CHAPTER 10
by @hafnancy
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Haɗuwar rayuka da ƙaddara ta tattara wuri guda.*🔥💔}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWARƊAKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 10.*
**HASEEB**
Har wa yau ya rasa samun cikakken natsuwa tun randa yaci zarafin Jidda a asibitin da amininsa Dr.Ansar ke aiki. Daga baya ya ji a ransa sam be kyauta ba, Bai kamata ya tsoma baki cikin rayuwar wata da bai ma sani ba.
Yana tsaka da aiki, Hadiza ta yi ta damun shi awaya, sai data bashi 2 missed call, a kira na ukun ne ya daga, bayan sun gaisa ta ce"Sorry na dameka alhalin na san kana bakin aiki."
"Ba damuwa ya akayi ? meke tsalle ne?"
"Dama so nake ka duba kan WhatsApp na turo maka hoton yarinyar da take shugaba a gidan Samha. Dakyar na samu hoton ta, ka duba in tayi shikenan sai in ci gaba da shirya komai kafin ku haɗu. Don wallahi, yarinyar nan tana bani ciwon kai sosai. Shegen taurin kai gare ta. Idan kuma bata yi ba sai a nemi wata."
Hadiza ta sauke numfashi mai nauyi sannan ta ci gaba "Ka sani ya zama dole ka nemi yarinya a cikin gidan mata, yin hakan shi zai sa Samha ta ji ciwo ganin mijinta na bibiyar yarinyar da ke ƙarƙashinta."
Runtse idanunsa ya yi gami da shafa kansa da yake jin yana sara masa sabida tsananin damuwa. Ita Hadiza a lallai sai tasa ya nemi yarinyar da take rayuwa a gidan mata don koyawa Samha hankali.
Sun san cewa Samha ba za ta iya jure ganin mijinta yana bibiyar wata yarinya da take ƙarƙashinta ba. Hakan zai matukar ɗaga mata hankali, kuma muddin tana sonsa, dole ne abin ya girgiza ta sosai.
A nan ne Haseeb yake ganin zai iya samun damar matsa mata lamba ta rushe gidan matan. Sai ya tabbatar da cewa lallai ta shiryu, tare da ɗaukar alkawarin ba zata sake komawa gidan jiya ba, a sannan zai sallami ita yarinyar da suka ƙulla soyayyar karya.
"Ok, zan duba amma ba yanzu ba sai na samu natsuwa."
Ya bata amsa sannan ya kashe waya ya maida aljihu, kana ya koma bakin aikinsa.
A ɓangaren Hadiza kuwa, sai sake kallon hoton yarinyar data tura masa take bayan sun gama waya ita da Haseeb.
Da ƙyar ta samu wannan hoton don na musamman ta kai ziyara gidan mata, amma a waje ta tsaya sai da ta kwashe kusan minti talatin sannan ta ga fitowar Azagwai.
Hadiza ta sha bakar wahala kafin ta samu hoton Jidda a wajenta shima ɗin wanda suka taɓa ɗaukawa ne tare a tsakar gidan, lokacin da suka shirya bikin cika shekaru shidda da kafuwar Gidan mata.
A hakan ma sai da Azagwai ta yanke fuskarta a hoton sai ya rage fuskan Jidda kaɗai sanye da doguwar riga peach color, ta yane kanta da bakin mayafi.
Sosai tayi kyau a hoton, murmushinta ya ƙara kawata kyakkyawar fuskarta.
Sai dai kafin samun hoton Hadiza ta sha tambayoyi wajen Azagwai kan mai take neman hoton Jidda tayi da shi?
Hadiza ta yi murmushi ta ce"Kar ki wani daga hankalinki abin alheri nake nufinta da shi ba sharri ba. Kuma hoton ai siya zan yi ba wai kyauta za ki ban ba."
Jin zancen kudi yasa Azagwai washe haƙora ta ce"Dakyau, yanzu naji batu, hoto kam kin gama samunsa kawai shiga xender mu yi shap shap fita zan yi."
Girgiza kai kawai Hadiza tayi cike da tausayin irin rayuwar da Samha ta jefa ya'yan mutane.
Shap shap ta tura mata hoton, ita kuma ta mata transfer ɗin dubu ashirin cikin asusun bankin ta.
Da sauri Hadiza tabar kofar gidan gudun kar su jame da wanda ya santa har ayi wani tunani a kanta.
Amma kafin ta tafi sai da ta gargaɗi Azagwai kan kar ta sake wani ya samu labarin ta zo neman hoton Jidda, kai hatta ita kanta Jiddan kar ta kuskura ta faɗa mata.
"Hajiya ki sa ranki a inuwa, babu wanda zai ji wannan labarin tunda kin riga kin rufe min baki da shegun."
Ta furta tana dariya, Hadiza bata ce komai ba, ta shige mota tayi tafiyar ta don ta lura yarinyar shakiyiya ce ta gaske, kuma za tayi maitar son kuɗi.
Taso karban layin wayar Azagwai sabida watarana tana iya kara neman wani taimakonta, amma kwata-kwata ta sha'afa.
Da isarta gida shine ta tura ma Haseeb hoton a lokacin yana bakin aiki.
***
Haseeb ya koma gida a matuƙar gajiye, jikinsa duk tsami kamar wanda akayi ma shegen duka. Ya sa Samha ta haɗa masa ruwan wanka sannan ta fita zuwa kitchen don kawo masa abinci.
Dakyar ya tashi daga saman gado ya tube kaya, ya dora towel a kugu. Matsalarsa da Samha kenan sam bata iya tarairayar miji ba. Kamar yadda zaka ga wasu matan ke yi idan mazajensu sun dawo aiki, su cire masu kaya, su ja su zuwa bandaki, kai hatta wanka ma sai su yi musu kamar jira-jiran goye.
Suna gamawa azo a shafa mai, asa kaya, kai abinci ma abaki za'a ba shi kamar ɗan yaye. Allah ya sani yana sha'awar irin wannan rayuwar ta ma'aurata masu shimfiɗa rayuwar turawa a gidajensu amma shi sam ko kadan bai yi dace ba.
Ina ma take da lokacinsa ? Shi ɗin banza a wajenta. Lokacin da take da shi a rayuwarta kawai shi ne GIDAN MATA.
Duk wani abin da ta san zai kawo ci gaba a wannan gidan shi take sa kai har sai ta ga an ci nasara.
Ga shi ya zama kamar wawa a wajenta, sam baya iya tabuka komai a kan duk wani motsinta. Ko wannan haɗi da Hadiza ke so tayi, ita ta kawo masa shawarar ba wai a son ransa bane.
Kuma har yanzu yana kokonto a kan irin aiki mai matukar hadarin da ta gabatar gareshi. Tunani yake zai iya ko ba zai iya ba ?
Sai a yanzu ma ya tuno da hoton data tura masa, da hanzari ya dauki waya, ya kunna data kana ya hau whatsApp.
Sai daya jira sakonni suka gama shigowa duka don rabonsa da hawa online tun safe, sabida ayyuka da suka sha gabansa.
Kai tsaye ya buɗe sakon Hadiza gabansa na bugawa da karfin gaske.
Hannu ya kai yana murza idanunsa don sake tabbatar da lallai fuskar yarinyar data addabi kwakwalwarsa da tunaninta a cikin kwanakin nan, ita yake gani a kan allon wayarsa.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wallahi ita ce....ita ce wallahi"
Ya furta hakan jikinsa na mugun rawa, a yayin da gabansa ya tsananta bugu.
"Wallahi yarinyar nan mai cikin nan ne wacce muka samu sa'insa a asibitin Dr.Ansar."
Jikinsa na rawa ya tura wa Dr.Ansar hoton ta, akasan hoton ya ce" Manchy ka gane wannan yarinyar??"
Ba ya online don haka kai tsaye ya kira shi awaya ya ce"Maza ka duba WhatsApp na tura maka sako,kuma ina bukatar reply cikin gaggawa."
Ya katse wayar, sake komawa kan hoton ya yi tare da zooming ɗin fuskarta. Tabbas ita ɗin ce wacce tun daga ranar da suka samu sabani bai sake samun natsuwar kirki ba.
'Yanzu dama ita ce shugabar da yake ji matarsa Samha na yawan magana a kai?'
' Yarinyar da Hadiza ke son ya nema kenan domin maganin Samha?'
Tuni ya ji cikinsa ya hargitse har yake ji lallai yana bukatar ziyartar toilet. Da sauri ya jefar da wayar kan gado ya afka bandaki sai kan toilet seat.
Shigarsa ke da wuya Samha ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci, dai dai lokacin wayarsa ya shiga vibrating. Dr. Ansar ke kiransa bayan ya gama kallon hoton daya turo masa kan WhatsApp.
Da sauri Samha ta dire tray ɗin hannunta sannan ta nufi inda wayar yake da kamar zai tsaga ɗakin da vibration.
Har ya fara zazzage dattin cikinsa, sai kawai ya tuna cewa ai ya manta bai sauka kan WhatsApp ɗinsa kafin ya afka banɗaki ba, balle azo kan hoton Jidda da ke kan allon wayarsa.
A kowane lokaci Samha na iya shigowa ɗakin, kuma abin da zai biyo baya ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba. Bai gama wannan tunanin ba ya ji motsinta, a hanzarce ya tsaftace jikinsa sannan ya fito bakinsa na ambaton sunan Allah.
"Shi wannan fa akwai nacin tsiya, mutum na tare da iyalinsa ma ba za a barsa ya sarara ba."
Har ta na shirin ɗagawa domin ta tsage ma Dr. Ansar kasancewar akwai wasa a tsakaninsu sai kawai ta ji an fuzge wayar a hannunta har sai da gabanta ya yi wani irin mummunar faɗiwa.
Da sauri ta waiga ta na ƙare masa kallon mamaki, sai uban zufa yake kamar wanda ya haɗiyi ɗan kunama. Duk yabi ya rikice, ya ma rasa abin yi har kiran ya yanke.
Sai da aka sake kira a karo na biyu sannan ya ɗaga bayan ya fita ɗakin ya na waigenta gudun kar ta biyo sahunsa. Gaba ɗaya yanayinsa ya nuna rashin gaskiya a tattare da shi.
A corridor ɗin ɗakunansu ya tsaya yana waya da Dr. Ansar cikin kwantar da murya kar Samha ta ji.
Sama-sama suka tattauna sannan a ƙarshe ya ce "Zan sameka a gida nan da mintuna ashirin."
Ya na gama faɗin hakan be jira ya sake jin ta cewar Dr. Ansar ba ya katse, bai ɓata lokaci ba ya goge hoton Jidda a kan WhatsApp ɗinsa, ya haɗa hadda chat ɗinsa da Hadiza ya goge tass, a sannan ya iya sauke ajiyar zuciya mai nauyi hadda wani dafe ƙirjinsa wanda ya yi daidai da fitowar Samha hankalinta a mugun tashe, har sai da ya ɗan firgita da jin motsinta a kusa da shi don ya bawa ƙofar ɗakin baya ne.
Cike da zargi Samha ta ce"Wai me yake faruwa ne na ga duk ka firgice? Wayan ma ka gagara yinsa a gabana har sai da ka fito waje?"
Sai da ya daidaita natsuwarsa sannan ya ce"Dama ciwon Inno mahaifiyar Ansar ne ya tashi tun safe ake ta fama da ita, shiyasa da na ga kiransa hankalina ya yi mugun ɗagawa. A zatona mummunar labari zan ji daga gare shi, ashe ya kira ya gaya min an sallameta tana gida."
Cikin wani yanayi na tausayi ta ce"Allah sarki Inno ciwon sigar nan dai ya sakata gaba, ubangiji Allah ya bata lafiya."
Haseeb ya amsa da amin, in dai magana ake ta tausayi to babu kamar Samha. kuma bai yi karya ba da gaske dama jikin nata ya motsa amma ba zancen yau bane, akalla zai yi kusan kwana uku shi dai kawai ya yi amfani da ita ne wajen kare kansa.
Bai tsaya cin abinci ba don baya da natsuwar da zai ji daɗin cinsa, rufaida yogurt kawai ya zuba a kofi ya ɗan kurba shima ɗin gudun ɓacin ranta ne, kar ta ga ta masa ɗawainiya amma ko kaɗan be taɓa ba duk da ba ita tayi girkin ba.
Haseeb ya tsani cin girkin 'yan aiki, ƙyanƙyami garesa sosai amma haka yake ɗaure wa yake ci don Samha ta riga ta tsabar masa da wannan rayuwar. Jallabiya mara nauyi ya jawo ya zura sannan ya fice da sauri abin har tsoro ya koma ba Samha ganin yadda yake ta rawar jiki duk da ance masa jikin Innon da sauki. Bata san ma anan ji yake kamar ya zama ɗan tsuntsu ya tashi sama ba ne.
Sai da ya tsaya ya gabatar da sallar magrib a kan hanya sannan kai tsaye ya nufi gidan Dr. Ansar.
Tuki yake amma gaba ɗaya kwakwalwarsa a caje take, sai cizan leɓuna da shafar kwantacciyar bakin gashin kansa kawai yake tayi da hannu ɗaya, ɗayan kuma a kan sitiyari ya na sarrafa shi.
Ya shafe mintuna talatin zaune cikin mota ya na jiran fitowar Ansar amma shiru-shiru bai fito ba. Sai a sannan ma tunanin kiran Hadiza ya faɗo ransa don shaida mata halin da ake ciki. Sai daya ba ta missed calls har uku, a kira na huɗu ne ta daga.
"Dama shi likita gaggawa ne dashi sam bashi da hakuri, wannan kira haka babu sassautawa kar dai ace har yarinyar ta samu ƙarbuwa ne?"
Ta furta hakan cike da tsokana har tana ƙyalƙyala dariyar, ita a ganinta har tarko ya kama ne.
"Ai kuwa ko kusa ba ta samu ƙarbuwa ba. Hadiza akwai matsala babba!"
Da sauri ta dafe ƙirji har ta na ƙoƙarin miƙewa tsaye daga kan sallayar da take zaune akai, ta ce" Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Haseeb wani irin matsala kuma? Idan ba ta maka ba ai babu dole a ciki sai a nemi wata gasu nan birjik, har sai ka zaba ka dirje."
"Hadiza ni fa zancen haɗuwar mace ba shi ne matsalata ba. Abin da kawai aiki zamu yi na ɗan gajeran lokaci, to ina ruwana da wani haɗuwarta? Kawai so nake in faɗa miki idan har yarinyar da kika turo min da hotonta, ita ce kike son ɗorawa a kan aikin namu to ki shafe batunta don ciki ne gareta."
A karo na biyu ta sake kai wa ƙirjinta bugu, a lokaci ɗaya ta na salati.
"Ciki fa Haseeb?"
"Yo! To meye abin mamaki? You should expect that from her tunda 'yar ƙwalta ce."
Huci mai zafin gaske Hadiza ta fesar kan ta ce"Haka ne! to amma taya kasan tana ɗauke da juna biyu? Dama ka santa ne?"
Kwashe labarin komai ya yi ya faɗa mata na rikicin da ya yi da ita a asibitin Dr. Ansar.
Sam bata so jin hakan ba, da yaya ta samu ta Shawo kan Haseeb ya amince zai nemi yarinya a gidan?Tana jin daɗi haka ta kusa cimma ruwa sai ga zancen ciki ya bullo.
"To, kin ga dole ta sauka a kan tsarin aikinmu. A canzata da wata don wallahi ba zan bari tsautsayi ya sake haɗani da ita ba. Yarinya ta ga dama ya samu ta ƙulla min sharri ta ce ni nayi mata ciki."
Ya faɗi hakan da iya gaskiyarsa.
Jiki a mace Hadiza ta ce"Wataƙila zuwa yanzu ai ta zubar da cikin...."
Haseeb ya yi saurin taran numfashinta "Kin san me? Ko ta zubar wallahi still bana bukatar wannan yarinyar, kawai a canzata da wata ɗin ina ganin zai fi. Kuma duk wacce kika kuma samowa kafin mu fara aiki ya zama dole aje a mata gwaji don tabbatar da cewa bata ɗauke da juna biyu. Don ba zai yiwu yanzu in kaucewa matsala, daga baya kuma in zo in afka ciki ba, ki huta lafiya."
Kit! Ya katse wayar yana fesar da zazzafar huci daga bakinsa kamar wanda ya ci uban gudu.
Gefensa Ansar ne zaune wanda ya ɗan jima da shigowa motar, ya kasa kunnuwa yana sauraronsu har suka gama waya. Kasancewar ya san kwanan zance, duba da irin amintar dake tsakaninsu, ɗaya baya taɓa aiwatar da abu ba tare da ya nemi shawarar ɗan'uwansa ba.
Hannu yasa ya dafe goshinsa da yake jin kamar zai tsage tsabar ciwon kai, a hakan ya ɗaure ya waiga sashen Ansar ganin shirunsa tayi yawa uffan ya kasa cewa.
"Manchy baka ce komai ba kayi shiru."
Girgiza kai Ansar yayi ya ce"Me kuwa kake son in ce? Ni na gaji da faɗa maka gaskiyar da baka son jinsa."
Ya ida magana yana mai kau da kansa gefe wanda hakan zai tabbatar maka da lallai aminin nasa ya ɓata masa rai ainun.
Jikin Haseeb ne ya yi bala'in sanyi hakan yasa ya kwantar da murya ya ce"I'm sorry if i hurt you amma don Allah ka yi min uzuri wallahi I'm just confused na rasa ta yadda zan bullowa al'amarin Samha ne."
"Kana ganin bullowa Samha ta wannan hanyar shi ne zai iya gyara komai? To, ka sani zaka sake haddasa matsalar data fi ta da muni ne. Bugu da ƙari, zaka ɓatawa kanka da family ɗinku suna. Idan har na fahimta ita wannan yarinyar da kuka taɓa samun saɓani a asibitina ita ce wacce Hadiza ke son ɗorata kan aikin naku right?"
"Yes!Yes ita ce, kuma ka ga tunanina a kanta ya tabbata gaskiya. Cikin shegen ne take ɗauke dashi wanda tayi yunkurin zubarwa."
Ansar ya gyara zama ya ce"Wannan tsari na Hadiza sam bai yi ba. Haseeb yanzu sai ka biye mata? Me yasa zaka ba mace damar sarrafa tunaninka? Da zaka karɓi shawarata da ni zance ka manta da batun neman duk wata mace mazauniya gidan mata da sunan haɗa kai da ita domin maganin Samha. Kar azo garin neman gira a rasa ido, muddin ba jihadi zaka yi na auren ba to kawai mallam ka sallama ka bari Allah ya yi ikonsa akan lamarin Samha."
Ya ɗauki tsawon lokaci sosai yana fahimtar dashi abubuwan da suka shige masa duhu, sai a yanzu yake ganin wautarsa na biyewa Hadiza da wannan shirmen banzan. Ya yi nadama sosai sannan ya yi hamdala ga ubangiji da ya azurtashi da aboki na gari.
"Ruwa a ɗan cokali ya ishi mai hankali wanka. Ka je ka natsu kayi tunani a kan zancen da muka tattauna akai, sai da safe my very own Manchy."
Daga haka suka yi sallama Haseeb ya tafi. Amma sai da ya biya ta gidan abincin Yallabai ya karbar wa Samha saƙo. Abinka da me juna biyu, wai gaɗaɗɗen kifi da arish chips take ƙwadayin ci.
**JIDDA**
Yau ta tashi ne da marmarin cin chicken parmesan wanda yana ɗaya daga cikin abin da tafi son ci a gidan abincin Yallabai. Da ace yazo ne da shi da kansa zai shiga kichin ya girka mata, kuma gaskiya ita ba zata iya jiran zuwansa ba don ji take muddin bata ci abin da take so ba, ba zata gane ma kanta ba.
Babu shiri ta nemi amintaccen kukunsa Aliyu wanda shi ke jagorantar babban branch ɗin gidan abincinsa. Kuma tabbas yana ɗaya daga cikin mutanen da suka san da matsayin da take da shi wajen ubangidansa. Aliyu mutum ne me riko da sirri bai ma fiye surutu ba, shiyasa Yallabi ya aminta dashi ɗari bisa ɗari wanda hakan yasa ita ma Jiddan sakin jikinta dashi.
Bayan ta kira shi ta bada odan haɗa mata lafiyayyen chicken parmesan.
Cike da girmamawa ya amsa mata "An gama ranki ya daɗe, amma aiko miki dashi za ayi ko dai da kanki zaki zo?"
Dayake tana so a yau ta leƙa gidan mata saboda akwai aikin da za tayi a gidan mata, don wata yazo ƙarshe akwai waƴanda suke so su biya kuɗin haraji. Ya zama dole ta je gudun kar ta sake shiga ukunta a wajen uwar ɗakinta, ganin kamar tana son fara mata wasa da aiki ne.
"No, karka damu zan biyo na karba da kaina dama fita zan yi."
"Ok ma! Ki ban nan da 1hr, idan yayi ready zan sanar dake."
"Ok thanks."
Ta furta sannan ta kashe wayar cike da mamakin yadda ake girmamata da kuma ɗaukakata saboda alaƙarta da babban mutum kamar Yallabai.
Ko awa ɗayan ma be buga ba ya kira yake sanar mata da cewa ya yi ready. A gurguje ta shirya cikin abayarta kalar ruwan hanta da ya yi masifar mata kyau. Ta yane kanta da mayafi sannan ta jawo face mask ta rufe kusan rabin fuskarta da shi.
Tana cikin feshe turare wayarta dake saman dressing mirror ya bada WhatsApp alert sound. Ta kai hannu ta ɗauki wayar tana dubawa, kusan alokaci ɗaya Saffy da Azagwai suka turo saƙo.
"Yaya kin tashi lfy? Dama so nake mu tattauna kan aikinki a gidan mata da kuma aurenki saboda na shiga wani hali na rayuwar da kike yi."
Kai tsaye ta bata amsa "Ki bari idan nasa mana lokacin haɗuwa zan sanar dake. Good morning and have a great day ahead, Nagode."
Da sauri takai hankalinta kan chat ɗin Azagwai.
"Shugaba! Yaushe zaki shigo gari akwai magana fa? amma wallahi sai kin bada wani ɗan ihsani kafin na faɗa ke kin san halina ai."
Gabanta ne taji ya bada rass! don ita fa muddin wani yace yana son magana da ita to kai tsaye take ganin kamar an gano alakarta da Yallabai ne, balle kuma kowa yasan halin Azagwai na gidan mata rediyo me jini kenan. Idan ka bari ta san wani sirri naka to kai kam ka gama yawo.
Ba ta tsaya reply ɗinta ba, kai tsaye ta kirata a waya, bugu ɗaya, biyu ta ɗaga tana" Shugaba! Ya akai ne? In yi pasting aza ɗin ne?"
Cike da takaicinta ta ce"Don Allah ki gaya min me yake faruwa ne?"
"Wallahi bazan faɗa ba ke ma kin sani sai kin biya, kina abu kamar yau kika fara sanina, haba Shugabar mata."
Tsoki Jidda ta ja sannan ta ce a hasale"Ke dai wallahi Azagwai sam baki da tausayi, idan aka baki dama tsaf! zaki iya yi wa gawa bulala."
Sai da aka tsadance ta tura mata ɗan ihsanin sannan ta fesa mata zance.
"Yauwa! dama ba wani abu bane fa Anty Hadiza ce ta zo shekaranjiya ta biya kuɗi na tura mata hotonki. Kuma kema kin san ba zan taɓa cin amanarki ba dole na faɗa miki abin da ke faruwa."
"What?? Wacce Anty Hadizar kike nufi?"
Har sai da Azagwai ta tsorata da tsawar da Jidda ta doka mata, taɓe baki tayi ta ce"Yo! Anty Hadizan guda nawa kika sani? To, ta amanar Uwarɗak nake nufi....."
A fusace Jidda ta tari numfashinta ta ce,
"Yanzu Azagwai don baki da hankali, ki bada hotona sabida son abin duniya irin naki, ko shakka babu zaki iya aikata komai a kan kuɗi. Yanzu sabida Allah idan wani muguntar za a min shikenan fa an ci nasara a saukake. Wallahi Shafa'atu baki mori hali ba, kuma bari kiji in faɗa miki duk abin da ya same ni mara daɗi sanadin hoton nan nawa da kika tura ma wata ba tare da sanina ba kin ji na rantse da Allah kuma ki rubuta ki ajje, zan tabbatar da na rabaki da gidan mata sannan in sa ki ƙare rayuwarki a gidan gwale-gwale, stupid girlllll kawai."
Tana gama faɗin hakan ta ja dogon tsaki ta yanke wayar zuciyarta na bala'in zafi tamkar wacce aka baɗawa barkono a ƙirjinta.
"Me yasa Anty Hadiza za ta min haka? A kan me za ta karɓi hotona wajen wacce ba ta iya rike sirrin mutum? Ta yi me dashi?"
Ranta a matukar ɓace ta nemeta a waya, A daidai wannan lokacin kuma Hadiza na kan traffic, danger ya tsai da ita, gashi sauri take ta isa wajen aiki da wuri saboda supervisors da za su kawo musu ziyara a yau. A jami'ar Kaduna take aiki wato KASU, non-academic staff ce.
Da ƙyar dai ta samu aka bata hannu ta wuce, wai ahakan kuma so take ta biya Alkaleri's kitchen ta karɓi breakfast package don ko kari bata tsaya tayi ba.
Shigowar ƙiran Jidda ba ƙaramin mamaki ya shayar da ita ba, don bata taɓa kawo aranta Jiddan za ta nemeta nan kusa ba kan batun da suka ajje. Paka motar gefe tayi domin amsa kiran nata
"Kamar kin san ina shirin nemanki sai kika riga ni."
Hadiza ta furta bayan ta daga wayar.
"Nima ɗin nemanki nake ruwa a jallo, ki faɗa min ina zamu haɗu?"
Jidda ta ida magana da ɗan zafi-zafinta. Ko kaɗan Hadiza ba tayi mamaki ba don ta san cewa dama ba wani jituwa ne a tsakaninsu ba kuma duk dalilin zancen Haseeb ne da ta bijiro mata da shi, hakan yasa raini me ƙarfin gaske shiga tsakaninsu.
Lokaci da kuma wajen haɗuwa suka ajje sannan Jidda ta kashe wayarta.
Sai data daidaita natsuwarta sannan ta fice zuwa gidan abinci, taso kiran Yallabai amma tana tsoro maybe yana tare da uwargidansa, tun asuba da suka yi waya basu sake ba amma dai ya san da cewa za ta ziyarci gidan mata a yau.
**Hadiza da Haseeb suna shirin amfani da Jidda wajen cimma burinsu, alhali ba su san cewa Jidda ta riga ta zama matar Yallabai a ɓoye ba.😳💔**
**Shin kuna ganin wannan shirin nasu ne zai tona asirin auren Jidda da Yallabai? 👀🔥**
**Update sai Allah ya kaimu monday in sha Allah...Barka da Juma'a my pipul, Allah ya sadamu da dumbin alherin da ke cikin wannan rana mai albarka, Ameen.🙏**
Hafnancy.
***.
NAGODE ALL❤️