CHAPTER 8
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 8.*
'Yan yatsunta da yake ta murzawa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula. Maganganunsa suna ta amsa kuwwa a kunnenta, tana jinsu kamar a mafarki.
Zuba masa ido tayi na wasu 'yan daƙiƙu, bakinta ya kasa furta komai. Da kyar ta iya cijewa ta ce"Jayman... ka san abin da kake faɗa kuwa?"
Ta faɗa cikin rawar murya, kuka na shirin kufce mata.
Yallabai bai ce komai ba ya ci gaba da murza 'yan yatsunta a hankali, idanunsa a kanta. Gyaɗa kai ya yi yana ƙoƙarin tabbatar mata cewa ba wasa yake yi ba.
Sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Tabbas na san abin da nake faɗa."
Ya ɗan dakata, sannan ya ce cikin nutsuwa"Cewa na yi, Jay. Alkaleri's Kitchen, wanda ake kan ginawa a Landan, ya zama mallakinki halak-malak. Na ba ki wannan kyautar ne saboda na ga kin fi kowa cancantar mallakarta."
Jidda ta lumshe idanuwanta, tana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai nauyi da ya tokare mata maƙoshi. Wannan ba ƙaramin abu ba ne. Yallabai na neman haɗa gangamin rikici tsakaninta da iyalensa.
Gidan abincin da ya kamata ya zama babban jari a rayuwarsu, gashi an bata a matsayin kyauta.
"Amma... Jaymannnnn..."
Ta ambaci sunansa cikin tashin hankali.
"Me ya sa ka bani?"
Ya yi murmushi ya ce "Saboda kin cancanta! Wacce kika so a ba, ta nuna min bata bukatarsa. Sai na ga dacewar in mallaka miki."
Jidda ta sunkuyar da kai. Hawayen daya taru a kwarmin idanunta, ya fara shatatowa a fuskarta. Ba don ba ta ji daɗin kyautar ba, sai don ganin kyautar na iya zame mata matsala.
Cikin kwantar da kai ta ce" Ranka ya daɗe! Nagode da wannan gagarumin kyautar amma kayi hakuri ba zan iya karɓa ba. Kar ka manta fa ni ce da kaina na baka shawarar mallakawa Samha Gidan abincin nan da muke ganin zai fi kowani gidan abincinka shahara. Mai yiwuwa yin hakan zai sa ka tsiratar da ita daga halaka ta dawo hanya mai kyau. To, don me zaka dawo ka maida kyautar kaina?"
Fesar da iskar bakinsa ya yi yace" To, Bukatar ki bata samu biya ba don maida hannun kyauta baya tayi. Kai tsaye tace min tafi samun alot of benefits da GIDAN MATA. So you see ai bazan mata dole ba, ko Allah ya gani nayi iyakacin bakin k'ok'arina na ganin Samha ta dawo kan hanya amma abun yaci tura. Kin ga Jidda, in zaki amshi wannan kyautar ki amsa tun kafin kema in canza ra'ayi akan ki. kuma kibar kawo min maganar Samha lamarin ta ya isheni haka, taje tayi duk abin da taga dama duniya ce kuma ta ishi kowa riga da wando."
Bata ci musu ba ta karɓa takaddun ta sa hannu.
Shikenan ta faru ta kare JAY. ALKALERI'S KITCHEN LONDON Wanda Ahalin Yanzu ake kan ginawa ya zama mallakin Jiddatulkhair.
Tana gama sa hannu ta miƙa masa takaddun tana hawaye. Cike da farin ciki Yallabai ya ce"Alhamdulillah! Yau Jiddatulkhair ta samu abin dogaro na kanta wanda ya fito daga halaltacciyar hanya. Ga sunanki dama ya fara da harafin 'J' kin ga waƴanda basu sanni ba za suyi tunanin gidan abincin ma naki ne."
Ganin abun take kamar a mafarki wai ita ce yau Allah ya ɗaukaka haka? Dama ita ɗaukaka baiwar Allah ce ta kan je wurin da Allah ya aiketa ne. Bata tsallake kowa matukar wajenka aka mata aiken.
Ita ɗin ta kasance mai saɓawa mahaliccin ta amma hakan bai hana shi lullub'eta cikin ni'ima ba. Taci kuka sosai kamar ranta zai fita bayan tafiyar Yallabai, tana mai nadamar rayuwar da tayi kafin aurenta.
Wani irin tsananin tsoron Allah ne ya shigeta ta kuma dau alƙawarin bazata sake bari ta koma ruwa ba koda ya kasance yau sun rabu da Yallabai.
Gashi har ya tafi bata iya labarta masa yadda suka kwashe da Samha ba sanda ta gayyaceta gida take faɗa mata kyautar da Daddyn nata ya yi mata amma take so ta mayar da hannun kyauta baya, ashe dai a ƙarshe kyautar kanta zai dawo.
Allah kenan mai yadda yaso ashe dai rabonta ne. Malam bahaushe yace"Rabon ka baya wuce ka koda ahannun makiyinka ne."
Sai dai tana matukar tausayin Samha, gani take ta mata illa sosai wanda zai yi matuk'ar wuya ace Samha ta yafe mata. Ita dai tana ta gayawa Allah ya kawo lokaci mafi alheri da zai fi dacewa iyalansa su san da ita.
**Ina labarin Saffy ?**
Batun ta ne ya fad'o mata arai ta hau salati don gabaki daya tashin hankali yasa ta yasar da zancen yar'uwan nata. Babu b'ata lokaci ta jawo waya ta nemeta, adaidai wannan lokacin kuma Saffy na k'ofar dakinta ta aza sanwar dare akan 3kg gas ɗinta. Jollof ɗin Shinkafa take girkawa kuma kaɗan ya saura ruwa ya tsotse.
'Yan matan gidan kowa na kai da komo kowacce na harkan gabanta, babu wanda ta kula aciki don ba shiri take da dasu ba. Sai Sady wacce tayi sanadin zuwanta Gidan mata, sannan kuma makobciyar ta mai suna Lulu amma shirin su sama-sama ne duk da taga yarinyar tana neman shisshige mata amma bata sakar mata fuskar da zata samu damar shiga jikin ta ba.
Wayarta ta ji ya hau kururuwa yana neman agajin ta. Ganin Jidda ke kiranta yasa farin ciki ya cikata fal. jiki na rawa ta shige daki bayan ta d'aga tana" Salamu alaikum Yaya kina lafiya ? Nayi matuk'ar kewar ki."
Ta furta ayayin da hawaye masu dumi suka biyo bayan furucin nata.
Murmushi Jidda tayi tace" K'anwata ni kaina nayi kewar ki shiyasa na kira ki. Kuma ki kwantar da hankalin ki ina cikin koshin lfy, ina fatar kema kina lfy ?"
"Sumul nake yaya ban ma jima da dawowa daga wajen gyaran kai ba yanzu haka ma sanwa nake.
Cike da tsokana Jidda tace" Sannu Safiyya shugaban 'yan ado kenan dama bakya ɗaukan na karshe in har akan ado ne."
Murmushi tayi mai ciwo wanda ya samu rakiyan sabbin hawaye masu zafi tace" hmm yayarmu kin dai manta ne amma karshen ado ai yana ga Zaynab ne, ni ko kama kafar ta ban yi ba"
Ta ida magana muryatta na rawa sosai. Furucin da tayi ba karamin jefa Jidda cikin sabon tashin hankali yayi ba.
Meyasa Safiyya ke neman fama mata tsohon gyambo na zuciyar ta?
Meyasa take neman tuna mata da Zaynab ?
Kuka ta fashe dashi mai d'aga hankali wanda yasa Saffy nadamar tuno mata da babban rashin da suka yi. Ita Jidda tayi rashin yar'uwa na har abada ayayin da ita kuma Saffy tayi rashin yar'uwa kuma aminiya.
"Yayarmu dan girman Allah ki gafarceni banyi niyyar sakaki kukan Zaynab ba."
Saurin taran numfashin ta tayi"Ai In dai Zaynab ce bazamu tab'a daina kukan ta ba, Allah dai yayi mata rahama yasa Aljannah makomar ta."
Saffy ta amsa da "Ameen." Kana ta cigaba" Yaya wai ina kika shiga ne haka kin dai hana mini ganin ki ko?"
Jidda tace"Shiyasa na kira don in baki izinin zuwa Inda nake, dama ina gari ban je ko'ina ba amma kiyi shiru karki sanar ma kowa inda nake, kawai ki samu lokaci ki zo."
Nan take ta mata kwatancen unguwan da take tare da sake Jan kunnenta kan kar ta kuskura ta gayawa wani Inda take.
Saffy tace" In Allah ya yarda bazaki samu matsala dani ba. Ina nan zuwa goben in sha Allah."
Bayan sun kammala waya ta fito da sauri don ta san shinkafar ta dahu. Tana buɗe murfi ta ga abun mamaki, shinkafar ce aka diba ya rage kaɗan a tukunya.
"Jar ubaa! Waya kwashe min abinci a kan wuta?"
A daidai lokacin Lulu ta fito ta kalleta ta ce"Ai idan kina girki a gidan nan sai kin sa ido sosai idan ba haka ba kina tashiwa zaki samu wata 'yar iskar da za ta fakaici idonki ta buɗe tukunya ta kwashe miki abinci."
Cike da rashin fahimta Saffy tace" Ban gane ba.. ya za ayi in ɗora girki a wuta sannan wata 'yar iska ta zo tasa hannunta mai najasa ta dibar min abinci? yanzu-yanzu na shige daki ai kina kallo akamin waya na shige amma sai in fito in ga an min wannan ɗanyan aikin? To, duk 'yar iskar da ta min wannan aika-aikar ta nuna kanta idan ba haka ba sai na nuna muku na fiku hauka."
Sai da ta kashe gas don har shinkafar daya rage a tukunya ya fara ƙonewa sannan ta girgiza kai ta ce cikin ɗaga murya"Ina ga baku san wacece Saffy ba, amma yau zan nuna muku kalata. Bana shiga tsabgar kowa amma duk 'yar macen da ta kuskura ta shiga nawa tsabgar sai naci tsakiyar uwarta. A fito min da shinkafa ko In hana Zaman lafiya a gidan nan yau."
Kafin kace meye wannan matan dake gida waɗanda basa bari ta kwana balle tayi tsami sun firfito kamar tururuwa.
'Yar Gala data fi kowa jin takaicinta ta kama baki tana fad'in"Iyyeh me nake gani haka ? Ina ruwan 'yar jeji an fara wayewa. Ido ya fara buɗewa, bariki kenan me mayar da yarinya da ke kwana da wandon maza fitsarriya mara kunya."
Wata ta cafe ita ma tana murza ido don ta tabbatar lallai Saffy ce ke kakatutun rashin mutunci yau abunda da wuya kaji ko sautin muryatta na tashi" Ikon Allah da alamu yarinyar nan yanzu ta fara riƙe kaciya don naga idanunta kamar sun tsaya ba kamar da da suke rawa ba."
A fusace Saffy ta nuna ta da 'yar yatsa tana"Ke! ki iya bakin ki don wallahi banda Mutunci kar ku ga ina shiru ina ƙyaleku kuna gurza min rashin mutunci wallahi nafiku hauka, shegu masu bakin iyaye ko a fito min da Shinkafata ko in nuna muku ainihin kalata wallahi."
Tuni aka yo caaaa! A kanta rigima ya kaure sosai har ana shirin dambe, masu rabo nayi masu zigi nayi amma fa sosai suka tsorata da yanayin Saffy don gabaki daya yau ta canza musu, ashe haka take kamar 'yar daba basu sani ba? Lallai shiyasa akace in kaga mutum kawai ka k'yaleshi karka raina masa. Shigowar ta gidan afarko ta nuna musu halin 'yar wahainiya ne, irin babu ruwanta ɗin nan ashe nan dai turmin Zani ce.
Ji ta yi ance "Ni ce nan na ɗibi abincin naki kuma kika sake furta wata kalma sai na ci uwar data haifi ubanki."
In ji ta bakin isasshiyar gidan wato SALA da rigima ya zama ruwan shanta. Bata jima da shigowa ba kuma ta dawo a gajiya ga yunwa shine ta fito da filet ta fakaici idon kowa ta ɗibi abincin Saffy. Dama ita kowa ya santa da wannan mugun halin, kwata-kwata bata son girki. Idan kasa sanwa sai kayi tsaye a kansa idan ba haka SALA da ire-irenta sai su ɗibar maka.
Saffy ta ce"Kuttttt! Dama ina da cikinki kuma yau sai na haifeki."
Sai da akaci Uwar Sabada tsakanin Saffy da SALA don sosai ta zage tana Zagin Saffy hadda kiran ta da mayunwaciya babu agidan mai dattin hula shiyasa aka zo GIDAN MATA tunda anan baka neman komai ka rasa ta fannin ci da sha da kuma wajen kwana.
Hakan data faɗa ya harzuka Saffy ta faffalla mata wawan mari. Dukan kawo ɗauki Saffy tayi wa SALA dakyar aka kwaceta ahannunta bayan ta tabbata ta fasa mata baki kan ta sarara don ƙarfi take ji dashi sosai kamar doki.
Tace tana Wani irin Girgiza"Kun ga abin da nayi ma mataimakiyar shugabarku ko? To ina ganin daga yau na goge duk wani rainin da kuke min acikin gidan nan In kuma abunda na mata bai isa ya koya wa wata 'yar yarinyar hankali ba to bismillah wata ta matso kusa In sake cire almatsusan kanta."
Da baya baya suka fara ja ganin tana nannaɗe hannun long sleeves ɗinta, daga can nesa SALA dake goge bakin ta dake zubar jini tace cikin rauni"wallahi kinyi zubin adashi dani wanda kwasan shi zai baki matuk'ar wahala. Kuma wallahi In har sunana SALAMATU sai na tabbata nasa gidan nan ya gagareki Zama sann……."
Bata karashe ba Saffy ta bita aguje, habawa ai bata tsaya ba ashe duk cika bakin na banza ne. ‘Yan gida nata dariya ganin yau dai an samu mai maganin mataimakiya a gidan.
Haka Saffy ta cigaba da bambami kowa sai mamakin ta yake tayi kuma sosai suka sha jinin jikinsu. Gashi an kasa samun wanda zai bada sanarwa agroup don uwarɗaki ta san halin da ake ciki, kowa gudun abunda zai biyo baya yake balle abu ne daya shafi mataimakiya kuma duk wanda ya sake ya yi kararta sai ya ci ubansa.
Abincin daya rage Saffy bata iya ci ba, karshenta ma almajiri ta bawa sadaka ita kuma tayi wanka ta shirya ta fita siyan takeaway awaje.
***
Haj. Nafeesa na zaune kan daya daga cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun katafaren falon gidan. Idanun ta akan gingimemen talabijin ɗinsu tana kallon wani shiri atashar Arewa24 amma a zahiri hankalin ta ba'a nan yake ba tayi nisa sosai cikin tunani. Kallo daya kawai zaka mata ka karanto tsantsar damuwar da take kunshe dashi.
Nan jira kawai take taji kira daga wajen kasurgumin Malamin ta Wanda aka jima ana damawa dashi, ta sanadiyyar taimakon da yake bata ne ma ta samu ta shawo kan Yallabai har ya aureta sannan duk abubuwan da Samha ke yi kuma ya zuba mata idanu bai dau mataki ba duk aikin ta ne. Kulle masa baki tasa akayi, kai hatta da bakin jama'a sa wa tayi aka rufe bakunansu akan Samha sai dai ido. Shiyasa har iyau hukuma ma taki maida hankali tayi kwakkwaran bincike agame da lamarin GIDAN MATA. Sai dai kuma abunda ta manta shine duk abunda mutum yake yi Allah na ganin sa kuma watarana dole dubu zai cika.
Wayar ta daya hau kururuwa ne yasa ta dawo hayyacin ta lallai kuwa wanda take ta jiran kiran nasa ne. Jiki na rawa ta d'aga bai jira tayi magana ba yace cikin tashin hankali da kakkausar Murya"Nafeesa kina jina ? Wallahi akwai matsala babba."
Gabanta ne yayi wani irin bugawa kamar kirjinta zai fashe, itama cikin maɗaukakin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Malam na shiga uku meyake faruwa ne ?"
Sai da Malam Shagala ya ja numfashi ya fesar kan yace"Zargin ki ya tabbata gaskiya, Mijin ki na tarayya da wata a waje. Wani karin tashin hankalin shine yarinyar tana da ɗauke da yaron ciki amma bai kai ga zama ɗan mutum ba."
Wani irin Sabon Tashin hankali ne ya mata Sallama ta miƙe tsaye gami da fashewa da kuka tana"Ni Nafeesa na shiga Uku haba biri yayi kama da mutum shiyasa Jalal ya canza min gaba ɗaya ma bata ni yake ba ashe wata karuwar ce ya ajiye awaje suna cin amana ta."
Saurin Taran Numfashin ta Malam Shagala yayi"Ai duk laifin ki ne, da kina yin abin daya dace da tuni mun daɗe da kau da wannan gagarumin matsalar. Ance miki dole duk karshen wata zaki dunga bada kudin shanu biyu da baƙaƙen akuyoyi biyu ana zubar da jini sabida aikin ki babba ne kuma ya kasu Kashi uku. Ga aiki kan Mijinki, ga naki ga kuma aikin ‘yarki amma bakya cika alkawari dole yasa kika fara ganin ba daidai ba don aljannu sun fara fusata. Kina da shegiyar maƙo bazan ɓoye miki ba Hajiya Nafeesa sai lokacin da kika so kike bada abun sadaka kuma abunda aljannu basa so kenan, kamar yadda kike jin daɗin aikin da suke miki haka kema yakamata ki faranta musu kiyi abunda suke so."
"Ma….malam…" Ta ce cikin rawar murya.
Da sauri ya ce" Ni dai a yanzu shawarar da zan iya baki shine ki hanzarta yin abin da ya dace da wuri kafin kizo kina cizon ɗan yatsa don muddin kika sake aka haifi Wannan ɗan to tabbas kin gama yawo. Ciki ne wanda haihuwar sa zaizo ne da albarka, mahaifin sa zai yi matukar alfahari da haihuwar sa, haka duniya zatayi alfahari dashi, kuma haihuwarsa zai kara ninka soyayyar mahaifiyar sa da darajar ta awajen mahaifinsa ke kuma zaki wulakanta Nafeesa, wannan shine iya abunda zan iya gaya miki abinciken dana yi. Wasu abubuwan dana gani ma baki bazai iya furta wa ba don zuciyar ki zata iya bugawa."
Sabon Kuka ta fashe dashi mai d'aga hankali har tana zare dankwalin kanta tace" Wayyooo ni Nafeesa Jalal na neman tona min asiri, Malam zan maida hankali in yi duk abunda kace in har zan samu cikar burina. Yanzu meya dace ayi ?"
"Ba maganar waya bane kiyi k'ok'arin kawo kafar ki Inda nake asan ta inda za'a fara bullowa. Kuma ina mai gargaɗin ki kar ki kuskura ki tada wani hayaniya ko nuna kin san halin da yake ciki, ki danne zuciyar ki. ki bari mu bullo musu ta karkashin k'asa amma kika kuskura kika nuna masa kin san komai to shikenan zaki b'ata mana aiki."
Sai daya gama gindaya mata sharuɗɗa tass sannan ya kashe wayar bayan tayi masa alkawarin ganin ta acikin wannan satin.
Idan ma za'a bi ra'ayin ta bata ki ya ganta Zaria awannan daren ba amma sai ya nuna mata washegarin nan zai tafi can garin Agadez aiwatar da wani aiki.
Duk da sanyin Ac daya karaɗe falon hakan bai hana Haj. Nafeesa haɗa uban gumi na tashin hankali ba. Sai kai da komo kawai take tayi tana zubar da ruwan hawaye masu ɗumi, ga zuciyar ta na zafi kamar ana hura mata wuta.
Duk yanda zatayi koda kuwa zai zamo karon ta na farko na Kashe mutum ne to wallahi sai tayi akan wacce take k'ok'arin raba miji da ita. Koda Yallabai ya dawo danne zuciyar ta tayi kamar yadda Malam ya umarce ta da tayi, bata nuna masa komai ba shi kansa yayi mamakin sanyin da tayi ba kamar zafin data nuna kafin fitarsa da safe ba.
***
Washegari Ko ƙarfe goma Saffy bata bari ya riske ta agida ba tayi wajen yar'uwar tata tare da taimakon Kwatance sai gata akofar gidan. Jidda ce ta fito cike da farin ciki ta jagoranceta zuwa ciki suna masu murnar ganin Junansu.
Sai santin ɗan madaidaicin gidan saffy take tayi har ta kasa hakuri tace"Yanzu Yaya kina nufin nan ɗin gidanki ne ? wallahi yayi min k'yau sosai kekam kin gama kuɗancewa abinki."
Murmushi Jidda tayi tace"Nagode kanwata kema In sha Allahu watarana zaki kasance cikin ni'ima fiye da wanda ni nake ciki ayanzu."
Girgiza mata kai Saffy tayi tana" Hmm amma ba haka muka so mu yi kuɗi ba ta hanyar siyar da mutuncinmu. Sai dai duk abin da ya faru damu laifin iyayemu ne.
Fashewa da kuka duk sukayi tare da rungume Juna daidai lokacin suka ji tsayuwar mota a kofar gida......
NAGODE ALL❤️