6
*ABDULSALAM*
Da mamaki ya kai kallonaa kan ƙofar gidan, sannan ya kalli direban yana nuna tsantsar mamaki shimfiɗe a fuskarsa ya ce
"Ikon Allah to ina za su je?" Ya tambaya tare da tunanin wanda zai bashi amsar tambayarsa.
Bai ma bi ta kan direban ba ya yi gaba yana dudduba wanda zai faɗa masa inda suke, domin tuni zuciyarsa ta fara zulumin inda Hasiya ta kwashe ƴaƴan ta tafi ba tare da sanar masa ba, kuma bayan ba a yi sadakar bakwai ba ma yana fatan da addu,ar Allah sa dai ba garin ta bari ba saboda idan har hakan ya kasance gaskiya to haƙiƙa zai shiga damuwa da tashin hankali a daidai wannan gaɓar da ya fi kowa buƙatar ta.
Wani yaro ya gani ya fito daga gidan da yake maƙotaka da gidan Hasiyar da sauri ya ɗaga masa hannu ai kuwa yaro ya taho da gudu saboda yana ganinsa yana zuwa gidan Hasiyar.
Yana zuwa Abba ya dafa kafaɗarsa ya ce
"Ina mutanen gidan nan suke?" Ya tambaya yana masa nuni da gidan.
Yaron kamar jira yake a tambaye shi a take ya hau faɗin
"Mai gidan ne ya kore su ai basu biya kuɗin haya ba" Ya faɗa yana kallon Abba.
Abba ya yatsina fuska ransa a ɓace ya ce
"Saboda kuɗin hayar ya kore su? Ina suka tafi kuma?'
Yaron hankali kwance ya ce
"Sun tafi su duka ni dai ban san inda suka tafi ba" Goshi ya dafe yana rasa abin cewa, ko kaɗan bai kawo cewar gidan mahaifiyarta suka tafi ba, ya cewa yaron ya tafi shikenan, shi kuma ya jingina da motar yana tunanin mafita.
Zuwa can zuciyarsa ta raga masa cewar
'Ba kana da lambarta ba ka kira ta a waya mana' Da sauri ya ciro wayarsa yana kamo lambar zai doka kiran sai kuma ya fara tunanin shin idan ya kira ya ce mai, kuma ma a ina xai ce ya samu lambar, kawai da wannan tunanin ya yj ya shiga kiran wayar.
Hasiya ko da suka dawo gidan, tana zaune a ɗaki ta rasa duniya mai yake mata daɗi, tunanin yadda za takr ɗaukan ɗawainiyar ƴaƴan take yi, domin ta san abin da Abdulsalam yake yi ya yi ne saboda farko amma ta san daga baya zai watsar da komai ne, kamar yadda a baya ma ba ua tallafa musu.
Ƙaran wayarta ne ya katse mata tunani, ta katse ba tare da ta ɗauka ba, kiran ne ya sake shigowa, bata ɗaga ba har ya katse ko da ta shiga ta duba miss call ɗin tana shirin hin kiran wani ya shigo.
Ɗaukan wayar ta yi ta kara a kunne, daga ɗaya ɓangaren ta ji sautin sauke ajiyar zuciya, da sauri ta janye wayar tana sake kallon lambar. Ta mayar kunnenta ta ji ana faɗin
"Hello bakya jina" Ɗan dim ta yi rana son gano mamallakin muryar. Kafin ta gama gano shi ta tsinkayi muryarsa yana faɗin
"Hasiya Abdulsalam ne" Ɗifff ta ɗauke wuta tunanin da ta fara yi shi ne
'Ya aka yi ya samu lambarta' Bata kai ga ba kanta amsar tambayar ba ta ji yana cewa
"Na zo gidan na tarar a rufe, shi ne wani yaro yake min bayanin abin da ya faru"
Cikin sanyin murya ta ce
"Wallahi kuwa mai gidan ne ya buƙaci mu tashi saboda kuɗin haya" Wani sonta ya ji ya tsarga masa zuciya jin yanayin maganar ta, tabbas da a ce sarewa take busawa ya san sai ta fi haka daɗin sauraro, shi bai ƙi a ce ya kwana yana jin daddaɗar muryarta, wacce yake jin kamar an saka zuma saboda daɗi, sai ya ji da tunanin amon sautin muryar Ramla matarsa ya faɗo masa ji ya yi ita tamkar dai wanda ake saka ƙuli-ƙuli.
Cike da wata murya mai kamar lallashi ya ce
"Haba Hasiya ina raye amma maimakon ki kirani ki faɗa min sai ku tashi daga gidan? Bayan ko zaman makokin ba a gama ba, ai da kin kirani na bashi kudin hayar"
Hasiya tq ce
"Bani da lambarka ne, sannan tunanin wannan bai zo min ba" Jin zai ɗora da wata maganar cike da ƙosawa ta ce
"Mun gode ƙwarai da kulawa" Jin wannan kalaman masu kamar dai sallama take masa shi kuma bai gama jin abin da yake so ya ji ba wato inda suke, da sauri ya ce
"Karki kashe watar Hasiya" Dakatawa ta yi tana tunanin abin da da sa ya dakatar da ita haka da sauri
Ta ce
"Ina ji" Sai lokacin ya lura da azarɓaɓin da ya yi wajen magana, hakan ya sa ya ce
"Daman tambyarki zan yi ina kuke je? Kin san ina so in baki kuɗin hayar a ba mai gidan, saboda a saukewa Zahraddin nauyi, tun da bashi ne wannan" Idanunta tana cikowa da ƙwalla ta ce
"Haka ne"
Ya sake cewa
"Kuna ina?" Ta ce
"Muna gidanmu" Da sauri ya ce
"Ok gani na zuwa" Yana faɗa kafin ma ta sauke wayar daga kunnenta ya kashe, tana saukewa ta bi lambar da kallo, a jerin sunayen missed call ɗin da aka mata, scrolling ta shiga yi, ai kuwa ta ga lambar a can ƙasa inda aka mata missed call sannan ma kamar an amsa kira. Sake duba lambar dai ta yi ta tabbatar ita ce, a lokacin ne hankali da tunanin ta ya bata cewar kenan ba a yau Abdulsalam ya samu lambar ta ba, tun da ya taɓa kira don tana duba date da time ta gane ranar da aka yi kiran. Shigowar Zajnaba ta dakatar da ita daga saƙa da warwarar ta ce
"Aunty ya na ganki kin yi shiru" Ta kalle ta ta ce
"Zainaba idan ban yi shiru ba mai zan yi, abubuwa ne suka taru suka yi wa ƙwaƙwalwata yawa"
Shigowar mahaifiyarta ta ce
"Ai kuwa damuwa ba abokiyar zama ba ce, gwara ki ajiye ta a gefe, in dai gida ne ba gashi nan kun dawo na ga"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"Haka ne, ai yanxu ma Abdulsalam ya kirani wai ya je can ba ma nan shi ne yake cewa zai zo ya bada kuɗin hayar tun da nauyi ne a kan Abbien su Zainaba" Baki ta taɓe ta ce
"Da can da yake raye vai biya masa kuɗin hayar ba sai yanzu, ai idan mutum yana buƙatar taimako tun yana raye ake masa ya san an yi, amma in mutum ya mutu taimakon mai za ka yi" Ta faɗa tana jan tsaki.
Hasiya ta ce
"Yanzun ma tun da nauyiin zai sauke ai kamar ya masa ne kuma dai koma mai zai yi dalilinsa ne"
Zainaba ta taɓe baki ta ce
"Ni fa Abban nan ba birgeni yake yi ba, lokacin da Abbie bashi da lpia ma ba zuwa yake ya duba shi ba, kuma idan ma ya ce ya taimaka masa sai ya ce babu" Ta faɗa tana wani taɓe baki.
Sallamar sa ce ta dakatar da su daga tattaunawar da suke, Nasira wacce ita ce a tsakar gidan ta amsa masa tare da gaishe da shi, ya amsa yana tambayarta ina ƴan gidan ta sanar da shi cewar suna ɗaki.
Fitowa suka yi su duka bayan Nasira ta ajiye masa kujera ya zauna, ya gaishe da mahaifiyar Hasiya yana mata ya haƙuri ta amsa tana kauda kai gefe. Hasiya ma ta gaishe shi ya amsa yana cewa
"Zainaba" Zainaba ta ce "Na,am Abba" Ta faɗa tana gaishe shi ya amsa mata.
Nan ya shiga musu bayanin bai san abin da yake faruwa ba, daga ƙarshe ya tambaya kuɗin hayar ta faɗa masa ya saka hannu a aljihu ya ɗakko linkin kuɗin sau biyu ya miƙa mata. Karɓa ta yi kowa yana binsa da kallo sai dai sun ɓoye mamakin su don kar ya zargi kansa duk da sun san su ma ya san dole za su yi mamakin saboda abu ne da bai saba musu ba.
Bayan sun gama ya musu sallama ya fita, hatta mahaifiyar Hasiya duk da tana jin haaushinsa amma da ya ga ya bada kuɗin sai ta ji daɗi a ranta, sannan ta ƙara ganin girmansa ya ƙaru a idanunta, da tunaninta yana yin komai ne saboda idanun mutane amma yanzu da ya biyo su wannan gidan ya bada kuɗin sai ta fahimci cewar ba wai don riya yake yi ba.
Yau ya kama kwana bakwai da mutuwar Zahraddin, tsawon kwanakin nan bai taɓa fashin zuwa ba, kullum sai ya je, sannan idan zai je sai ya tafi musu da abubuwan buƙata da na motsa baki. Hajiya Ramla ma ta koma ranar kwana biyar da kuma ranar kwana bakwai, inda shi ne ya faɗawa direba ya kaisu ita da yara tun da bata ma san sun tashi daga gidan ba sai ranar da ta ce za ta je yake faɗa mata ta koma gidansu, sannan kuma bai faɗa mata cewar mai gidan ne ya tashe su saboda basu bada kuɗi ba sannan bai sanar da ita ya biya kuɗin ba, shi kwata-kwata ma bai mata maganar abun da ya danganci su Hasiyar ba.
Ranar da Zahraddin ya cika kwana ashirin cif da mutuwa, da yamma suna zaune a tsakar gidan, suna ɗan taɓa hira, don yanzu mutuwar ta fara bin jiki. Sannan basu da wata matsala ta abinci saboda duk abin da babu Abba yana kawowa. Sallamar da ya yj ya sanya Zainaba amsa masa ak masa iso ya shigo, mahaifiyar Hasiyanda ta fito daga banɗaki riƙe da buta cike da nuna kulawa da kuma washe baki ta ce
"Haba Abdulsalam kai yanzu gidan nan sai ka tsaya neman izinin shigowa, ai an zama ɗaya daga ka yi sallama an amsa kawau ka shigo kanka tsaye" Yana gyara babbar rigarsa ya ce
"Daman saboda umarnin ubangiji a kan yin sallama tare da neman izini shi ya sa nake yi"
Tan zama a kan tabarma ta ce
"Ka fini gaskiya" Ƴar dariya yi ya zauna kan tabarmar da aka shimfiɗa yana ta ɗan kalle kalle ganin bai ga sanyin idaniyar tasa ba.
Bayan an gaisa, yaran ma sun gaishe da shi ya yi gyaran murya ya ce
"Daman Akwai makarantar da zan saka su Zainaba" Ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ciro mukulli fa ajiye a gabanta ya ce..
"Wannan sabin gidan da na siya muku ne za ku koma an zuba muku komai na buƙata har da kayan abinci"
*** [7/20, 6:48 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH
Daga marubuciyar
Ruwa cikin cokali Uwar agola Malamin bogi ƙazamin miji Yar zaman wanka Ruɓaɓɓiyar igiya Ƙara,in inna delu Bonono Ci ma zaune Ƴan adaidaira sahu Jalli joga Ungozoma Ƴar ƙanwata, Beelal Da sauransu. ***