KIBIYA A IDO

4

by @mamanafrah3028

*NURIYYA*

Ko da ta fita jikinta har lokacin karkarwar yake, musamman da ta ji ƙaran da Hajiya ta saki wannan ya ƙara saka ta a ɗimuwa. Don haka halin da take ciki ma bai bari ta ji ƙaran buɗewar get ɗin gidan ba.

Tana rakuɓe jikin bango sai ganin shigowar mahaifin nata ya yi, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, ɗakin Hajiya ya nufa hankali a tashe yana shiga ya ganta yashe a wajen tana riƙe da ƙugu cike da nuna damuwa da kulawa ya shiga faɗin

"Hajiya lafiya mai ya same ki"

Hajiya cike da langaɓewa ta ce

"Alhaji ban san mai na tarewa yarinyar nan Nuriyya ba, na.ɗauke ta tamkar ni na haife ta amma ni tana neman nakastani, da gangan ta ɗakko ruwa ta zo ta zubar a falon nan na taka na zame, yarinya ƙarama amma ta san mugunta" Ta faɗa tana ɗan sakin hawayen ƙarya haɗe da gogewa da bayan hannunta. Ransa ne ya ji ya ɓaci, shi idan ana sin ganin ɓacin ransa to a ɓatawa Hajiya rai.

A fusace ya ce

"Wannan yarinya ni dai ba wurina ta gado wannan mugun halin ba, sai dai can wajen uwarta ko dangin uwar tata" Ya faɗa yana nufowa waje da sauri, yana zuwa inda Nuriyya take ya hau ta da faɗa gabaɗaya bai lura da halin da take ciki ba, na farko kana ganinta ka san yunwa take ji, sannan ga sanyin da ake yi duk da tana da ɗaki a gidan amma Hajiya ta hana ta shiga ta ce ba yanzu za ta shiga ba, ga kuma fitsarin da ya suɓuce mata da ta ji azaba wajen Hajiyar.

Kamar zai fasa mata kunne saboda karaɗin faɗan da yakr mata, gabaɗaya ma ita a firgice take duk ta tsorata, hannuwanta ta haɗe wuri guda tana kuka taba bashi haƙuri, maganar da takr ji yake tsanaarta tana linkuwa a zuciyarsa hakan ya sa ya ɗaga hannu zai wanka mata mari, sai dai da ya kalli fuskarta sai ya ji gabaɗaya wani yanayi ya ziyarce shi wanda a zahiri ba zai iya fasalta mene ne ba amma a baɗini yana ji tamkar dai zuciyarsa tana son ta tausaya mata ne amma sai ya ji idan tausayin ya yunƙuro tamkar wani abu ne yake tokare shi, a take yake neman tausayin ya rasa, haka nan idan ya ji sonta zai bijiro masa sai ya ji tamkar an saka dutse an danne masa saitin zuciyarsa.

Abu ɗaya kawai ya sani kuma yake iya tunawa dangane da ita shi ne, ita ƴarsa ce kuma mahaifiyarta ta mutu, iya wannan ne kawai, amma daga wannan ba ya gane komai sai dai umarnin zuciyarsa. Hannun da ya ɗaga zai mare ta ne ya ɗauki wata irin karkarwa, haɗe da ɗaukan wani irin ɗumi tamkar mai zazzaɓi amma iya hannun hakan ya sa ya fasa kai mata marib ya janye hannun ya mayar bayansa yana aika mata mugun kallo.

Cikin faɗan yake cewa

"Ke wace irin yarinya ce a iya ƴan shekarun da kike da su a duniya har kin san ki cuci wani, wannan matar da take rufa miki asiri ta maye miki gurbin uwa ita ce wacce kike son ta shiga yanayi marar daɗi?" Kai kawai take girgizawa ita ko kaɗan ma ba fahimtar mai yake faɗa take yi ba, abu ɗaya ta sani shi ne laifi ta yi kuma bata san wane laifi bane, da son samu ne a bata abinci ta ci in ya so sai a mata faɗan don yunwa take ji.

Sai da ya gama masifar ya juya ya barta a wajen, tana ta kuka da sheshsheka. Ya koma ya ɗaga Hajiyar yana faman mata sannu dakyar ya taimaka mata ta hau kujera.

Ƙugu ta riƙe tana daga zaunen ta yamutsa fuska tana faɗin "Allah sa shegiyar yarinyar nan bata min sanadiyyar karaya a ƙugu ba, yarinya kamar yar aljana haba" Alhaji ya ce

"To ko mai gyara za a kira ya duba ki?" Ta karkata kai ta ce..

"Na yi ruwan zafi kawai" ,Ajiyar zuciya ya sauke ta tsura masa ganin kamar yanayinsa ya nuna alamar damuwa ta ce

"Ni Alhaji ban ji ƙaran dukan da ka mata ba"

Yana ɗan diriricewa ya ce

"Kin san ban san dalili ba in dai zan kai mata hannu hannuna karkarwa yake" A fili ta ce

"Makirar wataƙila addu,a take maka kar ka duke ta"

A zuciyarta ta ce

'Wannan mugun son da kake mata ne da na fi ƙarfinka a kansa yake ɗawainiya da kai dai, shi ya sa baka iya mata dukan ' Ta faɗa tana tunanin wata hanyar da za ta bi na sake farraƙa tsakanin ku don ka ƙara tsanarta har dukan ma kake mata na mutuwa'

Nuriyya bayan shigewar Alhaji ɗaki ta daɗe a wajen a tsaye har ta zauna ganin ta, ganin duhun magriba ya yi ta tashi ta je wajen famfo ta wanke jikinta har cinyoyinta, ta zo tana rawar sanyi, ta leƙa falon Hajiya ta windon ganin babu kowa a falon sai ƙaran TV da gudu ta koma ta tafi ɗakinta cikin sauri ta ɗakko wata rigar atamfa wacce duk ta yage, da gudu ta saje fitowa ta tafi can lungin kicin ta cire kayan jikinta ta saka rigar, bayan ta saka ta waiwaya bayanta ta duba wurin yagar wanda yake saitin mazaunanta. Amma ganin duk yawanci kayan a haka suke babu na kirki ta haƙura ta ɗakko wanda ta cire ta tafi can bayan gidan inda ɓangaren yan aikin yake ta shanya a igiya ta baro wajen.

Lokacin da ta dawo ta ga wulgawar mahaifinta, ya shige part ɗinsa, da sauri ta tafi wajen Baba mai gadi tana zuwa ta ga baya wajen, ta duba ɗakinsa ma baya nan, sannan kwanon abincinsa ma baya nan.

A ɗakin ta zauna ta kifa kai da gwiwa tana nan zaune ta ji shigowarsa ɗakin, cike da sanyin murya ya kira sunanta da faɗin

"Nuriyyan Daddyn ta"

Idanunta taf da hawaye ta ce

"Ba Nuriyyan Daddy ba ce"

Yana kama hannunta ya ce..

"Ta waye?"

Ta yi shiru sai ta ce.

"Ni ba ta kowa ba ce, ni kai ne kake taimaka min daga kai sai Yaya Ammar Daddy kuwa faɗa yake min kuma ba ya kula ni" Shiru ya yi ya ɗago ta ya dafa kanta ya ce.

"Nuriyya na faɗa miki kaf duniya babu wanda ya fi Daddnki son ki, yana son ki, wasu abubuwa ne suka sauya, saboda wasu dalilai da yarinta ba za ta bari ki gane inda akalar maganar ta dosa ba, amma dai ina da yaƙinin watarana gaskiya za ta yi halinta, Allah zai bayayana komai" Gabaɗaya bata gane kalaman ba, ta san dai kawai ya faɗa mata Daddyn yana sonta wanda ita kuma ta san ba haka bane kawai dai yana faɗa mata hakan ne a duk lokacin da ta zo masa da makamanciyar maganar.

Baba mai gadi ya ce

"Yanzu mai ya fito da ke?" Tana raurau da ido ta ce

"Yunwa nake ji, kuma ina jin sanyj Hajiya ta ce sai zan kwanta zan shiga ɗakin" ,Ya yi shiru yana tausayawa ƙaramar yarinyar kamar Nuriyya amma ta san wahalhalu da tarin tsangwama. Ji ya yi ya ƙara tausaya mata ko don irin zaman mutunci da mutuntawa da suka yi da mahaifiyarta mace mai karamci da sanin kima da darajar ɗan adam kowa nata ne talaka da mai kuɗi amma yanzu gashi ƴarta ɗaya tilo tana a hali da gararin rayuwa.

Yana mayar da ita ya zaunar da ita a kan sallaya ya ce

"Bari na fita na siyo miki awara a can inda ake siyarwa, zauna a nan kar ki fita wajen sanyi, nima Hajiya ta bani horon rashin bani abinci na tsawon sati guda saboda na baki abinci jiya an je an faɗa mata" Nuriyya bata yi magana ba ta bishi da kallo don yunwar da take ji maganar ma ƙarfin hali take.

Yana shirin fita ya jiyo muryar almairin gidan yana cewa Alhaji ya ce ya je yana kiransa. Da sauri ya yi hanyar cikin gidan cikin bin umarni.

Tun da Baba mai gadi ya tafi take ta jiransa amma ta ga bai dawo ba.

Can bayan wani lokaci sai gashi ya fito, da sauri ya fita ya siyo mata awarar da kunun tsamiya aka ɗaura masa a fara leda, yana shigowa ya kai mata, ta ci ta sha kunun ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

Baba mai gadi na gode!" Murmushi ya yi yana kallon ta da tausayawa kasancewar ga ta wacce ta fi ƙarfin abun amma abin ya fi ƙarfin ta, gidansu sai dai su ba wasu abinci amma ƴar mai gidan tilo cin abincin gidan ya gagare ta.

*BAYAN SHEKARA BIYU*

Yau ma kamar kullum har aka kira isha,i tana zaman jiran ta inda za ta samu abinci, domin har yau rayuwar bata sauya zani ba, yanzu da take da shekara takwas.

Hanya ta sata ta taho wajen Baba mai gadi amma kamar jiya da shekaran jiya ba ya nan, daman ta ji ana batun bashi da lafiya ya tafi ma garinsu neman maganin ciwon ƙafa, ranar da ya tafi ma tana makaranta.

Mai gadin da aka kawo ya maye gurbinsa ko kallo bata ishe shi ba. Tun da an bashi labarin idan ana taimaka mata, matar gidan har sanyawa take a daina ba mutum abinci hakan ya sa babu abin da ya haɗa shi da ita.

Lallaɓawa ta yi ta leƙo daga bayan ɗaya daga cikin motocin da ta ɓuya a bayanta ganin babu kowa a harabar wajen, sabon mai gadin ma yana banɗaki lokacin, fitowa ta yi ta sulale ta buɗe get ɗin ta fita daga gidan.

Tun da ta fito take haɗa hanya, kanta babu hula, ta kama hanya tana yi tana waiwayen bayanta, ga tsoro da take ji amma yunwar ta danne komai. Tana shawo kwanar gidan take fatan Allah sa yana nan domin shi kaɗai ne zai iya bata taimako a halin da ake ciki yanzu. Tana zuwa daidai wani gidan ƙasa da ya gaji da tsufa, kai ta kutsa cikin zauren ta sai sai kash tamkar ta kurma ihu haka ta ji domin kuwa ɗakin a kulle yake da mukulli.

A ƙofar ɗakin ta zauna ta miƙe ƙafarta. Ammar ɗan kimamin shekara goma sha uku, ya shigo zauren gidan ɗauke da kwalin da yake tallar biredi. Ganinta a zaune kamar ma gyangyaɗi take da sauri ya ƙarasa yana ajiye kwalin, ya ya riƙe hannuwanta yana faɗin

"Nury" Sunan da yake kiranta da shi, tun daga ranar fa ta faɗa masa sunanta ba ya iya ƙarasawa ya ce Nuriyya sai dai ya ce Nury, hatta kakarsa ma ya sanya da Nury ɗin take kiranta. Jin muryarsa ta buɗe idanunta da sauri tamkar zakin da yake jin yunwa ya ga nama haka ta yi, saboda ta san in dai ta ga Ammar to tabbas ta ga abinci.

Shekararsa sha uku amma idan ka ganshi za ka yi zaton ya kai shekara sha biyar ko sha shida, gashi da neman na kai kullum cikin wahala yake, ya wuni yana neman abin da za su rufawa kansu asiri shi da kakarsa ɗaya tilo. Su kaɗai ne gatan kansu kamar yadda ya taso tun yana ƙarami ya gani.

Cike da muryarta da ta fara ɗan bacci da kuma raunin yunwar da ta cinye ta ta ce

"Ya Ammar" Tana faɗar hakan sai hawaye. Lallashin ta ya fara yj yana cewa ta yi shiru a gafe ɗaya yana tambayarta mene ne, gabaɗaya ya shiga damuwa don a duniya mutum biyu ne ba ya son ganinsu cikin damuwa daga Kakarsa sai Nury in dai ya ga ɗayansu a damuwa shi ma yana tsintar kansa cikin damuwa.

Baki ta buɗe ta ce

"Ina jin yunwa, kuma malamin islamiyya ya koro ni yau ya ce kar na sake zuwa sai na kawo kudin makaranta" Ta faɗa tana saka hannu za ta share hawayen ya riƙe hannun ya saka nashi hannun ya share mata.

Cikin lallashi ya ce

"Ki yi haƙuri daman na taho muku da biredin da aka bani ladan tallata ke da Kaka, kin gani har da madara na siyo " Ya faɗa yana ɗago madarar leda yar ɗari biyu guda ɗaya, daga cikin kwalin da ya sako biredin sai kuma shinkafa rabin kwano da wake na ɗari biyu da ya siyo musu.

Ya ci gaba da cewa

"Kuma gobe zan je makaranta na kai kuɗin watan naki, shikenan ai ko?" Ya faɗa suka kyalkyale da dariya a tare. A daidai nan Kaka da take jiyo surutu daga cikin gidan ta taho don ta ji muryar Ammar amma bata jiyo muryar Nuriyya saboda ita a hankali take magana.

Kaka tana zuwa ta gansu suna dariya, su duka ta ji tausayinsu ya kama ta, shi kanshi Ammar ɗin da akwai hali yana buƙatar a tallafa masa bisa ƙananun shekaru da yake da su amma saboda yanayin rayuwa tun yana ƙaramin yaro ya san neman na kansa!.

_ALHAJI MUHAMMAD_

Gabaɗaya gumi ya gama wanke masa jiki, mugun ƙoƙari da ƙarfin hali yake bayan ya aro jarumta ya ratayawa kansa, wajen ganin babu wata alama da yanayinsa ya nuna wanda mahaifiyar tasa za ta fuskanci bai ji daɗin kalamanta ba. Duk da cewar ya san kamar yadda hausawa kan ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, to haka nan duk wata kwana-kwana da zai yi wajen daƙile rashin jin daɗin umarnin da ta bashi dole sai ta fuskanci in da ya dosa amma yana fatan kar ta ga hakan, wani murmushi mai iya laɓɓansa ya ƙaƙalo ya yi yana saka hannu ya goge gumin goshinsa ya ce

"Goggo sanin kanki ne ƙara aure ba ya cikin ra,ayina da mace ɗaya na yi niyyar ƙare iya kwanakin da Allah ya ƙaddara min zan shaƙi numfashi a doron duniya. Amma in har wannan umarnin zai sanya ki farinciki a shirye nake na bi umarmin ki matsawar hakan zai faranta miki, saboda na zaɓi na rayu cikin ƙunci ta kowanne fanni in har dai ke farinciki zai lulluɓe min ke" Ya faɗa yana sadda kansa, ba tare da ya bari idanunsu sun sarƙe da na juna ba!.

Kamar daga sama ya ji muryar Goggo ta ce

"Alhamdulillah, Aɗɗah na gode maka, Allah maka albarka"

Alhaji ya ce

"Amin ya rabby"

Goggo ta ce

"Bana son komai ya ɗauki dogon lokaci, komai a yi shi a gama"

Cikin sanyin murya yana ta tunanin ta yadda zai iya duba tsabar idanun matarsa Hajiya Naja'atu ya faɗa mata zai ƙara aure. Bayan ta sha faɗa mata sau shurin masaƙi cewar ita kaɗai ce matarsa, bata da kishiya a gidan duniya in dai shi ne matsayin mijinta, kuma sanin kansa ne ya sa cewar ta zauna a kan wannan magana irin zaman daram ɗin nan. Sanin ƙudurinsa ya sa ya bararraje ta saki jiki take yadda take so saboda ta san in dai a gidan duniya ne ba ita ba kishiya!.

Yana kallon Goggo ya ce

"Goggo shin wace ce zan aura? Waye zai zaɓa min macen da zan aura tabbas za ta zauna ne bisa zaman umarnin ki Goggo, Naja,atu ce kawai zaɓina"

Goggo ta kalle shi ta ce

"Muhammad kai ba ƙaramin yaro bane sannan kai ba jahili bane ka san hukuncin namiji da zai auri mace viyu ya nuna bambanci a tsakaninsu ko? Zai tashi a ranar ƙiyama ɓarin jikinsa ya shanye, saboda fifita matarsa ɗaya da ya yi"

Ya runtse idanunsa ya buɗe a hankali ya ce

"Ba za ta rasa komai ba na nauyin da Allah ya ɗora min ba, illa iyaka dai "zuciyata" Zuciyata ce kaɗai za ta rasa saboda ina jin zuciyata bayan ku mahaifana duk duniya Naja,atu ce kawai a cikinta, kuma kin san ubangiji ba xai kamani da daidaita soyayyarsu a zuciyata ba domin ba zan iya ba" Ya faɗa yana huro iska daga bakinsa.

Goggo ta ce

",Haka ne amma ni dai ina ji a jikina nan gaba za ka samu macen da zuciyarka za ta sp fiye da Naja, yanzu kana ganin Naja ne a wannan matsayin saboda babu kowa ita kaɗai ce" Da sauri ya ɗago kai ya kalli Goggo fuskarsa cike da mamakin kalamanta. Goggo ta jijjiga masa kai alamar gaskata maganarta.

Kasa magana ya yi don ba halayyarsa ce jayayya da babba ba ko da kuwa na gaba da shi ne, bare kuma mahaifiyarsa. Amma ba don haka ba tabbas da ya mata musu, domin ya san ba wai don matsayin Naja,atu a zuciyarsa ba da tuni ya daina ɗaukan duk wani cin kashi da take masa.

Ya jima zaune tana ta masa nasiha da kuma nuna masa ya mayar da hankali wajen samo macen da za ta kasance ta biyu a rayuwarsa, duk da shi dai yana jinta ne amma ba ya jin zai iya ƙara kallon wata mace da siga biyu wato so da kuma ƙauna. Daga ƙarshe ya mata sallama ya wuce ɓangarensa.

Sosai Goggos ta ji daɗin maganar da suka tattauna a kanta ko ba komai tana dab da ganin jinin ɗanta, wato take ganin yara ƴan dagwai-dagwai a gidan matsayin jikokin ta.

Washe gari da daddare yana ɗakinsa bayan ya kallama duba wani abu a laptop ɗinsa, ya kwanta ya yi nisa cikin tunanin Naja'atunsa kamar daga sama ya ji an yi nocking ƙofar haɗe da turowa lokaci guda. Wani iron tashi zaune ya yi ransa fari ƙal yana jin raguwa da saukar nauyin da zuciyarsa ta masa, tabbas ya yarda Naja'atu ce rayuwarsa amma bai san mai ya sa ko kaɗan ta ƙi bashi haɗin kai su shimfiɗa rayuwa mai inganci da nagarta ba.

Tana wani ɗan yatsina ta ƙaraso ɗakin shi kuma duk ya kasa samarwa kansa nutsuwa saboda farinciki, ya san tun da har ta zo ɗakinsa a daren nan to tabbas zai samu abin da yake so wato biyan buƙata.

Cike da nuna kulawa ya ce

"Sannu da zuwa Naja'atuna, da kin sanar da ni za ki zo da na sakko na goyo ki a bayana na hayo da ke saman saboda kar ki wahala" Zaunawa ta yi tana sakin wani murmushi ta ce

"Sai dai nan gaba yanzu dai aikin gama ya gama" Ta faɗa tana sakin murmushi. Tasowa ya yi yana zuwa kusa da ita ya zauna, kanta ta karkato ta ɗora a kan kafaɗarsa duk da bai shaƙi wani nau,in ƙamshi a jikinta ba amma dai bai ji wani abu mai kama da wari ba.

Hannu ta kai ta shafo fuskarsa wani farinciki ya baibaye masa zuciya ya ce

"Ke kaɗai ce tawa Naja"atuna ba zan taɓa iya haɗa soyayyar ki wata ƴa mace a duniya ba" Murmushi ya yi yana jin daɗin ganinta a turakarsa, yana so a ce ina ma koyaushe cikin ziyartarsa take ko kuma shi idan ya kai mata ziyarar kar take nuna halin ko in kula ya fi so koyaushe take maraba da shi su kasance a dausayin soyayya irin na masoyan da suke jin daɗin rayuwar aurensu.

Ya jima yana jifanta da kalamai masu taushi sai dai da yake ita wannan ba ya cikin tsari da ra,ayinta sai ta ji tamkar busar sarewa yake ko ma dai rera waƙa.

Daga nan komai ya sauya suka haura makwancinsu tare sa lulawa duniyar ma,aurata, bayan komai ya lafa duk da Alhaji Muhammad ya kasance mai ɓoye sirrinsa ga kowa wato sirrin iyalinsa, tun da bayyana irin wannan haramun ne.

Ba don kar ya yi ƙarya ba sai ya ce ba ya fuskantar komai dangane da kusantar Naja'atun tashi, saboda kawai dai yana aikata sunnar ne domin ya kawar da abin da yake ji a matsayinsa na lafiyayyan namiji, amma ba wai don yana gamsuwa ba!.

Sai dai yana so ya faɗa mata cewar ko dai akwai wasu abubuwan gyara da mata suke amfani da su wanda hakan zai ƙarawa aikata sunnar armashi da fahimtar inda aka dosa, amma yana jin shayin faɗa mata, yana tsoron ya sanar da ita ta ce ta daina bashi haƙƙin nashi ma gabaki ɗaya.

Abin da bai sani ba shi ne, Naja,atu tana da tsatstsauran ra,ayi a kan abubuwan da ya shafi gyaran jiki, ita bata cikin matan da za su sha wani abu domin gyara don farantawa miji da kuma samun wani matsayi ko kuma daraja a wajen mijin.

Ko lokacin da za a yi mata aure duk wasu kayan maganin mata da maganin sanyi da aka saya ko a kwalar rigarta, don kuwa ta ce ko a ƙasan takalmin ta ita alƙwari ne ta ɗaukarwa kanta cewa ba za ta taɓa shan wani abu don namiji ba. A cewarta idan har namiji yana sonka to babu ruwansa da ka gyara ko ka zauna a haka. Rashin sani hausawa suka ce ya fi dare duhu, a ƙalla ko da bata sha wani abu ba amma dai ta sha wanda zai daidaita mata ni'ima ko saboda kasancewarta ita kaɗai a wajen miji.

Tun da ta yi aure bata taɓa ko da haɗa wani abu ko da fruit ne kuwa ta sarrafa da madara don ta je wajen miji ba, hasali ma ko lokacin da ta haihu, babu abin da ta gabatar na daga gyaran jiki da mata suke yi idan sun haihu. Ko bagaruwa Naja,atu bata tsarkaka inda ɗa ya keto ya fito ba duk da ɗan ya zo babu rai amma dai haihuwa ta yi.

Haka ta karkaɗe zaninta ta koma wajen miji bata gyara komai ba bata sha komai ba.

Har kawo yau ba u wani abu da ta sha, ita kuma mahaifiyarta da yake ra,ayinta take bi saboda tana auren mai kuɗi tana mata abin da take so don haka duk abin da Naja'atu ta ɗaga ta ce fari to ko da kuwa baƙi ne sunansa fari.

A daidai gaɓar nan ne kuma ake batun ƙaro mata abokiyar zama ba tare da ta sani ko ta shiryawa hakan ba, tun da ta gama sakin jiki cewar miji da ita kaɗai zai zauna, yanzu kuma ƙaddara tana neman riga fata, shin wace irin mace xa a auro a kawo ya zaman zai kasance?.

Tun da ita duk wani abu da za a ce gyara ne bata damu da shi ba a taƙaice dai za a iya kiranta ƙazama ta wani fannin, tun da babu ruwanta da ƙamshi komai dai sai a hankali.

Sai da ta kai hannunta ta cusa a gashin kansa sannan ta ce

"Gobe ina son zuwa gidanmu akwai wasu kuɗaɗe da nake buƙata" Kuncin ta ya lakato yana ƴar dariya ya ce

"Kuma kuɗi ai kin fi ƙarfinsu ko nawa ne zan baki, wayarsa ya janyo ya miƙa mata ita ta cire paswrd ɗin ta yi transper zuwa account ɗinta don hatta pin ɗinsa na taranper ya sanar da ita.

Washe gari ta shirya ta nufi gidansu. Da la,asar sakaliya, Magajiya wacce ƙanwace a wajen Goggon ubansu ɗaya, sai dai tana yi wa Goggo mugun ƴan ubanci, ta tsani ta ga cigaban Goggo da ɗanta ta ƙi jinin ta gansu a walwala, duk da irin faɗi tashin ganin sun kyautata mata kuma bata rasa komai ba. Babban burinta shi ne ɗaya daga cikin ƴaƴanta su auri Alhaji Muhammad ɗin ta yi cizon yatsa da ta sai bayan sun yi aure ya samu aiki don lokacin da aka musu aure bai samu aiki ba bare har ya zama wannan hamshaƙin da take jin takaicin cewar ba ɗaya daga cikin ƴaƴanta ne a wannan daular ba.

Mai napep yana ajiyeta a ƙofar get ɗin ta turo ƙofa ta shigo, tana wani ɗagawa mai gadi kai ita ala dole masu gidan ƴan uwa. Wucewa ta yi ko kallo bai ishe ta ba yana gaishe ta ma ko amsawa bata yi ba. Tun da ta shigo harabar gidan idanunta suke yawo a gabaɗaya ɗungu da saƙon ginin gidam da irin tsaruwarsa, a zuciyarta tana faɗin

"Gaskiya wannan gidan da ace ɗaya daga cikin ƴaƴana ne ta auri wannan shegen yaron da ya je ya auro bare, da yanzu mu a juya akalarsa da ta uwar tashi zuwa inda muka ga dama, amma gashi nan ya je ya auro bare abin baƙincik da takaicin ma wai shi mai ƙudurin zama da mace ɗaya hummm ko ina haɗinsa da al,adar bature ban da yahudanci, da tuni ban samu na maƙala masa ɗaya daga cikin ƴan uwansa ba' Ta faɗa tana nufar ɓangaren Goggo.

Cike da murna Goggo ta tarye ta lokacin da ta je duk da cewar bata sanar da ita cewar za ta zo ba. Ta sanya Amira ta kawo mata kayan motsa baki sai ciye-ciye take, nan Goggo cike da murna ta ce

"Magajiya in sha Allahu ɗanki dai zai ƙara auren mata ta biyu, ki yi murna kin kusa karɓar jikanki ko jikarki da hannunki" Wani irin zabura da Magajiya ta yi tamkar wanda aka watsa mata ruwan zafi, tana mai ciccira maganar ta ce

"Au...au...aure fa kika ce? Shi da ya ce da mace ɗaya zai rayu?"

Goggo ba ta kawo komai game da diriricewar ta ba, cikin murna take sanar da ita cewar.

"Ai na sauke masa wannan ƙudurin nashi, yanzu ya yarda zai ƙara auren!" Magajiya ta ture farantin dambun naman gabanta ta ce

"Kuɓa wa zai aura?" Goggo ta ce

"Bamu tsayar da magana ba, kin san halinsa ba zaɓa zai yi ba, zan yi duban tsanaki dai na ga wacce zan zaɓar masa don ta share masa hawaye da mu baki ɗaya don ba na so a yi zaɓen tumun dare"

Magajiya ƙwaruwa ta yi da ɗan dambun da ya rage a bakinta, ruwan robar ta ɗauka ko tsiyayawa bata yi a kofi ba ta kafa kai a jarkar ta sha ruwa ta ajiye a zuciyarta ta ce

'Taɓɗi rigiji gabji miya da hanjin ɗan tsako, wallahi ba zan taɓa yin wasa da wannan damar ba, dole tsakanin Rumasa'u da Haulatu ɗaya za ta kashe auren ta, to zo ta yi saurin yin idda ta auri Muhammad ko ma karya ƙashi mu ci cinyar kaza, ai wallahi ɗaya daga cikin ƴaƴana ta aure shi nima sai an ware min ɓangarena a gidan nan na ƙauro, ai ba zai so barin sirikarsa a can wancan gidan wanda bambancinsa da maƙabarta kaɗan ne'

*** [7/18, 6:20 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH

Daga marubuciyar

Ruwa cikin cokali Uwar agola Malamin bogi ƙazamin miji Yar zaman wanka Ruɓaɓɓiyar igiya Ƙara,in inna delu Bonono Ci ma zaune Ƴan adaidaira sahu Jalli joga Ungozoma Ƴar ƙanwata, Beelal Da sauransu. ***