BOOK 1
🅿1️⃣1️⃣
*HASIYA*
Tana zaune mamaki ya yi tafiyar ruwa da ita, ta ga Dada ta shigo zani a hannu tana ɗaurawa yana neman faɗuwa ta damƙe shi da ƙarfi. Nasira da ta ƙyalƙyale da dariya ganin Dada tana gudu tana faɗawa Zainaba cewar ta fito ta ga Dada tana gudu ta shige ɗaki. Kasancewar Zainabar ta shiga banɗaki za ta yi fitsari.
Dada tana shiga ta sauke idanunta a kan kwalin wayar ta ce
"Allah mai iko da hikima, haƙiƙa tsuntsu ya faɗo daga sama a soye don ba zan ce a gashe ba" Hasiya ta zubawa Dada idanu da ta ɗauki kwalin wayar tana juyawa ta ce
"Hasiya ashe dai muna da rabon dandalar arziƙi a rayuwar duniya? Har na tuna lokacin da abin da za mu ci ma yake gagararmu tun mahaifinki yana raye, ki ga rabo na minallaho ashe dai akwai ƙashin arziƙi a jikinki rashin sani ya sa kika auri Zahraddini kika ƙare a gantalin talauci" Hasiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Dada ko ni na yi farincikin samun wannan damar, sai dai ina tunanin yadda zan auri mijin Ramla, ke kanki kin san dai ta taimaka min" Dada ta yatsina fuska ta ce
"Na ga annabi in na yi hali na gari, idan ana dara ai fitar da uwa ake, kuma dai ai ba ƙawarki ba ce bare ki ce mijin ƙawarki ne kika aura, matar abokin mijinki ce fa, to laifi ne don mijinta ya aure ki, kina ganinsa da ido fici-fici wannan da ganinsa kin san ko bai aure ki ba, ba zai zauna da wannan matar tashi ita kaɗai ba"
Ƙaran shigowar kira wayarta ne ya saka ta dakata, rana dubawa ta ga sunan Karima a fili ta ce
"To ita wannan da a ina ta tsaya, ita da ta kirani tun daɗewa amma gashi ana kiran magriba ba ta zo ba, ni gabaɗaya ma Abdulsalam lamarin da ya xo min da shi ya mantar da ni zuwan Karima"
Dada ta ce
"Ai gwara ma Karimar ta zo ko kya dawo hayyacinki don na ga da alama talauci ya kashe miki zuciya, wato ya kwantar miki zuciyarki ya sanya ta yi sanyi kin canja dag asalin Hasiyar da na sanki" Ba ta ba Dada amsa ba illa kawai ta ɗaga wayar Karima ta ce
"Ke yanzu da kika jini shiru ba kya kira ji ce ina na tsaya ba?" Dariya ta yi ta ce
"Ina kika tsaya to? Na yi baƙo ne wallahi shi ya sa na shafa'a"
Karima ta ce
"Inyeee ƙawata ki ce muna cikin alheri dumu-dumu, wai daga gama takabar taki har zawarawa sun fara kawo hari? Kamar dai wanda suke jira"
Hasiya ta ce
"Ke dai maganar nan ba ta waya ba ce, kawai ki ƙaraso, wai da a ina kika tsaya?"
Karima ta ce
"Ke dai bari akwai na shawo kwana kawia na ga wasu ƙawayena da muka daɗe bamu haɗu ba, shikenan fa na fita daga napep ɗin muke ta hira kin ganni na biyo kwatancen naki a ƙafata na kusa ƙarasowa ma"
Hasiya ta ce
"Bari na fito na ƙaraso da ke" Ta faɗa tana cire wayar daga kunennta ta tashi tsaye ta ce
"Dada bari na shigo da Karima" Ta faɗa tana fita, Dada kuma ta shiga ƙoƙarin buɗe wayar, Zainaba da Nasira suka shiga falon, Zainaba ta ce
"Dada wannn wayar fa?"
Dada ta ce
"Abbanku Abdulsalam ne ya kawowa Auntyn ku" Suna murna suna gani Dada tana buɗewa domin basu san wainar da ake toyawa ba.
Tana fita ta hango Karimar hakan ya sa ta ƙarasa suka taho suna ta dariya da murnar yaushe gamo, kasancewar Karimar ta je Niger ne wajen ƙanwar kakarta zaman jinya tana can ma Zaharaddin ɗin ya mutu da yake jikin kakar tata ba daɗi shi ya sa ba ta zo gaisuwar ba sai a waya suka sha koke kokensu, yanzu ta rasu ma shi ne ta tattaro ta dawo Nigeri,a don ba ta samu ta yi aure ba har yau.
Dada sai da ta gama yi wa wayar nan ɗai-ɗai daga cikin kwalin sannan ta tashi ta je ta yi alwala, sula yi sallah ita da su Zainaba. Karima tana hutun sallah sai Hasiya ce kaɗai ta gabatar da sallar.
Bayan ta gama suka gaisa ta sake mata gaisuwa tare da jimatawa ta ce
"Ko don ai wanda ya mutu ma ya mutu ma sai dai fatan Allah haɗa rai da gafara" Ta faɗa tana ɗauka cokali ta kai jallof na macaroni bakinta da Dada ta ajiye mata.
Hasiya ta nisa ta ce
"Kin san me? "
Ta kurɓi pure water ta ce
"Sai kin faɗa"
Hasiya ta ce
"Abdulsalam ne fa ya xo min da maganar aure, shi ne ya kawo min wannan wayar da zoben nan"Idanu ta zaro ta ce
"Wai dama diddiftun da yake ta yi kenan? Eh lallai ƙawata kin yi goshi, wallahi na jiye miki daɗin wannn lamarin, dole ki shiga gidan nan ki miƙe ƙafa daram, ai kar ma ki yarda maganar nan ta haura sati biyu"
Hasiya ta ce
"Wai kema kin yarda in aure shi, ni fa na dakatar da shi na ce sai na yi tunani da shawara" Tana aika mata harara ta ce
"Tunanin banza da wofi wace shawara ce ai wallahi da nice a take zan amsa masa da cewar Allah bamu zaman lafiya"
ALHAJI RUFA'I
Gabaɗaya daga dangin Hadiza har danginsa ya hana kowa ya ɗauki Nuriyya fa riƙo, daga an masa maganar karɓar Nuriyya sai ya fashe da kuka, haka dai wata ƙanwar Babarsa ta koma gidan nashi da zama don takr kula da ita amma fir tana gidan ma shi yake yi wa yarinyar komai, duk wata hidima kama daga wankin kashi tun Nuriyya tana jaririya ya koyi yadda zai wanke mata wanka ne kawai yake bari ƙanwar babar tashi ta mata shi ma da ya koya kullum kafin ya tafi kasuwa sai ya yi mata wanka ya bata madararta da kansa dakyar yake iya barinta a gidan, sannan sai ya dawo gida sau ɗaya kafin ya taso daga kasuwa kawai ya zo ya ganta ya bata madara ya koma saboda gabaɗaya hankalinsa yana kanta .
Lokacin da ya cika wata bakwai kawai ya saya baby carrier, yake sanyata a ciki take tafiya da ita kasuwa, itama da yake ta saba da shi ko ina suna tare.
Akwai wata mata da take zuwa shagon sarin atamfofi da lesuna mai suna Hauwa'u tun da ta ɗora ido a kan Nuriyya, duk da mahaifinta bai fiya amincewa da kowa a kanta ba saboda kawai sai yake ganin kamar za a cutar da ita, amma saboda yadda Hauwa'u take gwadawa Nuriyya so hakan ya sa ya yarda da ita, idan ta zo kasuwa ta ɗauke ta, ita ma kuma yarinyar ba ta ƙin ta dafa ta ganta ta yi ta ɗaga mata hannu.
A haka har aka shafe shekara lokacin Nuriyya ta yi wayo sosai, daga wannan lokacin ne wani sabon al,amari ya ɓullo take nuna soyayyarta ga Alhaji Rufa,i a sannan ne ya nuna mata sam hakan ba zai yiwu ba domin ya fara ɗaure mata fuska sannan yakr barin Nuriyya a gida sai dai ya koma ya gano ta kafin ya tashi daga kasuwar.
Lokacin buɗi ya samu ya ƙara ɗaukaka a harkar kasuwancinsa, yana shigowa da kaya daga ƙasashen waje saɓanin da, da yake sari a Nigeri'a .
Lokacin tana da shekara uku sannan ne ƙanwar mahaifyarsa Nanno da take zaune a gidansa Allah ya mata rasuwa, daga wannan lokacin mahaifiyarsa ta buɗe masa wuta a kan sai ya yi aure tun da ya hana ɓangaren Hadiza su ɗauki Nuriyya sai dai su zo su ganta haka sho ma nashi ɓangaren ya hana kowa ita.
Ya shiga damuwa matuƙa! Don a son samunsa ba zai sake wani auren ba. Hauwa bazawara ce daman aurenta biyu va ta zauna ba, kuma bata taɓa haihuwa ba, kawai sai ya je mata da maganar aure don har lokacin tana nuna masa ƙauna musamman ma ta fi nuna ƙaunar Nuriyya tana furuci tana cewa
"Wallahi Alhaji Rufa'i na shaƙu matuƙa da Nuriyya ko bacci nake sai na ringa mafarkin ta, don Allah ka bani yarinyar nan"
Ya kan yo murmushi ya ce
"Ai in kin ga na ba wani Nuriyya sai dai in ba na raye, Nuriyya rayuwata ce saboda irin ƙaunar da nake mata na gwammace na rasa komai na mallake ta ita kaɗai"
Da wayo da dabara ta samu ya amince da auren nata, amma kaso cassa,in a cikin ɗari ya yi ne saboda Nuriyya.
Tun da ta tare a gidan Alhaji Rufa'i lokacin ma ba a gidansa na asali bane ya sake gina tamfatsetsen gida, shigowarta rayuwarsa ta gane ashe soyayyar da take gani yana gwadawz Nuriyya duk nafila ce a kan sai da ta dawo gidansa.
Ɗakin Nuriyya kaya wasu ma ba a buɗe su ba kaya ne masu tsada, sannan kayan wasa kai duk gidan nan komai ka taɓa na Nuriyya ne, hatta bacci ba ya iya yi sai da Nuriyya a kusa da shi idan ya dawo gida abin da zai fara tambaya
"Ina Nuriyya? Ta ci abinci" Ko da aka saka ta a makaranta shi yake kaita komina zai je sai ya bar uzurinsa ya je ya kai Nuriyya haka ɗakkowa, fabaɗaya lokacin da yake ba Nuriyya Hauwa'u ta fara kishi da shi.
Ko Umra da ya biya musu Nuriyya tana shekara huɗu wai saboda ita ya biya musu komai sai ƙaramar yarinyar ta faɗa sannan zai aiwatar saboda soyayyar da yake mata.
A take hassada game da baƙin kishi suka wulga a zuciyar Hajiya Hauwa'u suka samu mazauni shikenan ta tsani Nuriyya daman can ta nuna tana son Nuriyya ne don ta samu ya aure ta.
Ganin ba za ta iya ganin kayan takaicin ba ta je ƙawarta ta mata jagora zuwa wajen wani boka ya yi wa Alhaji da Nuriyya farraƙu ya cire son Nuriyya a zuciyarsa kwata-kwata ya sanya kaf danginsa da dangin Nuriyya suka manta da ita, babu mai taimako ko tambayar halin da take ciki, wannan kenan shi ne asalin labarin mutuwar mahaifiyarta da kuma yadda Hajiya Hauwa ta shigo cikin gidan har ta samu nasarar cim ma burinta,. Domin kuwa duk wani gata da kulawa haɗe sa soyayyar da yake nunawa Nuriyya Hajiya Hauwa'u ta maye gurbin.
*RUMA*
Da wani uban tsallen da ta doka ta ce
"Alhamdulillahi, na godewa Allah da ka sawwaqe min" Duk da yana jin zafi haɗe da raɗaɗin faruwar wannan ƙaddarar sakin a lokaci ƙanƙani amma ya ɗauki hakan a matsayin ƙaddara. Daman yana haƙuri ne da ita amma ko kaɗan ba jin daɗin zaɓan yake yi ba saboda tana raina abin da yakr mata yau kuma gashi ta nemi saki ta hanyar cin zarafinsa wanda har ta kai ga ta zage shi.
Yana bin ta da kallo ta juya tana faɗin
",Wallahi na san akwai lokacin da za ka yi da na sani, da a ce ma ba saki uku bane ni nan Ruma na yi ban kwana da zaman gidanka, amma tun da dai ka yanke alaƙar zuwa matakin sai wani ya aure ni to ka sani ni daman babu wannan tunanin a raina na bar gidanka bari na har abada"
Da jan idanunsa da ɓacin rai suka rina masa su ya kalle ta ya ce
"Ruma inaso ki sani ko da ke kaɗaice kika rage jinsin mata a duniya ba zan sake aurenki ba ko da akwai sauran igiyar aure tsakaninmu, shi ya sa na yanke gabaɗaya igiyoyin Allah haɗa kowa da rabonsa"
Yana faɗar hakan ya yi cikin ɗaki yana zuwa ya hau kan gado ya ja filo ya ɗora kansa ya shiga latsa waya duk da ba ya ma gane mai yake yi a wayar. Buguzum-buguxum ta shigo ɗakin ta harhaɗo kayanta shi dai yana jin tana ɗaukan kaya amma ko kai bai ɗago ya kalle ta ba, da a ce bawa yana hana faruwar ƙaddara da yau ko fita gidan nasu ma ba zai barta ba. A zuciyarsa ya ce
'Na san wannan aikih mahaifiyarki ce ita ce ba ta son ku yi zaɓan aure kullum tana nuna ƙwararki ake yi, gaskiya iyaye irin mahaifiyarki ba sa yi wa ƴaƴansu adalci da ba sa barinsu su yi zaman aure'
Sai da ta gama haɗa kayanta tsaf ta fito daga ɗakin tana ɗauke da akwatin ta ajiye ta koma ɗakin da yake ciki da falo ne sai ta shiga ɗakin faran daman sun yi tsuru tsuru sun sha jinin jikinsu ta haɗo nasu kayan. Ta koma ɗakin ta tsaya a kansa ta ce
"Duk wasu bashin kuɗina da suke kanka ka tabbatar ka tura min su ta asusun bankina, idan ba haka ba kana iya tsintar kanka a ofishin ƴan sanda" Bai ko ɗago ya kalle ta ba ta ɗora da faɗin
"Ka gama hawa gado amma ka sani ba za a ɗauki wani lokaci ba za a zo a ɗauke kayan, duk da na san sai dai a siyar da su don ni yanzu sai dai masu tsada kai ni gadon da zan ke kwanciya ma yanzu mai ɗaga mutun ya ɗora a kansa ne ba sai ans ha wahala wajen hawa ba" Ji yake kamar ya tashi ya naɗa mata shegen duka amma ya danne zuciyarsa.
Dakyar ya tashi zaune ya sakko daga gadon ya fito falon lokacin tana ba yaran umarni su saka takalmansu.
Yana fitowa ya kama bango ya tsaya ya ce
"Inaso ki sani ke kaɗai aka kawo gidan nan to ke kaɗai za ki tafi, yarana babu inda za su je"
Ta ajiye ƙaramar jakar hannunta ta ce
"Wallahi baka isa ba, yadda na gama rayuwa a gidan nan a baƙin talauci haka ma ƴaƴana sun bar rayuwar nan!"
Umar ya matsa ya ƙanƙame uban ya saki kuka ta sanya hannu ta fisgo shi ta ce ..
"To sarkin ƴan maƙon uba, kai ne sarkin son ubansa to ka sani in dai na tafi duk uwar wahalar da za ka sha a hannun mahaifiyar ubanka babu abin da zai sa in ɗakko ka" Ta faɗa tana ƙanƙame hannun Usman ta ce
"Mu je in samu mai napep in zo in ɗauki kayan, shi kuma ya zauna gidan ubansa ta fi nono fari "
Hannunsa ya janye ya koma shi ma ya riƙe uban, hanninsa ya ɗora a saman yara, tana samo mai napep sai gata kamar an jefo ta, ta kwashe komai ta fita ta saka a napep ta dawo lokacin suna kuka duka yaran ta ce
"Na rantse da Allah ko kukan jini za su yi da ƴaƴana zan tafi" Ta faɗa tana fisge su, har ta fara tafiya tana riƙe da hannun kowanne maganar mijin nata ta katse ta inda ya ce
"Inaso ki sani tin da ƴaƴana ne na san ko ba daɗe za su nemi ne domin da uba ale ado, sannan ki sani matsawar kika tafi duk runtsi duk wuya ba zan ɗauki ɗawainiyarsu ba tun da sun bar hannuna, Allah ya raya su idan sun girma in muna raye za su nemi ni"
Wani wawan tsaki ta ja kamar za ta tsinke harshenta ta ce
"Allah suturibuƙwai in ji kishiyar mai doro, ai wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, babu wanda zai buƙaci ko da naira biyar ɗinka ce ka riƙe tsiyarka, ina kyautata zaton yaran nan ma sauran karatunsu ba a ƙasar nan za su yi ba sai dai ƙasar waje" Tana kaiwa nan ta ja hannunsu ƙiiii suna turjewa suka tafi, da sauri ya je ya rufe ƙofa r gidan ya dawo cikin gidan yana jin tamkar wanda mafarki yake ba zahiri ba
Suna fita suka shiga adaidaita sahin tana ta lallashinsu da faɗa musu za suke cin kayan daɗi za a saya musu kayan wasa hakan ya sa suka kwaɗaitu da maganar tata.
Jin sun saurara ta ɗaga waya ta dokawa Umma, Umma da take zaune a kan tabarma tana jin haushin Haulatu da ta ƙi amincewa da batun kashe aurenta ta cika mata burinta, bayan ita ce daidai kashe auren tun da ko kare ba ta ajiye a gidan mijin nata ba, bare kuma a yi zancen ɗa.Kuma ita ce take irin rayuwar da take buƙatar tallafi, amma sia gashi mai ƴaƴa biyu za ta share mata hawaye, duk da tana taraddadin Ako zai saki Rumar?.
Ƙaran wayarta ne ya sanya gabanta harbawa da mugun ƙarfi, don tana tsammatar wayar daman tun da sun yi magana da Ruma cewar duk yadda ake ciki za ta kira ta ta faɗa mata, to ita kuma Umma ta ce ko tsakar dare ne ta kira ta ta faɗa mata domin ta ui bacci cikin salama tun da ba ta da tabbas ɗin zai iya sakin, duk da a ranta tana ayyana cewa ko da ya ƙi aikata sakin matsawar dai ya ƙi sakin to abu daya ne za ya aikata wato su ƙulla masa wani sharri sai su maka shi a kotu hakan zai sa alƙali ya sanya ya saki Rumar dole.
Ganin sunan Ruma gabanta ya cigaba da zillo, hannunta yana karkarwa ta ɗaga wayar kamar daga sama ta ji muryar Ruma tana faɗin
"Albishirinki Umma"
Umma cike da ƙagauta wajen ganin ta ji abin da yake faruwa ba tare da an ja mata aji ba ta ce
"Ruma kar dai ki ce kin kaso auren"
Ruma ta ce
"Heheheheh Umma, ai in faɗa miki auren nan na kashe shi"
Umma ta rangaɗa guda don jar ta hangonta zama sirikar ɗanta na wajen Goggo wato Muhammad ta ce . "Da gaske ko wasa"
Ruma ta ce
"Ai auren nan da na tashi kashe shi Umma sai da na samu sabuwar adda mai tsini da kaifi na cakawa auren nan a ciki tsafff ya mutu ko gawarsa babu"
Umma ta ce
"Kar dai ki ce sakin uku ragas"
Ruma ta ce
,"Ai Umma ban bari ya bar igiyar nan ko ɗaya ba,"
Umma ta ce
"Allah miki albarka Ruma, ki kamo hanya yanzun nan ki zo mu san abin yi"
Ruma ta ce
"Sha kuruminki Umma ai ni nan da kika ganni ina cikin adaidaita sahu, ai zamana ya ƙare a wannan kurkukun"
Umma ta ce
"Allah sa dai baki bar masa yaran nan ba"
Ta yi ƴar dariya ta ce
"Ƙafata ƙafarsu wallahi, kin gammu na a tare ai ba zai yiwu a ce zama tare ci bamban ba, gwara mu shuga daular da su"
Umma tana dariya ta kashe wayar, ta tashi tana ta tiƙar rawa zuciyarta wasai sai sanyawa Ruma albarka take. Ta zauna ta ɗauki wayarta ta dokawa Haulatu, Haulatun ta ɗaga cikin sanyi murya ta yi sallama Umma ta ce
"Daman ai idan a cikin ƴaƴa wani ya cusa maka haushi, wani zai faranta maka rai, idan wani ya munana maka wai sai ya sanyaya maka, da kika ƙi kashe... Da sauri Haulatu ta yi ƙasa da murya tana faɗin
"Umma mai gidan yana nan fa... Umma ta ce
"Ke dalla rufewa mutane baki, ni wannan baƙin talakan da shi da babu uwar ubansu ɗaya wallahi, mutum jikinsa duk kantar talauci ta fito ta masa birɗi raɗo-raɗo to mutunci ko kikar mai zai yi a wajena" Haulatu dai ba ta ce komai ba don ma kar ya fahimci abin da yake faruwa, hakan ya sa ta rage volume ɗin wayarta Umma take ta zuba kamar an kunna famfo.
Ta daɗe tana faɗan ta kashe wayar Hauletu ta ajiye wayar cikin sanyin jiki a zuciyarta ta ce.
'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un yanzu sai da Umma ta sanya Ruma ta kashe aurenta, wannan abu bai yi daɗi ba yanzu idan Yaya Muhammad ɗin bai aure ta ba fa, ban san mai ya sa Umma ba ta dogon tunani da nazari ba ita dai kawai son zuciya!'
Tana kashe wayar ta ji ƙaran tsayuwar adaidaita sahun wayar ta ajiye, da azama ta tashi ta nufi ƙofa tana washe baki, ta kamo hannun Umar da yake ransa a ɓace babu walwala ta ɗakko jakar kayan ɗaya, Ruma ma ta ɗakko bayan ta ba mai napep ɗin kuɗinsa.
Gidan suka shiga tana faɗin
"Wai ya na ga mazajen nawa suna muzurai ne?"
Ruma ta ce
"Kukan rabuwa da ubansu mana" Umma ta ja tsakin wasa ta ce
"Yaro man kaza, ta yaro kyau take ba ta ƙarko, za ku yi murna a gaba yara idan kun ga mun koma wancan tangamemen gidan mana baza kifasitil(capacity).
Dariya Ruma ta tuntsure, ko a takalmin ƙafarta ba ta damu da sakin ba don ita in dai da naira kuma za a huta to duk wani buri ya bi bayan wannan. Har yaran suka yi bacci su Umma suna tattaunawa da tsara yadda za a gudanar da biki Umma ta ce
"Ba don iddar saki ba Ruma da sati guda va zai rufa ba sai kina ɗakin Muhammad matsayin amarya, sati na biyu ba zai rufa ba sai mun wullo wannan Najar daga cikin wannan gida na alfarma, don a iya ganina wannan gidan bai kamaci mata biyu ba musamman idan aka ce ke ce a ciki to kamata ya yi a ce ke kaɗai kike mulkin gidan, sannan ke kaɗai kike mulkin zuciyar mai gidan" Sosai Ruma ta rungume Umma tana faɗin
"Umma lokacin iddar ma kamar yau ne zai cika"
Umma ta ce
"Wallahi kuwa, ai daman mutuwar auren ce mai wuya, ban ma taɓa zaton abin zai zo da sauƙi cikin ruwan sanyi haka ba, Allah kaimu gobe in yi sakko in je gidan in samu Goggo" Da wannan tattaunawar bacci ya yi awon gaba da su.
Misalin ƙarfe tara na safe washe gari, Umma mai napep ya dire ta a ƙofar gidan, da wani irin ƙarfi ta hankaɗa kofar ta shiga tana yi wa mai gadin kallon harara jin yana faɗin waye ya turo ƙofa da ƙarfi kasancewar ya shiga ɗakin ne ya ji ƙaran ƙofar shi ne ya fito yana tambaya, amma Umma ba ta bashi amsa ba sai saƙon hararar da take jifanshi, a zuciyarta tana cewa
'Shan ruwanka ya kusa ƙarewa ne da zarar na gama samun damar wannan, ina gab da samu ma'
Goggo tana ɗakinta tana bacci lokacin da Umma ta zo, hakan ya sa ta zauna ta cewa Amira ta kawo mata kayan karin kumallo, tana gama karyawa ta saki wata gatsa mai ƙara ahhhhh.
Ta tashi ta nufi hanyar ɗakin da Goggon take ciki, Amira ta ce
"Umma Magajiya, Goggon fa bacci take, tun da ta yi asuba take bacci saboda kanta yana ciwo" Umma ta waigo tana yi wa Amira kallon kar ki raina min hankali ta ce
"Ke har kina ganin kina da damar da za ki kalleni ki faɗa min maganar banza? Ni za ki buɗe bakin ki mai kama da na jaɓa ki faɗa min cewar tana bacci, to da sannu zan sanar da ke matsayina ban da wanda kika sani, amma ki bani lokaci!" Tana faɗar hakan ta tura ƙofar ta shige ta rufo.
Goggo tana tsakiyar gado tana bacci sanyin AC da na freshner ya haɗe ɗakin, Umma ta banka mata harara tare da taɓe baki a zuciyarta ta ce
'Duniya sabuwa, hummm wato wai ke mai ɗa mai kuɗi zan miki shigo-shigo ba zurfi in saka ki sanya ya aure ta, mu zame muku ciwon ido' Kusan minti biyu tana tsaye sai da ta gama ƙaƙaro kukan ƙarya marar sauti ta bari ido ya yi ja, da hawayen kwance a dakalin fuskarta ta ƙarasa ta zauna a gaban gadon ta saka hannu ta ɗan bubbuga ƙafar Goggo, sai da ta yi sau biyu a na ukun Goggo da cikij baccin ta mai nauyi ta ji ana buga mata ƙafa, ta buɗe idanunta da suka mata nauyi, kaɗan-kaɗan ta fara hango mutum zaune, har dai ganin nata ya washe ta ga ƴar uwarta ce da suke uba ɗaya wato Magajiya.
Sai da ta ƙwara idanu kasancewar kanta da yake sara mata, sannan ta hangi hawayen da suke a fuskarta. Da ɗan hanzari ta tashi zaune tana faɗin
"Subhanallahi Magajiya, ke ce a gidan, lafiya kike kuka?" Ta jero mata tambayoyin a jere.
Umma ta saka hannu tana murje ido cike da nuna damuwa ta ce
"Ina fa lafiya" Goggo ta matso ta dafa ta ta ce
"Waye ya mutu?" Ta tambaya gabanta yana faɗuwa, don a tunaninta ma mutuwa ce aka yi tun da ta ga ƴar uwar tata tana ta kuka.
Umma a zuciyarta ta ce
'Hummm wai ke uwar ƴan tausayi da nuna damuwa da mutane, da wannan tausayi da raunin naki zan yi amfani ki gane shayi ruwa ne' A fili ta ce
" Mutuwa aka yi amma ta aure, aure ne ya mutu, wallahi wannan lamari ya ƙona min zuciya, tabbas ashe haka iyayen ƴaƴa mata suke jin ɓacin rai a duk lokacin da sirikansu wato mazajen ƴaƴansu suka sakar musu ƴaƴa ba tare da wani dalili ba, gaskiya mutuwar aure ba daɗi"
Goggo da ta ji cewar ba mutum ba ne ya mutu sai ta ji da dama dama wai KIBIYA A IDO ta ce
"Ya salam auren waye ya mutu?"
Umma ta ce
"Wallahi auren Rumasa'u ne ya mutu"
Goggo ta ce
"Kai amma abu bai yi daɗi ba, na cuta wannan magana, mai ya yi zafi haka ya kamata maza suke sara suna duban gatari fa, ba kowane lokaci saki yake zama mafita ko maslaha ba fa"
Umma ta share hawaye da gefen hijabinta ta ce
"Ai da ita babu laifin zaune ba na tsaye, haka kawai ya ce ya gaji da zama da ita, ya haɗo min ita da yaran ya koro min ita da dare ma, yanzu a gida ta kwana"
Goggo ta doka tagumi tana sauke ajiyar zuciya ta ce
"Aikuwa zai gane kurensa, don sai ya tabbatar da ya yi laifi sannan ko ya nemi komai za ta koma"
Umma ta ce
"Wane kome, ai saki uku ya mata ko sauran igiya ɗaya bai bari ba" Goggo ta yi salati ta ce
"Kai wannan mazan zamanin wasu basu ɗauki mata a komai ba, suna ganin mace kamar riga ce su cire wannan su canja wancan, ta yi haƙuri Allah zai bata wanda ya fishi, Allah sarki Rumasa'u"
Umma a zuciyarta ta ce
'Allah ma ya bata Muhammad, wato saboda baƙin hali ba kya ce ba Magajiya kyale shi zan share mata hawaye, ɗan uwanta yayanta Muhammad ya aure ta tun da kin ga jiya ma na faɗa miki zai sake aure' A fili ta ce "Amin to, Allah kawo ko a dangi ta samu ma wataƙila ma a fi riƙe ta da daraja".
***
[7/28, 5:52 PM] null: ***
*KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH