KIBIYA A IDO

9

by @mamanafrah3028

*MAMA RAMLA*

Da mamaki take kallonsa ta ce

"Shi shiga ɗakin naka wani abu ne? Ko dai baka da gaskiya ne"

Jin furucinta ya sanya ya fara tunanin ko dai ta fara zargin wani abu ne da sauri cikin hargagin muryar nan tashi mai kamar da yana aman wuta ya ce

"Rashin gaskiya na me? Sai dai idan ko diddigina kike bi, amma ki sani ni Abdulsalam babu wata mace a duniya da tsoronta zai sanya na ɓoye mata wani abu, wallahi ba a yi ta ba" Ganin ya haƙiƙance ita kuma ko kaɗan bata son abin da zai saka mata ciwon kai hakan ya sa ta ce

"Ina da abin yi a ɓangarena" Ta faɗa tana fara tafiyarta cikin nutsuwa, da kallo ya bi ta yana faɗin

"Da dai ya fi miki, ai faɗa da aljani ba daɗi" Ko waiwayensa ba ta yi ba ta fice don ta ga kamar dai neman magana yake, ita kuma ta san borin kunya ne saboda kawai yana naɗe tabarmar kunya da hauka ne.

Da sauri ya shige ɗaki ya rufo har da saka mukulli. Yanz zuwa ya nufi inda ya yi ajiyar sai dai yana buɗewa ya ga inda ya ajiye zoben wayam, da sauri ya shiga ɗaɗɗaga kayan wajen ko dai ya manta ya tura ƙasan kaya amma dai babu alamar akwatin zobe a take zuciyarsa ta shiga kitsa masa cewar Mama Ramla ta ɗauke akwatin zoben hakan ya sa a take ya harzuƙa ba tare da wani dogon tunani ba ya juyo a fusace fuuuu kamar an koro shi. Ƙofar ya buɗe ya fito rai a matuƙar ɓace ya nufi sashen ta.

Mama kuwa lokacin da ta fito ta leƙa kicin ta samu Talatuwa tana wanke-wanke hakan ya sa ta wuce ɗakinta har ta zauna a falo sai dai ta tashi ta nufi bedroom. Tana zuwa ta zauna a bakin gado zuciyarta tana wasi wasi da faɗin

'Ni ban san mene ne tunanin Abban Humaira a kaina ba, mutum kamar wanda aka haɗa sho rayuwa da maƙiyiyarsa a gidan, tamkar ba auren soyayya muka yi ba, a nawa ganin ai na wuce wannan cin kashin da yake min tamkar wata mai neman wurin zama a zuciyarsa... Bankaɗo ƙofar da aka yi ne da ƙarfi ya sa ta dawo daga saƙar zucin da take ta zubawa ƙofar idanu, ganinsa kamar ya haɗiyi taɓarya wato ya tsaya ƙememe a kanta ya sa ta zubawa sarautar Allah ido.

Cike da wata murya mai kamar yana mata kashedi ya ce

"Ina abin da kika ɗauka mini a ɗaki?" Ya tambaya yana jifanta da kallon tuhuma ta kalle shi cikin sanyin hali ta ce

."Tsawon zamana da kai a gidan nan ka taɓa neman wani abu ka rasa ? Da har yau kake zargin na ɗaukar maka abu, shin mai kake tunanin na ɗauk... Kafin ta kai aya ya ce.

"Ina tambayarki kina tambayata, kuma ai ni ban ce ki dawo min da maganar tsawon zaman mu ba, maganar yau ɗaya tak nake ban ga abin da na ajiye ba"

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke ta ce

"Da da ka koma ka duba ma,ajjinka kafin ka ɗora wutae zargi a kaina ko ma a kan mai kake naganar duk da ban gama gane inda maganar ta dosa ba"

Yana nuna ta da yatsa alamar tuhuma ya ce

"Ya isheki Ramla!. Ki fito da abuna ki bani idan ba haka ba, ko mene ne ya biyo baya wallahi kar ki zargeni ki zargi kanki da kanki" Saroro ta yi da baki tana kallonsa, ta dafa gadon da hannuwanta biyu ta miƙe tsaye ta kalle shi ido cikin ido ta ce

"Na faɗa maka ni ban ɗauki komai ba, sannan bani da lokacin da zan ɗauki komai don haka kar ka ƙara jifana da cewar na ɗaukar maka abu, wannan abun kunya ne a gareni a ce na ɗauki abin da ba a bani ba, kuma ba nawa ba"

Da yatsan da manuniya ya nunata yana neman tsone mata ido ya ce

"Kina so ki ƙaryata ni ne? Shi ne wuyanki har ya yi kaurin da za ki tashi kina gwada tsayo da ni ki tsaya mini ƙiƙam kina ƙaryatani, ina so ki sani Ramla yanzu ba da ba ce, idan kuma kina taƙama da halaccin da kike tunanin kin yi min a rayuwa ne shi ya sa har kike nuna min wuyanki ya isa yanka, to ina so ki zayyano min duk abin da kika yi ni kuma zan biya ki, in ce dai shi ne taƙamar ki? Wato tallafin da kika min a shekarun baya da sadaukarwa da ko ma mene ne kike gani ai za a iya yin kuɗinsa a ganina kuɗi babu abin da ba sa siyawa ɗan adam"

Idanunta suka ciko da ƙwalla, amma ta sunkuyar da kanta ta yi ƙoƙari ta mayar da su, ba ta so rauninta ya bayyana a wannan gaɓar, duk da furucinsa ya sanya ta ji wani zafi da ɗaci a cikin ranta, saboda ya zarge ta da abin da ba ita ta furta ba, don yana ganin yanzu yana da arziƙi ɗagowa ta yi ta ce

"Na san kana da kuɗi amma ka sani kamar yadda na zauna da kai a baya, cikin halin rashi, to na zauna da kai saboda Allah ne, kuma duk abin da na yi na yi domin sa ne, don haka a yanzu a halin da ake ciki ba zan sauya daga wancan ɓigiren da nake kai ba, amma ka sani ni na san ba komai ne kuɗi yake siyansu ba saboda akwai abubuwa da yawa wanda kuɗi, matsayi, mulki ko sarauta ba sa ba mutum shi!"

Kallon tsaf yake mata zuciyarsa tana raya masa tamkar ya sanya ƙafa ya shure ta shi a yadda yake jinsa yanzu gani yake ko ita kanta sukutum zai iya biyan kuɗinta ya siye ta

Ƙwafa ya yi ya ce

"Wallahi ko dai ki fito min da abin da kika ɗauka ko ki yi da na sani !" Idanunta cikin nashi ta ce

"Kana ta faɗar abu, to shi abun bashi da suna, sannan in dai har a kan abin da ban aikata ba ne zan yi da na sani to ba na jin akwai abin da zan yi da na sanin sa!"

Juyawa ya yi ya yi wajen madubi, yana zuwa ya tsaya gaban madubin yana duban fuskarsa itama ta cikin madubin take ganin fuskarsa da take cike da ɓacin rai, ta madubib ya kalle ta ya ce

."Ai kin san abin da kika ɗauka, a kan mai zan ba kaina wahalar sai na faɗa miki mene ne , ashe bin diddigina kike shi ya sa ina fita kika je ɗakina kika ɗauka, yanzu kuma kike borin kunya, to zoben da kika ɗauka a ɗakina za ki bani" Ya faɗa yana juyowa ya miƙa mata tafin hannunsa na dama.

Murmushi ta yi mai ciwo, tana tunanin lallai namiji bashi da kunya, in ban da rashin ta ido har ita Ramla zai kalla ya ce ta bashi zobe, zoben da ta san daga gani ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba cewar wata macen ya siyawa zai kaiwa.

Idanu ta lumshe ta buɗe ta ce

"Allah sarki, wallahi na fi ƙarfin in ɗauki zobe, kuma ka sani kaya na kai na saka maka a drower ba wai na je bin diddiginka bane kai ka san wace ce Ramla sai dai ka ba wani labari don ni babu ruwana da sabgar gabanka!" Tana kaiwa nan ta koma bakin gado ta zauna abin ta, ransa in ya yi dubu ya ɓaci kawai fuskar Hasiya yake tunanowa yana ganinta tana walwali kamar zinare, a take yake ganin bambancin ta da Ramla wacce yanxu gani yake ta masa wani irin dubu dilim saboda ba ta ita yake yi ba yanxu hankalinsa na ga halaliyar abikinsa da ya mutu ya bar masa.

Tana zama a zuciye ya yi hanyar drower ɗinta yana zuwa ya buɗe ta tashi tsaye ta ce

"Mai za ka mini a cikin drower ta?" Ko kallo ba ta ishe shi ba, bare ta sanya ran zai ba ta amsa. Kafin ka ce kwabo ya fara watso kayanta wanda suke a laye a goge tasss an shirya su a lokar. Tana tsaye a bayansa ta harɗe hannayenta tana cike da ruwan mamakin da ya shayar da ita, ganin ya kusa watso rabib kayan da suke saman ya sa ta taka a sannu ta ƙarasa gabansa ta sanya hannu ta riƙe hannun nasa.

Da mamaki ya juyo yana kallon ta lokacin ya saka haƙori ya dantse leɓensa na ƙasa yana tausar zyciyarsa da take bashi shawarar ya ɗauke fuskarta da kyakkyawan mari mai gigitarwa za ta dawo hayyacin ta ta bashi zoben.

Kamar daga sama ta ji ya ce

"Sakar min hannuna"

Ta ce

"Ka daina watso min kayana" Ta faɗa cikin sanyin hali. Wani takaici da ya shaƙa, da sauri ya saka ɗaya hannun nasa ya warɓar da hannunta daga riƙon da ta masa, ya bar wajen drower yana faɗin

"Gwara dai yau na bambance miki tsakanin aya da tsakuwa" Ya faɗa yana waiwayen inda zai fa takarda da biro, so yake yau ya auna mata ko da sako ɗaya ne, amma ganin bai ga komai ba ya sa ya yi hanyar fita a fusace tana ta tunanin abin da yake nema da kuma dalilin fitarsa bayan ta san bai ga abin da ya zo neman ba. Ita kuma ba za ta taɓa faɗa masa cewar ga inda zoben yake ba don ta san bai ganshi ba kuma bai yi tunanin ita ta ɗauka ba saboda ya riga da ya ga fitowarta daga ɗaki shi ya sa ya zargi iya ta ɗauka.

Kayan ta fara kwashewa tana mayarwa tana zancen zuci ta ce

',Hummm maza! Maza gumbar dutse, wallahi mace idan tana biya halin wani namiji sai ta nemi samun taɓin hankali idan ta biyewa abubuwan da ake ƙunsa mata na takaici ta tsantsar baƙinciki, da a ce Abdulsalam za ka duba rayuwar baya da tabbas ban cancanci duk wasu abubuwan ba' Ta faɗa lokacin ta gama mayar da duka kayan ta rufe drower.

Har neman faɗuwa yake a babban falonsa, yana zuwa ya shige ɗakin ko ƙofar bai gama rufewa ba, ya janyo wata ƙaramar loka ya ɗakko biro da wani memo ya ciro takarda yana daga sunkuyen ya ɗora a kan gado ya fara rubutu kamar haka

"Ni Abdulsalam na... Kafin ya ƙarasa faɗa kamar wanda aka ce ya kalli wajen da zoben ya faɗi a take idanunsa suka sauka a kan akwatin zoben. Saroro ya tsaya yana kallon akwatin kafin da sauri ya yi wajen yana zuwa ya ɗauka ya duba ya ga zoben a ciki. Juyawa ya yi wajen takardar da yake rubutun wacce ya ɗora biron a kai, ya ɗan yi shiru yana tuna irin abubuwan da ga je har ɗakinta ya mata, ya yi tsai yana tunanin yadda aka yi xoben ya faɗi, tabbas ya san da wuya daman ta ɗauka amma saboda ya san ita kaɗai ce ta shiga ɗakin shi ya sa ya ɗora zargin a kanta.

Buɗewa ya yi ya ajiye a drower ɗin, ya duƙunƙune takardar, ta yamushe ya ɗora a kan madubi, ya yi saurin ɗakko wata ash ɗin shaddarsa ya saka ya fesa turauuka masu ƙamshi, ya ɗakko akwatin xoben ya feshi ta da turare, ya je gaban madubi ya daka hula sai da ya tabbatar ta zauna daram, yadda duk wata mace idan ta ganshi ba za ta tsallake tayinsa ba, ya ɗakko takalmi ya saka ya fito yana ɗaura agogo bayan ya saka xoben a aljihu, tare da wayoyinsa.

Ko da ya fito ya rufe ɗaki bai ma bi ta kan Mama Ramla ba don tuni hankalinsa ya yi gaba. Yana fitowa direba ya ba umarni ya buɗe masa mota ya shiga ya rufe mai gadi ya wangale musu get suka haura saman titi.

Bayah ya faɗa masa inda za su je, waya ya ɗakko ya shiga kiranta, tana zaune tana yankan farce suna taɓa hira da Dada kiransa ya shigo, ƙaran keypad ɗin tata ta karaɗe falon, tana zuwa ta ɗau wayar tana cewa

"Dada Abban Humaira ne"

Dada ta ce

"To mai kuma kike jira ki ɗaga mana" Ɗagawa ta yi ya ce

"Gani nan zuwa" Kafin ta amsa ya ɗora da faɗin

"Mai kike so in taho miki da shi?" Da sauri ta juya ta kalli Dada, tana mamakin furucinsa ba ma iya abin da ya faɗa ne ya sanya ta a kogin tunani ba har yanayin yadda ya yi maganar cikin wata sassanyar murya haɗe da wani salo, kawar da tunanin yanayin da ya yi maganar ta yi ta ce

"Komai ma" Dada ta kafe ta da ido, don ta ga yanayinta ya canja.

Murmushinsa mai sauti ne ya karaɗe kunenta ya ce

"Kin bani zaɓi kenan?" Ta ta gyaɗa kamar yana ganinta, sai Dada ta ce

"Baki da baki ne Hasiya, wanda yake magana a waya ina ruwansa da gyaɗa kanki?" Ta faɗa duk da ba ta san mai ake gyaɗawa kan ba. Hasiya ta ce

"Eh" Tana faɗa ta sauke wayar daga kunenta ta ce ."Dada wai tambayata yake da mai zai taho...

Ƙaran shigowar wani kiran ne ya katse mata maganar da take yi, tunanin ta shi ne amma sai ta ga sunan ƙawarta Karima. Da sauri ta ɗaga ta ji muryar Karima tana faɗin

"Gani nan zuwa gidan, ki kwatan ta min inda gidan yake, saboda a adaidaita sahu nake daga mun shigo unguwar ina za mu nufa" Hasiya ta shiga kwatanta mata tana ta murnar yau xa ta ga ƙawarta da ta kwashe watanni ba ta gani ba.

A ɓangaren Abban Humaira, shagon waya ya sa suka je, ya siyo mata sabuwar waya fil a kwalinta.

Lokacin da suka zo ƙofar gidan, sai ya ji gabansa yana faɗuaa tunani da fargabarsa ɗaya kar Hasiya ta ƙi amincewa da buƙatarsa ta son mallakarta a matsayin mata, wato ya zama zaɓinta don ya maye mata gurbin mijinta da ya mutu!.

Ya ɗaga waya zai kira, amma sai ya fasa, ya yanke shawarar shiga gidan da kansa. Sallama ya yi Dada da take share baranda ta amsa tare da yi masa iso shigowa ya yi yau har da durƙusawa ya gaishe ta, Dada da take mamakin durƙuson da yau amma ba ta kawo komai ba, sai dai ta lura yau kamar dai akwai abin da yake jin nauyi. Yana zaune ya ce

"Dada akwai maganar da take tafe da ni, sai dai ban san yadda za ku ɗauki maganar ba amma tana da girma" Dada wani daɗi ne ya lulluɓe ta, a matsayinta na mai shekaru a iya furucin da ya sauka a laɓɓansa ta gane inda ya sanya gaba sai dai ba za ta yanke hukunci ba saboda tana so ta gama fane cewar jirgin da ta harbo shi ne ko kuwa akwai kwaskwarima a lamarin.

Ta nuna kamar ba ta fahimci inda ya sa gaba ba ta ce

"Ikon Allah magana kuma Allah sa dai lafiya" Ya yi gyaran murya ya ce

"Eh lafiya ƙalaw daman ina so za mu tattauna da Hasiya ne a kan wani batu" Hasiya da take falo jin abin da ya faɗa gabanta ya faɗi, don daman tun da ta leƙo ta gaishe shi ta koma ɗaki.

Dada ta washe baki ta ce

"Ka shiga falo to ai ba damuwa, nan ai gidanku ne, mu tsakaninmu dai ai sai addu,a da ffatan alkairi" Sosai ya ji daɗin furucin ta yana fatan ya dace a maganar da za su tattauna da wacce ya zo gidan domin ita, wacce yake yin komai domin ita, wacce yake kyautata musu don ita duk don ya cika nasa burin!.

Falon ya nufa, Hasiya kuwa tun da ta ji amsar da Dada ta bashi ta gyara zaman wuyan rigarta tare da ware ɗankwalin kanta ta yafa. Da sallama ya shigo ta amsa tana sake masa sannu da zuwa ya amsa.

Bayan shiru ɗan ƴan wasu daƙiƙu ya ce

"Hasiya ina da magana mai muhimmanci ina fatan za ki kalle ta da sigar da zan faɗa miki ita, sannan ina so ki amince" Kai kawai ta gyaɗa masa, tana jin yadda idanunsa yake yawo a kaf ilahirin jikinta, har sai da ta tsargu sosai da yanayin kallon da yake mata, ta ɗago idanunta ta kalle shi, idanunsu suka sarƙe da na juna, tana kallon ƙwayar idanunsa, idanun suka bayyana saƙon zuciyarsa, tabbas ita ba yarinya ba ce ko da ba a faɗa ba ta san wannan yanayin kallo furucinsa ba zai gaza soyayya ba, amma dai ta ƙaryata maganar zuciyarta da take mata labarin ƙanzon ƙurege.

Da wata irin murya ya ce

"Hasiya" Gabanta yana faɗuwa tamkar sabuwar budurwa ta ce

",Na,am"

Ya yi gyaran murya bayan ya yi jim kaɗan, ya ce

"Hasiya ina so ki dubi maganata da idon basira, na zo miki da batu mai girma, ina fatan ba za ki ƙi amincewa da shi ba, Hasiya idan kin amince ina so ki bani dama na maye miki gurbin abokina Zahraddin!".

*** [7/26, 4:04 PM] null: ***

*KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH