KIBIYA A IDO

8

by @mamanafrah3028

*HASIYA*

Fitowarta kenan daga ɗaki wannan maganar da ya yi ta sauka a tsakiyar dodon kunenta, gabanta ne ya buga da ƙarfi haka kawai sai ta ji wani iri, abu na farko da ya sanya ta jin yayanyinta ya sauya shi ne, lokacin mai gidanta yana raye, haka ake biyo ƴaƴanta kuɗin makaranta amma saboda halin rayuwa da babu sai ya zamana har wani term ɗin ya zagayo amma bai biya ba, daga baya da kuɗin suka masa yawa tun mai makarantar yana masa uzuri har ya kore su. A lokacin ya ce zai je wajen Abdulsalam ya ranta masa amma ya ce bashj da kuɗi a ƙarshe ya yanke shawarar cire yaran daga makarantar kuɗi ya mayar da su makaratar gwamnati saboda babu yadda ya iya sai dai dole!

Amma a ce yau Abdulsalam yana batun saka su a makaranta? Sannan wai har da mukullin gidan da ya siya musu. Shi da a baya ko gidansu bai iya biya musu haya ba.

Haka ta ƙaraso gaban su ta zauna jikinta sanyi ƙalau ta shiga gaishe shi ya amsa yana fara,a tare da tambayarta ƙarin haƙuri ya ɗora da basihar take kwantar da hankalinta tana yi wa Zahraddin ɗin addu,a wansa yana faɗar hakan ne don ta kwantar masa da hankalinta saboda ba ya son ganinta cikin damuwa.

Muryar mahaifiyarta ce ta katse ta da faɗin

'Hasiya kin ga abin arziƙin da aminin mijinki ya mana ko? Ai tsakaninmu da Abdulsalam sai godiya da addu,a"

Hasiya ta ce

"Haƙiƙa ubangiji ne kaɗan zai saka masa da alkairi, don shi dai ya yi zumunci"

Yaji daɗin yadda suka nuna jin daɗin su.

Washe gari Ramla da bata san wainar da ake toyawa ba, ta kira Hasiya a waya take sanar da ita za ta zo ta gansu, da to ta amsa mata tana nuna jin daɗin zuwan nata, ita ma tana farincikin zuwa wajan nata, saboda daman sun shaƙu dalilin mazajensu daga baya ne da Abba yake ta mata mitar ƙawancen nasu don lokacin ya fara miƙe ƙafa a cikin arziƙi.

Bai hana su ba, tun da ya san va za ta san abin da ya yi musu ba sai dai yana fatan kar su faɗa mata ya siya musu gida, ta sanya ya san halinta ba za ta yi baƙinciki ba amma ya san ta sai ta tuhume sa domin a baya ya sha nusar da shi a kan kyautatawa abokin nashi amma ya yi biris da ita.

Ta siyawa su Zainaba kaya sakawa da kuma ɗan abin motsa baki, sannan ta siyawa mahaifiyar Hasiyar turmin atamfa.

Ko da direba ya ajiye su a ƙofar gidan, yaran ta sanya suka ɗakko ɓanyan ledojin da ta yi musu siyayyar. Sun shigowa Nasira da Zainaba suka tafj da ɗan gudu suka riƙo hannun Mama Ramla sun ta murna abin su. Ɗaki suka tafi su da su Humaita ita kuma suka zauna da su Hasiyar a tsakar gida. Suna ɗan taɓa hira da jajanta lamuran rayuwa da wannan yawan mace-macen da ake mutuwar fuju,a.

Sai gabannin magriba direba ya zo ɗaukansu, har ƙofar gida su Nasira suka rako su, kowa ya shiga mota suna ɗaga musu hannu. Amma tsawon zaman da ta yi a gidan daga Hasiya har mahaifiyarta babhhha Bayan kwana biyu suka tattara suka koma sabon gidan, don ko ƴan unguwa basu faɗawa ba. Wai in ji Dada mahaifiyar Hasiya kar hassada ta shiga ciki wani mai mugun bakin ya saka tafiya sabon gidan fasuwa.

Gida ne madaidaici ƙaton falo ne mao ɗauke da ɗakuna uku kowanne da banɗaki a ciki, Dada ta ɗauki ɗaya Hasiya ɗaya ɗayan kuma su Nasira, an zuba komai a gidan matsakaita ba wai masu tsada ba. A tsakar gida ma akwai banɗaki sai kuma kicin tun da suka shigo gidan Dada baki ya kasa rufuwa sai albarka take sanyawa Abba tana ta yabawa da amintar da take tsakaninsa da abokinsa tun da gashi har bayan ransa amma yana tsayawa tsayin daka don ganin iyalan basu wulaƙanta ba, ta manta da lokacin da ya mutu take faɗin maci amana ne ba ya amfana masa komai abokantar bata da amfani, tun da ba ya tsinana masa komai amma yanzu saboda ya buɗe musu ido da abin duniya gashi nan har ta manta da waɗancan maganganun.

A ranar da suka koma daman shi ya aika direba ya kai su, sannan daman ba wasu kaya ne da su ba ɗan sauran tarkacen ma Dada duk ta haɗa ta siyar da su. Bai zo gidan ba sai washe gari ya zo ya gansu sosai ya ji nauyin zuciyarsa ya rago ko ba komai a ƙalla Hasiyarsa tana zaune a muhalli mai kyau duk da ya fi so ya ganta a wuri mafi kyau wato kusa da shi, cikin gidansa kenan idan ya ƙulla kyakkyawar mu,amala a tsakaninsu wato aure!.

Kwanci tashi asarar mai rai, Hasiya ta cika gama takabarta. Tun da suka koma sabon gidan Mama Ramla bata samu ta je ba abubuwa duk sun sha kanta amma ganin lokacin cikar iddarta ya yi ta ce za ta je ta gansu. Da farko ta da tambaye shi zuwan cewa ya yi ai Hasiyar ba sa gari ta tafi dangin mahaifiyarta tun washe garin gama iddar ta. Ta yi mamakin kasancewar suna waya lokaci zuwa lokaci amma bata ce mata za ta yi tafiya ba duk da ta lura yanzu kusancin nasu ba kamar da ba. A lokacin da yake sanar da ita maganar ta karance shi tsaf sai take ganin kamar dai akwai abun da yake ɓoyewa wato kamar dai ita ce ba ya so ta je, a nata tunanin irin waccan ɗabi,ar tashi ce ta rashin son kusantar inda abokinsa yake can ma yana raye bare yanzu da take ganin ƙasa ta rufe idanunsa zaton ta ko kaɗan ba ya son ta ci gaba da mu,amala da iyalan abokin nashi, ta ɗauka kawai yana zon yanke alaƙar ne.

Hakan ya sa ta ce

"Amma Abbab Humaira ko da kai ba za ka je ba, ni mai ya sa za ka hana ni zuwa kar ka manta mun saba da Hasiya da yaranta don Allah karka datse igiyar alaƙarmu" A fili ya ce

"Ni ba haka nake nufi ba, tun da kika ji na faɗa ai bata nan ɗin, nima na ji wannan labarin ne wajen wani maƙocinsu da muka haɗu" Ya faɗa a son ganin ya nuna mata shi ko kaɗan ba ya ma sanin halin da suke bare ya nuna mata yana zamewa yana zuwa.

A zuciyarsa kuma ya ce

',In dai wannan alƙar ce za ta ɗore tun da za ta dawo ku zauna a inuwar miji ɗaya ki shiga ɗakin miji ki fito ita ma ta maye gurbinki a ganina wannan kusancin shi ne mafi girma!'

Bayan kaana biyu yana ta tunanin yadda zai faɗa mata ta je saboda kar ta zargi wani abu amma ya san Ramla da shegen wayo da kuɓa hangen nesa tamkar mikiya, hakan ya sa yake ganin tana zuwa wannan sabon gidan za ta gane shi ya siya musu tun da dai daga Dada har Hasiya babu wanda yake da wani kuɗi da zai sayi gida kamar wannan, sannan uwa uba shi kansa Zahraddin babu wani abu na gado da ya tafi ya bar musu da za su iya sayan ko da akurkin kaji ne bare kuma gida.

Da yamma tana zaune a kan kujera a falonta tana azkar na yamma ya shigo fuskar nan a haɗe kamar hadarin gabas ba yabo ba fallasa, wannan yanayi ne da ta saba ganinsa a ciki don haka wannan ya zame mata jiki ko ta ganshi a wannan yanayin abun bai damunta in da sabo ai ta saba.

Bai zauna ba ya ce

"Gobe ki shirya direba ya kai ki gidan su Hasiyar, wani ɗan uwansu ya saya musu gida, sun tashi daga wancan gidan da kika sani" Ɗan jim ta yi kamar dai irin mamakin nan don wani abu ne ya ɗarsu a ranta mai kamar mamakin amma sai ta ce

"Ba gidan mahaifiyarta da suka koma ba ai na sha zuwa fa" Dakewa ya yi ba ya so ya bar wata ƙofa duk ƙanƙantar ta da za ta iya gane wani lagonsa na ƙaryar da ya shirga mata ya ce

"Sabon gida fa na ce, to ke a tunanin ki baki san dare ɗaya Allah ya kan yi makaho ba? To shi arziƙi ko mallakar wani abu ba ya kusa ba ya ga nesa a wajen ubangiji" Da sauri ta ce

"Allah sarki, ba abin da nake nufi ba kenan, ai na san babu abin da ya gagari ubangiji mabuwayi, sannan ni shaida ce a kan sauyin rayuwar da ya mana, daga duhu zuwa haske, daga baƙin talauci zuwa arziƙi mai yalwa, daga wancan lokacin da komai yake gagararmu zuwa yanxu da...

Jin za ta tuno da baya shi kuma ba ya son ta tuna duk wasu abubuwan da suka shuɗe, gani yake kamar dai tana son tuna masa irin faɗi tashi, da kuma gwagwarmayar da ta yi rawar gani a cikin rayuwarsa, irin jajircewa da namijin ƙoƙarin da ba kowace mace ce za ta yi wa namiji shi ba, idan tana irin wannan furucin sai yake ganin kamar tana son nuna butulci ya mata da yake nuna har yanzu ita ba komai ba ce kuma bata da wata daraja ko kima a wajensa, wanda shi kansa idan za a bashi damar rubuta sunayen mutane mafi daraja, mafi halacci mafi komai da komai a cikin rayuwarsa ya san Ramla tana sahun farko!.

Juyawa ya yi yana fara takawa ya ce

"Direba ya san gidan, ni ban ma san wace unguwar yake ba, ya dai ce ya taɓa ganinta a unguwar za ta shiga gidan" Iya haka ya faɗa ya fita. Ta yi shiru na kamar minti biyu duk da maganganun sun cunkushe ta kasa gane ma mene ne, amma kuma sanin waye mijinta ba ya son mu,amala da abolin nashi tun yana raye saboda ganin ya masa fintinkau wato ya hau tudun tsira daga talauci zuwa arziƙi.

Washe gari yaran ma suna makaranta ta tafi, da sha tara ta arziƙi don ko a baya lokacin suna cikin rayuwar takauci tana tallafawa Hasiya da abubuwan da ba a rasa ba, hatta kayan sawa Mama Ramla ta sha ɗaukan kayanta masu ɗan dama-dama ta ba Hasiya don wani lokacin kayan Hasiya duk sun kuɗe har suna yagewa a ƙara ɗinkewa, hatta kayan su Humaira tana ba su Nasira duk da su ɗin ma ba wasu kayan kirki ba ne gare su amma don ganin dai ta tallafa musu. Ajiyar zuciya ta sauke a zuciyarta tana faɗin

'Rayuwa kenan, Alhamdulillah bikulli ni,imatika ya rabb' A ƙofar wani matsakaicin gida mai kyau ta ga direban ya ja ya tsaya, ta kalle shi da alamar tambaya ta ce

"Ina ne gidan?" Ya ce

"Hajiya wannan ne gidan ai" Ya faɗa yana mata nuni da yatsan sa. Kai ta ɗaga ta kalli gidan, ta ganshi sabo dal ya sha fenti ga ƙwayaye nan suna aiki .

Ta ce

"Kai ya aka yi ka sani?" ,

Ya ce

"Hajiya da na kawo yallaɓai na sani" Ido ɗaya ta ƙanƙance kasancewar direban ba ita yake kallo ba, lokaci ɗaya tambayoyi barkatai suka fara cunkuso a ƙwaƙwalwarta, maganar da ya faɗa mata jiya na cewar wani ne ya faɗa masa ta faɗo mata, a gefe ɗaya ta tuna ranar da ya ce ba sa gari. Ɗan taɓe baki ta yi ta watsar da maganar don ta san halin mijinta sarai daman wani lokacin zancensa rabi ruwa rabi iska ne

Bata ce komai ba ta buɗe ta zuro ƙafafunta ta juya ta ɗakko jakarta tana gyara yafa mayafin ta, ta fito. Don ita ba kasafai take jiran direba ya buɗe mata mota ba, ba ta manta lokacin da take hawa napep ko motar haya yanzu a ganinta don ta samu motar gida ba sai ta jira ana wani buɗe mata mota ba tun da ita ma da hannunta.

Da sauri ya fito ya fara fitowa da kayan, ita kuma ta fara takawa zuwa cikin gidan, tun da bata sanar da su zuwanta ba saboda ta yi ta kiran wayar Hasiyar a rufe. Sallama ta yi daga soron gidan da yake ƙaramar ƙofa ce a gidan ma ba get ba.

Hasiya da take zaune a baranda tana tsifa ta ji muryar Ramla dan dim ta yi gabanta ya faɗi, tana tunanin ko dai ta ji mijinta ya siya musu gida yana hidima da su har ya saka yaran a private school.

Kafin ra gama wannan tunanin ta ji sallamar Mama Ramlar ta katse mata tunanin, kafin ta amsa mata Dada da ta fito daga ɗaki ta yi karaf ta amsa. Don ita ko a jikinta wai an tsikari kakkausa a ganinta duk abubuwan da Abdulsalam ɗin ya musu sun cancanta ne a yi musu saboda aminta da take tsakanin abokan biyu.

Shigowa ta yi cikin nutsuwarta da takunta mai nuna sanin darajar kai. Hasiya ta washe baki tana faɗin

"Oyoyo Mama Ramla yau muna da babbar bakuwa" Ta faɗa tana ɗaure kanta da ɗankwalinta ta tashi ta je wajen famfo ta saka sabulu ta wanke hannun ta. Lokacin ta ƙaraso tsakiyar gidan tana ta dariya haɗe da ƙarewa gidan kallo.

Tana ɗan kauda kai gefe ta ce.

"Ni ai fushi nake da bakya ko nema na, maimakon da kika gama takabar ki je ki ganni shi ne kika ƙi zuwa" ,Ita ma dariyar ta yi ta ƙarasa Dada tana mata iso, sallamar direban ce ta dakatar da Hasiya shiga ɗakin ta tsaya ta amsa masa tare da masa iso ya shigo ya ajiye ledojin ta juya ya sake kawo wata ledar guda ɗaya ya fita.

Falon ta shiga tv tana aikin ta, kasancewar ma babu nepa amma akwai sola, shigowa ta yi a ɗan ɗarare bata dai saki jiki ba kamar yadda suka saba, don tunanin ta abokin mijin nata ya faɗawa Ramlar cewar ya siya musu gida ya saka yaran a makaranta a ƙalla dai ko ba don Ramlar ya yi ba ai da ta kira ta ta faɗa mata. Ramla kuwa bata kawo komai ba suka gaisa cikin aminci, ta gaishe da Dada tana tambyar yaran aka ce suna makaranta, su ma da sula tambayi su Huamaira ta ce musu suna makaranta.

Ta yi wa Hasiya barkar kammala takaba cikin aminci tare da jajanta mata mutuwar da kuma yi masa addu,ar Allah sa yana cikin aminci. Suka amsa a tare da Dada. Nan ta ce ga kaya nan ba yawa ta faɗa suka shiga yi mata godiya sun faɗin bata gajiya da hidima ta ce babu komai.

Daga nan ta ce

"Ai ranar nan nake tambayar Abban Humaira zan zo ya ce min kin je dangin Dada gaishe su" Ɗan diriricewa Hasiya ta yi amma kuma ta yi kokarin dannewa ta ce

"Allah sarki, ashe ya faɗa miki"

Dada ta ce

"Eh ni na ce ta je ta gaishe su, kin san tun da suka zo gaisuwar nan ba a gaisa ba ita ma kuma in tana son zuwa wani lokacin kudon mota yake gagara"

Mama Ramla ta ce

",Allah sarki daman haka ne"

Ta ɗora da faɗin

",Ashe ɗan uwanku ya siya muku gida, Allah sanya alkairi"

Sai da Dada da Hasiya suka kalli juna amma sanin da Hasiya ta yi wa Ramla na cewar idan da ta san mijinta ne ya siya ba za ta ɓoye ba hakan ya sa ta amsa, Dada ma ta ce

"Ai kam ya yi kokari sai dai Allah biya shi" ,Su duka suka ce

"Amin"

Ta ce.

"Ai da na ce zan je can ɗin ne ya ce kun tashi shine yake faɗa min"

Dada ta ce

"Ai kam dai" Daga Dada har Hasiya suna mamakin dalilin da ya sa ya ɓoye cewar shi ya siya don haka ma basu faɗa mata cewar ya saka yaran a makarantar kuɗi ba, har da wanda yake kai su ya ɗakko su duk da babu wani nisa sosai.

Sai da ta yi sallar azzahar ta tafi, don ana cewar ta tsaya a gama abinci ma amma ta ce wata mata ce ta yi oder snacks shi ne take so ta je a haɗa mata, kasancewar shi ne sana,arta kuma tana samu sosai kasancewar Allah ya dafa mata ya saka mata albarka.

Sai bayaj tafiyar ta Dada da Hasiya suke ta maida magana a kan abin da Abba ya faɗawa matarsa ba su dai gane dalilin sheƙa ƙaryar da ya yi ba sai dai Dada ta ce gaskiya akwai wata a ƙasa duk da basu hango komai ba.

A ɓangaren Ramla kuwa ita babu komai a ranta don haka ma ko da ta ɗan ga alamun diriricewa a fuskar Hasiya lokacin da ta mata maganar gidan bata ɗauka cewar akwai wani abu ba, da yake ita ta fi mayar da hankali ga sana,arta da lamuran ƴaƴanta tun da mijin shi ba kasafai yake son ma a shiga lamarinsa ba.

Ɓangaren Abba, a ranar wata asabar ya siyo wani rantsatstsan zoben azurfa mai hoton zuciya a jiki, zoben yana cikin ɗan akwati ƙarami da ake sanya zobuna.

Lokacin da ya dawo ya buɗe drower ɗinsa ya saka akwatin, sai dai da ya shiga wanka ya fito zai ɗauki kaya sai ɗan akwatin ya faɗo kuma bai lura ba. Hakan ya sa ya yi alwalar la,asar ya fita masallaci yau zuciyarsa wasai yake ji zai fitar da abin da ya daɗe a zuciyarsa shekara da shekaru, duk da a wani sashe na zuciyarsa yana jin fargabar kar a samu akasin lissafi amma dai ya fi danganawa da cewar za a dace!.

Mama Ramla wacce ta shiga ɗakinsa za ta ajiye singlet ɗinsa da gajerunan wanduna. Ɗaya drower ɗin ta buɗe ta sanya su a ma,ajjin su. Ta tura murfin za ta rufe idanunta suka sauka a kan ƙaramin akwatin da yake ajiye a ƙasa. Ƙarasa rufewa drower ta yi, tana kallon ɗan akwatin ta sunkuya ta ɗauka idanunta suka sauka a kan kyakkyawan zoben da yake ta walwali abin sa tun daga ma cikin akwaitin ba tare da ta buɗe ba. Ido ɗaya ta ƙanƙance tana kallon zoben abubuwa barkatai suna mata yawo a kwanya, ta kasa gane dalilin wanzuwar zoben a ɗakin ta kasa gane mai zai yi da zobe shi da ba ma,aboncin sanya zobe ba. Sannan uwa uba hoton zuciyar da yake jiki shi yake alaƙanta zoben da cewar wataƙila na soyayya ne, tun da ta san halin mijinta da shegen son mata. Baki ta taɓe tana kawar da duk wani tunani daga zuciyarta, ta sunkuya ta ajiye ɗan akwatin a inda ta ɗauka ba tare da ta buɗe ba.

Fitowa ta yi daga ɗakin ta janyo ƙofar tana juyowa shi kuma ya kawo kai, suka yi kiciɓis da sauri ya ce

"Ramla mai kuma kike yi a ɗakina daga fita ta?" Tambayar ta zo mata a bazata don haka ta kalle shi ta ce.

"Abban Humaira don na shiga ɗakin naka kake tuhumata?" Kai ya kawar gefe yana faɗin

"To ai na ga yanxu na fita kuma baki zo ba sai da na fita" Ya faɗa yana ta tunanin kar dai ta ga zoben da ya ajiye a drower yana ma tunanin kar dai ta san yau yake da niyyar zuwa ya amayarwa da Hasiya ɗimbin soyayyar da zuciyarsa take mata, da kuma bayyana mata irin ƙudurin auren ta da yake da niyya a zuciyarsa ya kai ta gidansa su yi rayuwar mai ɗimbin tarihi!.

*ALHAJI RUFAI*

Jin furucin ta gabaɗaya ya rikice ya ce

"Ko dai haihuwar ce?" Ba ta samu damar bashi amsa ba kasancewat waninirin murɗawa da marar ta mata. Cikin hanzari ya yi wajen inda ya jefar da jallabiyar ya ɗauka ya saka da sauri garin sauri ma a baibai ya saka.

Da matar maƙocinsu suka tafi kai ta asibitin mijin nata yana tuƙawa. Tana ta murƙususu maƙociyarta yana ta faman mata sannu amma bata iya amsawa saboda zafin ciwon naƙudar da ya turnuƙe ta, abin ka da haihuwar fari. Alhaji Isma'il gabaɗaya ya rasa nutsuwarsa tamkar dai a jikinsa ciwon yake. A duniya ba ƙaramin so yake yi wa Hadiza ba yana ta roƙon Allah ya bashi tsawon rai da lafiya da wadata ya ci gaba da gwada mata gata ita da abin da za ta haifa musu, sai dai a halin da ake ciki yanzu ya fi damuwa da kuma addu,ar Allah ya sauke ta lafiya.

Ana zuwa aka shiga da ita ɗakin haihuwa, ko waya bai ɗakko ba shi ya sa ma ko gidan su Hadizar bai kira ba. Yana ta safa da marwa amma yana jiran a ce ta haihu shiru, duk ya shiga damuwa makociyarta kuwa kusan ita ma tana cikin tashin hankalin musamman idan ta tuna yadda naƙuda take fa wahala duk da tana xuwar wa wasu da sauƙi.

Sai wajen ƙarfe goma na safe, wata nurse ta fito tana faɗin ta haihu, sai dai fuskarta da alamar damuwa kasancewar tana son sanar da su cewar jini ya ɓalle mata. Alhaji Isma,il bai jira cewar ta ba ya yi cikin ɗakin a guje kana ganinsa ka san ba a hayyacinsa yake ba cike yake da fargaba. Ko da ya je an fito da ita an ɗora ta a wani gado an kewaye ta da labule ana ta ƙoƙarin tsayar da jinin, yana zuwa ya shige wurin kasancewar sai ka bi korido ne za ka shiga can cikin ɗakin inda sauran mata suke. Ganin babban likita da nurse guda biyu suna bata taimakon gaggawa.

Yana zuwa ya ce

"Hadiza" Lokacin ƙarfin ta ya ƙare garau idanunta suka yi ba ta amsa ba ta miƙo masa hannu, nurse ɗin tana ƙoƙarin dakatar da shi, likitan ya ce a ƙyale shi don shi tausayi ya bashi, kamar zararre haka yake, ko kaɗan ya ma manta da batun abin da ta haifa hankalinsa yana kanta.

Hannunsa ya saka a nata, ta masa murmushi tana lumshe idanunta ta buɗe, ya ce

"Sannu Hadiza"

" Likita ya ce za a ƙara mata jini"

Da sauri ya juyo har lokacin hannunsu sarƙe da na juna, ya ce

"Likita a ɗauki nawa" Kai likitan ya gyaɗa masa.

An ɗauki jininsa kenan sai ga ƴan uwan Hadiza sun zo, kowa hankalinsa tashe da ya ji an ce za a mata ƙarin jini duk da cewa likitan ya kwantar musu da hankali cewar jinin ma ya tsaya amma za a ƙara mata ne saboda ya zubar da jinin da yawa.

Ana cikin saka mata jinin da yake ya yi daidai da nata, sai kawai ta fara kalmar shahada, lokacin Alhaji Rufa'i yana tsaye a kanta hannunsa riƙe da nata, tun da ta fara kalmar shahadar nan gabansa yake wani irin bugawa, idanunsa suka firfito don ba ya son idanunsa su tabbatar da abin da yake zargi. Tun da ya ga idanunta sun kafe bai ma san yadda aka yi ya yanke jiki ya faɗi ba, har aka sallaci gawar ta amma yana kwance a asibiti bai san inda kansa yake ba bare ya san waye a kansa.

Sai washe gari da rana ya farfaɗo, da kiran sunanta ya farfaɗo sai dai ya samu mummunan labarin da ba zai taɓa iya mantawa da wannan rana da kuma mugun labarin mutuwar Hadiza ba wacce yake ji tamkar wani sashe na jikinsa, zai iya kiranta da ɓarin jikinsa saboda tsananin so da ƙauna amma mutuwa ta musu shigar sauri ta musu yankan ƙauna!.

Kuka yake tamkar ƙaramin yaro a gefe ɗaya yana ganin komai tamkar a mafarki. Ko da ya je makabarta dakyar aka ɓanɓare shi daga kan kabarinta.

Bayan ya dawo gidan, sai a sannan ne aka bashi ƴar da ta bari, ko da ya karɓe ta a take wasu zafafan hawaye suka sauka a dakalin fuskarsa. Yana kallon jaririyar da take kyakkyawa ajin farko wacce babu abin da ta bari na mahaifiyarta kamar su har ta ɓaci tamkar an tsaga kara, cikin kuka ya ce

"Ashe dai haihuwar nan ita ce silar barinki duniya, ashe abin da muka ci burin ma ke ba za ki ɗauke ta ko da a tafin hannunki ba ne, mai rabawa ta raba ku a cikin jikin ki kaɗai ta rayu, amma a duniya baku gana ba, Allah jikan ki da rahma Hadiza Allah sa aljanna ce makomarmu baki ɗaya, haƙiƙa na yi rashin da Allah kaɗai ne ya san iyakarsa" Ya faɗa yana kukan gabaɗaya mutanen wajen tausayinsa ya kama su, wasu kuma suka shiga share ƙwalla.

Tun daga wannan rana kullum da asuba sai ya je makabarta, ya je ya mata a ddu,a sannan ya yi ta surutu a kabarin yana faɗa mata irin kewa da kuma rashin da ya yi, da kuma jaddada mata da alƙarwanta mata cewar zai riƙe ƴarsu zai cike ata gubi rashin ta ba zai taɓa bari ta yi kukan rashin mahaifiya ba, in har yana raye ba zai taɓa barin hawaye su zuba a idanunta ba.

Tun daga wannan mutuwar Hadiza ya zamana ba ya iya nisa da Nuriyya, wannan sunan Hadiza ce ta zaɓe shi lokacin tana numfashi a doron duniya, ta ce idan mace ta haifa Nuriyya za ta saka mata saboda irin son da take yi wa sunan.

***

[7/25, 5:32 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH