BOOK 1
🅿1️⃣0️⃣
Tun da ya yi furucin Falon ya yi shiru Kawai sai sautin agogon bango ne ake ji tik-tak... Tik-tak...
Hasiya ta kasa kallon idanunsa. Zuciyarta na bugawa kamar wacce ta yi tseren gudun tsawon kilomita.
A zuciyarta ta ce
'To ashe Abdulsalam zai faɗi haka? Kamar dai ya gane ina jira wannan kalmar da zuwan wannan ranar?'
Wani sashe na zuciyarta ya ce
'Haba Hasiya ki tuna fa shi ne abokin mijinki da ya mutu, ko ma in ce ya wuce matsayin aboki shi amininsa ne tamkar ɗan uwa na jini. Shin idan kika amince masa baki ci amanar Zahraddin ba?'
Sautin maganarsa ya katse mata zancen zucin da take, ya ce
"Kin yi shiru Hasiya, don Allah kar ki watsa min ƙasa a ido, kar ki ce min a,a"
Cike da nuna tsantsar kunyar furucinsa ta ce Abban Humaira... ban fahimci abin da kake nufi ba"
Ya karkatar da kai gafe yana hura iska daga bakinsa idanunsa kafe a kanta yana mata kallon tausayi. Ya sanya hannu a aljihu ya ɗakko akwatin zoben daga aljihunsa ya buɗe.
Zoben ya bayyana yana sheƙi a cikin akwatin. Ya ce "Ina nufin aure Hasiya. Na san ba a daɗewa bada rasuwar abokina Zahraddin. Na san da wuya ki amince min amma ki sani na yi hakan ne don in ba iyalin abokina kulawar da ta dace a bayan ransa don kar ahlinsa su tozarta, inaso na kula da ku don kar ku yi maraici musamman su Nasira zan zame musu uba na gwada musu gata na har iya numfashina!."Ya faɗa yana ɗaukan akwatin zoben da hannun hagu ya ɗora a tafin hannunsa na dama ya matsar da hannun gabanta. Idanunta suka sauka a kan hoton zuciyar da yake jikin zoben, ta runtse idanunta da ƙarfi tana fatan Allah sa dai ba mafarki take yi ba, ba ta karɓa ba har lokacin idanunta a rufe, ya ɗora a kan kujera tare da furta
"Ina zuwa Hasiya" Kafin ta bashi amsa ya fito amma bai ga Dada a tsakar gidan ba, Dada wacce tun da ya nemi kaɗaicewa da Hasiya za su tattauna ta ɗora masa ayar tambaya, hakan ne ya sa ta tattara ƴan ƙafafunta ta koma daga can jikin bango yadda ba za a hango ta ba, tana son sanin abin da zai furtaw Hasiya tana fatan zaton ta ya zama gaskiya da kakarsu ta yanke saƙa. Duk abubuwan da suke wakana a falon a kan dodon kunnenta, ji take tamkar ta saka hannu ta fisgo Hasiya ta ce ta amince amma babu dama kuma babu hali.
Jin ya ce yana zuwa ta tabbatar fitowa zai yi hakan ya sa ta yi saurin shigewa kicin, tana so ta fito ta je ɗaki ta cewa Hasiya kar ta yi wa arziƙi dundu, sai dai ta san ma ko ba ta faɗawz Hasiya ba, lallai ba za ta ƙi amincewa ba domin ta san wa ta haifa, a fili ta furta
"Na san kin haifu a cikina Hasiya, wa zai so zama a gidan talauvi gidan raba larura da ɗa namiji, kullum yana babu ai ko a fatar baki kalmar babu ba ta da daɗin ji, ai aure tamkar dai an ɗaura shi ne"
A ɓangaren Hasiya yana fita ta zare idanunta tana son gaskata a gaske ne Abdulsalam ya furta mata kalmar zai aure ta da sauri ta sanya hannu ta ɗauki akwatin zoben da ya ajiye a kan kujera ta ce
"Taɓɗi! Daman Allah ya san halin jaki ne da bai bashi ƙaho ba! Wancan auren ma ƙaddara ce amma talauci kam ni da auren talaka wallahi haihata -haihata, ka ji munafuki to daman dai ko ƴan hidindimun da yake min a wasu lokuta da manufar so a zuciyar... Ba ta ƙarasa faɗa ba ta ji sallamar shi, da sauri ta ajiye akwatin a inda ta ɗauka ta gyara zamanta tare da doka wani uban tagumi, ta lanƙwasa murya ta marairaice ta irin ta masu nutsuwa kamar yadda ya santa ta ce
"Alaikumus salam" Ya shigo falon, ƙaran ledar da ta ji a zuciyarta ta ce
'Allah sa sarƙa da ɗankunnen gwal ne'
Bayan ya zauna ya ciro kwalin wayar daga ledar ya miƙo mata, ya ce
"Ga wannan wayar"
Hasiya ta rufe baki da hannuwanta, idanunta suka ciko da ƙwalla, a zahiri ta yi hakan ne don ta nunawa Absdulsalam tana tune da abokinsa, amma a baɗini ƙwallar farin ciki ne da mamaki.
Ya ja numfashi ya ce
"Zan aure ki Hasiya, amma zan baki kwana biyu ki yi shawara ki yi tunani amma don Allah roƙon da nake miki kar ki ce a,a"
Hasiya ta gyaɗa masa kai cike da nuna tana jin nauyinsa.
Dada kuwa daga kicin ta ji komai, ta tsaya da cokali a hannu tana addu'a a zuci ta ce 'Ya Allah ka nuna min wannan ranar, ranar da zan zama sirikar attajiri kamar Abdulsalam, Allah na gode maka da ka yanke min zama sirikar faƙiri kamar Zahraddin, haba ina dalili ka siyar da akuya ta dawo tana cinye maka danga, kullum yarinya tana ƙarewa kamar hatsin guzuri, kullum tunanin abin da za su ci ma kaɗai aiki ne, hausawa suna cewa Allah ba ya barin wani don wani ya ji daɗi, to mutuwar Zahraddin dai Allah ya ɗauke shi gashi Hasiya za yi aure a gidan arziƙi".
Ya miƙe tsaye yana faɗin amma ki sani Hasiya tun daga ranar da na ga jana'izar abokina na ce a zuciyata, idan Allah ya nufa, zan tsaya miki. Zan zama karfin ki, na jagorance ki da ke da ƴaƴanki"
Hasiya ta ɗaga kai ta kalle shi. A karo na farko tun bayan rasuwar mijinta ta ji wani yana magana da ita kamar mace, ba kamar gwauruwa ba.
Ta ce a hankali: "Abban Humaira zan yi tunani in yi istihara, sannan zan tattauna da Dada. Amma... na gode. Na gode da ka tuna da mu"
Wani sanyi mai kamar hucin AC ya daki tsakiyar zuciyar Abdulsalam, iya furucin nan da ta yi ya ƙara tabbatar da ya samu mai ɗebe masa kewa, a zuciyarsa ya ce
'Zan cika burina na tsawon shekaru, zan mallaki zaɓina Hasiya, na san kallon ki kaɗai a cikin gidana zai warkar da ni wani ciwo da na daɗe ina fama da shi a zuciyata, zamanki wani sashe na daga rayuwata zai sa na daina hange-hangen da kalle-kallen ƴan mata don na fi zaton Ramla ta gaza ne, ba ta da wasu abubuwan da za su kawar mini da maganaina daga kallon mata ne shi ya sa amma ke za ki zama katangar da zan jingina in ji daɗi, za ki zama tabarmar da zan zauna, sannan ki zame mini garkuwa!'
Ya mata wani kallo ya ce
Na san za ki yi tunani da shawara mai kyau!" Ba ta san murmushi ya suɓuce mata ba amma sai ta yi saurin gyara yanayin fuskarta da ya nuna alamun murmushin ta ce.
"Sai dai ina jin nauyin Ramla" Kamar ta faɗa masa mutuwarsa haka ta ga ya sauya akalar kallon soyayyar da yake mata haɗe da murmushin ya ce
"Kar ki ma fara wannan tunanin, zaman aure take, ke ma shi za ki je yi, wataƙila ma idan kika zage dantse ki karɓe gidan a hannunta, ki karɓe mijin ya zama naki, kin san faɗar hausawa da suke cewa, ƙwace goruba a hannub kuturu ba zai yi wahala ba"
Cakkkk bugun zuciyarta ya tsaya tana masa wani kallo mai ma,anoni da tambayoyi masu tarin yawa, a zuciyarta ta ce 'Ikon Allah mai hakan yale nufi, ya na ga yana wasu furuci tamkar dai bai damu da Ramla ba? Shin duk wannan ƙoƙarin da nake gani nata a kansa ina suke? Duk yadda take ɗaukansa namiji uba ina wannan abubuwan ko dai daman yana da matsala ne ba ta faɗa? Ko kuwa ita ce take da gazawa, kai amma dai na san yadda wannan yake da sauƙin hali ai kamar ba zai yi butulci ba na kasa gane bakin zaren'
Kai kawai ta gyara masa don ya ɗaure ta da jiniyoyin jikinta.
Da wannan ya mata sallama, yana fitowa daidai nan Dada ta fito daga kicin, wani irin washe baki ta yi, tana ɗan kallon tsakar gidan nasu a zuciyarta ta ce
',Gidan nan ya kusa dawowa mallakina tun da Ramla da yaranta za su koma gidan Abdulsalam, lallai Allah ya mana gyaɗar dogo ai babu mai hana wannan auren'
Cike da fara,a ta ce
"Har an fito?"
Yana ɗan murmushi ya ce
"Eh Dada zan wuce ne, sauran saƙon maganar za ki ji a wajen Ramla" Dada ta hau sanya masa albarka, ya sanya hannu a aljihu ya ciro ƴan ɗari biyar sabbi ya bata dubu ashirin, ta karɓa tana zabga godiya, shigowar su Nasira daga islamiya da sallama shi ya amsa musu ma suka gaishe shi ya amsa, ya mayar da hannun aljihu ya dakko dubu buyar ya basu su raba, suka hau masa godiya.
Yana fita ya samu direban yana zaune a cikin mota, ya fito ya buɗe masa ya shiga ya rufe ya koma mazaunin direba, ya tada motar suka bar unguwar lokacin ana kiran sallar magriba.
Ko da ya dawo ya samu yaran suna jam,i a falo su da mahaifiyarsu, daman ya leƙa su ne, amman Aslam a bakin get ya ci karo da shi zai je masallaci, a gaggauce ya yi alwala ya fita shi ma, lokacin har ana raka,a ta biyu.
Bayan sun idar da sallar suka zauna Mama Ramla tana musu tunin karatun islamiya, sai da aka yi isha,i Abba da Aslam suka shigo gidan. Gabaɗaya Mama Ramla ta kasa gane mene ne abin da ya sa mijin nata yake ta wata irin walwala, wanda a iya saninta za ta iya cewa tun rabon da ta ganshi a haka ta ɗauki tsawon lokaci, idan ma ba a shekara ba shi rayuwarsa kullum ba ya sakarwa mace fuska sai ɗaure ɗauren fuska sai a lokacin da ya ga dama sannan zai yi walwala. Ko da suka je dining cin abincin ma yana ci yana ta biyewa yaran da hira, kowa yana walwala sai dai ita tana ɗan murmusawa ne haɗe da saka baki a hirar lokaci-lokaci saboda ta san dai sun rabu cikin faɗa har yana zargin ta da ɗaukan zobe sai dai tana tunanin wataƙika da ya ga zoben ne ya sakko daga dokin fushin ko kuma inda ya kai zoben ne aka karɓe shi da hannu biyu.
Bayan an gama cin abinci, Talatuws mai aiki ta zo ta kwashe kayan. Abin mamaki ya ɗan zauna a falonsa da yaran suna ta hira ita dai Mama Ramla abin ya ɗaure mata kai.
Bayan yaran sub musu sallama sun tafi ɗakunan su, tana jaddada musu kan kowa ya yi alwala sannan ayi addu,ar idan za a kwanta. Suna fita ya miƙe tsaye ya ce
"Sai da safe" Da mamaki take kallonsa ta ce ."To mene ne na min sallama mu da za mu kwana ɗaki ɗaya"
A zuciyarsa ya ce
'Ramla kenan! Ko da kin zo ɗakin nan babu abin da za ki samu, wannan babban tanadin amarya zan yi wa shi, dole na nuna mata akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa, dole na nuna mata na fi mijinta marigayi komai da komai ta yadda ba za ta yi kewarsa ba ta yadda zan sa ta manta da shi kwata-kwata a fannoni da dama sai yayin da take sallah shi ma don ta yi masa addu,a ne'
A fili ya ce
"Ai na zaci a ɗakin ki za ki kwana?" Saroro ta yi tana mamakin wannan kora da halin
Ta yi shiru na sakanni tana mamkin da a ce kishiya gare ta za ta iya cewar an mata farraku da bawan Allahn nan tun da ya yi kudin nan duk wasu abubuwan da suka shafi auratayyarsu ya saka ƙafa ya yi fatali da su, musamman fagen aikata sunna ko kaɗan ya zama rago sai yake ta noƙewa, abubuwan dai barkatai.
Miƙewa ta yi ta ce
"Shikenan sai da safe" Ta faɗa tana jin zuciyarta tana mata nauyi, tana tuna yadda ƙawarta Asma,u take faɗa mata tana cewa
"Ramla ki yi wa kanki karatun ta nutsu ki cire lamarin namiji a ranki, kina dai ganin yadda yake nuna halin ko in kula da al,amuranki amma ke kin sanya shi tamkar dai shi ne linzamin rayuwarki, duk wata sadaukarwa da ake buƙatar mace ta yi namiji kin masa amma har ila yau Abdulsalam bai san darajarki ba kawai saboda ya san kina son sa kuma za ki jure koma dai in ce kin jure kuma kina kan jurewa, wasu mazan idan suka gane mace ba za ta rayu sai da su ba ko suna gane lagwanta shikenan ta shiga uku"
Ta kan yi murmushi a duk lokacin da ta ce mata hakan ta ce
"Asma'u kenan,ni gani nake idan ban so Abdulsalam ba wa zan so, son shi tamkar da numfashina yake a haɗe" Tana ta tunawa da maganganun har ta ƙarasa ɗakinta.
Tana zuwa ta shiga banɗaki ta yi wanka tare da alwala ta fito ta shirya cikin kayan bacci farare masu taushi, dogon wando da riga mai hannun vest.
Kwanciya ta yi haɗe da lumshe idanunta, tana ta faman tunane-tunane da saƙe saƙe bacci ya yi gaba da ita.
*MAMA MAGAJIYA*
Bayan ta idar da sallar ta sake kiran Rumasa,u amma wannan karon ma ba ta faɗa mata abin da yake faruwa ba, danne zuciyarta ta yi ta fi so ta faɗa musu gata ga su ido da ido don gudun samun tangarɗa.
Hakan ya sa ta sanar da kowacce cewar gobe su tambayi mazajensu su zo tana da magana me muhimmanci. Washe gari ta tashi tun da sanyin safiya ta dokawa Goggo kira, Goggo wacce take zaune tana karyawa ta ɗaga wayar cike da faɗuwar gaban Allah sa dai lafiya, kasancewar abu ne da ba ta saba da shi ba wato ƴar uwar tata ta mata kira a wannan lokacin.
Bayan ta ɗaga sun gaisa take cewa
"Yaya ina wajen Muhamamdun" Goggo ta ɗan yi jim ta ce
"Yana lafiya ƙalau ya wajen su Rumasa,u?" Ta amsa mata tana faɗin
"Ya maganar ƙarin auren nashi, kin samu wacce za a haɗa su ɗin?" Mamaki ne ya yi wa Goggo dirar mikiya, tana tunanin si da suka yi maganar jiya kusan magriba to a yaushe har aka samu matar, tana ƴar dariya ta ce
"Kema dai Magajiya da wani abu wallaho, to Allah na tuba ina fa aka samu a gaba dai za a cigita kin san abun yana buƙatar nazari da tunanin ta nutsu don kar a kuma wato mace ta sake haifar mace, kin dai ga yadda muke gwawarmaya da ta cikin gidan" Wata nannauyar ajiyar zuciya mai sauti Umma Magajiya ta saki ta ce
"To Alhamdulillahi, wannan abu ya yi kyau ai zatona ko an samu" Ta faɗi hakan a fili amma a zuciyarta ta ce
'Ah har yanzu da sauran dama, dole ne in yi hanzari kar a samo masa' Da sauri ta ɗan wayince don kar Goggon ta harbo jirginta, ta ce
"Allah dai ya zaɓa mana abin da ya fi alkairi, daman kira na yi in ji ya kika tashi"
Goggo da mamaki ya kashe ta ta ce
"Na tashi lpia ƙalaw"
Suna gama sallama ta ajiye wayarta ta tashi tana taka rawa a tsakar ɗakin rana ganin kakar su ta kusa yanke saƙa.
Har wajen sha ɗaya na safe babuu wacce ta zo gidan, Umma Magajiya sai doka musu waya take tana maganar ta rasa uban abin da suke a gidan da ba su zo ba.
Tana nan tsaye a bakin ƙofar gida ta kasa zama a gidan shi ya sa ta fito, adaidaita sahu ne ya ajiye Rumasa,u ita da yaranta Umar, Usman ta fito tana ba mai napep ɗin kudin su kuma yaran suka ruga zuwa wajen Umma Magajiya, baki ta washe ta tisa su gaba suka shige gidan Rumasa'u tana biye da bayansu tana faɗin
"Ni Umma na rasa wannan kiran na mene ne dakyar kika bari muka yi baccin kirki tun sassafe kike mana kira, yanzu ma ina wa yaran nan wanka kiranki ya fi a ƙirga" Umma ta fashe da dariya ta ce
"Yaro man kaza, to Ruma ai da sanyin safiya ake kama fara, dafa rana ta yi in ka je kama ta guduwa za ta yi" Jakarta ta ajiye tana cewa
"Bani in sha" Umma ta ce
"Bari Haulatu ta zo ta ce min ta kusan ƙarasowa kin san ita kuɗin napep ɗin ma wannan Allah baku mu samun mijin nata ba bata yake yi ba kullum jiya iyau talauci ya masa kanta" Da dariya suka fashe a tare ta miƙawa su Umar biskit kamar daga saman sallamar Haulatu ta sauka a kunnuwansu suka amsa, ta shigo tana ta murnar ganinsu ta zauna aka fara zantawa.
Umma ta yi gyaran murya ta ce
"Da a ce ina da wasu ƙattin kuɗi a ajiye da sai na siya muku naman kaza da lemo, lemon ma ba na roba ba na gwangwani" Jin haka su Umar suka zo suka baibaye ta suna faɗin ta ɗakko musu lemo ta ce
"Yara ku sha kurinminku in dai lemo ne sai kun ture!"
Gabaɗaya aka yi dariya ta ce
"Jiya na je gidan wannan uwar taku mai ci ita kaɗai duk da an ce wanda ya ci shi kaɗai to shi kaɗan zai mutu"
Haulatu ta ce
"Wai Goggo?" Umma ta aika mata harara kamar za ta fito da idanunta ta ce
"To da wa" Shiru ta yi ba ta ce komai ba, Umma ta ɗora da faɗin
"Abin mamaki abin al,ajabi abin farinciki shi ne Muhammadu za a ƙarawa aure!" Rumasa,u ta dafe ƙirji da hannu biyu ta ce
"Aure fa Umma? Ina Hajiya Naja'atun?" Tsaki ta doka ta ce
"Shegiyar tana nan, ai babu inda za ta je sai na aura masa ɗaya daga cikin ku" Su duka da kallon mamaki suka bi ta, amma ta ce
"Da zarar ɗaya ta kashe aurenta, ta shiga gidansa za mu yi waje da ita, ke ba ma ita kaɗai ba hatta uwarsa sai ta san na yi, ni kaina wannan katafaren gidan zan koma, mu wanke biyar mu tsoma biyar"
Ruma ce take ɗan tunani, amma Haulatu ta tsorata da lamarin aynun.
Haulatu ta ce
"Umma ta yaya mutum yana gidan aure zai kashe auren da gangan ya auri wani mijin?" Wani mugun kallon da Umma ta aika mata shi ya sanya ta yi ɗiff ba tare da ya shiryawa hakan ba.
Umma ta ce
"Shi auren mutum ne da za a ji shakakr kashe shi, ni fa kiranku na yi in fala muku ga arziƙi yana mana dundu, to ni daman can ma da na san Muhammad a gaba zai yi kuɗi wallahi da gwara ɗaya daga cikin ku ta zauna babu aurr har ya gama karatun ya samu aiki, don haka shawara za mu yi a matsayinmu na tsintsiyar da take maɗauri ɗaya a ware wacce za ta nakasta aurenta wato ta masa lahani miji ya sake ta shikenan sai mu san ƙulla-ƙullar da zan yi a wajen uwar tasa wacce ta kashe auren ta aure shi"
Rumasa'u ta ce
"Allahu akbar kabiran, idan Allah ya baka uwa mai hikima ka huta" Umma ta washe baki ta ce
"Ai gata nake muku, babu uwar da za ta so ɗanka ya zauna a halin babu da ƙuncin talauci, shi fa rashin kuɗi shi kaɗai ma babbar jarabawar rayuwa ce"
Ɗakin ya yi tsit, Hauletu ta katse shirun da cewar
"Umma ni dai ba zan iya kashe aurena ba sai dai ko Ruma... Kafin ta kai ƙarshe Umma ta ce
"To ƴar a nace wato ke ba za ki bari mu yi shawarar ba ma, har kin yanke hukunci? To don ma ki sani a ƙarshe dai ke ce za ki kashe naki auren tun da dai babu kare babu kwikwiyo, ke kaɗai ce ba haihuwa kika yi ba, ita Ruma tun da tana da ƴaƴa ta haƙura tun da idan kin samu mu duka mun samu"
Ruma ta ce
"Ni wallahi Umma yaran nan ne kaɗai xa su min cikas amma don kashe aure ai kamar kashe kiyashi ne a wajena, tsaf zai ɗagawa ɗan babarsa hankali ya bani takardar saki, to namiji da ba ubana ba kuma ai miji goma ba uba goma ba ne."
Umma ta ce
"Ke daman kin fi kama da jinina tsatsona, wannan sheigiyar yarinyar gani nake da ba a hayyacina na haifeta ba da zan ce ba jinina ba ce wallahi"
Haulatu ta ce
"Wallahi ba zan kashe aurena a kan auren da babu tabbas za a aureni ba, ni fa ko da tabbas na gwammace na zauna a ɗakina inda Allah ya ajiyeni"
Umma ta hayayyaƙo mata da faɗin
"Uban waye ya ce babu tabbas?" Ta faɗa tana kutuntumo ashar mai maiƙo ta zabgawa Haulatu.
Ruma ta ce
"Umma ki rabu da ita ni zan share miki hawaye, ai wallahi ko ƴaƴa dubu ne kashe auren nan nawa zan yi" Umma ta dafa ta ta ringa sanya mata albarka, suka rufe Haulatu da faɗan ta fi so ta je gidan mijin nan na ta ta ci gaba da zaman bauta zaman talauci ita ba ɗa ba ba jika ba amma ta ringa bautawa talaucii.
Ƙarshe aka watse Haulatu ce ta fara tafiya kasancewar a ƙafa za ta tafi gashi gidan ma ba ya mata daɗi saboda Umma sai faɗa mata maganganu mararsa daɗi take, masu sosa zuciya, ita kuma ta gwammace Umma ta faɗa mata komai a kan ta kashe auren!.
Bayan tafiyar ta Umma da Rumasa,u sun zauna suna tattaunawa kan yadda za ta kashe auren. Umma ta ce
"Ruma idan kin kashe auren nan ko bai karɓi yaran ba ki taho da su nan" Ruma ta yi shewa ta ce
"Umma ya za a yi in bar ƴaƴana a can ai ƙafata ƙafarsu, duk da babansu yana iya ƙoƙarin ganin ya sauke haƙƙinmu amma dai wannan ba zai hana na rabu da shi ba,"
Umma ta ce
"Tuni ma, wani ya ga lokacin ma"
Ruma ta ce
"Allah sa ya yarda ya saka ni"
Umma ta ce
"Dole uwar naƙi idan ya matsa ma muna iya maka ɗan ba za a kotu, tun da ba tare aka haife ku ba, idan kin je ki tada bala,in da dole ya damƙa miki takarda, daman ita wacan shashashar na so ta kashe auren nata tun da mijinta ne ba ya sauke nauyin haƙƙin ciyarwa da sauransu ga baƙin talauci kamar yana bacci aka ƙera injin kuɗi"
Sai bayan magriba ta tafi gidanta Umma tana ta sanya mata albarka, shi kuwa sai kiranta yake amma don ta ƙular da shi ba ta ɗauka ba.
Napep yana sauke ta a ƙofar gidan ta banka ƙofae gidan da ƙafa, ƙofar ta buɗu ta bugu da jikin bango, yana zaune ta shigo ko sallama babu. Ya ɗago ya kalle ta ya ce
"Wannan wane irin abu ne Ruma ya xa ki shigowa mutane gida haka" Ta yi wa falon kallon tsaf ta ce
"Ina gidan yake? Gida ko dai akurkin kaji" ,Ganin abin da ta ce ya ɗauke kai gefe ya yi banza da ita, kawai ya tsinci muryarta ta narko zagi mai maiƙo, ya ƙanƙance ido ya ce
"Da wa kike? " Ko gizau ba ta yi ba ta ce
",Da uban wa nake kuwa in ba da kai ba?" Da tsantsat mamaki ya ce
",Ruma ni?" Ya faɗa yana nuna kansa da yatsa.
Ta taɓe baki cike da hargowa ta ce
"Ƙwarai kuwa, ka ɗauki mataki"
Ya ce
"Mataki"
Ta sake ɗura ashar don ta ɗaukarwa kanta alƙawarin yau auren nan nasu ba zai kwana a ɗaure ba ta ce
"So nake idan ka haifu ɗan halak a cikin uwar da ta haife ka, ba a titi aka samo ka ba, ka yanke igiyar aurena da kai"
Ya yatsina fuska tana mata kallon mamaki bakinsa a sake, sai da ya gama ganewa tsaf a hayyacin da take, ya saka hannu ya kwashe ta da wani rikitaccen mari, ta doka tsalle ta kaiwa tashi fuskar marin, ya sake ɗaga hannu ya sauke mata yana nuna ta da yatsa ya ce
"Ki je duk inda za ki je na sake ki saki uku!"
*** [7/27, 6:33 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH