KIBIYA A IDO

2

by @mamanafrah3028

Jan hankali ga wanda za mu yi wannan tafiyar, labarin yana ɗauke da ɓangarori a ƙalla guda uku, kowane ɓangare da muhimmiyar rawar da zai taka, ku biyo ni sannu a hankali don mu nutsa a cikin labarin.

_ALHAJI MUHAMAMD_

Kafin Alhaji ya gama dawowa daga shan ruwan mamakin da ta shayar da shi ta ɗora da faɗin

"Don haka ka ma daina tunanin samun ɗa a kwana kusa." Ta ƙarasa maganar tana juya masa baya, ta ja bargo ta rufe jikinta, hankalin ta kwance kamar tsumma a randa. Shiru ya ratsa ɗakin sai ƙaran AC. Shiru ya yi irin shirun da bakin mutum yake masa nauyi ya kasa furta komai. Alhaji Muhammad ya ci gaba da kallonta. Yana jin kalamanta suna karyar masa da zuciya. A iya rayuwarsa bai taɓa tunanin matar da yake so fiye da komai za ta gaya masa cewa burinsa ba shi da wani muhimmanci a wurinta ba, tun da a iya sanin sa bayan mahaifiyarsa ba ya haɗa son Naja'atu da komai, kuma ta san babban burinsa a duniya shi ne haihuwar ƴaƴa masu yawa kuma hakan shi ne burin mahaifiyarsa ma, sai dai ga bai dace da matar aure ba. A hankali ya sauke ƙafafunsa daga gadon kamar zai tashi sai ya fasa ya buɗe baki ya ce. "Naja'atu" Ya kira sunanta muryarsa tana rawa .

Ko kallonsa bata yi ba bare ya saka ran za ta amsa ba. Ya sake cewa, "Da gaske kike abin da kika faɗa?" Ba tare da ta waiwayo ba ta ce, "Fiye da yadda kake zato ma za ka ji, a ganina wannan ba sabon abu bane, abu ne wanda ka san da shi kuma ka san ni Naja'atu ba zan taɓa sauya ƙudurina ba duk runtsi." Idanunsa. ya runtse na ɗan lokaci ya ji kamar numfashi yana masa wahalar shaƙa. Ganin abun ba na ƙare bane don ya san Hajiya Naja'atu da kafiya ba za ta sake canja ra,ayi ba kamar yadda ta faɗa, saboda macw ce ita kaifi ɗaya, amma a yadda ya san mata suna da son ƴaƴa suna son su ga sun haihu bai taɓa zaton akwai mata irin Naja'atu a duniya ba, kuma tunaninsa za ta canja ra,ayinta ne watarana shi ya sa yake tu tuɓar ta.

Ajiyar zuciya ya saukeaga cikin sanyin murya ya ce "To idan na kasa jira tsawon shekaru gomar da kika gindaya mini fa? Shin ma ina da tabbacin zan kai shekara gomar nan gaba, ko kina so Allah ya ɗauki rayuwata ban ga tsatsona a duniya ba?" Ya faɗa yana dakatawa don bata damar ta furta wani abun. Nan take ta juya ta kalle shi. Idanunsu suka sarƙe da na juna Murmushi ta yi, wani irin sanyi ya ji a zuciyarsa ganin ta saki murmushi bai san ba murmushin rainin hankali bane. Bauɗar bakinta sai ta ce "To ka je ka nemo inda za ka samu abin da kake nema." Kalmar ta fito daga bakinta cikin sauƙi, amma ta sauka a zuciyar Alhaji kamar an caka masa wuƙa. Ya zura mata ido kafin ya yi ƙarfib halin faɗin. "Mi kike nufi da hakan?" Ta ɗaga kafaɗa,.alamar ko a jikinta.

Ya sake faɗin

"Ya kike so in yi da rayuwata ne, ko so kike in bar duniyar? Ya tambaya don ganin ko zai samu lagwanta ta karaya ta haifa masa ɗa. Ji ya yi ta ce "Ni ban ce maka ka yi ba, ban kuma ce kada ka yi ba kar ka saka ni a bakin duniya." Ta faɗa tana mayar da idanunta kan wayarta tana murmushi kamar babu abin da ya faru. Alhaji Muhammad bai sake furta komai ba.

Ya jima zaune, kafin ya sake cewa, to na ji batun haihuwa zan jira ki zuwa shekaru goman, duk da na san da a ce yanzu za ki haifa min ɗa da zuwa shekara goma ai ya girma, amma babu komai haka Allah ya tsara kowa da ƙaddararsa ni wannan ce tawa" Baki ta taɓe, ya ja numfashi ya ce

"Batun haƙƙin fa" Ta kalle shi ta watsar sai kuma ta ce

"A duniya idan akwai abin da na tsana to maimaita magana ne!. Ai tun wayar da muka yi na faɗa maka bani da tsarki amma ka zo kana wani neme-neme" Ya kalle ta kallon tsaf ya ga duk kalaman da take furta masa ko a jikinta da alama bata san irin zafi da ƙuna haɗe da raɗaɗin da suke saka masa a ƙoƙon ransa ba, amma ya zai yi? Amsar guda ɗaya ce haƙuri!. Tsaye ya miƙe yana saka hannayensa duka biyun a cikin aljihun rigar baccin nashi, ya tsaya na kimanin mintuna biyu kafin daga bisani ya fara takawa don a zuciyarsa ya yanke shawarar gwara ya koma ɗakinsa hakan zai fi sauƙi da salama a wajensa, domin ya san muddjn zaj zauna a ɗakin to ransa zai yj ta ɓaci ne ba tare da ya samu abin da yake so. Bin bayansa ta yi da kallo yana taku cikin nutsuwa sai dai kana ganinsa ka san yana takun ne cikin karayar zuciya haɗe da ƙarfin hali domin raunin da zuciyarsa ta yi ya bayyana a gabaɗaya yanayinsa!.

Yana zuwa jikin ƙofar ya saka hannu ya riƴe handle ɗin ƙofar, a hankali ya waiwaiyo yana mai buɗe baki cikin sassanyar muryarsa ya ce

"Sai da safe Naja'atuna!" Ɗan juya idanu ta yi ta danna wayarta hasken ya ɗauke ta miƙa ta can saman kanta daga gefe ta ajiye a kan gadon ta sake janyo bargon ta gyara rufar da ta yi ta ce

"Mu kwana lafiya" Tana faɗar hakan ta ja bargon ta rufe har kanta. Kallon ƴan sakanni ya yi mata ya juya yana murɗa handle ɗin ya buɗe ƙofar ya fita tare da rufo mata.

Yana baro part ɗinsa ya tsayar da idanunsa a hanyar ɓangaren mahaifiyarsa, yana jin kamar ya yi kuka, saboda ya san ita kaɗai ce take lallashin sa idan yana cikin damuwa, take faɗa masa kalamai masu taushi, haƙorinsa ya saka ya dantse leɓansa na sama, ya kama hanyar nasa part ɗin yana zuwa ya tura ƙofar ya haura sama, ɗaya daga cikin ɗakunan ya buɗe ya shiga inda nan ne ya fi amfani da shi kuma daga nan ne ya fita ya je ɓangaren Hajiya Naja'atun.

Har ya kwanta ya ji gabaɗaya zuciyarsa ta cushe, duk ya shiga wani irin yanayi, ga buƙatuwa sannan ga damuwar alwashin da matarsa take ci a har kullum na rashin son haihuwar nan a kwana kusa, gashi mai son yara da son ganin ya tara zuriya, ga tsaurin ra,ayin cewa shi bashi da ra,ayin mata biyu da mace ɗaya kawai zai rayu sai dai kuma kana naka ne Allah yana nashi wato bai samu macen da ta dace ta riƙe masa buƙatunsa da kuma faranta masa ba. Kamar an tsikare shi ya sakko daga gadon ya cire kayansa ya ɗaura towel banɗaki ya nufa yana zuwa dakyar ya samu yjn addu,a shiga banɗaki yana shiga ya sakarwa kansa shower, tsaye yake kawai ruwan yana zuba a jikinsa, ya jima a haka sannan ya fito jikinsa ya goge ya mayar da kayansa, da wasu zai saka ma sai dai ƙamshin turarukan da ya shafawa Hajiya Naja'atu a jikin kayansa hakan ta sa ya ji yana son kwanciya yana shaƙar ƙamshin, duk kuwa da sai da ya yi wanka ya shafa nashi turaren amma dai saboda soyayya ba ya jin zai cire kayan sai da asuba.

Ƙwayayan ɗakin ya kashe yana shirin hawa gadon ya ji ya fara jin wani irin sanyi, ya san kuma ƙarfin buƙatuwar da yake da ita ne, zai haifar masa da zazzaɓi saboda bai samu abin da yake so ba a wajen wacce ya dace ta bashi shi kuma mutum mai kamun kai da tsoron Allah, ko kaɗan ba ya sha,awar neman abin da ya rasa a gidansa a can waje, wato mutum ne da ya tsani zina, mugun tsantsanin duk mai aikatata ma yake.

Haka ya rufa yana ɗan karkarwa, shi kansa tausayin kansa yake ya rasa yaushe ne zai samu farinciki irin farincikin da ma,aurata suke samu, gashi da aure amma kamar gwauro.

Vibrating ɗin da wayarsa ta shiga yi, kasancewar ya mayar da ita silent, shi ya sanya ya sake juyi ya rufa har saman kansa, yana ji har ta daina alamar kiran ya katse, ba a jima ba ta sake ɗaukan wani rurin yana zumzumzum. Idanu ya rufe da ƙarfi yana jin takaicin mai kiransa a daidai wannan lokacin, sai da kiran ta shigo a karo na uku wata zuciyar ta ce

',Baka tunanin ko Naja'atunka ce ta jnaye ƙudurinra take kiranka ka je ku kasance a tare" Da sauri ya tashi zaune yana cire bargon da ya rufa ya miƙa hannu ya janyo wayar yana fatan zatin da yake ya zama gaskiya, sai dai kash yana ɗakkowa ya ga wannan lambar ce dai wacce ake yawan kiransa da ita, don daga lambobin ƙarshen lambar yake ganewa. Wani tsaki ya ja sau biyu a jere yana jin kamar ya janyo mai lambar ya yi ta duka.

Wurgi ya yi da wayar a kan gadon ya koma ya kwanta amma saboda naci aka ci gaba da kiran, wannan kiran da ya shigo karo na biyar ne. Yana katsewa wani ya shigo a zuciye ya janyo wayar da nufin ya shuka mata rashin mutunci, don ya san daman mace ce shi dai bai san wace ce ba amma dai abu ɗaya ya sani ranar da ta fara kiransa da lambar ya ɗauka sun yi magana ta kawo masa buƙatar tana so ya aure ta, a take ya dakatar da iya ba tare da ya tsaya ya saurari sautan bayanin ba, tun daga ranar idan ta kira ba ya ɗagawa.

Yana ɗaga wayar sai da ya ɗauki sakanni kafin ya kara a kunnensa, yana kaiwa kunnensa da sauke ajiyar zuciyarta kunnesa ya ci karo, kafin daga bisani ya ji ta ce

"Alhamdulillah, na gode Allah da ka amsa kiran" Takaici ne ya kama shi, bayan takaicin Naja'atunsa da yake ciki a gefe ɗaya ga wata ta zo za ta ƙara masa ciwon kai, wannan dalilin yana cikin ƙananun dalilan da ya sanya ba ya son auren mace sama da ɗaya, don ba zai jure cakwakiyar mata ba na kishi da neman magana da dai sauran abubuwan da suke idan suna kishi da junansu a kan miji.

Baki ya buɗe ya ce

"Ki faɗi abin da ya kawo domin ina da abubuwan yi masu yawa"

,Murmushi mai sauti ta yi ta ce

"Ni kuma na ajiye abubuwa da yawa don na gana da kai, a ganina kaima za ka iya bani aron lokacinka ko da awa biyar ne babu yaw... A ƙufule ya dakatar da ita da faɗin

"Tun ranar da kika kirani na ce miki ina da aure"

Buɗar bakinta ta ce

"Ubangiji dai ya halalta maka mata huɗu"

Cike da gajiyawa da maganarta ya ce

"Tun da ya bani damar zaɓi ni da mace ɗaya tak zan zauna, don ba zan iya adalci ba"

Shiru ya ɗan ratsa wayar kafin ta ce

"Ka mini wannan alfarmar zan share maka hawaye"

Da ƙarfi ya ce

"Uban waye ya ce miki kuka nake?"

Dariya mai sauti ce ta kuɓuce mata ta ce

"Ba kukan hawaye ba kukan zuci nake nufi... Tun kafin ta kai ƙarshen maganar ta ji ƙittt ya katse wayar, shi kuma a nashi ɓangaren da ya katse sai da ya kashe wayar ma baki ɗaya.

Jin ya kashe wayar ta ɗan yi jim tana tunanin nan ba da jimawa ba zai shigo hannunta sai yadda ta yi da shi, da zarar ta damƙi alakar zuciyarsa sai yadda ta so za ta sarrafa shi, ta san wannn duk yana ƙi ne saboda farkon haɗuwar su ne har za ta sake kira sai dai ta bar shi sai zuwa wani lokacin.

Fitarsa ke da wuya ta buɗe rufar ta sakko ta je ta kashe fitila tana mai jan dogon tsaki, dawowa ta yi ta kwanta tana ɗaukan wayarta ta kira mahaifiyarta, sau biyu tana kira har ta tsinke ba a ɗaga ba, hakan ya sa ta sanya a ranta cewar mahaifiyar tata ta yi bacci.

Washe gari

Cikin shirin fita office ya fito bai san mai ya sa ba yau kawai ya ji ba ya son zuwa inda Naja'atu take, sai dai ya san hakan ba ya rasa nasaba da abin da ta masa jiya, duk da bai cika barin zuciyarsa tana ɗaukan fushi da ita ba, ko da ya ji alamar hakan yana dannewa ne don ta daban ce ita.

Dining ya nufa kamar yadda ya yi zato kuwa hakan ce ta kasance don Mero ta gama haɗa kayan karin kumallon ta jere a dining ɗin. Zaunawa ya yi ya zubawa kansa yana ci tamkar wani marar gata, tunani yake a ransa shin kowane gida ne yake cike da irin ƙalubalen da nashi gidan yake ciki ko kuwa dai shi ne ya tsinci kansa a cikin hakan? A tunaninsa ko da a ce ba matarsa ce za ta shirya kayan karin kumallon ba a ƙalla au ta zo ta kula da shi ta zuba masa su ci tare amma ita Naja'atu ta daban ce a cikin mata ko kaɗan bata damu da miji ba, bata damu da sabgar miji ba, bata damu da damuwarsa ko farincikin sa ba, abu ɗaya ta sani shi ne son kanta, tana sob kanta da yawa. Yana cikin ci Mero ta shigo bayan ya amsa mata sallama kofuna da tea spoons ne ta ajiye ta rusuna tana gaishe da shi ya amsa, ta juya ta tafi a ransa yana raya cewa ita Mero bata san daɗin jikinta da ciwon kanta bane da take ta faman kai kawo a kicin ta samarwa kowa abin da zai ci ko kuwa? Wani ɓangare na zuciyarsa ya ce

'Baka ganin ita bata da gata, kuma wannan aikin da take shi ne hanyar da take samun rufin asiri' Da wannan ya ajiye fork ɗin hannunsa, ya haɗa tea kurɓa ɗaya ya yi ya ajiye ya tashi duk ji yake abincin ma babu wano armashi hakan ba ya rasa nasaba da damuwar da take cikin ransa.

Yana fitowa ya nufi part ɗin mahaifiyarsa, lokacin da ya shigo Amira ce ɗaya daga cikin ƴan aikin gidan tana goge - goge ta gaishe shi cike da girmamawa ya tambaye ta Goggon ta ce tana ɗaki yanzu ta shiga za ta shiga banɗaki. Zama ya yi yana danna waya bayan kamar minti huɗu ta fito, tun da ta buɗe ƙofar ta hange shi zaune ta kafe shi da ido tana nazartarsa har ta ƙaraso tsakiyar falon, sannan ne hankallinsa ya kai gare ta. Cike da ladabi ya zamo daga kujerar ya gaishe ta ta amsa masa bayan ta zauna.

Cikin sanyin murya ta ce

"Ko a kawo maka koko da ƙosai za ka ci?" Ya ɗago ya kalle ta bayan ya zauna ya ce

"Ai mun karya" Ta kalle shi ta ce

"Kun karya ko ka karya?" Kafin ya bata amsa ta ce

"Ai na san Naja ko giyar wake ta haɗiya ba za ta tashi yanzu daga bacci ba bare har ta karya"

Shiru ya yi ta ce

"Muhammad ka daina saka damuwa a ranka, idan ka nakasta kanka Naja bata da asara fa, ni ɗin nan dai ni ka taƙaita gwara ka watsar da lamarinta, tun da har Allah ya haɗa ku zama kuma kana ƙaunarta sai ka yi haƙuri da halayyarta" Idanunsa ne suka ɗan ciko da ƙwalla amma bai bari Goggon ta gani ba ya mayar da su ya ce

"Goggo ni ba na saka damuwa a raina, kawai dai maganar haihuwar nan ce har yau tana kan bakanta jiya ma mun yi magana da dare ta ce ba gudu ba ja da baya'

Goggo takaicinsa da ya cika ta ta ce

"Ta min daidai" Da sauri ya ɗago ya kalle ta ta ce

"Eh mana, ai duk wanda ya samu rana shanya yake yi ta yaya za ka zauna mace take juya ka a gidanka, a ce wai haihuwa wannan sai ta zaɓi lokacin da za ta yi, gashi gabaɗaya lamarinka matsayinta na matarka babu ruwanta da al,amuranka, kuma ni na rasa shegen da ya sa ƙaiƙayin bakin ka ya sa ka ce wai da ita kaɗai za ka rayu, wannan banzan ƙuduri ne na ranka ka ga ai yanzu sai ta ja zarenta yadda take so" Kai ya sunkuyar ya ce

"Goggo don Allah ki mata magana ko Allah zai sa ta canja ra,ayi"

Goggo ta ce

"Uhm in ji mai ciwon haƙuri yarinyar da bata da ta ido, ta min rainin ƙare dangi, ita ce har zan faɗa mata ta ji, da a c kishiya ka danƙaro mata ai da ta nutsu ta san inda yakr mata ciwo" Gabansa ne ya buga da ƙarfi a take ya shiga jujjuya kai alamar a,a.

Goggo ta ce

"To tun da ka ji ka gani, ma ji ma gani an rufe tsohuwa da ranta"

Magiya ya shiga yi mata a kan ta daure ta samu Naja'atun tausayinsa ya saka ta amince da hakan, tashi ya yi ya mata sallama, ta shiga ƙwalaw Amira kira a kan ta zo ta ɗakko mata ruwa. Shi kuma ya nufi hanyar fita tana ta masa addu,a tare da sanya masa albarka yana ta ambaton amin.

*NURIYYA*

Zaune take a tsakar gidan tana ta rawar sanyi kasancewar garin yau an tashi da sanyi, sannan a lokacin ma duk da yamma ta yi amma sanyin yana nan. Tashi ta yi a karo na biyu ta lallaɓo ta zo ƙofar falon, a hankali ta ɗaga labulen falon ta leƙa bata hango kowa ba a falon hakan ya sa ta saki labulen ta tsaya a wajen. Jim kaɗan ta fara jiyo muryar Momma a falon tana waya hakan ya sa da sauri ta matsa daga jikin kofar ta koma gefe ta tsaya.

Jin shiru alamar an gama wayar ta leƙa gabanta yana faɗuwa, ta leƙa ta ce

"Momm... Wata uwar harara da Hajiya Hauwa'u ta daka mata shi ta sanya jikinta karkarwa kamar mazari, gabaɗaya sai ta diririce saboda yarinta kasancewar shekarun ta shida kacal. Maimakon ta fita tsabar tsawar da ta doka mata sai kawai gata a tsakiyar falon, sai da ta zo tsakiyar falon ne sannan ta gane ba waje ta fita ba, a ruɗe ta juya a guje don ficewa gudun kar ta janyowa kanta laifin da za ta sha uban duka. Hajiya Hauwa'u ta ɗaga murya ta ce.

"Zo nan munafuka, gidan uban wa za ki je" Da hanzari ta dawo jikinta yana karkarwa idanunta kuwa sun fara zubar da hawayen tausayin kanta.

Kafin ta ƙaraso inda Hajiyar take ta durƙusa a gwiwoyinta a ƙasa.

Hajiya ta zara mata idanu ta ce

"Mai kika zo mini falo? Ko munafurcin naki ne ?"

Nuriyya ta hau girgiza kai bakinta yana rawa ta ce

"Yu...yu...yun...wa nake... ji" Ta faɗa a ciccire saboda tsabar tsoro idan akwai wanda take tsoro a duniya to Hajiya Hauwa'u ce saboda baƙar azabar da take sha a hannun ta.

Tana aika mata wani kallon tsana da tsangwama ta ce

"Uban wa ya ce ki shigo min falo, shegiya baƙar annoba" Nuriyya ta shiga faɗin

"Ki yi haƙuri Momma" Hajiya Hauwa'u cike da mugunta ta tashi ta nufi gaban Nuriyya, Nuriyyar tana ja da baya amma ta kama kunneta guda ɗaya ta murɗe da ƙarfi, ƙara ta saki cike da azaba. Bata san lokacin da fitsari ya kufce mata ba, tsoron fitsarin da ta ji ta yi gudun kar Hajiyar ta sake gana mata azaba, hakan ya sa tana sakin kunneta ta miƙe a karo na biyu ta nufi hanyar waje, Hajiya kuma ta juya za ta ɗakko wayarta a kan center table domin tana son kiran mai gadi ya sa a siyo mata dorina ta mata dukan da ko hanyar falon ta ba za ta ƙara nufowa ba.

Lokacin har Nuriyya ta bar falon ita kuma ko kaɗan bata san Nuriyya ta saki fitsari ba, tana tahowa cikin rashij sani ta saukar da ƙafarta a cikin fitsarin da yake kwance a kan tiles ɗin wata uwar sufa ta yi tamkar an ɗaga ta a jefar a wajen cike da karaɗi ta ce

"Wayyo Allah kwankwasona!"

Ihun da ta ƙwalla ya yi daidai da ƙaran buɗewar get ɗin gidan, inda direban Alhaji Ahmad Jarma mahaifi ga Nuriyya ya kutso da hancin motar cikin harabar gidan, Alhaji yana bayan motar.

Comment & Share

Maman Afrah *** [7/13, 6:05 PM] MOM MASHKR & AFRAH: ***

*KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH

Daga marubuciyar

Ruwa cikin cokali Uwar agola Malamin bogi ƙazamin miji Yar zaman wanka Ruɓaɓɓiyar igiya Ƙara,in inna delu Bonono Ci ma zaune Ƴan adaidaira sahu Jalli joga Ungozoma Ƴar ƙanwata, Beelal Da sauransu. ***