1
Jan hankali ga wanda za mu yi wannan tafiyar, labarin yana ɗauke da ɓangarori a ƙalla guda uku, kowane ɓangare da muhimmiyar rawar da zai taka, ku biyo ni sannu a hankali don mu nutsa a cikin labarin.
Hankali tashe Hasiya take kallon likitan cike da mugun firgici, da fargaba haɗe da ruɗani ta ce
"Likita wai ya na ga kana rufe shi?" Ta tambaya tamkar wani ne ya fisgo maganar daga bakinta. Doctor Asim ya ji gabaɗaya tausayinta ya tsarga masa, sai dai laɓɓansa sun kasa bashi haɗin kan da zai furta mata cewa Allah ya yi wa mijinta Zahraddin rasuwa!.
Bayan wasu awanni. Ana idar da sallar la,asar mutanen da suka yi sallah a masallaci mafi kusa da gidan Zahraddin suka yi cincirindo a ƙofar gidansa, domin su yi rakiya zuwa gidansa na gaskiya. Saboda bayan an gama shirya gawarsa tsaf, kuma hakan ya yj daidai da lokacin sallar ka,asar shi ya sa aka bada umarnin cewar a yi sallah sannan a tafi maƙabarta.
Wasu sun yi sallar a masallacin unguwar da yake kusa da gidan a inda wasu suka yi jama,i a ƙofar gidan nashi. Hasiya ce tsaye a ƙofar gidan tana rungume da Nasira a gefen hagu, Zainaba a gefen dama. Su duka kuka suke mai cin rai, domin suna hangen gawar shimfiɗe a gaban liman ana gabatar mata da sallah, har sai da aka ɗaga makarar a nan ne hankali ya kai ƙololuwa wajen tashi, har sai da mutane suka shiga riƙe su suna basu baki, aka kamo hannuwansu aka shigo da su cikin gida.
Bayan an dawo daga kai Zahraddin makwancinsa, Hasiya tana zaune idanu duk sun kumbura, tana tunanin mutumin da ya sadaukar mata abubuwa da dama yau ya tafi ya barta da marayu har biyu, tunanin duniyar take, tana tunanin yadda za ta ci gaba da kula da yaran bayan mahaifinsu bai bar musu komai ba na gado!.
Da magriba tana zaune a kan sallaya, masu gaisuwa suna zuwa, don yanzu mutanen ma tsirarru ne saboda tun bayan sutura wasu suka watse, daman rayuwar kenan idan ka mutu kai taka ta ƙare.
Shigowar Abdulsalam ne ya katse mata tunani, sallamarsa ce ta dawo da ita hayyacinta.
Mutanen da suke zaune a wajen suka gaishe shi, ya amsa suna masa gaisuwa, ya ɗago ya kalli Hasiya wani irin tausayinta yana shiga jiki da jijiyoyinsa, da raunin murya ya ce
"Ki yi haƙuri Hasiya, Allah ya gafarta masa" Ya faɗa hawaye suna zubowa a dakalin fuskarsa, mutane wajen suna bashi baki ya ce
"Na yi rashin aboki, irin abokin da ba kasafai ake samun irinsa a duniya ba yanzu" ,
Ɗaya daga cikin matan ta ce
"Ai yadda Zahraddin yake sonka, tamkar ɗan uwa na jini ya ɗaukeka, yana jinka sosai a ransa" Abdulsalam ya runtse idanunsa yana tuna halaccin abokin nashi.
Hasiya kai ta sunkuyar tana share hawaye, Abdulsalam ya ce
"Hasiya karki damu, idan akwai wanda zai tsaya miki to ni ne" Wannan kalmar ta yi daidai da shigowar matarsa Ramla wacce ta fita yin alwala, bayan ta yi alwalar ne ta zauna a tsakar gidan ta gabatar da sallah, domin ita tun da aka yi sutura bata koma gida ba.
Ɗan dimmm ta yi jin furucin mijin nata, ta fara tunani a ranta cewar ita bata ga amfanin tallafi ko taimakon da za a yi wa mutum bayan babu ransa ba, saboda ta san irin faɗi tashin da take da naci a kan mijin nata yake kyautatawa abokin nashi, abin da Ramla bata sani ba shi ne, Abdulsalam yana taimakawa Hasiya.
Kai kawai Hasiyar ta gyaɗa ba tare da ta furta komai ba, domin idan ta tuna cewar yau Zahraddin ne ya bar duniya tana jin abin har ƙasan ranta.
Ko da ya tashi zai fita daga ɗakin ya ce yana son magana da ita, da to ta amsa ta biyo bayansa da yake yana faɗar hakan ya fito. Yana fitowa ya ja ya tsaya daga can gefen yana ƙarewa gidan kallo a zuciyarsa ya ce
'Lokaci ya yi! Da zan fitar da ke daga wannan gidan, ko kaɗan gidan nan bai dace da ke ba Hasiyata, zama a ƙangin talauci bai dace da kyakkyawar mace irinki ba' Ya faɗa yana sakin wani murmushi wanda vai bayyana ba, Ramla da take zaune daga can a kan tabarma tana kallonsa ta fara tunanin dalilin da ya tsayar da shi kuma tana mamakin da bata ji ya neme ta ba, bayan ya san a gidan ya barta. Maganar Hasiya ce ta dawo da shi daga ɗan guntun tunani da ta ce
"Abban Humaira gani" Yanayin yadda ya ji saukar muryarta cikin rauni ya sa ya ji tamkar ya fashe da kuka, cike da kulawa ya ce
"Hasiya mai kuke buƙata ne?" Kanta ta sunkuyar ta ce
"Duk abin da aka kawo Allah sanya albarka" Daga haka idanunta suka ciko da hawaye. Ramla tashi ta yi tana linke sallayar da ta yi sallah ta nufo su, Abdulsalam ganinta ya tuna masa cewar ashe fa tana gidan, don ya ma manta da wanzuwarta a gidan ko kaɗan ya manta a gidan ya barta sai yanzu da ya ganta.
Tana zuwa ta kama hannun Hasiya tana faɗin
"Ki yi haƙuri Ammyn Nasira, kowa lokaci yake jira" Jin furucinta ya sa Hasiya ta rungume ta, tana sakin wani kukan. Gabaɗaya ya kasa nutsuwa sai kallonta yake kukanta yana sanya zuciyarsa karaya, a take nashi idanun suka cika da ƙwallar tausayinta, jin sun gangaro ya yi sautin kauda kai gefe ya goge, yana mayar da kallonsa kan wasu mata guda biyu da suke wajen murhu ɗaya tana kaɗa miya.
Sallama Ramla ta mata bayan ta lallashe ta, shi ya fara yin gaba, ya fita waje yana jin wani iri. Ko da ta fito ta ganshi riƙe da ledoji manya guda biyu kallonsa ta yi da alamar tambaya yana ɗan aro jarumta ya ce
"Hasiya da yara na siyowa kin san ba lallai su ci abinci ba, amma idan... Katse shi ta yi da faɗin
"Haka ne ka kyauta" Furucinta ya sanya ya ji ƙwarin gwiwa, saboda shi dai Hasiya ya siyowa amma bai ma san lokacin da tunanin ya faɗi har yaran ya siyo ba sai da ya ga tana kallonsa. Tana kallonsa ta ce
"Kawo na kai mata, ka ga ai baka koma gidan ba, tun da har yanzu akwai mutane duk da basu da yawa" Amsa mata ya yi da cewar haka ne ya miƙa mata ta karɓa ta shiga gidan, mota ya koma ya zauna ya jingina bayan ya rufe ƙofar yana mai lumshe idanunsa, tunanin Hasiya yana bijiro masa ga wani tausayinta, sai dai ya so a ce shi ya kai mata kayan da ya siyo domin bai gaji da kallonta ba.
Ramla lokacin da ta koma ɗakin Nasira da Zainaba ƴaƴan Hasiya suna ɗakin don daman suna ɗaya ɗakin ne ɗazu, yanzu kuma sun fito sun dawo ɗakin, mahaifiyar Hasiya tana ta lallashin Hasiyar tare da yi mata nasiha a kan ya daina kuka ta yi wa mijin nata addu,ar don a halin yanzu addu,a ya fi buƙata da a kan komai!.
Da ta kawo ta ce gashi in ji Abban sh Haumaira, Hasiyar ce ta ce an gode, amma mahaifiyar Hasiya wani kallon ƙasan ido ta yi wa Ramla saboda tana jin haushi har yau da mijin Ramlar ya yi kuɗi ya bar mijin ƴarta a baƙin talauci abincin da za su ci ma yana gagararsu. Gashi kuma da aka kwantar da Zaharaddin ɗin a asibiti aka yanko maƙudan kuɗaɗe da za a yi masa magani amma, Abdulsalam ɗin ya ce kuɗaɗen sun yi yawa wai a koma a yi masa maganin gargajiya, ta san da a ce Zaharaddin ne Abdulsalam ɗin bashi da lafiya sai inda ƙarfinsa ya ƙare, amma shi asibitin ma sai ya shafe kwanaki bai je ya ga Zahraddin ɗin ba, amma yanzu saboda gulma zai zo yana wata hidimar munafurci.
Ramla dai bayan ta ajiye ta juya ta fita, tana riƙe da ƙaramar jakar ta, wacce wayarta take ciki. Tana fitowa daga gidan, ta samu Abdulsalam ya sako kanshi daga windon motar ya ƙurawa waje ɗaya idanu, juyawa ta yi ta kalli inda yake kallon, zaton da ta yi a zuciyarta ne ya zama gaskiya domin kuwa wasu ƴan nata ne guda uku suke tafiya sanye da kaya iri ɗaya, da alama anko ne mayafinsu a gefen kafaɗarsu suna tafiya kamar basa son taka ƙasa. Wani takaici ne ya kamata sa,a ɗaya ma mazan wajen babu kowa kasancewar an shiga sallar isha,i da alama suna masallaci, duk da cewar dama tun da dare ne kowa watsewa zai yi daga zaman makokin.
Juyawa ta yi ta koma ɓangaren mai zaman banza ta buɗe ƙofar ta shiga ta zauna, amma bata rufe ƙofar ba, saboda tsabar ya yi nisa a kallon ƴan matan bai ma san ta zo wajen ba bare ya san har ta shigo motar, cike da takaici ta sanya hannu ta taɓo shi, gabansa ne ya faɗi, don tunani ɗaya ne ya faɗo masa, wato ko dai aljani ne a cikin motar, juyowar da ya yi da sauri a firgice ya yi ido biyu da matarsa, wata bayyananniyar ajiyar zuciya ya sauke yana saurin faɗin
"Ikon Allah har kin kai mata?" Tana ɗan haɗe rai kafin ta ce wani abu ya ce
"Ai mutuwar Zahraddin ta taɓa ni sosai, har yanzu ina hango lokacin da aka saka shi a kabari, yanzu ma tunaninsa nake" Banza ta yi masa, a zuciyarta ta ce Allah masa rahma ta rufo ƙofar, yana ji a jikinsa maganarsa bata yi tasiri a gareta ba, ya murɗa key ya tada motar yana mai jan suka fara tafiya.
suna fara tafiya ta ɗan ja numfashi ta ce
"Abban Humaira na faɗa maka maganganun nan sun fi shurin masaƙi, tun shekarun baya nake fama da kai a kan wannan halayyar taka amma ka ƙi dainawa, shin kai baka tunanin ƴaƴanka? Kai mai ƴaƴa mata amma a ce kana irin wannan mummunar ɗabi,a da ka kasa barin ta... Bata kai ƙarshen maganar ba cike da tsawa ya ce
"Ramla ya isheki! Har sau nawa zan faɗa miki ki daina kiran wannan maganar da mummunar ɗabi,a kin san mene ne mummunar ɗabi,a kuwa? Sai ka ce wani mazinaci za kike kiran ina mummunar ɗabi'a? Ke kullum tunaninki ɗaya shi ne abu ɗaya nake, kin zo kin sameni ina cikin tunani da alhinin aboki, amini, kuma ɗan uwana amma maimakon ki tayani jimami kina wani zargin abin da ba haka bane" , Gabaɗaya ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, maganganunsa da kuma yadda yake furtawa cikin tsawa tamkar wanda ta masa wani laifi mai muni daga maganar fatar baki.
Murya ta tausasa ta ce
"Allah ya baka haƙuri, ni ba da wata manufa na faɗa ba, sannan ba ƙagar abin da na faɗa na yi ba, sai dai ina nuna maka abin da ya dace da kuma wanda ya kamata ka yi ne, da idanuna na sameka ka kafe ƴan matan nan da ido har baka san na fito daga gidan makokin ba sannan baka san na shigo motar ba, har sai da na taɓa ka, sannan ne ka zabura alamar ka dawo hayyacinka, ita zina anayinta da ido domin ido shi yake jagotancin abin da zai faru a gaban abin da mutum... Hannunsa ɗaya ya cire daga kan sitiyarin yake tuƙin da hannu ɗaya ya shiga ɗaga yatsa yana faɗin
"Idan kika ƙara danganini da yin zina sai ranki ya yi mummunan ɓaci" Shiru ta yi tana tunanin shi ko mutuwar nan ma bata sa ya saduda ba, motar ya harba bisa titi suka nufi gidansu.
A can ɓangaren Hasiya kuwa bayan fitar Ramla komawa ta yi ta jingina da bango, domin bata son cin komai, mahaifiyarta ce ta janyo ledojin ta buɗe ledar farko ta buɗe kaji ne manya gasassu guda uku, ɗaya ledar sanyi ne kala - kala. Tsaki ta yi kafin ta ɗakko tana sanyabsu Nasira suka ci duk da ba wani da yawa suka ci ba itama ta ci amma Hasiya ta ƙi ci lemo ne ma ta sha kaɗan.
Abdulsalam kuwa har suka isa gida bai sake magana ba haka itama Ramla sai azkar da take ta faman yi a zuciyarta. Suna zuwa ya yi horn me gadi ya buɗe musu get, ya shigar da motar yana yin parking ya fice daga motar har ya rigata fita ma, itama fitowa ta yi ta nufi cilin gidan.
Ɗakinta ta wuce don ta ga alamar fushi yake da ita saboda ko kallo bata ishe shi ba, waje ma ya fita da alama masallaci zai ke don ta ji masallacin yanzu suke sallar isha,i.
Ko da ta shiga banɗakinta shiga ta yi wanka tare da alwala, daman lokacin da ta shigo ta leƙa ɗakin su Humaira ta ga suna sallah. Tana fitowa ta sanya doguwar riga marar nauyi bayan ta shafe jikinta da turaruka, ta saka hijabi tare da shimfiɗa sallaya ta kabbara tata sallar. Bayan ta idan ta gama azkar da addu,a ta yi shiru tana tunani da nazarin rayuwa, ta ɗago kai ta kalli ɗakinta yadda yake cike da komai na rayuwa da za a buƙata a ɗaki, amma kuma zaman lafiya ya yi ƙaranci, tana tuno irin fama da gwagwarmayar da ta sha lokacin suna cikin ƙangin talauci, amma yanzu ma duk da sun yj hannun riga da talaucjn sai dai maimakon ta samu kwanciyar hankali haɗe da karramaaa daga mijin nata sai dai har yau bata sauya zani ba.
Tana nan zaune Humaira da Aslamiyya suka shigo ɗakin da sallama, juyawa ta yj ta amsa musu, ƙarasowa suka yi cike da kadabi da biyayya suka zauna kusa da ita suna gaishe da ita haɗe da mata sannu da zuwa. Ta amsa tana miƙa hannu ta shafa kansu tana sanya musu albarka haɗe da faɗin
"Ina Aslam?" Humaira ta ce
"Ya tafi masallaci"
Sun jima suna hira har suka jiyo shigowar Aslam da Abba, ko da suka shigo Aslam ɗakin Ramlar ya tafi domin ya san suna can tun da Abba ya ce tare suka dawo da Mamar tasu. Da sallama ya shiga ɗakin, a tare suka amsa masa, yana ɗan rusunawa ya gaishe ta, tare da mata barka da dawowa mahaifiyar tasu, yana shirin zama ta ce
"Mu je a ci abinci" Da to suka amsa gabaɗaya suka fito.
Gabaɗaya an jera kayan abincin, kowa ya zauna a kujera, rabiya mai aiki ce ta shigo da sallama ta ajiye wasu kofuna da ta kawo su a kan tire, ta gaishe da Mama ta amsa ta juya ta fita, kujerar Abba ce ba ya nan kuma dole a tare suke cin abincin, Humaira ce ta ce
"Abba bai fito ba ko wanka ya shiga?" Murmushi Mama ta yi ta ce
"Bari in je in taho muku da shi" Ta tashi ta tafi.
Da sallama ta tura ƙofar ɗakin, yana tsaye gaban madubi ɗaure da towel a ƙugunsa, bai juyo ba kuma bai amsa ba, mayar da ƙofar ta yi ta rufe, ta takowa ta yi zuwa gare shi tana faɗin
"Yallaɓai kai kaɗai muke jira fa, abinci ya hallara a kan dining, ashe ma shirin shiga wanka kake" Tamkar mai ciwon baki haka ya amsa da uhmmm. Tana zuwa ta fuskanci shi ta ce
"Idan laifin da na maka ɗazu ne ka yafe mini, ina neman afuwarka ranka shi daɗe" Ƙara haɗe fuska ya yi ya ce
"Ya wuce" Ya faɗa yana nufar banɗaki. Hannu ta kai ta riƙo towel ɗin jikin nashi, kaɗan ya since da sauri ya riƙe da hannu yana faɗin
"Kar fa ki mini tsirara malama" Dariya ta yi ta ce.
"Banda abinka wane dare ne jemage bai gani ba" Ɗan sakin fuka ya yi ya ce.
"Kuma fa haka ne, sakani in watsa ruwan yara suna jirana" Ta ɗan langaɓar da kai ta ce
"Mu je in taimaka maka" A zuciyarsa ya ce
'Da a ce Hasiya ce kafin ma ta furta hakan ni zan buƙata' Amma a fili sai ya ce
"A,a ki bar shi, na hutar da ke, zan yi sauri na fito" Yana faɗar hakan bai jira cewarta ba ya raba hannunta da towel ɗinsa, ya wuce ya tura ƙofar ya shiga tare da rufo banɗakin.
Ajiyar zuciya ta sauke, tana juyawa ta koma kan luntsumeman gadonsa ta zauna daga bakin gadon, tana jiran fitowarsa, saboda bata so ta koma wajen yaran su ga ita kaɗai ce.
Ko da ya fito daga wanka ya saka jallabiya ya fesa turare, ya zauna ya ɗauki waya, yana dannawa, ta ce
"Mu je ko?"
Bai ɗago ba ya ce
"Ki je gani nan fitowa, zan yi magana da Tukur ne"
Da mamaki ta ce
"Yanzu in zauna zaman jiranka saboda kar yaran nan su ga na dawo ni kaɗai amma kake batun in tafi" Kai ya ɗago fuska babu annuri ya ce
"Ai ban ce ba zan zo ba ko?" Mirsisi ta yi ta ƙi tafiya, haka ya ajiye wayar yana tashi suka fito, don daman akwai number da yake son kira amma kuma ta ƙi bashi daman kuma ba ya son ya kira a gabanta ta zargi wani abu, duk da shi ma yana ajiye da number ne tsawon wani lokaci ba tare da ya taɓa kira ba, asali ma mamallakiyar number bata san yana da number ba, yau ne karon farko da yake son kiran ta!.
ABUJA
Hajiya Naja,atu ce zaune a makeken falonta, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana latsa waya chart suke da ƙawarta Hajiya Zuhra tana bata labarin yadda Alhaji Muhammad ya kafe a kan maganar haihuwa bayan ya san ƙudurinta da burinta na haifar ƴaƴa biyu rak a rayuwarta. Mero mai aiki ce ta shigo da sallama, ganin Hajiyar bata amsa ba ya sa ta ƙaraso ta durƙusa a gabanta ta ajiye bowl ɗin wanda yake ɗauke da fruit salad.
Mero duk da yadda aka gyara falon aka sanya abin ƙamshi amma da Hajiya ta zauna sai ya zama ƙamshin dabam. Sanye take da rigar bacci a jikinta ko bra babu.
Tana ajiye mata ta fita daga falon ta, ɗauka ta yi ta sanya spoon ɗin tana sha tana danna waya da ɗaya hannun.
WASHE GARI
Da sauri Alhaji Muhammad ya shigo falon Hajiya yana ta faman share zufa duk da sanyin safiyar da ake yi. Fuskar sa cike take da damuwa, idanunsa sun yi zuru-zuru kamar wanda ya ya tashi daga gagarumar jinya.
Ya daddage ƙarfinsa yana kwaɗawa Hajiya kiran yana faɗin "Hajiya" Ya kira amma shiru bata amsa ba ya sake kiranta a karo na biyu. "Hajiya Naja'atu." Kusan sau hudu yana kiran ta sai gata ta fito daga ɗaki tana hamma. Doguwar rigar bacci ce a jikinta, gashinta ya watse kasancewar kanta a tsefe, fuskarta da alamar tashinta daga bacci kenan ko kallon Alhajin ba ta yi ba, ta wuce ta zauna tana yatsina. "Kina lafiya?" Alhaji ya tambaya. "Lafiya lau." Ta bashi amsa cikin halin ko in kula "Kin ga lokaci kuwa? Na yi tsammanin za ki shirya min karin kumallo kin ga yau monday zan fita aiki da wuri." Ta ɗaga kafaɗa tana faɗin "Mai ya sa baka faɗawa Mero ta yi maka ba?"
Tamkar dai ya fara jin wannan kalmar haka ya bi Hajiya da kallon mamaki ya ce
"Wai shin Mero nake aure ko ke?"
Sai da ta diri hammar da ta fara sannan ta ce
"Ai saboda haka ake biyanta albashi, ko ba aiki aka ɗauke ta ba?." Alhaji ya sauke numfashi. Ba wannan ne karon farko ba. Tun bayan aurensu ne yake ƙoƙarin jure halayenta saboda tsananin son da yake mata. Ya matso kusa da numfashin su yana gauraya ya sassauta murya ya ce "Naja'atuna kina kula min da kanki don Allah, sanin kanki ne ke kaɗaice muradina da ke kaɗai zan yi rayuwa har abada! Shi ya sa nake son samun duk wani abu da nake buƙata daga mace daga wurin ki ke kaɗai amma ke sai kike wasarere da buƙatuna kai har ma da wasa da kula da kanki" Ya kai maganar yana miƙa hannunsa ya kamo hannunta, bata ce komai ba kuma bai sa ran za ta ce ɗin ba, ya rasa mai yasa Hajiya Naja,atu ita ce rauninsa, ko yanzu a fusace ya fito kamar kumurcin xaki don ya zo ya tsawatar mata amma kuma da ya ganta sai ya ji sonta ya danne gabaɗaya laifinta.
Yana mai sassauta murya ya ci gaba da cewa
" Ki yi kwalliya ko da ba za mu je ko'ina ba. Ina son idan na dawo gida in tarar da matata cikin ƙamshi." Ya faɗa yana rausayar da kai kamar ƙaramin yaro.
Ta yi dariyar rainin hankali ta ce "Kai ma dai Alhaji! Wai duk wannan maganar kwalliya da gayu da kake ta batunsu, duk saboda namiji Ni ban ga amfaninta ba, in banda ɓata lokaci da ɓata kuɗi." Ya yi shiru. Ta ci gaba da magana ba tare da ta kula da yadda maganarta take sukar zuciyarsa ba. "Ni ba irin matan nan ba ne da kullum sai yin abubuwan da za su birge namiji, gabaɗaya su ƙarar da rayuwarsu a kan namiji, tunaninsu kullum a kan abu ɗaya shi ne ya za su birge namiji, kullum suna shagon siyar da mayuka, zuwa wajen gyaran gashi, saboda ɗaurewa ƙarya tsantsa hatta wankin ƙafa sai mace ta je ta zauna ta miƙa ƙafa a wanke mata ni dai ba na sha,awar yin abubuwan nan saboda ba sa birgeni ko kaɗan na fi ganewa in zauna ina charting da ƴan uwa ƙawaye da abokan arziƙi. Idan kana so, ka fita ka kalla a waje." Alhaji ya haɗiye abin da yake son faɗa. Ya juya zai fita, sai ta sake cewa, "Kuma ka daina damuna da maganar haihuwa. Na faɗa maka tun kafin aure, ni yara biyu kacal zan haifa. Na farko ma ya rasu, yanzu sai bayan shekara goma zan sake tunanin wani." Kalmar ta sauka a ƙahon zuciyar Alhaji kamar dutse, amma haka ya daure ya fita daga falon ita kuma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.
Sama ya haura ransa duk babu daɗi, ya shirya don zuwa office, a wannan halin yadda yake jin ransa duk a jagule ba zai iya cewa Mero ta sama masa abin da zai ci ba don ya san babu abin da zai iya ci.
A wannan lokacin kuwa, a ɗaya ɓangaren gidan... Hajiya Kaltume tana zaune tana jan carbi, amma zuciyarta cike take da damuwa. "Ya Allah" Ta furta a hankali. A zuciyarta tana faɗin 'Ni ɗana guda ɗaya Allah ya bani. Yanzu kuma jikoki ma sun gagara. Ni da na ci burin ta tsatson ɗana zan tara zuri,a mai tarin yawa amma abu ya ci tura!' Ta ɗago kai lokacin da ta ji Alhaji Muhammad ya shigo. Kallo ɗaya ta yi masa, ta gane damuwar da ke tattare da shi. A ranta ta ce, "Lokaci ya yi. Dole na ceci rayuwar ɗana, ko da kuwa Naja'atu ba za ta so hakan ba, dole ne na sanya ya ƙara aure don na matsu na ga jikokina.
Bayan ta amsa masa sallamar ya shigo ya zauna yana rataye da jakar aiki ya gaishe da ita ta amsa, masa ta yi masa addu,a bayan ya mata sallama ya fita tana mai masa fatan alkairi.
Ko da ya fito bai nufi ɓangaren Hajiya ba sai ya wuce office yana baya direba yana jansa.
DARE
Kwance yake a ɗakinsa a katafaren gadonsa sai juyi yake, zuwa can ya kasa jurewa ya ɗaga waya ya kira Hajiya Naja'atu, har ta tsinke ba ta ɗaga ba, haka ya ci gaba da kira amma shiru maye ya ci shirwa.
Sai da ya jera mata kira goma, amma bata ɗaga ba, a kira na sha ɗaya ta ɗaga wayar bata ce komai ba, sai dai yana jin ƙaran Tv alamar tana jinsa maganar ce ba za ta yi ba.
Iska ya hurar daga bakinsa har sai da ta ji sautin hakan ya buɗe baki ya ce
"Naja,atuna ina kika shiga ne ina ta kiranki amma baki ɗaga ba?" ,Ya faɗi hakan cikin wata murya da ita kaɗai ta san abin da yake nufi. Baki ta taɓr kamar yana ganinta ta ce
"Ina ɗan uzuri ne" Ta faɗa bayan babu wani uzuri da take yi tana zaune tana ganin kiran. Mantar da maganar ɗaga waya ya yi ya ce
"Ki zo ɗakina ina son ganinki" Kasancewar ta san manufarsa ta ce
"Ina priod ne" A kiɗime ya tashi zaune ya ce
"P... me?"
Hajiya ta ce
"Priod, wai ko baka gane ba in maka fashin baƙi ina nufin al,ada" Hannu ya sanya ya dafe ƙirjinsa ya ce
"Da gaske ko wasa?"
Tana yatsina fuska ta ce
"Haba Alhaji wai ya ina magana kana neman ƙaryatani mene ne amfanin faɗin maganar da ba gaskiya ba? Ina ganin babu amfani babu alfanu a faɗar ƙarya"
Yana jin damuwa ya ce
"Wai daman ba ciki ne da ke ba Naja?" Wani murmushin rainin hankali ta saki har yana jin sautinsa a kunnensa ta ce
"Ciki kuma? Wannan ai labarin ƙanzon kurege ne"
Kamar zai yi kuka ya ce
"Wallahi wancan watan da baki yi ba duk zatona an samu ƙaruwa ne" Baki ta taɓe ta ce
"Ita al,ada ai tana yin haka wani lokacin sai ta yi tsallakiya amma bani da komai" Zai yj magana ta ce
"Ina jin bacci"
Ya ce
"Kar ki kashe waya, ki zo mu kwanta a ɗakina"
Tana farrr da ido ta ce
"Na riga na hau gado ba zan iya sakkowa ba" Ƙittt ya ji ta kashe wayar.
Wayarsa ya ɗauka ya sako takalminsa mai laushi wanda yake iri ɗaya da lafiyayyan shimfiɗaɗɗan bargon kan gadonsa, wanda ya kasance browan colour.
Ƙofa ya buɗe ya fito yana tako matakalar ya sakko ƙasa, ya nufi part ɗin Hajiya Naja,atu.
Ƙofar ya tura ya shiga ya mayar ya rufe.
Zaune take a tsakiyar gado, ga plate nan gabanta tana cin chips tana danna waya. Plate ɗin ya matsar mata gefe kusa da ita ya hau gadon, sai dai duk wani ɓurɓushin abu kamar biskit ya ji a kan shimfiɗar, ƙorafin da ta yi ya sanya ta sauka daga gadon tana faɗin ya karkaɗe alewar madara ce da ta sanya Mero ta mata ɗazu shi ne duk ta zube. Maimakon ya karkaɗe kamar yadda ta yi zato sai ta ga ya cire zanin gadon gabaɗaya har pillow case ya saka cikin kwandon kayan wanki ya ɗakko wani ya shimfiɗa ya saka pillow case ɗin, ya koma ya kwanta yana ta kallonta tamkar hoto sai da ta gama ja masa rai ta zo ta kwanta har lokacin wayarta da ta fi ba ta muhimmanci fiye da shi tana dannawa yau dai ya yi sa,a ba ta bashi-bashin rashin sanya turare da alama bata daɗe da yin wankan ba.
Sauka ya yi ya ɗakko turare a kan madubi, sure, humra da wasu guda biyu masu daɗin ƙamshi, duk shi yake siyowa gasu nan a kan madubin kamar za a buɗe shago saboda yawansu, amma kuma wani ma sai ka samu bata taɓa buɗewa ba saboda ba damunta suka yi ba.
Da kansa ya shafa mata, tana wani noƙewa, yana gamawa ya mayar ya ɗauki plate ɗin da ta gama amfani ya fita da shi kicin ɗin falonta ya dawo. Fitila ya kashe ya ƙara gudun AC ya haura kan gadon sai dai mai? Yana kai hannunsa jikinta ta ce bata san zance ba, kamar an tsikarenta ta tashi zaune tana faɗin
"Haba Alhaji, ni wallahi na gaji da wannna abun, kullum mutum ba zai huta ba sai ana naniƙarsa"
Hankalinsa in ya yi dubu ya kai ƙololuwar tashi ya ce
"Haba Naja,atu a ƙalla mun doshi sati uku bamu kaɗaice da juna ba, ina binki kin gocewa, yau ki ce wancan gobe ki ce wancan, shin wajen wa zan nema, kin san dai ke kaɗai ce halaliyata to ina kike so in je in nema?"
Cike da gadara ta ce
"Alhaji bari ka ji in faɗa maka, idan ma a tunaninka yawan yin mu,amala ne yake kawo mace ta samu ciki to ka cire wannan a ranka saboda na faɗa maka ni sai bayan shekara goma zan sake haihuwa don haka ka ma daina tunanin samun ɗa a kwana kusa...
Ranakun posting
Asabar Lahdi Litinin Talata Laraba.
Share & comment😍🤚
Maman afrah
*** [7/12, 5:27 PM] MOM MASHKR & AFRAH: ***
*KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH
Daga marubuciyar
Ruwa cikin cokali Uwar agola Malamin bogi ƙazamin miji Yar zaman wanka Ruɓaɓɓiyar igiya Ƙara,in inna delu Bonono Ci ma zaune Ƴan adaidaira sahu Jalli joga Ungozoma Ƴar ƙanwata, Beelal Da sauransu. ***