KIBIYA A IDO

7

by @mamanafrah3028

*NURIYYA*

Kaka da take kallon su ta buɗe baki ta ce

"Nuryn Ammar"Kasancewar ba su san ta zo wajen ba sai suka waiwayo lokacin kowa da fara,a shimfiɗe a fuskarsa. Nuriyya ta ce

"Kaka" Kaka ta mata hararar wasa ta ce

"Ni babu ruwana da ke ai, tun da idan har za ki zo gidan nan sau dubu bakya shiga inda nake sai dai ki zauna a ƙofar ɗakin Yayanki Ammar har sai ya dawo saboda ki nuna min ƙoƙon usulin shi kila fara sani kafin ni, idan ba ni na ji motsinki ko kukanki a soron gidan nan na fito ba ba za ki shiga ba sai dai idan kin yi zaman kin ga gaji bai dawo ba shi ne za ki shiga ki tambayeni inda yake, da yake ni ba zan miki maganin abin da kike buƙata ba ko?" Ta kai ƙarshen maganar tana naɗe gannayenta a ƙirji ta zuba musu ido.

Nuriyya tsabar kunya sai ta sunkuyar da kai tana ƙunshe dariyarta, don tana son irin yanayin nan da ake ƴar tsama tsakanin ta da Kaka ta gansu kowa yana dariya tana jin farinciki a gidansu su Ammar, gashi dai tana ganin gidansu marar kyau ne sannan abincin su ma sannan basu da motoci da ƙaton gidan kamar gidansu amma kuma farncikinta yana wanzuwa ne a wajensu sau tari sai ta ji daman nan ne gidansu.

Ammar ne ya yi karaf ya ce

"Ai daman yanzun ma shirin shiga cikin gidan take yi sai na zo" Ya faɗa yana kallon Kaka. Kaka ta harare shi shi ɗin ma ta ce

"Rufe min baji sarkin ƴan son kai, ai ni wariyar launin fatar da kuke nuna min ta isheni, gashi daga kai har ita bakwa son laifin junanku babu wanda zai faɗi laifin ɗaya sai ɗaya ya kare shi" Nuriyya ta ɗago kai ta kalle Ammar suka kwashe da dariya.

Kaka ta ce

"Dan ma dai ni kakar ku ce daman da uwa ce cewa zan yi kun mayar da ni kakarku" Ta faɗa tana sunkuyawa ta ɗauki kwalin da ya zo da shi, ta juya tana faɗin

"Za ku gamu da ni duk zan yi maganinku" Tsaye ya miƙe daga tsugunnon da ya yi a gabanta, yana riƙe da hannunta suka marawa Kaka baya, duk da tana jin yunwa amma ɗan farincikin nan da ta yi sai ta ji duk ta daina jin yunwar sosai. A kan tabarma suka zauna, Nuriyya tana ta masa surutu ya ce

"Ni dai bari na fara yin wanka Kaka wannan yawon da nake a rana sai na yi ta tin gumi" Kaka da take zuba ruwan zafi a jug za ta haɗa shayin ta juyo tana kallonsa da tausayawa.

Ruwan wankan ya fara zubawa, ya ga ya kusa ƙarewa ma, haka ya shiga wankan ya bar su Nuriyya tana ba Kaka labarin yadda malam a islamiyya ya mata bulala da bata bada kuɗin makaranta ba ya kore ta.

Kaka ta zo ta zauna a kusa da ita a kan tabarmar, tana jera kofina guda uku ta ce

"Haba shi ma malamin nan naku ban da ɗaukan alhaki, ta yaya zai miki bulalar rashin biyan kuɗin makaranta, ai ba laifinki bane, shi yaro ba sai an bashi kudin a gida zai kai makarantar ba" Ta faɗa tana tsiyayawa Nuriyya shayin ta miƙa mata ta bata biredin amma sai ta ƙi karɓa, Kaka tanyi saroro tana kallon ta ta ce

"Ya ina baki ba za ki karɓa ki ci ba, bayan kuma daga ganinki ma yunwa kike ji?" Nuriyya ta ce

"Ki bari Yaya ya fito daga wanka" Tsaki Kaka ta yi ta ce

"Kedai Nury Allah yayw miki wannan maƙon wallahi, a ce kina jin yunwa amma sai kin jira ya fito kin san shi da shegen daɗewa a wanka kamar zai canja fatar jikinsa" Baki ta zumɓura, Kaka ta mayar da biredin leda ta ƙulle ta gutsuri nata ta shiga ci

Ko a jikinta wai an tsikari kakkausa ta ce

"Shi fa Malam cewa yake babu ruwansa kowa ya faɗa a gidansu a bashi kuɗi ya kawo masa idan baka kawo ba laifinka ne, ni kuqa daman Yaya Ammar ne babana ke ce babata ko Kaka?" Ƙwallag ce ta taru a idanun Kaka bata ankara ba ta ji hawayen yana gangaro mata tsabar tausayin Nuriyyar.

Kasan furta komai ta yi sai ta tsinci kanta da gyaɗa mata kai" Ganin hakan Nuriyya ta ƙyalƙyale da dariyar farinciki.

Ammar yana fitowa ya nufi soro ɗakinsa ya je ya buɗe ɗakin ta canja kaya ya fito y nufo tsakar gidan, yana zuwa ya zauna yana cewa

"Kin sha naki?" Ya faɗa yana kallonta, Kaka ta ce

"Hauka take za ta sha, ai ta gwammace ta zauna yunwar take ƙwaƙular ƴaƴan hanjinta har sai lokacin da ka gama dirjar wannan fatar taka ka fito daga wankan" Bai yi magana ba illa murmushi da ya yi ya ɗakko ledar biredin, ya zuba shayin a kofi ɗaya, ya sake zubawa a ɗaya kofin ya miƙa mata ta karɓa ya gutsuwa biredin ya bata, Kaka tashi ta yi ta ɗakko wata ƙaramar silba mai ɗauke da dambun masa da ta yi ɗan kaɗan ne dama ta ajiye masa ta kawo musu ta ɗora cokali guda ɗaya ta dawo ta zauna.

Tana kallon yadda ake shan shayin shi dai sunan yana sha ne, saboda Nuriyya yake ta ƙarawa biredin tana ci, sosai take ci saboda yunwar, ita kuma ba lura take shi ba ci yake ba kawai kaɗan yake gutsura sai ya daɗe sannan yake ƙara ci. Nuriyya ce ta ci rabi da kwatan biren nasu, ganin ya shanye shayin ya miƙa mata nashi kofin ya ce

"Ungo shanye ni cikina ya cika kamar ya fashe" Ta ƙyalƙyale da dariya ta ce

"Yaya daman ciki tana fashewa" Dariyar yake shima ya ce

"Nima haka na ji ana faɗa ana cewa an ƙoshi ciki ya cika kamar zai fashe"

Nuriyya ta ce

"Kuma waye zai ɗinke maka?" Kaka ta tuntsurw da dariya ta ce

"Ku dai in kuka haɗu a wuri ɗaya kun ringa sanya mutum dariya ko bashi da niyyar yi"

Yana dariya ya ce

"Ke za ki ɗinke min"

Nury ta ce

"Sai dai Kaka ni nan ban iya ɗinki ba" Yana dariya ya janyo kwanon dambun ya buɗe ya yi bismilla ya fara ci, ya miƙa mata cokalin ta ci ta miƙa masa, ya ci ya sake miƙa mata cokalin ta ce

"Ni dai na ƙoshi" Ta faɗa tana miƙo cokalin gabansa, ya san daman tun da ta sha shayin da yawa ba za ta ci dambun ba, haka ya shiga ci ita kuma suna hira da Kaka har ya kammala.

Ko da ya gama ya miƙe tsaye yana hamdala ita ma ta miƙe ya kalle ta ya ce

"Mu je in raka ki gida, so nake na dawo na yi ɗaukan ruwa" Ta noƙe kafaɗa ta ce

"Nima ɗaukan ruwan zan yi, taya ka zan yi ai" Ya girgiza kai ya ce

"A,a dare ya yi, kawai mu je in raka ki" Baki ta zumɓura ta tsaya"

Kaka ta ce

"Ki je ya raka ki gida, kin san wannan mai gadin kar ta hana ki shiga fa" Ta yi narai-narai da ido ta ce

"Ni a nan gidan zan kwana"

Kaka ta ce

"A'a Nury ki rufa mana asiri ki je ya raka ki gida" Ta ja ta tsaya babu alamar za ta je a rakatan. Ya haɗe rai ya ce

"To ki zauna ki kwana a nan ɗin, amma dai ni ba zan kaiwa malam kuɗin watan ba tun da bakya jin magana, in ya so goben sai ya sake miki bulalar" Kasancewarta mai son karatu ta ce

"A,a zan tafi Yaya Ammar ka rakani, ai goben in dai ba a kai kuɗin ba ba zan je bama saboda ya ce duk wanda vai kawo ba idan ya je sai ya masa bulala zai kora shi gida, ko aji mutum ba zai shiga ba, ba na so a yi mana ɗori a wuce ni in kasa bada harda" Dariya suka yi daga Kaka har Ammar saboda ya san daman ya kamo lagonta.

Hannunta ɗaya a hannun Ammar ɗayan kuma ta ɗaga tana yi wa Kaka bye-bye ta ce

"Sai da safe Kaka" Kaka ta ce

"Allah tashe mu lafiya Nury"

Nury ta ce

"Amin" Fita suka yi suka kama hanyar gidan su Nury suna tafiya sun ta zance abinsu, har suka je ƙofar gidan, yana ƙoƙarin janye hannunsa ya ce

"Ki shiga gida sai da safe Nury" Ta ƙanƙame hannunsa ta ce

"Ni dai sai ka raka ni har cikim gidan, ka kaini ƙofar ɗakina in na shiga sai ka tafi"

Ya girgiza kai ya ce

"So kike a saka mai gadi da ma,aikatan gidanku su karya min ƙafa in dawo gurgu" Dariya ta ƙyalƙyale sosai tana dariyar ta ce

"Ni kuwa in muna tafiya sai in ke gudu ina barinka a baya tun da baka da ƙafafu" Dariya ya yi ta dungure mata goshi ya ce

"Ba zan shiga bama bare kike guduwa kina barina a baya in an karya min ƙafar"

Dariya suka yi su duka ya ce

"Je ki shiga ina so in je in ɗakko ruwa"

Cewa ta yi shi zai buɗe mata ƙofar, haka ya ja hannunta suka je har bakin ƙofar ya saka hannu gabansa yana faɗuwa don shi a kan kansa ba ya jin tsoron komai amma yana tsoro ya yi abin da za a cutar da Nury. Yana turawa kuwa idanunsa suka sauka a kan mai gadi da yake zaune a kan benci da wasu samari guda biyu, masu gidimar gidan, abinci suke ci suka zubowa su Ammar idanu, Ammar ya haɗe fuska kamar wani babba ya ɗauke kai, daman wancan Baba mai gadin shi ne suke amintawa da shi amma yanzu da baya nan kaf gidan ba ya ganin kan kowa da gashi.

Shiga gidan ta yi, tun da ta saka ƙafar ta a gidan sai ya ga yanayinta ya sauya, ta zama jikinta sanyi ƙalau tana tafiya a ɗarare, ko hannu bata ɗago masa ba, hasalima tun da ta fara tafiya bata juyo ba, shi kuma ya kasa sakin ƙofar kuma ya kasa tafiya, sai da ya saina hango ta, yana shirin rufe ƙofar ya ji mai gadi ya ce

"Kai mai kake a nan ne?" Ammar ya ƙara haɗe rai ya banka musu harara, ya juya ya saki ƙofar ta bugu da ƙarfi tare da bada ƙara. Daman ƙaramar ƙofar jikin get ɗin ya buɗe mata.

Juyawa ya yi ya kama hanya yana jin ƙunci a ransa, ya tsani ganin Nuriyya a damuwa, ya rasa mai ya sa wasu matan ba sa tsoron Allah. Ko da ya koma gidan ma Kaka ta ga yanayinsa ya sauya bata masa maganar komai ba, ya ɗauko bokoti ya fita yake ɗakko ruwan a famfon layin nasu wanda babu nisa da gidan.

Nuriyya kuwa ko da ta shiga tana sauri da alla-alla ta shiga ɗakinta ba tare da ta ci karo da Hajiya ba, abin da bata sani ba Hajiya tana sama a ɓangarenta tana kallon shigowarta, don daman tana ankare da dawowar Nuriyyar tun da ta san ta fita, lokacin sa ta ji ƙaran buɗe ƙaramar ƙofar get ɗin da sauri ta leƙa windown da yake ko yaya aka taɓa ƙofar sai ta yi ƙara, sannan kuma hankalinta yana kan ƙofar daman.

Tasowa ta yi cikin sauri ta leƙo, amma sai ta hangi Ammar ɗin a tsaye ta ga Nuriyya tana tafiya lafiya lau, ita a har kullum buri da fatan ta bai wuce a samu wani a titin ya lalata Nuriyyar ba, ko kara zuben nan da take fita da dare matsayinta na mace kuma ƙaramar yarinya da take ɗauke da yunwar da za a iya bata abinci a mata komai matsayinta na mace, a lalata mata rayuwa tana sane kuma haka take fata.

Amma sai ta ga babu abin da ya samu Nuriyyar.da kafin ma ta kai haka duk sanda ta fita ta dawo sai ta duba jikinta ta ga ko an taɓa ta amma sai ta ga tana nan yadda take!.

Wannan abin yana ƙona mata rai, ƙwafa ta yi tana cewa a fili

"A juri zuwa rafi watarana na san tulun zai fashe, ya yi raga-raga ma kuwa, muddin kina fita titi dole za a samu wani mai rangwamen imanin da son zuciya ya keta miki haddi, tun da shi wannan wawan yaron da kike zuwa wajensa da alama har yau bai balaga ba, shi ya sa amma nan gaba kaɗan na san komai zai tafi kamar yadda na tsara, a yadda zamanin nan ya lalace wasu ƙananan yaran tun basu tafasa ba suke ƙonewa, shi ma na san yana dab da fara kai kallonsa wajen da nake burin ya kai, sannan ya kwaɗaitu da abin da nake fatan ya kwaɗaitun da shi, har ya kai ga yin abin da zan ɗora hannuna a hanci na yi guɗa son raina, ai muddin ina numfashi Nuriyya sai kin tozarta sai kin zama abin tausayi, sai na nunawa tsohonki illar nunawa ɗa tsantsar so da kulawa, sai na nuna masa cewar ya yi sake ɗan zaki ya girma, zan nuna masa cewa ba ni Hajiya Hauwa'u ake nunawa ɗan wani so ina matsayin matar gida, ni duk wanda ya ci tuwo da ni ma ya tabbatarwa kansa miya ya sha yanzu wa gari ya waya? Tun ba a je ko ina ba ina nuna muku shayi ruwa ne, kuma wallahi, wallahi, wallahi, sai na mayar da soyayyar da ubanki yake miki tsantsar ƙiyayya kamar yadda na sanya a yanzu ya manta da wancan matsayin naki da kike da shi a wajensa!" Ta faɗa tana sakin labule windon da take tsaye ta juya ranta yana ƙuna.

*ASALIN LABARI*

Alhaji Rufa'i shi ne mahaifin Nuriyya, babban ɗan kasuwa ne wanda yake saro kaya daga ƙasashen waje yana shigowa da su gidan Nigeri'a. Lokacin yana ƙaramin ɗan kasuwa yana da shago ne a cikin kasuwa, saboda tun yana matashi ya taso da son kasuwanci kafin mahaifinsa ne yake tafiya da shi kasuwa a ranakun da babu makaranta, idan kuma ranar da makaranta in ya dawo daga makaranta sai ya je kasuwar. Har dai mahaifinsa ya ɗora shi a kan kasuwancin nashi bayan Alhaji Rufa'in ya yi aure.

Matarsa sunan ta Hadiza ita ce mahaifiyar Nuriyya, auren soyayya suka yi irin soyayyar da kowa ya tabbatarwa abokin rayuwarsa cewa da shi zai rayu in babu ɗaya rayuwar ɗaya tana cikin halin ƙaƙanika yi. Bayan sun yi aure da wata takwas Hadiza ta samu ciki, wani irin so da kulawa yake nuna mata, ba ta barin ta yi komai da kanta tun da lokacin da bai tunbatsa ya yi arziƙi haka ba sai dai suna da rufin asiri sannan babu abin da ta nema ta rasa duk abin da take so yana mata, duk abin da take so cin yana ajiye mata, wani ma kafin ta furta tana so ya tanadar mata da shi.

Hadiza ta gama sadaukarwa cewa Rufa'i ne rayuwarta gabaɗaya, sannan ta alƙanwartawa kanta cewar daga shi ba za ta iya rayuwa da wani namiji ba ko da a ce wata ƙaddara da bata cikin zato ko tsammani ta faru.

A haka har cikin da take ɗauke da shi ya girma ya isa haihuwa. Daga lokacin ya daina fita yaran shagonsa yake bari a kasuwar don ba ya so ya yi nisa da ita haihuwar ta zo wani abu ya same ta. Kulwa da soyayya yake nuna mata, idan tana gidan su zauna su yj ta labarin irin kulawa da soyayyar da za su ba abin da za a haifa, yana nuna irin gatan da zai nuna musu ita da abin da za ta haifa masa.

Ana gobe za ta haihu suna zaune da dare suna hira bayan sun kammala cin abinci ya dube ta ya ce

"Na matsu ki haihu, ko kya huta da wannan zama dakyar tashi dakyar ɗin" Ya faɗa cike da tausayawa.

Ta ɗora hannunta a kan hannunsa ta ce

"Ita fa haihuwa lokaci ne da ita, daga lokacin fitowar ɗan duniya ya yi to fa za ka ga naƙuda ta tashi, babu makawa sai an haife shi, don haihuwa lokaci gare ta kamar dai yadda mutuwa take da lokaci, idan lokacin mutum ya yi sai ka ga ya tafi ko da ya shirya ko kuma bai shirya ba" Ya ɗora hannunsa ɗaya a saman hannunta da ta ɗora a ɗaya hannunsa ya kafe ta da ido ya ce

"Ni ban san mai ya sa a rayuwa ba na son zancen mutuwa ba, abu ɗaya nake tunawa wataran sai mutuwa ta ce xa ta raba mu fa ko?" Ya faɗa yana kafe fuskarta da ido.

Murmushi ta yi wushiryarta ta bayyana ta ce

"To mutuwa ai dole ce, duk wanda ka ga bai mutu ba lokacinsa ne bai yi ba" Hannunsa ya ɗauke daga samab natan ya ce

"Ki daina faɗa, ni na fi so a ce duk ranar da mutuwa za ta ɗauke ɗaya daga cikinmu ta haɗa mu duka ta ɗaukemu ni dai a ɓangarena wannan ne salamar da zan samu"

Idanunta ne suka kawo ƙwalla, ita dai a tsawon rayuwarta bata taɓa ji ko ganin mijin da yake so da ƙaunar matarsa kamar ya haɗiye ta kamar mijinta ba, ƙauna iya ƙauna irin ƙaunar da babu algus a cikinta. Kullum buri da fatan ta Allah sa ƴaƴan da za ta haifa su samu masu son su kamar yadda mahaifinsu yake sonta, duk da ta san zai yi wahala su samu fiye da soyayyar da mahaifinsu yake mata, saboda idan aka samu fiye da hakan tana ganin son zai yi yawa.

Tana kallonsa ta ce

"In sha Allahu, mutuwa za ta mana jinkiri, zuwa lokacin da za mu ga tsatsonmu, mu tara zuri,a mu basu tarbiya kulawa, sannan idan za ta ɗauke mu a lokacin ta ɗauke mu rana ɗaya lokaci ɗaya" Ta faɗa tana kallonsa har lokacin shi ɗin ma bai ɗauke idanunsa daga gare ta ba ya ce

"Idan son samu ne a saka mu a kabari ɗaya, duk da ba a yi haka" Su duka hawaye ne yake sirnano musu.

Washe gari da asuba bayan ya dawo daga masallaci tana kan sallaya tana jan carbi, yana ƙoƙarin cire jallabiyarsa sai ya ji ta ce

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da sauri ya yi wurgi da jallabiyar ya yi wajenta da gudu yana cewa

"Mene ne?"

Tana riƙe da mararta ta ce

"Marata, marata ce ta yi wani irin murɗawa ta ɗaure mini ciwo take min kamar za ta bar jikina".

_MUHAMMAD_

Ɓangaren ta ya nufa yana jin sanyi a ransa, yana shiga ya samu ta kulle bedroom ɗin da take ciki, ƙwanƙwasawa ya yi lokacin har ta cire mayafintana shirin ajiyewa ta ce

"Waye?"

Ya ce

"Waye zai zo a daidai lokacin nan in ba ni ba, ni ne na zo na ga lafiyarki na tambayi yadda kika dawo" Ƙaramin ɓoyayyan tsaki ta ja ba tare da ya ji tsakin ba, daman ba son ya ji ta yi ba, ta yi ne don yadda ta ji haushin zuwansa.

Sai da ta jim kamar wacce yake magana da bango, tamkar ba amsar za ta bashi ba a taƙaice ta ce

"Ina zuwa kayana zan cire dawowata kenan"

Da sauri ya ce

"Kar ki cire kayan don Allah, ki buɗe"

Ta ce

"Ka jirani ina zuwa" Ya san halinta sai ta cire kayan, tun da ba wannan ne karon farko da yake zuwa tarɓar kwalliyaerta ina ta dawo ba, bai san mai ya sa bata ƙaunar ya ga kwalliyar ba, bayan kuma ba yi take yi ba idan tana gidan.

Jin bata buɗe ba, ya sa ya ce

"Wayyo Allah, wayyo Allah nah" Ya faɗa cikin wata irin murya,

Ɗifff ta yi rana ɗan zaro idanu a zuciyarta wani daɗi ya zuyarce ta tana fatan Allah sa wa,adinsa ne ya yi ta ci gadonsa tun da dai shi ba ɗa gare shi ba sai wancan tsohuwar uwar tasa da tana iya sakawa a ƙara mata gudu zuwa lahira, ta ci karen ta babu babbaka. Da hanzari ta taho tana faɗin

"Alhaji lafiya" Ta faɗa tana saka hannu ta kama mukullin ta buɗe ƙofar, Alhaji Muhammad wanda ya dawo dab da ƙofar ya yi shirin ta buɗe ya shige, ya shiga danne dariyarsa yana jin daɗi a ransa domin gani yake ta yi wannan ne don nuba soyayya da kulawa gare shi saboda yana jin ruɗewa a yanayin maganar da ta yi.

A zuciyarsa ya ce

"Ashe dai tana sona kawai ɓoyewa ne take yi" Ya faɗa yana jiran fitowar ta. A tunaninta idan ta buɗe za ta ganshi zube a wajen anna tana buɗe ƙofar kafin ta gama tantancewa sai ganinsa ta yi ya rungumota ya jata cikin ɗakin ya mayar da ƙofae ya rufe yana ƙyalƙyala dariya.

Wani takaici ne ya cika ta.

*** [7/22, 5:04 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH