BABAN KAWATA

Chapter 40(mini chap)

by @smauta

Kokowa aka shiga yi da manar ta kankame kaka saida dede ta daka mata tsawa sannan ta shiga taitayin ta ki sani yanzu a ƙarƙashin wani kike kin tambayi izinin shi jin abinda dede ta fada yasa da sauri khalil ya koma cikin gida yana ayyanawa a ranshi bazan iya barinki ba,sai lokacin kaka tayi mata ta manya tace wuce ciki ki nemo izinin mijinki muna nan saimu tafi aiko ba musu harda gudunta tayo cikin gidan............





Dukkansu dariya sukayi kawu labaran ya fada motar shi driver ya tada tasu kawu na biye dashi wurin coffee chairs dinsu ta sameshi kasa ta zube dan Allah zanbi su kaka,kallonta yayi daga sama har kasa yace haka ake tambayar miji idan za'a fita da baace kizo ki fadaman ba ma da bazakizo ba,ba inda zakije go and eat kafin raina ya ɓaci............





Da sauri ta dago suka hada ido kafar shi ta rike gamm dan Allah kabarni wata na nawa bana tare dasu daria ma ta bashi dagota yayi ya kara maimaita mata bazakije ba rushewa tayi da kuka ta fada jikin shi taro ta yayi ya rike gammm parlour suka dawo idan na barki ki tafi kinsan inda suke ne?kamar fa sun tafi basaso ma ki bisu da jajayen idanuwanta ta kalle shi alamar kamar ya????






Gaban window parlour yaje ya dage labulen aikuwa ta leka basu ba alamun su,fuuuuuuu ta wuce sama kamar zata tashi daria ma ta bashi baby girl rigima bayanta ya biyo baibi ta kanta ba dakinshi kawai ya shige yasan yau akwai drama wanka yayi kawai yayi kwanciyar sa,daga gefen manar kuwa taci kuka harta gode Allah wanka ta shiga tayo a gaban mirror ta zauna tana shafa mai a jikinta karar kofa taji an buɗe ko ba'a fada mata tasan waye dan zuciyarta ta fada mata mai zuwan.............





Ta cikin mirror ta hango shi kara daure fuska tayi gammm a hankali yazo ya tsaya bayanta ya dora hannunsa akan kafadunta ta cikin mirror suka hada ido baby girl ya furta cikin salon lallashi ban hanaki binsu ba dan ranki ya baci dan Allah karkiyi fushu dani kinji durkusawa yayi a gabanta ya kama hannayenta biyu kalleni Manar,ta dago ni Ibrahim khalil nayi maki alwashin duk lokacin da kikeson ganin kaka ki fadaman zakije amma kaka dince tace bazaki bisu ba kinga ki daina fushi dani ba laifina bane kaka uwa ce a garemu dole mubi umarnin ta koda munaso ko bamaso indai muna neman albarka....


Yayi shiru shafa kumatunta yayi yace kin karaman kyau da sauri ta kalli mirror dagaske?dariya ma ta dagaske nake sarauniya taaaaaa tashi tsaye tayi ta rungume shi da karfi har tuntudo take yi wata ajiyar zuciya ta saki duk lokacin da ta kasance da mijinta wata natsuwa ta musamman ke zuwar mata,kinyi hakuri ko da sauri ta daga masa kai alamar eh ɗaukar ta yayi cak kamar yarinya ya zaunar da ita gefen gado ya jawota jikinshi ta kwanta a kirjin shi lufff wannan daren ya shafa gashin kanta bana kowa bane naki ne shuru tayi baby girl magana nake a kunya ce tace your wish is my command.....