KIBIYA A IDO

3

by @mamanafrah3028

Jan hankali ga wanda za mu yi wannan tafiyar, labarin yana ɗauke da ɓangarori a ƙalla guda uku, kowane ɓangare da muhimmiyar rawar da zai taka, ku biyo ni sannu a hankali don mu nutsa a cikin labarin.

*GOGGO*

Bayan fitar Alhaji Muhammad da jimawa lokacin ta san hamshaƙiyar ta samu fitowa, ta aika Amira tw ce ta kirawo ta tana son ganinta. Amira ko da ta je daman a ɗarare ta je ta same ta zaune ta kame a kan kujera tana shan lemo. Sai Mero da take durƙushe a gabanta tana mata faɗa tana faɗin

"Ke kece uwar ƴan ƙaƙale-ƙaƙalen jaraba da shegen tsaftar munafurci, ban da rashin aikin yi da wahala a ce ɗaki kullum sai an share an goge ba cewa na yi kike bari bayan kwana biyu ko uku ki gyara ba, tun da ba wani zama nake yj ba ma sai lokaci,-lokaci sannan ma ba wani yara bane a gidan" Haƙuri Mero take bata kamar za ta ari baki. Dogon tsaki ta je ta umarce ta da ta ɗauke mopper ta fice mata a falo. Tana gamawa ta juyo kan Amira ta ce .

"Ke kuma uban mai kike min a nan" Amira ta ce

",Daman Goggo ce ta ce in kiwo ki tana son ganinki" Wani kallon ɗaya saura kwata ta mata tana mai baya amsa da faɗin

"Ita Goggon ce ta ce in je? To mai zan je in yi a ɓangaren ta? Gida ne ta kafa ƙwawa ta dawo da zama ta zo cikin yara ta miƙe ƙafa tana manyance shi ne yanzu za ta wani aiko ta ce in je saboda kawai samun wuri tusar asuba" Kai Amira ta sunkuyar tana jin babu daɗi don ta san hakan rashin kunya ne da rashin girmama na gaba.

Tana nan tsugunne tana jiran amsar da za a bata amma sta mayar da hankali kan waya, kusan minti biyar tana zaune Hajiya ta juyo ta ce

"Wai zaman mai kike? Ko rahoto ta aiko ki ki ɗauka mata a kaina ne?" Amira ta shiga girgiza kai tana miƙewa tsaye cikin sanyin jiki ta nufi hanyar fita, tana dab da fita Hajiya Naja'atu ta ce

"Ta jira ni idan na ga da dama zan iya zuwa" Da to ta amsa ta baro part ɗin. Tana zuwa Goggo ta shiga tambayar ta dalilin daɗewarta saboda kar ta sanar da Goggo cewa ƙyaleta ta yj tana zaune ta san Goggon ba za ta ji daɗi ba sai ra samu kanta da yin ƙarya ta hanyar cewa Hajiyar ce a banɗaki. Goggo ta tambaye ta amsar da aka bata nan Amira ta ce ta ce tana zuwa.

Duk da Goggon ta san halin ta amma sai ta ja bakinta ta yj shiru.

Hajiya Naja'atu kuwa Amira na fita ta ja ƙaramin tsaki ta gyara kwanciyarta a doguwar kujerar bayan ta gama shan lemon. A fili ta furta

"Idan kin matsu da maganar kya zo inda nake ki sameni aikin banza shafa lalle a mazaunai, ai ni wallahi banu macen da don ina auren ɗanta za ta zo har gida ta juyani ta yi kaɗan wallaho don ba iyayena ne suka ce jeki kya gani ba da zan zama tamkar sitiyarin mota a gidan miji sai yadda aka so za a juyani"

Goggo har aka yi azzahar bata ga ko da ƙeyar Hajiya Naja'atu ba, sosai ta ji haushin rashin nuna isar da ta mata. Da la,asar ta kama hanyar ɓangaren Hajiya Naja'atu, tana zuwa ta tura ƙofar da za ta sada ta da ɓangaren ra shiga, ƙofar babban falon ta dosa wanda shi ne mashigar ɓangaren tana zuwa ta samu ƙofar a rufe ƙwanƙwasawa ta yi, shiru ba a amsa ba bare a buɗe ta ci gaba da bugawa, duk abin da takr Hajiya Naja'atu tana babban falon tama ji, abin da ya sanya bata amsa ba saboda ta san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato ta san ba ya wuce Goggo tun da ta aiko bata zo ba ta san za ta iya tasowa takanas ta zo nemanta.

Kusan minti shida tana tsaye idan ta buga aka ɗan jima sai ta sake bugawa. Hajiya Naja'ati ta taso ta zo jikin ƙofar ta leƙo idonta ta inda aka yi don leƙawa yar tula a jikin ƙofar baki ta taɓe kafin ta fara magana cikin hargowa tana faɗin.

"Wai waye yake min wannan bugun tun ɗazu, kamar na ci bashi ban biya ba" ,Goggo ta ce

"Ni ce"

Hajiya Naja'atu duk da ta ɗauki muryar amma saboda wulaƙanci ta ce

"Ke ce wa? Ko shaiɗan ai ban san nice ba"

Goggo ta ce

"Ni ce Goggon Muhammad" Baki ta taɓe a zuciyarta tana faɗin

'Gwara da kika ce Goggonsa don ni ba tawa bace saboda ko hanya bamu haɗa da ke ba' Tana gama faɗar hakan ta buɗe ƙofar buɗe ƙofar ke da wuya ta juya ta fara tafiya abin ta. Goggo ta biyo bayanta cike da sallama, tana jin babu daɗi a zuciyarta saboda ko a mafarki bata taɓa tunani ko zaton cewar ɗanta zai auri mace irin wannan sai dai sanin ɗan adam ba ya wuce ƙaddararsa, Muhammad mutum mai ladabi biyayya da girmama manya ko baka san shi ba in dai ka girme shi zai girmama ka, sannan uwa uba kyakkyawar ma,amala sai gashi Allah ya jarabce shi da auren wata mace wacce zama da ita sai dai haƙuri.

Sallamar da Goggon take Hajiya Naja'atu bata amsa ba, har sai da ya je ta zauna a kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ta ce

",Maraba" Ta faɗa a maimakon ta amsa sallamar. Lokacin da ta faɗi hakan Goggom ta zo tsakiyar falon, tana zuwa ta zauna a ɗaya daga cikon kujerun da suka yi wa falon ƙawanya.

Hajiya kuwa daga maraba bata sake cewa wani abu ba ta tsurawa waya idanu tana jijjiga ƙafafu.

Goggo ranta ya ɓaci amma sai ta danne ta ce

"Naja saƙon kirana bai same ki bane?" ,Kamar ba za ta yi magana ba sai ta ɗago tana ɗan wano murmushin rainin hankali ta ce

"Saƙo ya zo Goggo kawai dai ban samu lokaci bane ina aiki" Goggo ta mata kallon tsaf ta ga rigar bacci ce a jikin ta, babu alamar ma jikin ta ya ga wanka, ga gashin ta nan babu kitso gata kuma mace mai gasho baƙi sannan yana da tsawo sosai sai dai bata son kitso ko kuma ta je wajen wankin kai a tsaftace mata.

Goggo a zuciyarta ta ce.

'Ni damuwata ma da Naja rashin ibada ko kaɗan bata damu da ibada ba, to ibada ma ai sai da tsaftar jiki' A fili ta ce

"Gaskiya ne aiki ne ya hana ki zuwa yanzu ma na same ki kina cikin yinsa" ,Ɗagowa ta yi ta xubawa Goggo idanu rai a ɓace domin ta lura Goggo magana ta faɗa mata hakan ya da ta ce

"Aiki kuma?" ,

Goggo ta ce

",Aiki mana latsa waya ke ai shi ne aikin ki, ko kina da wani abu bayan wannan?" Ido ɗaya ta ƙanƙance ta ce

"Goggo shi ne daman kiran da kika min? Sannan shi ne dalilin da ya sa kika tako har ɓangarena"

Goggo ta yi banza da ita tana jin takaicin kasancewarta matar tilon ɗanta.

Gyaran murya ta yi ta ce

"Naja na zo ne mu yi magana ta fahimta ni da ke, ina so ki ajiye wannan wayar, ki bani aron hankali da lokacinki" Baki ta taɓe irin na marar mafaɗi ta ce

"Kina iya faɗar abin da kika zo da shi, Allah bani ikon saurara ko da ba zan yi aiki da shi ba, kin san an ce ji ba ɗauka bane"

Goggo cike da mamaki ta ce

"Au haka kika ce"

Ta ajiye wayar tana faɗin

"Allah bani iko, kin san komai sai Allah ya bak ikon yi"

Goggo ta ce

"Dama maganar dai da kika sani ce ta kawo ni"

Hajiya ta ce

"Wace magana kuma?"

Goggo ta ci gaba da cewa

"Magana dai a kan haihuwa kin...

"Dakata! Goggo, wannan magana ce da kowa ya san amsar ta, ko in ce kin san amsar ta, sannan na daɗe da faɗawa shi wanda shi ne mai alhaki da wannan maganar wato wanda ya ajiye ni kenan, ni ban ga abin da zai sa a dameni a kan magana ɗaya ba, ko bango ne ake damu watarana rushewwa zai yi dan Allah a sama mini lafiya a barni na sarara na sakata na wala a gidan mijina, wallahi da kun san yadda na tsani damu da ba za kuke damuna ba, ni fa na fi son kowa ya yi harkar gabansa"

Maganarta ta yi wa Goggo zafi amma sai ta ce .."Naja ya kamata ki dawo daga rakiyer shaiɗan ko zuciya, inaso ki sani shi lokaci ƙarewa yake, rayuwa kuma ba a tsaye take ba tafiya take, a kowane lokaci mutum mutuwa tana iya riskarsa shi ya sa ake so kowane lokaci ka zama cikin shirin tafiya..."

Hajiya ta tari numfashin Goggo da faɗin

"Goggo ce miki aka yi bana sallah da za ki ce bana yin shiri"

Goggo ta ce

"Naja ba wai haka nake nufi ba shi shiri ai ya haɗa da komai, kamata ya yi a ce kin bar ƴaƴan da za suke miki addu,a a bayan ranki, a lokacin da su kaɗai ne za suke tunawa da ke, sannan kina can cikin kabarin da a lokacin addu,ar kawai kika fi buƙata, sannan ki sani rayuwar mace taƙaitacciya ce sannna girma yana kama mace ƙarfin jikinta yana raguwa, rauni yana baibaye ta, ɗaukan ciki da yunƙurin naƙuda zai yi mata wahala saboda halin girma, ta yaya za kike tunanin ke ƴaƴa biyu kaɗai za ki haifa a rayuwarki? Kuma ki ce idan kika haifi ɗa ɗaya ba za ki sake haihuwar ɗayan ba sai bayan shekara goma? Yanzu kin samu ciki kin haihu ɗan ya rasu kenan kinmce sai bayan shekara goma za ki sake haihuwa? Shin idan ma kwanakin ki sun kai shekara gomar ki haɗa shekara goma da shekarun ki na yanzu ki ga lokacin shekaru nawa kike da su?" Goggo duk wannan bayanin da take Hajiya Naja,atu ta yi shiru tana saurarenta hakan ya sa Goggo ta bada ƙaimi wajen bayani da jan hankalinta don ganin ta watsar da mummunar ƙudurinta ta ajiye makamanta.

Sai dai sai da Goggon ta yi shiru tana jiran jin Hajiya ta amsa mata da magana mai daɗaɗawa amma sai ta ji ta ɗan yj wata ƴar dariya kafin ta ce

"Wallahi har kin bani ƴar bazawarar dariya, wannan dai kin jifan tsuntsu biyu ne da ditae ɗaya in ba haka ba ta yaya za ki zo kina faɗa min abin da kike ganin gatan ɗanki ne, amma kina nuna min kamar dai ni kike yi wa gata? Gaskiya ɗaya zan faɗa miki Goggo wannan ra,ayina ne ƙudurina ne kuma babu ranar da zan canja shi, kuma ba u mahluƙin da zai kawo min wargi a kan maganar nan"

Goggo ta ce

"Wato duk bayanin nan nawa ta kunnen hagun ɗinki ya shiga ya fita ta kunnen dama kenan? Kiina nunawa har yanzu kina kan bakanki"

Bata ba Goggo amsa ba, ta ɗauki wayarta. Goggo ta ce

"Zan ɗauki mataki " Kallin Goggo ta yi ra watsar saboda ta san dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato faɗawa mijinta ta san kuwa zai yi wahala ya iya mata wani hukunci saboda son da yake mata duk da ta san shi mai biyayya sannan ba ya gaɗa mahaifiyarsa da kowa kasancewar ita kaɗai yake da ita.

Goggo tana faɗar haka ta tashi ta fita saboda bata ga amfanin yin tufka ana yinw arwara ba. Goggo da ta fita haushi ya sa ma bata rufo ƙofar ba, Hajiya tana ganin hakan ta tashi da sauri tana zuwa ta tura ƙofar da ƙarfi har sai da ta yi ƙara, Goggo ta ji ƙaran bugowar kuma ta san saboda ita ta yi don raini, kawai tana dai ɗagawa Hajiya Naja'atu ƙafa ne saboda irin son da ɗanta yake yj mata.

Bayan ya dawo daga office ya dawo a gajiye kasancewar ya yi ayyuka sosaia a iffice ɗin. Bayan ya yi wanka ya zauna a huta, ko ƙeyar Hajiya bai gani ba, zuwa can ya kira ta sau biyu amma bata ɗauka ba. Da magriba ya je ya yi sallah a masallaci, sai da aka yi isha,i ya dawo, dining ya nufa ya tarar Mero ta girka tuwon shinkafa da miyar karkashi, ga man shanu har da yajin daddawa, ga kuma kunun gyaɗa. Sosai ya ji daɗin hakan, yana gama ci ya zuba kunun ya sha, hamdala ya yi kafin ya tashi sai ya nufi ɓangaren Goggo.

Ko da ya je ya same ta tana kallon sunna tv, bayan ta masa barka da dawowa ya mata barka da gida suka shiga taɓa hira, a nan ne ma yake bata labarin abincin da Mero ta girka, nan take faɗa masa cewar ita ta ce a masa saboda ta san yana so, kuma ta lura da safen kamar bai ci abincin kirki ba, sannn ta san ba gwanin cin abinci ne a office ba sai dai in kamawa ta yi.

Bayan shiru ya gifta ya hurar da iska daga bakinsa ya ce

"Goggo kun yi magana da Naja'atu?" Goggo wani tausayinsa ne ya kamata, hakan ya sa ta ɓoye damuwa daga saman fuskarta, ta ce

"Eh mun yi magana, ai nan na sanya aka kira ta muka tattauna" Ta samu kanta da ɓoye masa cewar Hajiyar bata zo ba, don kar ya ji babu daɗi a ransa, bata so ya san ita ce ta je ɓangaren ta.

Cike da zaƙuwa yana fatan an dace ya ce

"Goggo ta amince?" Ya faɗa yana ɗagowa daga jinginar da ya yi a jikin kujera ya zubawa Goggo ido tamkar mai karanto karatun hadda.

Goggo kai ta girgiza alamar a,a sai kuma ta ga jikinsa ya yi sanyi, amma babu dalilin da zai sa ta ƙi faɗa masa gaskiya domin ta ƙosa su samu mafita, idan kuma tana biyewa cewar ba za take faɗa masa za take ɓoye masa abu saboda kar ya ji haushi ko ya shiga damuwa tabbas za a tafi a haka ne.

Gyaran murya ta yi ta ce

"Wannn matar taka ta yj nisa ba za ta ji kira ba, don haka ka dawo daga rakiyarta, ka san dai kai kaɗai ne ɗan da Allah ya bani a duniya, hakan ya sa nake son ka hayayyafa, in samu jikoki bila adadin ta tsatsonka, sannan kaima ƴaƴanka ne za su zama abokan shawararka, tun da baka da ɗan uwa na shawara duk da na maye maka wannan gurbin amma yana da kyau a ce ka haifi ɗa domin saboda wataran rayuwa banu tabbas"

Cikin sanyin murya ya amsa mata da faɗin

"Haka ne Goggo"

Goggo ta ce

"Ni ba zan tilasta matarka ta haihu ba, amma ina so ka sani dole zan ɗauki mataki kamar yadda na faɗa mata, matakin kuwa ba komai bane illa iyaka inaso ka auri wata matar" Ɗan zabura ya yi saboda kiɗima kafin ya zaro idanu bakinsa yana karkarwa ya ce

"Aure kuma Goggo? Ya tambaya a zuciyarsa kuma yana taraddadin kalmar da matar nan mai kiranshi da baƙuwar lamba wacce ta kira shi yana office kalmar da ta furta masa ita ce ta sanya shi saurin ƙara kallon Goggo domin jin maganar Goggo tana kamanceceniya da ta mai kiransa a wayar inda ta ce masa

"Ni ba komai nake buƙata ba illa iyaka ka aure ni, burina ya cika idan ka aureni kuma ina maraba da shigowa gidanka" Daga wannan kalaman da ta furta ya katse wayar tare da yin blocking ɗin lambar domin shi a rayuwa ya tsani kalmar kishiya da kalmar ƙarin aure tamkar dai shi mace ne ba namiji ba. Tun da kowa ya san mace ake yi wa kishiya ba namiji ba.

Maganar Goggo ce ta katse masa tunanin in da ta ce

"Aure mana wanda hakan umartarka nake ba shawara ba!.

*ABDULSALAM*

Shi ne farkon tashi daga wajen cin abincin, daman kawai yana cakala ne, yana miƙewa Ramla ta ce

"Abban Humaira ya na ga ka tashi, baka ci da kirki ba" Buɗar bakinsa ya ce

"Haba Ramla yanzu ni kike so in shiga ƙwaƙwalwarki in kissima miki yin abin da ya dace? Shin baki san a yau ne na yi babban rashin ɗan uwa kuma aminina Zahraddin ba, amma maimakon ki taushini kin je har ɗaki kin kirani in zo in ci abinci, ba tare da la,akari da cewar shin zan iya cin abincin ko akasin haka"Gabaɗaya yaran sai suka sunkuyar da kai, duk da wannan ba sabon abu bane wato mahaifinsu ya yi wa mahaifiyrsu faɗa gaɗe da cin kashi a gabansu, ko kaɗan ba ya daraja ta, ba ya kimantata idanuwan yaransa ba ya sanya ya fasa duk wani abu da ya yi niyya, wannan abu da ya faɗa cikin isa, gadara , sannan kuma cikin tsawa tamkar dai ta masa wani gagarumin laifi.

Aslam ne ya ce

"Abba... Tsawa ya daka masa ya ce

"Rufe min baki ko na baka damar magana ne, to babu wanda na ba damar magana uwarku kawai nake faɗawa domin ta yi abin da ya dace!" Yana faɗar hakan ya janye kujerarsa da ya zauna ya bar dining ɗin.

Humaira ce ta ajiye nata cokalin ta miƙa hannu ta dafo kafaɗar ta, ta ce .. "Mama ki yi haƙuri don Allah" Ita gabaɗaya ma kunyar yaran take ji, in ban da ma yaranta tana basu tarbiya da tuni wani batun ake ba wannan ba, saboda shi yaro yana la,akari ne da abin da ake yi a aikace ba wai abin da baki yake furtawa koyaushe ba.

Aslamiya ce ta ce.

"Ni wallahi bana son faɗa, shi kuma Abba ya fiye faɗ... Mama ce ta dakatar da ita a tsawace, daman ta yi shiru ne tana yaƙi da ƙwallar da take kokarin zubo mata.

Ta ce.

"Kul na sake jin makamanciyar maganar nan daga bakin ki, shin kina son shiga wuta?" Kai Aslamiyya ta girgiza da sauri.

Mama ta ce

"To idan kina son shiga aljanna ki girmama iyaye, mahaifi ba abin wasa bane, sannan girmansa ne ya yi faɗa a koyaushe kuma a lokacin da ya ga dama saboda ni ai a ƙarƙashin sa nake, kin ga kuwa ai idan na yi ba daidai ba dole ya nuna min kuskurena na gyara ko?" Kai ta gyaɗa, Aslam ya karɓe maganar da faɗin

"Mama amma ai mutum sai ya yi laifi babba ake masa faɗa wannan ai ba laifi bane ko?

Mama ta ce

"Laifi ne mana, ai nima ban kyauta ba ai rashi aka masa babban amininsa ai kun san dai bashi da kamarsa ko?"

Aslamiyya ta ce

"Mama wannan ai lokacin muna tsohon gida ne, wannan gidan hayar shi ne fa koyaushe da Abba da Abbie suke tare amma da muka dawo sabon gida Abbie sai ya daɗe ma bai zo gidan nan ba, shi ma Abban na san ba zuwa yake b... Mama ta tari numfashin ta da faɗin

"Ai ba a canjawa tuwo suna, abin da ya sa kuke ganin haka saboda lokacin muna tsohon gidan Abbanku bashi da ayyula sosai, da muka dawo sabon gida kuma ai kun ga lokacin ya samu aiki shi ya sa haɗuwar takr musu wuya" Tana ɗan jansu da hira suna cin abincin ita dai bata ƙara ko da cokali ɗaya ba saboda ji ta yi komai ya fice mata a rai.

Ko da suka tambaya mai ya sa bata ci sai ta ce ai ita ma tana taya Abbansu jimami ne.

Sai da suka kammala, suka koma falo, Talatuwa ta zo ta kwashe kwanukan bayan ta ƙara yi wa Mama gaisuwa ta fita. Suna ta hira, Aslam da Aslamiyya kuma school back suka ɗakko home work suka yi. Kowa ya yj mata sallama ya tafi tana nannaga musu cewar kowa ya yi alwala sannan a yi addu,a sai a kwanta. Ta ɗan jima zaune a wajen, kafin ta tashi ta nufi ɗakinsa.

A ɓangaren Abba kuwa yana barin wajen ya koma ɗakinsa, yana zuwa ya hau gadonya janyo wayarsa, saboda gabaɗaya hankalinsa yana ga kiran wannan lambar da yake ta taraddadin kira. Ko da ya kamo lambar wacce babu suna sai wani alama na emoji. Gabansa yana faɗuwa amma haka ya daure, sai da ta kusa shiga ya katse, kusan sau biyar yana katsewa har da ya daure ya bar kiran ya shiga, wayar tana ringing ne haɗe da bugun zuciyarsa, sai dai kash har kiran ya katse ba a ɗauka ba, ajiyar zuciya ya sauke tamkar wanda daman ba wai so yake a ɗauki wayar ba. Yana shirin sake kira a karo na biyu sai kawai ya ji Mama tana ƙwanƙwasa, shiru ya yi sai da ta yi sau biyu kafin ya ce ta shigi tamkar wanda ya saka ƙwallon goruba a bakinsa, kana jin yanayin yadda ya yi magana ka san tamkar an masa dole, ko kuma wanda ya haɗiyi maɗaci. Yana katse kiran ya yi sauri ajiye wayar ya haɗe rai.

Sallama ta yi ya amsa a ciki-ciki ta zo rufe ƙofar ta ƙaraso ta zauna a kusa da shi ta ce

"Barka da hutawa"

Ya ce

"Ba hutawa nake ba"

Da sauri ta ɗaga ido ra kalle shi ta ce

",Mai kake?"

Ya ce

"Jimamin mutuwa"

Ta ce

Allah sarki, Allah masa rahma"

Baki ya buɗe zai amsa ƙaran wayarsa ne ya hana shi amsa mata, idanunsu ne suka kai kan wayar a tare, ita bata kawo komai ba, shi kuma wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce shi, ganin lambar gabaɗaya wani gumi ne ya tsatstsafo masa ba tare da ya shiryawa hakan ba.

A can ɓangaren lokacin da Abba yake kiran wayar nan, Hasiya tana kwance tana tunanin makomar rayuwarsu ita da ƴaƴanta, tun da ta san mahaifiyarta ma ba wani ƙarfi ne da ita ba.

Tana kwance tana jin mahaifiyarta da tana ɗan munsharin baccin da ya yi awon gaba da ita, ƙaran wayar ta ne ya katse mata tunani, idanu ta runtse tana tuno yadda idan ta duba wayarta kafin ta ga kiran kowa ta ga kiran mijinta yau kuma mutuwa ta ɗauke shi, hakan ne ya sa bata ma iya ɗakko wayar ba bare har ta amsa kiran.

Har kiran yana shirin katsewa, mahaifiyarta wacce kiran ya falkar da ita ta ce

"Hasiya, kina ji wayarki tana ƙara, da daren nan ma waye zai kira, Allah sa dai ba wata mutuwar ce aka yi ba, wannan mace-mace da ya zama yanzu za ka ga mutum an jima ya zama gawa" Ta faɗa tana tashi zaune daga ɗan ringisawar da ta yi har bacci ya ɗauke ta.

Jin wannan kalaman ya sa ta yi ƙarfin halin janyo wayar, tana dubawa ta ga baƙuwar lamba, hakan ya sa ta bi kiran duk da kudin naira ashirim da biyar ne ta san a ciki. Ta kira har ta katse ba a ɗaga ba.

A ɓangaren Abba kuwa, yana ji yana ganin kiran har ya katse sai kawai ya yi tsaki yana faɗin

"Mutane gaisuwar ce ba za a kira ka tun lokacin mutuwar a jajanta maka ba sai yanzu da dare ya yj za a ishe ka da kiran waya" Ita dai bata masa magana ba.

A ɓangaren Hasiya kuea jin ba a ɗaga ba ta ajiye wayar, ai kuwa mahaifiyarta ta ɗauka ta shiga kiran lambar. Abba babu zato da tsammanj ya ga kiran ya shigo, ya so a ce shi kaɗai ne a ɗakin da ya lallashe ta, duk da yana tsoro da kuma tunanin ta inda zai fara.

Mahaifiyar Hasiya ta dage tana ta kira. Abba dai ya kasa ɗagawa har sai da Mama ta ce ya ɗaga mana sai kawai ya kashe wayar gabaɗaya yana ta bambamin cewar an dame shi da kiran banza da wofi ya kashe wayar ya ajiye.

Mahaifiyar Hasiya kuwa jin da ta sake kira an ce a kashe sai ta fara faɗa tana cewa wataƙila daman ƴan damfara ne.

Mama kuwa bata ce masa komai ba, ta ɗan furzar da numfashi ta ce

"Abban Humaira ina son magana da kai"

Bai bata amsa ba, daman ta yi zaton hakan ta ci gaba da faɗin

"Daman inason yin tsokaci ko na ce jan hankali, da kuma shawara, duk da ba wannan ne karo na farko ba, sai dai ba zan gaji da faɗa maka ba har sai ranar da na ga maganar ta yi tasiri ma,ana ka yarda da ita ko ka yi aiki da ita, idan na gane ka yi na,am to zan daina faɗa maka"

Idanu ya zura mata yana mata kallo mai kamar harara ta ce

"Ba zan ɓoye maka ba, har ga Allah ko kaɗan ba na jin daɗin abin da kake mini, tun kan mu fara haihuwa nake faɗa maka ka koyi yin abin da ya dace, ko ba don ni ba ko don ƴaƴanka da goben ƴaƴanka, amma baka ji shawara ta ba har muka haihu, tun yaran nan basu da wayo gashi yanzu har sun yi wayo amma bata sauya zani ba, yanzu Haumaira shekara goma sha biyu, Aslam da Aslamiyya shekara goma, amma kullum kana abu kamar wani ƙaramin yaro" Hannunsa ya kai haɓa ya riƙe haɓarsa ya kifa tagumi yana kallonta.

Ta ci gaba da cewa

"Idan har kana wulaƙantani a gaban ƴaƴana, kana muzantani, baka bami daraja ta yaya kake so su su baka daraja, bayan bamu daraja kanmu ba? Idan kana min abubuwan nan za suke ganin kamar ƙwarata kake sannan kamar Aslam idan ya koyi ɗabi,ar nan zai je gidansa yana yi wa matarsa, saɓanin idan ya ga kana bani daraja kana girmamani, ka san muhimmancina to shima zai tashi da sanin muhimmancin tashi matar, ban ce kar ka min faɗa ba amma kake min a bayan idonsu, idan har ya zaɓa dole ka min a gabansu to ka san irin kalaman da za kake amfani da su, karka manta tarbiyar ƴaƴanmu nake karewa"

Cike da kosawa ya ce

"Kin gama? Na ce kin gama, sarkin ƴan wa,azi to ni yanzu ta mutuwar abokina nake faɗa kuma dole a miki shi in dai kika yi laifi" Yana faɗar hakan ya kwanta a gadon tare da maido wayarsa kusa da shi.

Baya ya juya mata, tana jin zuciyarta tana zafi amma haka ta hau gadon ta kwanta, ita ba don ma kar yaran su lura tana kwana a ɗakinta ba bayan sun san tun da suka taso a ɗakin mahaifinsu take kwana, ita kuma duk abin da zai kawo rarrabuwar kai ko su gane akwai ɓaraka a tsakaninta da mahaifinsu to bata ƙaunar a samu hakan, amma ya za a yi namiji yake mayar da kai famko da kai da babu a wajensa kenan duk uwar ubansu ɗaya?.

Da sassafe ya shirya ya tafi gidan makokin, bayan sun tsaya shi da direba sun yi siyayyar da za su kai gidan makokin, sun samu akwai jama,a a ƙofar gidan makokin. Daman ya faɗa mata ita ta taho daga baya idan ta shirya, shi kuma hankalinsa ne ya yi wajen Hasiya yana so ya je ya ga yadda ta tashi.

Mama kuwa ganin hakan sai kawai ta bari da yamma ta je ita da yaran tun da juma,a a ce babu islamiya.

Abba tun daga ranar nan bai sake kiran lambar Hasiya ba, kuma ba a sake kiransa ba.

Yau kwana huɗu kenan da mutuwar Zahraddin, misalin ƙarfe shida na safe, mai gidan ya rangaɗa musu sallama, daman ya zo tun lokacin mamacin bashi da lafiya ya faɗa masa ya basu kwana uku su tashi tun da ya ɗaga masa ƙafa wajen sati uku amma ziryar asibiti bai bari ma sun sake tunawa da maganar ba, bare ma da rai ya yi halinsa. Bayan ya sake musu gaisuwa don daman ya zo sutura ya ce su fita daga gidan a yau ba sai gobe ba tun da dai an yi uku an daina zaman makolin domin daman sadakar uku da ta bakwai aka haɗa.

Mazan ma duk sun tashi sai mutanr da suke shiga jefi-jefi su jajanta, daman hakan duniyar take zancen banza ce, daga ka mutu shikenan kai kana can a kabari kana karɓar abubuwan da ka shuka, mai kyau ko akasin haka, a nan kuwa haka, a duniyar kuma mutanr suna can suna ci gaba da yin hulɗarsu don mutuwarka babu abin da za a fasa.

Kayan suka tattara daman ba wasu kayan kirki bane, suka fito suna share hawaye. Adaidaita sahu suka hau guda biyu suka nufi gidan Inna wanda wajen kwama ma zai musu wuya a gidan.

Suna fita mai gidan ya saka ƙaton mukulli ya datse gidan ya yi tafiyarsa saboda wasu mutanen za saka a ciki.

A ɓangaren Abba, yau ya leƙa office ya cike wasu takardu, hakan ne ya sa bai je gidan makokin da safen ba, musamman da ya san ma an yi sadakar uku da bakwai kawai dai a zahiri yana so ya leƙa iyalin mamacin saboda amininsa ne, a baɗini kuwa yana kai musu ziyarar ne don ya ga Hasiya wacce yake saka ran nan ba da wani lokaci ba idan ta yi idda ya yi wufff da ita.

Daga office ɗin ko gida bai je ba ya wuce gidan makokin, bai lura gidan a rufe yake ba sai da ya fito daga motar bayan direban ya buɗe masa, kafin ma ya gani ya tsinkayi muryar direban yana faɗin

"Alhaji gidan ai a rufe da mukulli"

***

[7/15, 5:17 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH

Daga marubuciyar

Ruwa cikin cokali Uwar agola Malamin bogi ƙazamin miji Yar zaman wanka Ruɓaɓɓiyar igiya Ƙara,in inna delu Bonono Ci ma zaune Ƴan adaidaira sahu Jalli joga Ungozoma Ƴar ƙanwata, Beelal Da sauransu. ***