HARAMTACCIYAR GADA

CHAPTER 9

by @hafnancy

HARAMTACCIYAR GADA.

*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.}*🔥💔

NA

HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).

SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.

BOOK 1

PAGE 9.

Saffy ta sake ƙare wa ko'ina kallo, hawaye na ci gaba da zubo mata. A hankali ta ɗaga kai ta zubawa Jidda ido ta ce "Yanzu Yaya... kina nufin nan gidan ake biyoki a yi duk abin da ake so da ke, sannan a biyaki?"

Ta yi tambaya cikin ɗacin rai tana share hawayen daya gangaro mata kan kumatu.

Jidda ta ce"Eh, nan ne amma meyasa kika yi tambaya?"

Cikin jin nauyi Saffy ta ce"Ki yi haƙuri, na yi wannan tambayar ne saboda na tuna ranar da kika yi min faɗa a kan kai maza gidan mata. Kin ce min idan kana son muamala da wani, sai dai ka fita ka haɗu da shi a wani wuri, amma ba a yarda ka kai shi cikin gidan ba."

Jidda ta fahimceta amma kafin ta kai ga bata amsa, suka ji ana buɗe gate. Da sauri Jidda ta miƙe ta nufi taga tana dubawa, Yallabai ta gani yazo yana so ya shigo da mota ciki.

Ta juya ta kalli Saffy tana cewa"Maigidan ne."

"Maigidan? Ashe ba ke ce maigidan ba?"

Jidda ta murmusa ta ce"Zan warware miki komai amma a yanzu dai ki gyara zama ga maigida nan shigowa."

Saffy bata ce komai ba don ta fahimci kamar gidan bana Jidda ba ne. Wani ne ya kawota ya ajiyeta ya kuma mayar da ita matarsa yana biyanta kuɗi mai tsoka don ko ranar data tura mata dubu ɗarin nan sai da tayi mamaki. Ashe dai babban kamu ne ta yi.

Yana shigowa kallo ɗaya ya yi ma Saffy ya ɗauke kai, tana gaishe ma shi ciki-ciki ya amsa, kana ya nufi bedroom ransa a matuƙar ɓace. 

Bakin ciki kamar ya kashe Saffy don a rayuwarta ta tsani wulakanci. Bin ƙeyarsa tayi da harara da siririn tsaki, sannan ta mayar da kallonta ga Jidda ta ce" Amma Yaya a gaisheki dama can kina da ɗaukar ƙaniya, ni kam bana iyawa wallahi." 

Cike da mamaki Jidda ta ce"Meya faru ?"

"Yanzu ke baki ga abin da ya faru ba ? har yaushe ni Safiyya zan bari wani ƙato ya shigo min gida, kuma kai tsaye ya wuce ya shige uwar ɗaka yana wani jin kansa ai wallahi bai isa ba sai kace...." 

Da sauri Jidda ta kai hannu ta toshe mata baki ta ce kasa-kasa" Saffy ki shiga hankalinki, kar ki sake kiransa da ƙato a gabana don baki san matsayinsa a gare ni ba. Kuma ni ban ga laifinsa don ya nuna jin kai ba tunda gidansa ne.

"Yanzu kina nufin wannan mutumin har ya fi ni matsayi a wajenki uhmmm Yaya Jidda?" Saffy ta yi tambaya cikin ɗacin rai.

Jidda ta kwantar da murya ta ce"Ki yi hakuri zan je in same shi don bai kamata ace ya shigo ban je na masa maraba da zuwa ba."

Har ta yi gaba sai kuma ta dawo tana kallon Saffy da mamaki ya cikata na ganin yadda Yaya Jidda ke jin tsoron mutumin da shi ba mahaifi ba kuma ba miji ba.

"Saffy don Allah ki saki ranki zamuyi magana idan na fito. Kuma ki ɗaure ki ci abinci na ji kin ce baki karya ba kika fito."

"To.." kawai ta ce, sannan ta kalli gabanta soyayyen arish ne da aka lulluɓe da soyayyen ƙwai da kuma peppered chicken a wings a gefe. Ga kuma kayan tea da flask da zata haɗa shayi.

Jidda na shiga ta same shi har ya kwaɓe rigarsa, ya rage daga shi sai farar singlet da jeans, zaune bakin gado yana shigar da bayanai a system na gidan abincin da ake kan ginawa daya mallaka mata.

"Jayman welcome."

Ta faɗa bayan ta yi hugging ɗinsa cike da so da ƙaunarsa.

Ko ɗagowa ya kalleta bai yi ba ya ce "How you?" 

Ta ce"I'm fine alhamdulillah."

 "Kun yi break?"

Cikin mamaki ta ce"Break? Ni da wa?" Tayi tunanin ko Saffy yake magana a kai.

Ta ji ya ce"Daga yanzu idan nayi tambayar kun ci abinci? Ina nufin ke da babyna da ke rayuwa a mahaifarki."

Zama tayi gefensa tana kyalkyala dariya ta ce"Na fahimta, ni da shi mun ci mun yi nak! Yauwa Jay baka ga baƙuwa a falo ba ne? Ban ji kace min komai ba."

Kallonta ya yi ya ɗauke kai yana"Kin faɗa min zakiyi baƙuwa? Baki faɗa min ba and I'will pretend as if I didn't see her."

Tana so ta masa bayani ya yi maza ya ce"Alkhairi please je ki sami baƙuwarki kin ga ina aiki ne mai matukar muhimmanci a nan."


Da sauri ta kai dubanta kan system ɗin. Sunanta ne ta gani farko a heading ɗin bayanansa. Aka sa _Jiddatulkhair Kabir_ a kasansa kuma aka rubuta _Owner of JAY.ALKALERI'S KITCHEN LONDON._

Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke amma bata ce komai  ba ta tashi zata bar masa ɗakin, har ta kusa ƙofa ta tsinkayi muryarsa yana tsokanarta.

"You pretend as if you didn't see anything."

Ta juyo tana murmushin ƙarfin hali ta ce"Sunana kawai na gani."

Da sauri ya ce"Sai me?"

Ta ce"Shikenan."

"Lalalalaaaa karya kike yarinya...me kika gani? Owner of what?"

Kunya yasa ta rufe fuskarta da tafin hannayenta sannan ta ce"Owner of JAY.ALKALERI'S KITCHEN."

"Yauwa! Shikenan je ki."

Ta ce"Jayman godiya nake."

"Thank your wonderful God." 

Ya furta yana lumshe ido. Yana kallo ta fice da sauri tana farin ciki.

Tana zuwa ta ga Saffy tayi break amma bata ci abincin sosai ba wai ta ƙoshi.

Ta zauna suka fara magana ta ce"Safiyya ban san ya zaki ji wannan maganar ba. Amma gaskiyar ita ce Shi wannan mutumin da kika gani ya shiga ɗaki..ba mutumin da kike zato ba ne, shi ɗin mijina ne."

A razane Saffy ta ce"Kamar ya mijinki? kina zaune a nan tare da namiji kuna rayuwa, sannan ki ce min shi mijinki ne? A kan me zai zama mijinki bayan ba a shaida ba?"

Jidda ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani iri a ranta don tambaya ce da take tsoron ayi mata shi.

Ta matsa kusa da Saffy, ta riƙe hannunta.

"Safiyya..."

Ta ambaci sunanta cikin sanyin murya.

Sai da ta ɗan yi shiru, sannan ta ci gaba da magana cikin damuwa.

"Dama na san ba lallai ki yarda da abin da kika ji ba."

Saffy ta ƙura mata ido kafin ta buga tagumi ta ce,

"To ki faɗa min, Yaya. Ni kam ina son jin gaskiyar magana daga bakinki."

Jidda ta lumshe idanunta na wasu daƙiƙu, sannan ta buɗe su a hankali ta fara bayani daki-daki.

"Ina so ki sani an shaida aurena kuma ƙanin Abie da ke Jimeta wato Abba Habibu shine ya bada aurena ga wannan mutumin."

Saffy ta ɗago kai da sauri tana faɗin "Abba Habibu? Ƙanin Abie dai dana sani?"

"Eh, wajensa aka je aka nemi aurena."

Saffy ta yi shiru, zuciyarta na bugawa.

"Ba tare da sanin Abie ba?"

Jidda ta gyada kai. "Tabbas, ba tare da saninsa ba. Ai da Abie ya sani kuma dole zaku sani."

"Amma Yaya... me ya sa?"

Jidda ta sauke numfashi mai nauyi.

"Saboda na san halin mahaifina. Na san da ace wajensa aka je neman auren ba zai taɓa bari a ɗaura aurena da wani ba. Shi yasa aka yi komai cikin sirri. Abba Habibu ne ya karɓi maganar. A wajensa aka yi abin da ya kamata, sannan aka ɗaura mana aure bisa yadda addini ya tanada."

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba

"Bayan Abba Habibu da mutanen dake da kusanci da mutumin dana aura, babu wani wanda ya san da batun aurenmu."

Saffy ta kasa magana saboda tsananin mamaki, Jidda bata damu ba ta cigaba da bayaninta tana kallon cikin idanunta.

"Ba zaman ɗadiranci nake yi da shi ba, Saffy. Ba zama nake a gidansa yana yin abin da yaga dama dani yana biyana kuɗi ba. Shi ɗin mijina ne da aka ɗaura mana aure kimanin wata uku kenan."

Ta ɗan haɗiye yawu a lokaci ɗaya hawaye na zubo mata.

Ta ce"Kuma kafin a ɗaura mana auren, mun tsarkake kanmu. Mun yanke shawarar barin duk abin da bai dace ba, muka bi hanyar da ta halatta. Ana ɗaura auren muka tafi ƙasa mai tsarki domin ƙara tsarkake kanmu, daga nan muka tafi honeymoon a scotland. Amma ita uwarɗaki gani take kamar manemi na ne ya tafi dani muje mu shakata. Yanzu maganar da nake miki ina da ɗauke da rabo na juna biyu."

Saffy ta ce"Har kin samu juna biyu? To, Amma Yaya ni abin da ya ɗaure min kai shine, ya za ayi kina da auren wani a kanki kuma kina rayuwa a gidan mata?"

Jidda ta murmusa ta ce"Nan shine gidan da nake rayuwa, gidan mata kuma a yanzu aiki ke kai ni. Amma ina so ki sa a ranki kamar har gobe ina rayuwa ne tare da ku a gidan, saboda gidan mata mafaka ce da ta rufa min asiri."

Ta fara shessheka kana ta ci gaba da magana"Ki sami, Yau ko bana tare da mijina gidan mata zan koma don nan ɗin ne nake kira da gida. Mazauna gidan kuma nake kiransu da ahalina, ita kuma mai gidan nake mata kallon uwa a gareni."

Saffy ta fashe da kuka tana faɗin "Gaskiya bamu yi dacen iyaye na gari ba, yanzu duk wanda ya samu labarin mun gudu mun bar gida tunaninsa zai bashi cewa duniya muka shiga ba tare da sanin cewa ba bisa son rai muka ƙulla abota da ita duniyar ba...."

"JIDDA...."

Suka tsinkayi muryarsa yana kiranta cikin tsananin ɓacin rai daga can ɗaki.

Jidda da Saffy suka kalli juna kowa da tunanin da yake a kansa. Ita dai Jidda ta san babu mamaki ransa a ɓace take, a yayin da Saffy take ganin kamar shi ɗin namiji ne me zafin kai.

Jidda ta amsa da"Na'am" sannan ta tashi ta kalli Saffy ta ce"Ina zuwa..."

Tana shiga ɗaki sai da gabanta ya yi mummunar faɗiwa ganinsa yana jeka ka dawo a cikin bedroom.

Yana ganinta ya ce cikin ɓacin rai"Ki je ki sallami baƙuwarki na gaji da ganinta a gidan nan."

"Jayman wannan ba baƙu.... "

Cikin ɗaga murya ya katseta"Ki je ki sallameta ko kuma ni in fita in sallameta."

Da sauri ta juya ranta ɓace tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ke taso mata don kar Saffy ta fahimci komai.

Tana zuwa ta ce"Saffy ki je zan nemeki."

Saffy ta ce"Yaya lafiya kuwa? Ko wani abu ne ya faru?"

"Babu abin da ya faru kawai akwai abin da za ayi masa ne yanzu haka."

Saffy ta taɓe baki ta ce" Yaya ni dai zan faɗa miki gaskiya, wannan aure da kika ce kin yi in har kin san kina fuskantar matsala to tun wuri kisa ya baki takaddarki babu dole a ciki."

"Ni babu wata matsala da nake fuskanta, Ki tafi za muyi magana."

Bayan sun bar falon Saffy ta dubeta da kyau ta ce"Wani irin aure ne wannan ace mijinki ya kasa nuna kansa in gan shi ko don a san juna?"

Jidda ta murmusa ta ce"Ki kwantar da hankalinki a sannu zaku san juna, amma ina rokon kisa riƙe min sirrina domin kakaf gidan mata har uwarɗaki babu wanda ya san da cewa na kafa rayuwar sirri da wani."

A sanyaye Saffy ta ce"Kar ki damu Yaya, kin fi kowa sanin halina, akwai ni da riƙe sirrin wani in binne a ƙasan raina balle kuma ke? Babu wanda zai samu labarin rayuwar sirrin da kika kafa daga gareni."

"Nagode yar'uwata. Nima ina ganin gobe ko jibi zan shigo gidan mata."

Suka yi sallama sannan ta koma ciki bayan ta rufe gate.
 
Tana shiga ɗakin ta jiyo motsinsa a banɗaki da alamun ya shiga kama ruwa ne. Rai ɓace ta tsaya gaban madubi tana kallon yadda ta ɗan faɗa a ƴan kwanakin nan sabida shigar ciki, a lokaci ɗaya tana mamakin irin kora da halin da ya yi ma Saffy.

"Yanzu abin da ki kayi a ganinki kin kyauta kenan?" 

Ta ji ya watso mata tambaya bayan ya fito daga banɗaki. A hanzarce ta waiga ta watsa masa dara-daran idanunta masu matuƙar jan hankali. Cike da fargaba ta ce"Yanzu me na yi wanda ba ka ji daɗinsa ba?"

Ƙwayar idanunsa ya jefa cikin nata Ya ce"Wacece ta zo wajenki ? Kar dai ace kin fara gayyato min 'ya'yan ƙwalta cikin gida?"

Kalmar 'ya'yan ƙwalta' ba karamin sosa ranta ya yi ba, cikin tsananin ɓacin rai ta ce,

"Ai duk wanda ya siyi rariya, yana sane da cewa tabbas zata zubda ruwa. Amma shawarar da zan baka shi ne, lokaci yayi daya kamata ka fara daraja waɗannan ya'yan ƙwaltan saboda a cikinsu ka hangi wacce ta kwarfe maka zuciya, ka kasa hakuri sai daka bita, gashi yanzu kana shirin samun iri daga tsatsonsu."

Ta ida magana tana nuna shafaffen mararta da ɗan yatsa.

Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa yaga sam bai kyauta ba. Har ta juya za ta bar dakin, ya yi maza ya fuzgota ya rungumeta, jikinsa da bakinsa na rawa sosai ya ce"Alkhairi don Allah ki gafarce ni!! ban yi hakan da niyyar cin zarafin ki ba, kawai dai bana ƙaunar ganin wata mace daga gidan mata ta tako kafarta gidan nan ne. Ni ban hanaki zuwa ba amma kar wata ta kuskura ta tako kafarta cikin gidan nan."

Kuka ta fashe dashi ta ce"Jayman ashe akwai ranar da har zaka iya kallon cikin ƙwayar idanuna ka kirani da ƴar kwalta indirectly?" 

Ta ida magana tana runtse idanunta da karfi wanda hakan zai tabbatar maka da lallai abun yayi mata ciwo sosai. Bakinsa ya kai kan nata, ya cafki pink lips ɗinta ya shiga tsotsa, bata hana shi ba kuma bata yi responding ba, amma tabbas saƙonsa na isa da kyau. Har hawayenta sai daya lashe tas yana"Alkhairi I'm so sorry ba zan sake ba kinji."

Sai daya tabbatar da ta samu natsuwa sosai sannan yasa kai yabar gidan, ba tare da sun sake tada zancen Saffy ba balle ya san dangantakar da ke tsakaninsu.

**
SAFFY

Tana barin gidan, tafiya kaɗan tayi ta fita junction ɗin unguwarsu Jidda. Bata yi wani dogon tsayuwa ba ta samu adaidaita sahu empty ya ɗauketa.

Ana gaba kaɗan ya sake ɗaukar wata fasinja. Matashiyar budurwa ce wacce bata wuce sa'arta ba. Ta masa kwatancen inda zai kaita.

An taki sa'a hanyarsu daya ne, sai ya fara sauke Saffy a Unguwar Shanu sannan ya ajiye ita budurwar a can gaba nan Rabah rd.

Sallama tayi ma Saffy bayan ta zauna gefen hagunta. Ta amsa mata sama sama idanunta akan zanen kunshin hannun Muwadda dake masifar ɗaukar ido. Sosai ya mata kyau, balle abun ka da farar mace sai ya kara haskaka fatarta.

Kasa hakuri Saffy tayi da dole sai data ajje girman kai gefe ta ce"Baiwar Allah kunshin ki ya yi min kyau sosai, don Allah ina aka zana miki shi ?"

A yangance Muwadda ta ce cike da jindadin ganin an yabawa kunshinta "Thank you so much sis. Meema's henna ce tayi min, ai kin santa ko? daga nan ma na fito, na raka cousins ɗina ne na nuna musu gidanta, don basu san wuri ba amma nawa tun shekaranjiya aka zana min."

Ta ida magana tana yarfa hannunta cike da iyayi irin nasu na 'ya'yan manya.

"Ban santa ba, don Allah ki kwatanta min gidan nata in yaso in wannan na hannuna ya goge sai inje nima ta zana min."

"Wooo! kina garin kaduna kice min baki san meema's henna ba ? ai duk wani mazaunin kd yasan da zamanta sabida in ana maganar kunshi kawai a bar wa meema, sauran masu kunshi su jira kawai."

"Bakuwa ce a garin."
Muwadda ta taɓe baki ta ce"Ah lallai kam naga alama." 

Ta kwatanta mata har da bata lambar wayar matar. Saffy tayi godiya daga nan ta ja baki tayi shiru don ita ɗin ba mai cika son shisshige wa mutum bane, kuma ita ma bata son a shigeta, wannan ɗin ma kamawa tayi don bata iya kau da kai daga duk abin da ya birgeta balle kuma magana ake ta ado.

Tana jin yarinyar sai waya take tayi da mutane mabanbanta, ga dukkan alamu biki suke dashi kuma ita ce aka dora kan gaba a shirye-shirye.

"Ni fa wallahi an takura ni haba sai kace ni kaɗai ce ƙawar amarya, komai ace sai ni, sai ni zanyi mtsww."

Muwadda ta furta cike da gajiyawa da lamarin 'yan gidansu bayan ta kammala wayarta.

"Ko don iyayin ki ma ya isa a doraki kan gaba." 

Saffy ta furta hakan, a tunaninta zancen zuci tayi ashe ya fito fili sai ji tayi Muwadda ta fashe da dariyarta me birgewa har ƙananan fararen hakoranta suka bayyana.

"Haba wai don Allah da gaske ina da iyayi? Meyasa kowa ke min wannan kallon? haka ma duk wanda na hadu dashi, a tashin farko sai ya yi min kallon ina da iyayi? Ni dai na san ina da fara'a da kuma son jama'a amma iyayi gaskiya ban yadda ina da ita ba haka dai yanayi na yake."

Wasa-wasa fa hira ta barke tsakaninsu sosai wanda sai ka rantse kace dama can sun daɗe da sanin juna.

"Gaskiya kin matukar birgeni, ban taɓa haduwa da mutum ace tashin farko na sake jiki dashi muna hira har wai a cikin napep ma." 
A cewar Muwadda tana kallon tsakiyar idanun Saffy.

Kayatacciyar murmushi Saffy tayi kan ta ce" Nima haka wallahi."

"Nice to meet you. I'm Muwaddah Aliyu Gamawa, I'd love to build a friendship with someone like you."

Ta mika hannu da niyyar musabaha. Cike da mamaki Saffy tabi hannun nata da kallo, jikinta duk a sanyaye sabida tun bayan rasuwar Zaynab ba ta sake kulla wani abota ba.

Tuni hankalinta ya tashi har Muwaddah taji rashin daɗin hakan. She felt so embarrassed.

Har zata sauke hannu, kawai taji hannun Saffy cikin nata ta ce cikin rauni"ki yi hakuri don Allah, kin sa na tuno da best friend ɗina ne wacce ta jima da rasuwa."

"Allah sarki I'm so sorry about that, ki gafarceni Allah yaji kanta. Stop crying ok? In sha Allahu zan yi kokarin maye miki gurbinta."

Murmushin yake kawai tayi amma ita ta tabbata babu wata wacce zata taɓa iya maye mata gurbin Zaynab.

Har akazo inda Saffy za ta sauka sai fira suke, sune har da musayar lambar waya. Muwadda da zaƙewa ita ce har da gayyatar Saffy bikin cousin ɗinta da za'ayi kuma ita ce babbar ƙawa. Washegari za'a fara events. 

Saffy bata ki tayin nata ba amma ita ta kwana da sanin cewa ba zuwa za tai ba. Ta dai amsa da zata halarta ne don shafawa kanta lafiya.

"Unguwar shanu anan kike da zama ? kin san GIDAN MATA ?"

Muwadda tayi mata tambaya bayan ta sauka har tana kokarin biyan kudin napep taji wannan tambayar tamkar saukar aradu.

Banza tayi da ita kamar bata ji abin da ta ce ba ta mika wa mai adaidaita kudi, sai ji tayi Muwaddah ta ce masa" Malam Ja mu tafi karka karbi kudinta ni zan biya."

Haka ko aka yi ɗan sahu ya ja babur suka tafi suka barta nan tsaye cike da mamaki. Sosai Muwaddah ta birge Saffy har take jin za ta iya kulla ƙawance da ita. Sai dai ta lura yarinyar za tayi surutu sosai ga kuma iyayi.

Jan jiki tayi ta ɗauki hanyar layinsu na GIDAN MATA wanda gini ne aka danƙara a tsakiyar unguwar kamar gidan marayu amma nan gida ne na matasan mata da suka rasa gatansu, da kuma waɗanda suka baro gida suka shiga duniya, kuma suka samu mafaka a arha.

Ita fa a wajenta abun kunya ne ta bari wani yasan da cewa gidan mata take zaune, balle mace kamar Muwaddah mai aji da gayu, ta san sosai za ta raina mata wayau shiyasa ta yi banza da ita sanda ta jefo mata tambaya.

**Yau Jidda ta warware mana yadda aka ɗaura musu auren sirri da Yallabai**

**Akwai damuwa fa amma mu je zuwa don ba a fara komai ba…**


NAGODE ALL❤️