KIBIYA A IDO

5

by @mamanafrah3028

MAGAJIYA

Kamar daga saman ta ji Goggo tana faɗin

"Subhanallahi Magajiya ƙaruwa kika yi?" Magajiya wacce idanunta suka ɗanyi ja saboda yanayin ƙwaruwar da ta yi, ta kalli Goggo tana faɗin

"La ba komai fa" ,Ta faɗa tana ta hasashen wacce za ta saka daga cikin ƴaƴanta ta kashe aurenta ta zo ta yi auren daula, tun da ga tauntsu daga sama gasashshe kar wannan garaɓasa ta wuce su.

Ruwan robar ta ajiye domin gabaɗaya sai ta ji dambun naman ma ya fice mata a rai daman kwaɗayi ne ya sa ta farwa dambun amma yanzu tana ganin za su tsinci dami a kale saboda duk wacce ta auri Muhammad ɗin daga cikin ƴaƴanta to tabbas ta san za su ci karensu ko babbaka babu.

A zuciyarta ta ce

'Idan na samu damar nan ai ba don naman alade babu kyau a ci namansa ba, to da har dambun naman alade sai an yi mini'

Goggo ta ci gaba da faɗin

"Ai idan har aka dace yaron nan ya samu macen da za ta share masa hawaye, ta haifa mana ƴan dagwai-dagwai to da lallai zan iya cewa ni an biyani" Murmushi Magajiya ta yi ta ce

"Wallahi biya ma ai ba ɗan ƙarami ba, ai da Allah zai samu a samu a dangi ma, sai a yi tuwona maina hakan zai fi armashi" Goggo da bata gama gane manufar ta ba ta ce

"Ai yanzu a dangi babu wacce nake ganin za a a yj wannan haɗin, kin san yaran zamani ma, kawai dai zan duba lamarin za ku ma mu yi addu,a da neman zaɓin Allah, amma dai ba za a ɗauki wani dogon lokaci ba"

Magajiya ta haɗiye wani yawu tana jin takaicin da Goggk take cusa mata na ganin za ta mata sakiyar da ba ruwa, saboda iya ganinta dai Goggo bata fahimci manufarta ba, kuma ta san dai ba za ta fahimta ba tun da ta san ƴaƴanta sun yi aure don ita Goggo ko lissafin su bata yi saɓanin ita Magajiya da take son su kashe auren su xo su yi wani auren a nan.

Abu ɗaya ta iya faɗa mata shi ne.

"Shi dai jinkiri alkairi ne, ya kamata a ɗan jinkirta" Ta faɗa a kokarinta na ganin ta ja ra,ayin Goggon ba a sama masa matar da wuri ba har ta yi fafutukar kashe auren ɗaya daga cikin ƴaƴanta ta san kuwa a wannan lokacin idan ta zo wa Goggo da batun maganar dole ba za ta yi musu ba sai dai ma a jira wacce ta kashe auren ta yi idda a ɗaura da Alhaji Muhammad ɗin.

Goggo ta ce

"Wannan haka yake, Allah sa jinkirin ya zama alkairi" Da amin ta amsa tana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya jin tana dab da cim ma baragurbin burinta.

Ana fara kiran sallah ta yi wa Goggo sallama ta tafi, saboda gabaɗaya ta kasa nutsuwa, so take su je su fara shirya yadda komai zai kasance ita da ƴaƴan nata. Don haka Goggon tana ta cewa ta yi sallar amma fir ta ƙi ta ce sai ta je gida ta yi. Ko da ta zo fitowa mai gadi da yake alwala wani kallon tara saura kwata ta masa a zuciyarta ta ce

'Wallahi wuyarta ƴata ta zama matar gidan nan sai na cisgeka daga wannan ɗan muƙamin gadin ƙofar da aka baka kake ganin tamkar wani hamshaƙin aiki ne, in samo wani in ɗora' ,Ta faɗana zuciyarta tana buɗe get ɗin ta fice.

Hajiya Naja'atu ko da ta je gidansu da sallama ta shiga bayan direba ya ajiye ta, zaune ta samu Mom tana sakatar hakori, ta amsa mata tana mai rungume ta da faɗin

",Sannu da zuwa ƴar albarka ina ta tunaninki ashe dai kina tafen ai na zata ba zuwan xa ki yi ba' ,Tana shagwaɓe fuska ta ce

"Mom mai zai hanani zuwa?" Dariyar suka sakarwa junansu, Mom ta riƙe mata jakar hannunta suka nufi falo.

Zaune suke bayan Mom ya gabatar mata da drinks masu sanyi, sai dublan da ta xubo mata a plate tana ci suna hira.

Mom ta ce

"Naja'atu baki ƙarasa min labarin ba"

Baki ta taɓe ta ce

"Mom kenan, ni fa wallahi da za a barni daga ni sai tsohuwar nan a wannan gidan, da shegen duka zan mata, ina dalili tana shigar min hanci a karkace" Idanu Mom ta zuba mata ta ce

, "Ni ai har yanzu ban ma gama gane inda maganar ta dosa ba"

Hajiya Naja'atu ta lumshe idanu ta buɗe ta ce

"Mom matar nan dai tana nan tana nacin in ajiye makaman yaƙin da na ɗaukan kan ƙudurin rashin sake haihuwa kwana kusa, saboda ta rainani wallahi har ɓangarena ta je ta sameni da ta aika in je na ƙi zuwa" Mom ta riƙe baki cike da mamaki tana kanne ido ɗaya ta jijjiga kai ta yi ƙwafa haɗe da jan dogpn tsaki ta ce

"Ni na ga jaraba da masifa wallahi, wai mai ya sa mutane suke son takurawa wanda suke ganin suna ƙarƙashin ikon su? Shin ta manta cewar da ɗanta take iko ba da ke take iko ba? Sannan ma ita wa ya hana ta tara ƴaƴan da yawa da ta zauna ta haifi ɗa ɗayan, yanzu da ke za ta xo ta sako ki a gaba a kan sai kin haifawa ɗanta ƴaƴa da yawa ita ta samu jikoki da yawa saboda zuri'arta su haɓaka?"

"Kema dai kya faɗa Mom, na kasa fane dalilin wannn wallahi matar nan da a ce fuska na sakar mata va ƙaramin tuwo za take ci a kaina ba"

Mom ta ce

"Kin ce ba yanzu za ki ƙara haihuwa ba shin ita ce cikin naki ko kuwa ita za ta miki naƙuda?"

Hajiya Naja"atu ta ce

"Rabu da ita wallahi so take idan ta taɓoni haihuwar ma gabaɗaya ba zan sake ba, in ga wanda zai sa in yi dole, ban da abin da shi ɗan nata ba shi ya ce ya ji ya gani ba amma ita sanyawa yana damuna shi ma da maganar haihuwar nan, in va ma ni ɗin nan ba wace shegiyar macen ce za ta jure zaman da wannan ɗan nata mai shegiyar uƙatar naci, mutum koyaushe yana maka dibdibtun ka vashi haƙƙinsa, wannan na ga idan ban yi da gaske ba, ko ban haihun ba tsufar da ni zai yi in na biye masa, ko sati uku na ɗauka bamu kaɗaice ba sai ki ga duk ya shiga damuwa" Ta daɗa tana jan tsaki.

Mom wani yawu ta haɗiye, tana ɗan ƙiƙƙifta idanu, ta san cewar abin da ƴar tata ta faɗa ba daidai bane take yi, yanzun ma ta san wannan maganar haihuwar ba a kan daidai take ba sannan maganar hana shi haƙƙinsa ma ba ƙaramin tauye shi take yi ba, amma saboda son zuciya da kuma son kai haɗe da ganon bata ɓatawa ƴarta rai ba, saboda abin duniyar da take bata, da kuma tsoron zuciyar Hajiya Naja'atun ya sa ta taɓe baki ta ce

"Ke kaɗai na haifa, don haka kema za ki iya sake haihuwar ɗaya nan gaba, tun da wanda kika haifa ya mutu, idan ma wanda kika haifa ɗin ne za ko bari matsayin wanda za ki haifa shi kaɗai, kona da wanann damar sabosa haihuwa ba komai bace saitsufar da mata da take yi, su mazan da a ce su ne suka haihuwa suka san wahalar ɗaukan ciki, naƙuda, wahalar shayarwa da daga ɗaya ba za au ƙara ba, amma mace ta ƙarar da ƙarfinta wajen haifa musu ƴaƴa da raino sai dai daga sun ga ta tsufa sai idanunsu su fara kalle kalle masu jini a jika, sannan zuciyarsu ta kwaɗaitu a kan son auro wata, yawanci ba koqane namiji ne yake yarda ya riƙe mace ɗaya ba kawai ki sha shagalinki ƴata" Ta faɗa tana miƙawa Hajiya Naja"atu hannu suka taɓa haɗe da sheƙewa da dariya.

Hajiya Naja'atu ta ce

"Wallahi fa Mom duk da na yarda da soyayyar da Alhaji Muhammad yake min ɗari bisa ɗari, na san ba zai taɓa juya min baya ba, na san ba zai so na shiga damuwa ba sau tari da in shiga damuwa ya gwammace shi ya shiga damuwar, duk da ban nemi komai na rayuqa da kuma kulawa na rasa ba, sannan na san matsawar na haifa masa ƴaƴa ko da sun kai ɗari ba zai taɓa guduna ko ya canja min saboda tsufan da jikina zai nuna ba, amma dai ni ɗin nan ba na cikin matan da za su bautawa wahalar namiji, ko bin son zuciyarsa ko kuma ƙarar da rayuwarsu wajen gina tashi rayuwar, ni fa Mom duk wani abu da zan yi don farantawa ɗa namiji ba ya daga cikon ra,ayina, kuma har abada ba zan taɓa yin wani abu duk ƙanƙantarsa don na birge ko na farantawa ɗa namiji ba!" Ta daɗa tana wani irin haɗe rai tamkar bata taɓa dariya ba.

Mom ta ce

"Shi ya sa kike birgeni Naja'atu ai kyan mace ta zauna a kan bakanta ba tarw da ta bari wani shege ya canja mata ra,ayi ba, ki ja zaren ki iya son ranki, ki ja ragamar cikin gidanki iya yadda zuciyarki ta miki daɗi, hakan zai sa yake ganin darajarki ya san kimarki, yake ganinki da daban a cikin mata"

Wani farrr ta yi da idanu ta ce

"Bare ni da nake da lasisin zama da zai yi da ni, ni kaɗai, ai wallahi na san ko alwashi na ci a kan Alhaji ba zai bani kunya ba, kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara a kansa ba, na san da matuƙar wuya ko mutuwa na yi ya kalle wata mace da sunan so, na san ko mutuwa na yi a yadda yake sona sai dai ya riƙe kabarina wajen zuwa ya taɓa ƙasar kabarin don yake jin tamkar dai ina raye, amma a yadda yake sona a yadda ya ƙudurci zama da ni, ni kaɗai ba tare da wata macen ba, ai ni yanzu na fara cin karena babu babbaka" Ta faɗa tana janyo jakarta wacce sai walwalin sabunta take, jakar kala ɗaya ce da takalmi da mayafin da ta yafa, wanda suke light green kasancewar leshin nata maroon aka masa kwalliyar manyan flowers light green shi ya sa ta saka su, kunnenta da wuyanta sarka da ɗankunen ne masu tsada, sosai ta yi gayu abin ta sai dai kash duk wannan gayun iya idan za ta tafi unguwa ne amma matsawar a cikij gida ne bata damu da wani abu kwalliya ko gayu don birge kanta ko birge miji ba.

Ga ƙamshin turarukan da Alhaji Muhammad yake son ji daba gare ta, amma bata taɓa sanyawa a cikin gidan sai dai shi idan yana son shaƙar ƙamshin ya shafa mata da kansa, ko kuma idan yana son jin ƙamshinta a kusa da shi ya ɗakko irin turarukan nata ya shafa, domin yana da duk wani kalar turarenta a kan nashi madubin kuma yana yin hakan ne don idan ta ƙi masa da daɗi ya ɗakko turarukanta ya shafa har jikin bed sheet ɗin da zai kwanta sai ya ji tamkar tare suke.

Sun jima suna hira da mahaifiyar tata, a inda daga ƙarshe ta mata sallama, bayan ta tura mata kuɗi dubu ɗari, daga cikin kuɗin da ta sanya ya tura mata. Sosai take sanya mata albarka, tana wani irin wasata tana faɗin

"Godiya nake ƴata ta kaina, mace ɗaya tamkar da dubu a gidan Alhaji Muhammad, sa gabanki inda kike so, daga ke ya rufe ƙofa babu ƙari"

Ta yi dariya ta ce

"Ko bayan raina kuwa" Suna dariya ta rako ta bakin ƙofar gida tana faɗin

"Mom zan san yadda zan yi ya saya miki gida na gani na faɗa, wannan da ya siya miki bai min ba, na fi so in ganki a gidan da kowa ya kalla sai ya sake kallo, in ya so wannn sai ki bar shi a mazaunin kadara, don ba zai yiwu ƴarki tana gidan mai kuɗi ke kike zaune baki da kadarori ba a hankali zan ke sama miki filaye ma kina ajiye takardun, kafina ankara kin keta hazo a sahun wanda za a ke lissafawa masu hannu da shuni" Wani irin gingiringim kan Mom ya yi ta ce

"Allah dai ya miki albarka ɗaya tamkar da miliyan a wajena, shi ya sa hausawa suke faɗin da taron yuyuyu gwara ɗa ɗaya ƙwakƙwara, kin ga yanzu ke kaɗaice na haifa amma kuma kina min abin ko da ƴaƴa goma na haifa ba lallai ne su mini ba" Kafaɗar Mom ta dafa ta ce

"Kar ki damu, ai mu biyu ma za mu iya rayuwa da kanmu ba wai sai na haifa wasu ƴaƴa ba, ni kaɗai kike da nima ke kaɗai nake da ke" Ta faɗa tana yin gaba ita kuma Mom bakinta ya ƙi rufuwa, tana tsaye har direban ya fito da sauri cikin girmamawa ya buɗe mata bayan motar ta shiga ya mayar da ƙofar ya rufe, ya koma mazaunin direba ya tashi motar ita da mahaifiyarta suna ɗagawa juna hannu, daman ita ta dakatar da direban a kan kar ya tafi har sai ta gama abin da take, saboda bata so ya tafi ya dawo wannan dalilin ne ta sa duk tsawon daɗewar da ta yi yana zaune yana jiranta.

Daga nan gidan ƙawarta Zuhra ta sa direban ya kaita, daman sun yi waya za ta je. Direban ya kutsa hancin motar cikin katafaren get ɗin bayan ya yi horn mai gadi ya buɗe masa. Yana gama parking ya fito ya buɗe mata ta fito tana riƙe da jakarta a hannu, kasancewar jakar ba irin manyan nan bane ƴar madaidaiciya ce.

Tun da ta fito daga motar, ta fara takawa daga inda take tana kallon Zuhra da mijinta suna tsaye suna ta dariya da alama wata magana suke, baki ta taɓe ta ja ƙaramin tsaki don da ƴar tazara tsakaninsu kasancewar gidan yana da girma.

Ta zo daidai inda suke Zuhra tana faɗin

"Ni dai idan ka dawo sai ka kaini"

Shi kuma yana cewa.

"Ni dai idan na yi sallah isha,i gida zan dawo kuma babu inda zan fita na fi so in ganni kusa da ke" , Yana dariya har da mata ɗan gwalo ta kumbura baki. Daidai nan Hajiya Naja'atu ta ƙaraso tana faɗin

"Ga zara ga wata" Zuhra ta yi dariya tana faɗin

"Manyan mata maganin ƙanana-ƙanana" Shi kuma ya murtuke fuska ba yabo ba fallasa ya ce

"Barka da zuwa" Hakan ma ya yi ne saboda Zuhra ya san mace ce wacce take girmama shi da girmama iyaye da ƴan uwansa duk wani baƙo duk ƙasƙancinsa in dai ya zo gidansa sai ta mutunta shi wannan dalilin ya sa shi ma a nasho ganon ko kare ne ya zo gidan domin ta tabbas ba zai wulaƙanta shi ba, amma dai shi ko kaɗan Hajiya Naja'atu bata masa ba ba ya son hulɗarta da matarsa sai dai ba zai raba su ba don tare ya gansu, ƙawaye ne tun yarinta.

Hajiya Naja'atu cike da nuna izza ta kalle shi ta watsar ta ce

"Barka" Bai ƙara bi ta kanta ba ya juya ya tafi ya barsu suna ta magana, duk da Zuhra ta ji haushin rashin gaishe da mijinta da Naja,atun bata yi ba amma babu yadda za ta yi da ita tun da har ta gaji da faɗa mata kowacce irin gaskiya ta kowacce fanni.

Tana ɗaga ƙafafunta dakyar kasancewar kumburar da suka yi, dalilin cikin da take ɗauke da shi. Har falo suka ƙarasa tana zaunawa haɗe da faɗin

"Wash Allah"

Hajiya Naja'atu ta ce

"Sannu da ƙoƙari ƙawata, kin sanya kanki a wahala, ni fa shi ya sa bana son haihuwa yanzu kalli mijinki ya fice jikinsa babu nauyi amma ke ya barki kina zama dakyar tashi dakyar juyi dakyar kwanciya dakyar" Kallon ke dai ba za ki canja halinki ba ta mata ta ce

"Daman ai haka Allah ya tsara"

Ta kalle ta ta ce

"Me?"

Zuhra ta ce

"Haka Allah ya tsarawa mata su ne da ɗaukan ciki da raino, maza kuma ya basu nasu kason da ban wato ɗaukan ɗawainiyar iyalin" Idanu ta ɗaga ta kalli saman siliin ta dawo da su ta dire a lan TV da take ta aiki, tashar arewa 24 ne a kunne fatima rabi,u gwadabe tana koya girkin dambun alkama da kunun acca.

Zuhra ta ce

"Ban san ranar da za ki canja halinki ba, ki ɗauki samun ƴaƴa a matsayin rahmar ubangiji, duk da ubangiji da kansa a qur,ani ya kira ɗaukan ciki da shayarwa wahala kan wahala amma ai bayan wuya sai daɗi kuma ya ambaci hakan ne don ƴaƴa su san matsayin da uwa take da shi, da irin faɗi tashin da ta sha wahala wajen ɗaukan cikin da haihuwar su."

" Bani ruwa in sha, don yanzu kika fara wannan jawaban naki da wa,azi sai ki kwashe lokaci mai tsawo" Ruwa ta buɗe freezer ta ɗakko mata haɗe da kofi ta tsiyaya ta bata. Sha ta yi ta ce

"Kin ga na yi dare duk da ni bana amfani da wani lokaci wajen komawa gidana"

Zuhra ta ce

"To ba sai in za ki koma ki kula da miji ne za ki kiyaye da lokaci ba, shi da ko kina gidan da ke da babu duk ɗaya kin ga kenan wane kiyaye lokaci za ki yi, wallahi Naja'atu ki yi wa kanki faɗa"

Baki ta taɓe tw ce

"Ke dalla rufe min baki, na faɗa miki ni ba a yi namijin da zan ƙarar da lokacina wajen kyautata masa ko masa wahala ba"

Zuhra ta ce

"Ke fa haka kike idan kika saka gaba gabas babu wanda zia ce ki koma arewa, Allah ganar da ke"

Hira suka ɗan taɓa gar mai gidan ya dawo daga sallar isha,i, da ya koma part ɗinsa ya shiga kiran matarsa a waya bayan ta ɗauka ya sanar da ita yana jiranta, ta amsa masa cikin girmamawa da cewar tana zuwa. Baki Naja'atun ta taɓe tana tashi ta ɗauki jakarta tana faɗin

"To tattabaru sarkin soyayya, ni bari na koma in da na fito" Tana mata tsiya ta ce

"Ke ai na ga ke da soyayya kun raba hanya mu kuwa ko ƙafa bamu saka ba, don ni wallahi a tara ko wuri ban dauka ba yanzu" Dariya Hajiya Naja'atu ta yi ta ce

"Allah baki sa,a kawai dai ina jiye miki butulcin ɗa namiji watarana!"

Zuhra ta ce

"Ku fa yawanci mata damuwarku da kuma faɗin cewar maza suna butulci bai wuce a ce sun ce za au muku kishiya ba watarana, ni kuma a nawa hasashen da nawa ganin sai in ga ai tun da halal ne hakan matuƙar namiji ba zai wulaƙantani ba wallahi ko mata uku zai jera a bayan ni babu abin da ya dameni kowacce fa da halinta za ta zauna, gwargwadon iya takun mace a wajen miji gwargwadon matsayinta a zuciyarsa"

Hajiya Naja'atu cike da mamaki ta ce

"Allah shirya min ke Zuhra kare ya ɗauke zuciyarki, ai son da kike yi wa mijin naki ma na banza ne tun da har bakya kishin sa"

Zuhra ta ce

"Ba haka bane, babu macen da za ta ce bata son mijinta ko bata kishin sa, sai dai kai baka isa ka ja da iko da faɗar Allah ba, ai ƙarin aure halal ne"

Dariya ta yi ta ce

"Wannan duk ku aka bari da tunani da fargaba ko neman ya za ku yi, ni da na yi wa sauran mata fintinkau ai mijina ya yarje min in kwantar da hankalina in rayu babu wani tunanin samun kishiyata a doron ƙasa, da ni kaɗai zai rayu kin ga ni tunani wani abu kishiya ma ba ya gabana" Zuhra ta ce

"Kuma fa haka ne, amma kuma gashin kin kasa bashi kulawar da ta dace"Ƙaran wayar Zuhrar ne ya katse musu maganar, Zuhra ta waiwaya kan kujerar da ta ajiye wayarta Hajiya Naja'atu kuma ta juya ta fara tafiya tana faɗin

"Wannan ba zai barki ki sake ba ma, ai da ni ce in sha biyun dare za ki kai ma babu ruwanki da takurawar mijina saboda shi yana ɓangarensa ina nawa, amma ke yana can ɓangaren nashi ba ba zai sakar miki da mara ki yi fitsari ba hummm wannan soyayya ko wahala" Ita dai bata kula ta ba, ta ɗauki wayar tana mai dannawa ta kai kunneta tana faɗin

"Afwan Allah ya ja min da kwananka" Da haka ta lallaɓa shi ta kashe wayar ta fito ta takawa ƙawar tata har baki mota, direban ya buɗe mata bayan ya taso daga kan bencin mai gadi da suke ɗan tattaunawa, shiga ta yi Zuhra tana riƙe ta murfin ƙofar sa da suka yi sallama ta matsa direban ya rufe ya koma ya tada motar suka fara tafiya, ita ma juyawa ta yi ta nufi ɓangaren mijin nata ta san sai ta sha mita a wajensa, sai dai ta san akalar rigimarsa, don haka ta san yadda za ta lallaɓa shi a zauna lafiya.

A ɓangaren Alhaji Muhammad bayan ya dawo daga wajen aiki ya samu bata dawo ba, daman ya san ita bata cika dawoqa dagan unguwa a kan lokaci ba wani lokaci har ƙarfe tara tana kaiwa. Banɗaki ya shiga ya yi wanka ya fito, drower kayansa ya buɗe zai ɗauki jallabiya amma ya ga duk masu ƙananun hannun sun yi datti ba sa ciki suna cikin kayan wanki, rufewa ya yi ta nufi wajen singlet da gajerunan wanduna nan ma jiya i yau domin duk sun ƙare, shi bai ma san sun ƙare ba, drower da sabbin kaya suke wanda ba a buɗe ba da suke rataye ta ɗakko komai sabo ya saka ya feshe jikinsa ya nufi masallaci, bayan ya dawo ya je ɓangaren Goggo suka taɓa hira, wajen ƙarfe takwas ya nufi ɓangaren ta amma bata dawo ba. Shayi kawai ya je ya sha ya koma sama ya shiga ɗan dube-dube a laptop wajen takwas da rabi ya ji shigowar motar alamar ta dawo gidan, ajiyar zuciya ya sauke.

Tashi ya yi ya leƙo daga windown yana hango ta aka buɗe mata ƙofa ta zuro ƙafafunta da suke aanye cikin takalmi mai kyau, kasancewar hasken lantarki ya haske gidan tamkar da tsakar rana.

Fitowarta ya ɗauki hankalin ta yadda ta ɗaura ɗankwalinta, da kuma kayan da suka mata kyau, gabaɗaya ya raja,a wajan kallonta tamkar dai ba Naja'atunnsa ba wacce take zama babu kwalliya a gida, duk tarin kayan da yake siya mata masu tsada amma ta jibge ba za ta sanya masa su a gida ya gani ba, idan har ya ga kwalliyarta ya ganta cikin shiga me kyau to tabbas fita za ta fita ne.

Jingina ya yi a bangon yana kallonta har ta ƙulewa ganinsa daga ƙarshe ya juya ya kashe laptop ɗin ya fara tako matakalar da sauri da sauri ya sakko, hankalinsa gabaɗaya ya karkata ga ya je ya ganta a gabansa ba tare da ta cire kayan ba.

Magajiya, kasa haƙuri ta yi wajen ganin sai ta je gida za ta kira ƴaƴan nata, tana hanyar tafiya ta shiga kiran Haulatu har ta tsinke bata ɗaga ba, a fili ta ce

"Wannan an yi shegiyar yarinya ko uban me take ana kiranta, arziƙi yana kiranmu" Ta faɗa tana tare me napep amma jin kiran da ta yi wa Rumasa,u yana shiga sai ta tsaya bata hau napep ɗin ba ta kara wayar a kunne. Mai napep ya ce

"Hajjaju ya kin tsayar da ni kuma baki shiga ba, nan fa kan hanya ne ya kamata ki shigo mu tafi" Banza ta masa kamar ma ba da ita yake ba, jin Rumasa,u ta ɗauka ta ce

"Ruma mai kike waya tana ta ringi, ni wallahi yadda labarin nan take ci na ji nake kamar na yi tsuntsuwa na taho gidajenku na faɗa muku"

Rumasa'u ta dafe ƙirji ta ce

"Umma kar dai yaya Muhammadu ne ta biya miki makkah... Katse ta ta yi da faɗin

"Ke banza wannan ba batun tafiya makka bane amma in dai cinikin nan ya faɗa to tabbas ni kaina ban san sau nawa zan biyawa kaina aikin hajji ba"

Rumasa,u ta ce

"Mama miliyan nawa ya baki" Ganin mai napep ya zura mata ido sai gabanta ya faɗi, ta fara tunanin tana waya a gabansa kuma bata san halinsa ba kar ma su tafi ya bi wata hanyar da ba kowa ya doke ta a banza ita bata kashe auren ƴaƴab nata ta samu sun shiga gidan bare ta je aikin hajjin ya je ya ƙarya ta a banza" Da sauri ta wayince tana faɗin

"Ke wasa fa nake miki daman kiranki na yi in ce ki aiko min naira ɗari zan sayi klin in wanke ƴan tsummo karana " Ta faɗa tana kallon mai napep ɗin da ta ga ya ɗauke kai kamar ma har tsaki ta ji ya yi, hakan ya sa ta yi saurin kashe wayar ba tare da ta jira ta ji mai Rumasa,un za ta ce ba. Tana gamawa ta shiga ta zauna ta ce

"Yanzu ɗan nan sai kana min faɗa kamar wani ubana a ƙalla dai ai na haife ka in ma ban yi jika da kai ba" Banza ya mata ya ja suka fara tafiya ta faɗa masa inda zai kai ta.

Ko da ta koma gida dakyar ta yi sallah, don wasi-wasi ya cika mata zuciya, ko da ta idar da sallar haka ta duƙufa wajen ɗaga hannu ta shiga jero addu,ar Allah sa ɗaya daga cikin ƴaƴanta ta auri Muhammmad ɗin

Ranakun posting

Asabar lahdi Litinin, talata laraba [7/19, 7:06 PM] Baiwar Allah: ***

*KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH

Daga marubuciyar

Ruwa cikin cokali Uwar agola Malamin bogi ƙazamin miji Yar zaman wanka Ruɓaɓɓiyar igiya Ƙara,in inna delu Bonono Ci ma zaune Ƴan adaidaira sahu Jalli joga Ungozoma Ƴar ƙanwata, Beelal Da sauransu. ***