kawai inda aka samu matsalar shine shigar bata dace da ango ba ne. "Wannan shigar mahaukatan fa?" Inji Hajiya Turai, juyar da kai yayi ya ce mata. "Daga turu nake!" Ya kalli Hajiya yana faɗin. "Na gaya miki wallahi ban yarda wani ya kara shiga harkan gabana ba kai hatta matata ban yarda ba har ke kika taɓa min ita zaa a jimu da kowa, idan nace kowa har da ke Hajiya." Yadda yayi maganar haka yake nufi, don haka ya mike tare da fita parlourn. Yana barin parlourn Hajiya ta kalli Yaranta. "Na shiga Uku ni Asma'u, anya ba wani abu suka mishi daga aure ya juya min baya ku taya ni janyo min hankali Uban kowa!" Mikewa Hajiya Turai tayi tana fadin.
"Hajiya sai da hakuri amma wanan ita ce babin ƙaddaran Uban kowa da ke Allah yasa Rakiya kada ta juya miki yaron da yake tausayinki!" Wani irin tsoro ne ya cika Hajiya domin bakiɗaya suka hada baki tare da nuna mata auren nan fa ƙarshen zaman lafiyarta da jikanta. Sannan suka mata sallama suka barta da Atikah. Ita kuwa tana ganin sun tafi tayi ta zuga Hajiya tare da cewa akwai wani babban malami da zai mata aikin da za a raba uban kowa da Naanah Asma'u. Ita kuwa Hajiya yan kudaden da Ƴaƴanta suka bata ta haɗa ta bawa Atikah.
A kofar gidan
Iyayensa maza ya gani a kofar gidan ya nufe su tare da gaishe su. Sannan ya wuce wurin motarshi ya shiga kiran layin asibitin yayi tukun domin yana fitowa daga wanka na ga sakon likitan ya ce mishi. *Matarka fa wasu mata sun tafi da ita*
Maamah bata bukatar surukuta, zai girmama ta amma ba zai yarda da iko da Matarshi ba. Sai da ya tafi wani babban shagon sayar da kayan masarufi, yayi sayayya. Sannan ya wuce gidansu Maamah bai shiga sai da yayi sallah magriba, abinda ya bashi mamaki shine yadda Mutanen gidan musamman mazan family din Zaki Family suke ina ina dashi, sai da yaji kunyar zuwa da kayan jikinshi. Idan ka cire Mahmoud da ko kallo bai ishe shi ba, amma iyaye maza da sauran malamai na family, wani irin kulawa suke bashi, haka da suke shiga bashi abincin bude bakiɗaya bakiɗaya suka tattara kauna suka nuna mishi.. "Ya ishe ka ko a kara maka!" Inji Baban Mahmoud, "ya ishe ni!" Suna zaune a wurin wasu baki suka shigo wurin buɗe bakin, Baban Mahmoud ya ce musu.. "Ga danmi surukinmu, Adam mijin Naanah Asma'u." Mika mishi hannu mutanen suka yi cikin girmamawa ya amsa yana gaishe su shima. Bakiɗaya sai ya zama bako a cikinsu musamman da suka juya harshen Zarma songhai, a hankali ya tsame hannunsa daga cikin abincin ya cewa Baban Mahmoud.
"Kawu nazo gaida Hajjama ne!" Murmushi dattijon yayi ya ce mishi.. yasan ba wurin Hajjama ya zo ba, ya biyo matarsa ce yadda Rukayyah take ta fada baya kaunar Naanah Asma'u bai ga haka a tare da shi ba, Yana lura da yadda ya nutsu kamar akwai abinda yake son sani game da su"To ai ba kome, Sadiq kai shi ya gaida Hajjama."kasa tashi yayi don ya fahimci yadda Baban Mahmoud yake murmushi sai yaji kunya, can ya mike yana ta godiya, ya bi bayan Sadiq din tare da cewa Sadiq ya jira ya dauko sako a motarshi. Yana zuwa ya kwaso leda uku, Sadiq ya amshi ɗaya suka shiga barin wurin.
"Abbi me yasa ka sake mishi?" Inji Ya Moud, murmushi mahaifinsa yayi yana faɗin. "Da da dukiya ba a musu mugunta, sannan idan kace lallai sai yadda kake so zaka samu har abada ba zaka taɓa samu ba, ya burge ni ya kuma nunawa Rukayyah shi fa yana tare da Yarta duk abinda zata yi sai dai tayi. Aure kuma babu fashi" ya fada yana yana bin bayan Uban kowa da idanu yadda suka shiga cikin gidan.
"Abbi amma ita Naanah Asma'u bata sonshi, kuma wannan kamar auren dole ne, idan wani abu ya same ta fa?" Janye idanunsa yayi daga kansu Uban kowa ya zuba akan Mahmoud ya ce mishi."Babu abinda zai faru da ita sai ikon Allah!" Ya Moud zai kara magana Abbinsa ya dakatar da shi. "Kada na ji labarin ka ingiza ta ga kashe aurenta, idan haka ya faru har abada na maka iyaka da ita kada kuma naji kayi wani abu da zai taɓa mutuncin gidan nan ka ji ko." Gyad'a kai yayi tare da mikewa ya bar massalancin. Domin yadda yake jin zafin Uban kowa kamar yabi shi da duka.
.... Lokacin suka shiga cikin gidan, har bangaren Hajjama, duk suna tsakar gida. Masu sallah suna yi masu bude baki suna yi, Sadiq ya shiga da sallama ya ce musu. " Mijin Naanah Asma'u ne ya zo gaishe ki Hajjama."
Shigowa yayi da sallama, Maamah da take addu'a mamaki ya cikata wani irin Yaro ne Adam da bai da mutunci ne? Akan me zai biyo su, dole ta taka mishi burki, fuskarshi dauke da murmushi ya nufi gaban Hajjama ya zube tare da gaishe ta cikin nutsuwarshi. "Alhamdulillahi, Masha Allah Malam Adamu kai ne da kanka? Masha Allah sannu angona domin da ni kake auren ko?" Sunkuyar dakai yayi yana murmushi. "Da fatan an sha ruwa lafiya, ya ibada?" Ya tambaye ta, "Alhamdulillahi, ya aka ji da jama'a. Sai kuma muka ji abin arziki Masha Allah Ubangiji ya baku hakuri da juna ya kuma kara muku zaman lafiya da juna."
"Amin" duk yan wurin suka amsa, shi dai idanunsa yana kan Maamah da taki juyowa. Nan suka shiga hira da Hajjama, hira sosai a hankali hirar ta juye zuwa nasiha mai shiga jiki da jan hankali akan rayuwa da aure. Nasiha da yaji tsoron Allah ya tuna girma da hakki na aure. Ya tuna halin da Naanah Asma'u take ciki ya kalli kanshi a matsayin Uba ko yaya, ya tuna yadda rayuwar da ta taso, ya tuna cewa ita yarinya ce mai hakuri da juriya, ya tunani shi namiji ne, ya ciyar da ita daga halal ya tsaya mata a matsayin miji. Ya kula da ita a matsayin ɗan uwa, kada ya manta Allah ya bashi ikon akanta, ilimin da sauransu. A nan ne ya cewa Hajjama. "Ai ba zan katse mata karatunta ba, idan ta gama ta ce zata cigaba duk ba zan hanata ba. Idan tayi karatun nan al'ummarmu da kasar nan zata yiwa hidima, idan na hanata nima ai kaina na cutar domin kamar na tauye kaina ne, Hajjama matuƙar ina raye zan tsaya mata kai da fata tayi karatu. Sannan tana gama hutun zata koma makaranta, babu abinda zai dakatar da haka."
Cikin wani irin yanayi Maamah take jin maganar shi, sai kuma ta ji maganar ya tsaya mata a rai domin a karon farko da ta fara wasi-wasi. Murmushi Hajjama tayi tana fadin."Masha Allah Ubangiji ya cika maka burinka, ya baka ikon cika alƙawarin da ka ɗauka."
Yar dariya yayi ya ce mata. " Hajjama ko bana raye Naanah Asma'u zata yi karatu ba zata zauna a haka ba, in sha Allah."
" Allah ya raya ka!"
Murmushi yayi yana kallon fura da nono da ta turo mishi, ya shiga sha yana faɗin." Gaskiya na ji daɗin furan nan, dama yau bani da kunun sahur wannan ma ya ishe ni!" " A'a idan zaka tafi zan saka a zuba maka ka tafi da shi. "
Maamah ranta bata so hiran da Hajjama take da Uban kowa ba, ganin yadda Mahmoud ya shigo a fusace, murmushi Hajjama tayi tare da nuna mishi wuri ya zauna shima ta haɗa su bakiɗaya ta musu nasiha sosai sannan ta kalli Mahmoud ta ce mishi." Bana son tashin hankali ko wata fitina, Adamu ga Mahmoud ina fatan ba zaka shiga tsakaninsu da yar uwarsa ba ko? Kai kuma Mahmoud Adamu surukinsa ne domin yana auren Kanwarka" Gyada kai yayi amma Allah ya gani bai yarda da wata zumunci ba. Matarshi da zumunci da cousin ɗina akwai matsala babba. "Ka shiga tana kwance a dakina. Ka ga jikin nata domin ni dai ban yarda sallamarsu aka yi ba!" Ya jima yana jin kunyar yadda zai mike kafin Hajjama ta kara maimaita mishi ya mike ya ga jikin Naanah Asma'u. Haka ya tashi jikinsa a mace, ya shiga parlourn Faɗime ce zaune tana kallo a wayar Maamah, bakinta yana rawa ta gaishe shi. Ya amsa mata tare da kallonta.. "ga ɗakin can!" Ba musu ya nufi dakin da yake tashin kamshin turaren wuta. Ya samu tana dunƙule tsakiyar gadon. Hannunta dauke da ƙarin ruwan.. jan kujerar da yake gaban Mirror yayi ya zauna. "Ke ya jikinki?" Sake dunƙulewa tayi a wurin jikinta yana rawa. "Kai zo ka fita bana son rashin mutuncin da ka saba yiwa mutane." inji Moud, bude ido tayi tana kallonsu. "Husnah!" Ya kira sunanta a hankali wanda ya sanya ta kara bude ido. " Zan maka rashin mutunci idan baka fita ba." Bai kula shi ba ya cigaba da cewa." Ya jikin naki? " Bata amsa mishi ba sai ma kara lumshe idanunta da tayi. "Sannu ina yake miki ciwo?"
Kai mishi naushi Ya Moud yayi tare da fitar da shi waje, yana faɗin. "Ka fita kuma wallahi sai ka sake ta." Murmushi Adam yayi ya ce mishi. "Ni da kai babu matsala kuma babu wannan batun, wurin Matata nazo ganinta kawai sai ka saka hannu ka naushe ni ba kome ni wurinta na zo ba wurinka ba!" "Ba zata so ba dan iska mutumin banza dan kwaya dan lu.. " " kai Mahmoud!" Mahaifinsa ya daka masa wata uwar tsawa da yasa shi bai karasa abinda yake nufi ba. "Baka da mutunci dama? Me yayi zafi da zaka ci zarafinsa haka? Ban ja maka kunne akan shi ba ne?"
" Abba kayi hakuri!" Ya furta a hankali.
"Adamu dauko Matarka ku bar gidan nan, ita Rukayyah da ta ga zata iya zama bismillah ba zata kashewa yarinya aurenta ba! " "A'a naga tana barci a barta. "
" Wuce ka dauko Matarka nace!"
"Yaya idan ka min haka ba ayi min adalci ba, wallahi idan aka bashi ita wannan ba adalci ba ne."
...."Ayi hakuri nima ganinta da jikin nazo yi ba ɗaukarta nazo ba." Ya ajiye katin bank a gabansu ya musu sallama zai fita Hajjama ta ce mishi. "Idan ka samu lokaci kazo ka dauke ta!"
Kallon Maamah baban Mahmoud yayi ya ce mata. "Kin kyauta ko, kin ji daɗi ko?" Ya juya ga Mahmoud ya ce mishi. "Ina baka shawara, ka rabu da ƙaddaran kowa lafiya shi baƙin alkalami bai da wani abu wanda ya wuce rubuta ƙaddarar wanda ya mishi. Sannan ba zaɓa yake balle kace ya zaɓi nashi ya bar naka. Shi baƙin alƙalamin alkalami ƙaddara kawai ya iya rubutawa, ba hisabin rayuwar wani ba."