BOOK 1
🅿1️⃣2️⃣
*DADA*
Dada ta shigo falon ta bar yaran a tsakar gida ta zo ta zauna haɗe da naɗe ƙafafu ta ce
",Karima ke da yake kin da hangen nesa ai gashi kin gane arewa ba kudu ba ce, yanzu a wannan zamanin idan har Hasiya ta kafa kujerar zawarci ga yaran Nasira tana da shekara sha huɗu, Zainaba tana da shekara sha biyu yaushe ne za ta samu mijin aure? Mazan nan na yanzu yawancinsu ba sa son wahala bare ma wahalar da ba ta ƴaƴansu ba wasu hatta ɗawainiyar ƴaƴansu gudunta suke su bar mace da nauyin da nasu ne wanda Allah ya ɗora musu, bare kuma har su yarda su ɗauki ɗawainiyar ƴaƴanta, wallahi wasu mazan saboda yaran nan ba za su doso inda kike ba Hasiya"
Karima ta kama haɓa ta ce
"Dada kina dai ganina gani nan ni auren farin ma har yau bai samu ba, kuma a haka muna nan muna jiran ranar da Allah zai kawo ko mai mata uku ne mu cike gurbi amma ita Allah ya bata miji kuma bayan mijin ya mutu ya sake kawo mata wani a kwana kusa amma shi ne har za ta tsaya dogon tunani"
Hasiya tana kallon bayan wayar tata sabuwa ta ce
"Baku gane mai nake nufi ba fa, ni fa duk runtsi ba zan ƙi auren Abdulsalam ba ai namiji da kowace mace za ta so ta ga ta mallake shi kawai dai ina tuna Ramla ne"
Wani dogon tsaki Karima ta ja ta ce
."To tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa kina da tabbas ɗin da a ce ita ce ta samu damar da kika samu za ta miki halacci ne kowa fa kansa yake so"
Hasiya ta dara ta ce
"Ƙawata kin sanni dai sarai ina nan a Hasiyar da kika sani ba wai na canja ba, hatta Zahraddin Allah jikan rai ba wai ina ƙyale shi ba ne, shi da babu wata mamora ma a jikinsa sai baƙin talauci, bare kuma wannan ai ba mijin wata ba ke sai dai ma a yi ɗaya ko dai Ramla ta ɗauki haƙuri ta zauna idan kuma ta ji zafi ta ja ƙafafunta ta bar min gidan, don ni wallahi gida tuni na fara lissafinsa a zuciyata, har na hangeni ina shimfiɗa tabarmar soyayya zama daram ga ni ga yarana" Da dariya Karima ta kwashe, ta kai hannu suka tafa da Hasiya, Dada ta ce
"Haba ko ke fa Hasiya wallahi da na ɗauka ba za ki amince ba, don na lura kamar zaman gidan Zahraddin ya sanya zuciyarta ta kwanta"
Ita ma dariyar ta yi, Karima ta ce .."To ni idan an cire sim ɗin daga tsohuwar wayar sai a bani tsohuwar na ƙarasa ta"
Hasiya ta ce
"Sha kuruminki"
Abdulsalam tun da ya kwanta yake hangen fuskar Hasiya, irin yadda take nuna tsantsae kunyarta shi ne yake birgeshi, ga wani murmushi da ya ga ta yi sai da ya yi ƙiyasi bai taɓa ganin wata mace ta yi murmushin da ya ƙawata fuskarta irin wannan da Hasiya ta yi ba, a yadda yake jin wutar sonta tana ruruwa a ruhinsa yana jin zai iya rabuwa da kowa wanda zai kawo masa tsaiko a yanayin zamantakewa ko auren Hasiya.
Juyi ya yi ya ja filo ya kawo kusa da shi, ya ɗakko wayarsa a zucuyarsa ya ce
'Ko ta canja kayan ƙaramar wayar tata ta mayar babbar da na kai mata? Ko kuwa ba da amince ba kar ba je ma ta ƙi karɓar wayar' Ya faɗa yana jin wai dan jijjiɓin tashin hankali. Sunanta ya kawo ya rangaɗa mata kira lokacin sha ɗaya na dare har ta gota, tana ta shige shige a wayar domin sai da ta caja ta ma, tun da za ta tadi ta raka Karima ta sanya wayar a caji sai da ta kwanta ne ta ɗakko ta kunna lokacin har cajin ya cika.
Gabanta ne ya buga da ƙarfi ganin kiransa ya shigo, sunansa ya bayyana a saman screen ɗin wayar yana yawo. Wayar ta ɗora a ƙirjinta ta kifa ta, ta kasa ɗagawa tana jin sautin ringin ɗin da yake fita a wayar mai sauti a hankali. Tunani take yau ce rana ta farko da za ta amsa wayarsa da wata manufa, wato da manufa irin ta soyayya saɓanin da wanda take ganin zumunci ne kawai. Har kiran ya katse ba ta ɗaga ba, ganin hakan ya sa ya yi mata message kamar haka
"" _Hassy na san kina jina, a wannan lokacin ba za ki iya bacci ba, na san zuciyarki tana cike da tunani kala-kala a kan abin da na zo miki da shi amma ki sani ni kuma na kasa bacci saboda fargabar amsar da zna samu daga gare ki, ki taimaka in samu amsa mai daɗin sauraro!"""_
Ƙaran shigowar saƙon ya sa ta duba da sauri, hannunta har karkarwa yake, ta shuga karantawa, ko kaɗan ba ta so saƙon ya tsaya a iya nan ba ji ta yi ina ma dogon rubutu ya yi domin wani irin nishaɗi da shauƙi ta samu kanta a ciki yayin karantawa. A zuciyarta ta ce
'Ashe haka Abdulsalam ya iya kalamai, ashe ya iya kalamai masu taushi da ratsa zuciya, in dai haka ne ya fi Zahraddin sau dubu a fannin iya soyayya, wannan ban ma amince ba idan na amince ya zan tsinci kaina lallai na tabbatar zan zama sarauniya a zuciyarsa, ni abin da ya fi birgeni ma irin yadda ya sakaya sunana Hassy, iya zamana da Zahraddin bai taɓa sakaya sunana ba sai dai ya kirani da Hasiya, tabbas wani hanin ga Allah baiwa ne babba ma kuwa!"
Idanu ta lumshe tana tunanin abin da za ta ce masa sai ta ga ya ce
"Ki hau whatsapp please" Idanu ta zaro ta ce
",Wannan za a je da shi" Tana faɗar hakan ta buɗe data daman a layikanta kullum sai ƴan layi sun bata kyautar data hakan ya sa ta sauke hau whatsapp ɗin dama ta buɗe, don ita a gidan Zahraddin waya sai keypad wataran ma idan talauci ya matsa sai ta cire sim din a siyar da wayar su ci abinci idan ta sake samun wayar ta saka sim ɗin yau kuma ga waya mai tsada.
Tana hawa ta ga ya ce
"Na kasa bacci ina tunanin ki, ki min voice na ji muryarki ko na samu bacci" Idanu ta zaro ta ce
'Wannan ko dai son nan nawa ba yanzu ya fara ba, anya wannan son don ya riƙe ƴaƴan abokinsa ne kuwa ko dai kansa yake yi wa tanadi?' Ta faɗi hakan a zuciyar ta ta rubuta masa.
"Ina Ramla?" Iya abin da ta rubuta masa, don sai ta ji wani kishinsa ya ɗarsu a zuciyarta, irin yadda yake nuna ya damu da ita a yau kawai da kuma irin yadda Karima ta yi ta mata kuɗuba da ta tafi ta raka ta tana faɗin
"Kar ki kuskura ki nuna duhun kai, ko kunya ko kara a kansa, ki nuna masa so idan ya nuna miki so, kin ga dai yana da mata idan kika tsaya kina jan aji ko wasu abubuwa makamanta wannan tana iya sawa ya manta da ke, kin ga daga mantuwa sai fasa aure.
Shi kuma jin tana tambayarta sai ya fara tunanin ko nauyinta take ji, a zuciyarsa ya ce
',Ba zan ce miki tana ɗakinta ba ki zaci ba ni da adalci ko don ina sonki ne na watsa ta kwandon shara, saboda an ce wasu matan idan suka ji ana wulaƙanta uwar gidan suna fasa auren mutum hakan ua sa ya ce mata
"Gata nan tana bacci abinta" Wani abu ne mai tsini kamar mashi ya soki zuciyar Hasiya a take ta ji tana jin haushin Ramla, hakan ya sa ta ce
"Ka kwanta kaima, ba na son in shiga haƙƙinta ko ni aka yi wa hakan ba zan ji daɗi ba kawai ka kwanta" Tana faɗar hakan ta kashe datar, domin ji ta yi gabaɗaya kishi ya baibaye ta.
Kashe wayar ma ta yi gabaɗaya, ta kwanta zuciyarta tana ƙuna, har ta fara tuhumar kanta a zuciyarta ta ce
'Idan na shigo gidanka ni ba zan juri ganin wata mace a kusa da kai ba'
Shi kuma abin da ta yi sai fa ɗauka saboda tana son ya yi adalci a tsakaninsu, shi ya sa sai ya ƙara zage dantse don ganin kar ya yi wani abu da za ta fahimci yana da ɓaraka a tsakaninsa da iyalinsa, sannan ma ya yi mamaki don hakan ya sake nuna masa cewa Ramla matar rufin asiri ce tun da gashi duk irin yanayin zaman da suke amma ba ta faɗawa Hasiya ba saboda, gashi dai tana nuna akwai zaman mutunci tsakaninsu.
Dakyar ya samu baccin ya yi awon gaba da shi wajen ƙarfe uku, ya yi bacci da mafarkin Hasiya, yana gani a mafarkin sun yi aure suna zama da soyayya mai tsayawa a rai.
Ɓangaren Hasiya da safe ya kira ta ya gaishe ta, ya ce kawai ya kira ne don ya ji lafiyarta, hakan ya sa ta ƙara jin lallai abin nashi azimun ne.
Wajen ƙarfe sha biyu na rana ya kira ta , lokacin ma yana office ya ce muryarta kawai yake son ji, sai wani kashe murya yake ta zuba mata kalamai gani ta ɗan saki jimi don nunawa take kunyarsa take ji, ganin hakan ya sa ya ce
"Har yanxu dai ina miƙa kokon barata, na ƙagu in ji amsa ta"
Ta yi murmushi mai sauti ta ce..
"Na amince Allah bamu zaman lafiya ya baka ladan riƙe iyalin abokin naka" Ta faɗa tana sanya kukan ƙarya a wayar, ya shiga lallashin ta yana faɗin
"Kar ki zubar min da hawayenki, shi yana buƙatar addu,a ne in sha zan riƙe ku amana ba za ku koka ba"
Ta karyar da murya ta ce
"Ni kunyar Ramla nake ji, ka dai ga yadda muke da ita kar ta zargi wani abu"
Jin za ta masa sakiyar da ba ruwa ya ce
"Kar ki nuna mata komai, ki yi mu,amala da ita yadda kuke yi, idan abu ya matso da kaina zan sanar da ita dik da ba wani abu za ta ce ba" Daɗin furucinsa ta ji.
Tun daga wannan rana soyayya ta ƙullu tsakanin Hasiya da Abdulsalam, koyaushe suna manne da juna a waya shi kuma duk zuwa da zai yi gidan sai ya kai musu sha tara ta arziƙi. Soyayya suke yi sosai Hasiya har mantawa ma take da Zahraddin, yanxu kam Abdulsalam ya shafe Zahraddin a zuciyarta.
Wata ranar talata tana zaune suna charting kiran Ramla ya shigo, don ita ma ba a fi kwana biyu da Hasiyar ta kira ta a waya suka sha hira ba, ita Ramla da zuciya ɗaya saboda ba ta kawo komai a ranta ba kuma ba ta san komai ba, ita kuma Hasiya tana iya takunta ne ba ta so ta yi wani abu ko da ƙyas ne da zai ja hankalin Ramla ta gane akwai wata alaƙa mai kama da soyayya a tsakanin ta da Abban Humaira.
Ɗagawa Hasiya ta yi tana faɗin
"Aunty Nasira an wuni lafiya?" Amsa mata ta yi cikin fara,a ta tambayi Dada da sauran yaran, nan dai suka ɗan taɓa hira daga ƙarshe Ramla ta ce
"Ni dai kin yada ni, tun da Abbien su Nasira ya rasu baki taka ƙafarki a gidan nan ba"
Hasiya ta ce
"Kar ki damu in sha Allah zan zo, fita ce take min wahala"
Ramla ta ce
"Aikuwa dai ko tana miki wahala kya zo ki gammu mana" Nan ta amsa mata da faɗin za ta zo ranar asabar.
Ranar asabar da da tashi zuwa, wajen ƙarfe uku da rabi ta gama shiryawa, lokacin yaran suna makarantar islamiya, ta sha atamfarta T bubu an mata kwalliyar stones sai walƙiya suke, ɗaya daga cikin kayan da Abban Humaira ya kawo mata ta kai ɗinki ya biya kuɗin. Ta sha ɗauri ta yafa mayafi daidai da kalar atamfar son kowacce da takalmi da jaka da mayafi, kuɗi yake kashe mata. Saɓanin ita kuma Ramla da ba zai ɗauki kuɗin takanas ya bata ba, wasu abubuwan duk ita take wa kanta da sana,ar snacks ɗin da take tun da biki ko suna tana yi, ko birthday cake da sauransu.
Har ta fito falo ta tuna da zoben da ya bata hakan ya sa ta cire ta ajiye a jakarta, domin ya kwashe komai da ya faru tsakaninsa da Ramla ranar da zai kawo mata zoben ya faɗa mata, amma yadda ya faɗa da ban da yadda abun ya faru domin ya ɓoye laifinsa na nuna rashin ba uwar ƴaƴan nasa kulawa, da kuka nuna mata ita ba kowa ba ce a wajensa.
Wannan dalilin ne ya sa ta ajiye zoben. Shi kaɗai ya zo babi direba, don haka tana fito ya zage glass ɗin motar gabaɗaya ya zuba mata mayun idanunsa da yake ji tamkar ba su taɓa tozali da wata mace da ta yi wa idanun kan gani ba a doron duniya!.
Ganin ya raja,a a kallonta ta canja tafiya tana taku ɗaya bayan ɗaya tamkar tarwaɗa. Da sauri ya buɗe ƙofar ya fito ya buɗe mata ɓangaren mai zaman banza, sai da ta zauna ta ɗago tana masa wani murmushi mai ma,anonin ƙauna da dama a hankali cikin siranta muryarta ta ce
"Na gode" Yadda ta zaƙaƙa muryarta ya sanya ya ji tamkar an zuba maggi da gishiri a murya yana riƙe da murfin ya ce
"Hassy tah, girmanki ne, don ko zan ƙare rayuwata a yi miki hidma ba zan gajiya ba" Da murmushin na dai mai kashe masa jiki ta bashi amsa, hakan ya sa ya rufe mata ƙofar, ya zagayo yana buɗe nashi ɓangaren ya shigo ya rufe ƙofar, maimakon ya ja su tafi sai ya ɗota hannunsa ɗaya a kan sitiyarin idanunsa tsam a kanta ya ce
"Sai ina?" Cikin nuna kunya ta ce
"Sai gidanka" Ya ƙyalƙyale da dariya irin ta ƴan duniya ya ce
"Gidanki dai"
Ta kalle shi tare da kawar da kai gefe daɗi yana cika ta, idan ta tuno kyau da haɗuwar gidan da ya kira da nata, sai ta ji kamar ta fito daga motar ta taka rawa.
Ta juyo ta ce
"Gidanmu dai"
Ya ɗauke ɗaya hannun daga kan sitiyarin yana gyara zaman hularsa ya ce
"Ke da wa?"
Ta yi farrr da idanunta ta ce
"Ni da Ramla mana" Ya yi dariya mai kamar ta rainin hankali amma har yanzu ba ya so ya nuna yana yi wa Ramla abin da bai dace ba ko don kar martabarsa ta zube a wajen Hasiya ko ma ta fasa aurensa baki ɗaya, duk da cewar wasu matan ko da a ce namijinya yi wa wata macen abubuwan da ya cancanci a ƙi aurensa amma da zarar ya je musu da maganar aure sai su murɗe kunnuwansu daga maganganun mutane su karɓi ƙoƙon bararsa.
Ƙaran wayarta ne ya katae musu magana, ta ciro a jaka ta duba ta ce
"Ita ce"
Ya ce
"Ita wa?"
Ta ce "Ramla"
,Ya ce Ki ɗauka mana to"
Ta murmusa ta ɗaga wayar, idanunsa a kan hannunta da ya sha zanen lalle, wata mai ƙunshi a layinsu ce ta mata na sticker duk da ba wani ƙwarewa ta yi ba, amma ya birge shi, bayan ga zanen ƙwararriyar mai ƙunshi can da aka ƙawatawa Ramla hannunra da zanen jan lalle da baƙi amma shi wannan wanda ba halalin nashi ba shi ya ji ya birge shi, don shi duk da kasancewar Ramla mai yawan ƙunshi amma vai damu ya kalla ko ya yaba mata cewar ya birgeshi ba, wani lokacin ma sai a yi mata ƙunshin har ƙunshin ya fita amma ya yi kamar ma bai gani ba.
Tana ɗaga wayar ta ce
"Hello Maman Humaira"
Ramla ta ce
"Na,am baki fito ba? Daman tambayarki zan yi in turo direba ya ɗakko ki?" Ta juya ta kalli Abdulsalam da yake gefenta ta ce
"A,a na hutar da ke, kin ganni ma zan tare adaidaita sahu in sha Allah yanzu zan ƙaraso"
Mama Ramla ta ce
"Allah kawo ki lafiya"
Da amin ta amsa ta kashe wayar, ya kalle ta ya ce
"Ina mai napep ɗin" Sosai abin ya bata dariya ta ce
"Gaka kuwa" Shi ma dariyar ya yi, ya tada motar ya ja suka tafi, yana tafiya a hankali don ji yakr tafiya ce ta musamman in dai da Hasiya a kusa da shi yana tuƙi ba ya so abin da zai dakatar da wannan tafiyar.
Sun kusa zuwa gidan ta ce
"Ka ajiye ni a nan na ƙarasa, kar a je a yi abin kunya fa, wani ya ga fitowata daga motar ko kuma ita mai gayya mai aikin wato Ramla ta fito"
Yana tuƙin ya ce
"Ban yarda ki taka da ƙafarki ba sai na kai ki har ƙofar gidan, kuma ita ina za ta je babu izinina kin ga ai dole sai ta tambayeni za ta fito daga gidan ko?" Kai ta samu kanta da gyaɗa masa.
A bakin get ɗin ya ja ya tsaya, ya zuba mata idanu ya ce
"Ban gaji da ganinki ba Hassy, wallahi ba na taɓa gajiya da ganinki, kuma ba na jin akwai wata rana da za ta fito daga gabas ta faɗa a yamma da idanuna za su gajiya da kallonki" Ta ce
"Ka jika ko, ni dai ba da ni ba ka bari ma yi wannan maganar daga baya" Ta faɗa tana buɗe ƙofar ta fita, shi kuma ya ja motar ya bar layin ma baki ɗaya.
Get ɗin ta tura ta shiga, mai gadi ya gaishe da ita, duk da ya santa a baya amma yau sai ya ga gabaɗaya ta canja masa yanayin shigarta da ma wayar da take hannunta, bayan ya san wani lokaci ta taɓa zuwa Ramla ba ta nan ta ce wayarta ta mutu sai shi ya ciro batir ɗin wayarsa ya bata ta saka a wayarta ta kira Ramlar.
Ramla da murna ta tare ta suka nufi part ɗinta hannunta cikin nata. Bayan sun zauna aka gaisa amma Ramla ta kalli kayan jikin Hasiya da kuma wayar hannunta, tana ta mamakin irin wanna sauyi da Hasiyar ta samu bayan mutuwar mijinta, wanda a baya talauci ya ɓoye yarintar ta duk wani tsufa ya kamata na dole amma yanzu ta dawo kamar budurwa daman da yake ƙaramin jiki ne da ita amma tana da diri.
Lemo kaɗai ta sha cikin kayan da Talatuws ta cika gabanta da su, ta ce ba ta daɗe da cin abinci ba ma. Suna nan suna taɓa hira aka kira la,asar suka gabatar da sallah. Zuwa can wajen ƙarfe biyar ta ji shigowar motar mai gidan, ta tashi tana sanar da Hasiya tana zuwa Abban Humaira ya shigo. Da to ta amsa mata tana fita ta taɓr baki ta ce
"Ke baki san ma tare muke ba ya ɗan wuce ne don ya miki basaja" Message ta masa ta ce
"Barka da shigowa" Shigar Ramla ɗakinsa ya yi daidai da shigowar saƙon, ya ɗauki wayar yana karanta saƙon, Ramla dai murmushi ta gani kwance saman fuskarsa. Duk da ta san ba ya maraba da zuwanta amma ta je ne don kar Hasiya ta gane akwai ɓaraka tsakaninta da mijinta, tun da ita a duniya ta tsani a ga wata hanya duk ƙanƙantar ta da za a gane rashin jituwar da Abdulsalam yake mata, sannan ta je ne don ta sanar masa da zuwan Hasiyar don kar ta ga ta xo gidan abokin marigayin mijin nata amma basu gaisa ba bayan ta san yana gidan.
Bayan ta zauna ta ce
"Barka da shigowa"
A taƙaice ya ce
"Barka"
Ta ce
"Daman Hasiya ce za ku gaisa" Ya ɗaure fuska ya ce
"Ni fa ba na son wani gaishe-gaishe, ba kun gaisa da ita ba to mene ne na cewar mu gaisa ni fa ba na son takura, idan abinci ne suke buƙata ki auna musu shinkafa kawai" Idanunta suka kawo ƙwalla, ta ce
"Wai sai yaushe za ka daina wannan halin don Allah, bawan Allahn nan ya rasu ma amma ba za ka can... Tsawa ya daka hakan ya sa ya haɗiye sauran maganar.
Tashi ta yi za ta bar ɗakin tana zuwa bakin ƙofa ya ce
"Ki shigo da ita minti biyu na bata mu gaisa" Da to ta amsa masa, saboda ba ta so ko kaɗan Hasiya ta ji babu daɗi idan aka nuna mata halin ko in kula.
Tare suka shigo, lokacin yana danna waya ya dawo falo, Hasiya tana ɗan nuna baƙunta ta zauna a kujera daga kusa da Ramla ta ce
"Abban Humaira ina wuni"
Ya amsa da faɗin
"Lafiya ƙalau, ina wajen Dada da yara" Ta amsa da faɗin
"Kowa lafiya"
Ya ce
"Madallah" Ya faɗa idanunsa a kan waya.
Tashi ta yi cikin sanyin jikin tana masa sallama, Ramla duk ba ya ji daɗin yadda ya amsa ba, kafin mutuwar Zahraddin ba, da yake nuna kulawa har wani lokacin yana yi wa Hasiyar kyauta.
Hakan da ya nuna ya sa Mama Ramla zargin ko don daman yana ganin Zahraddin ɗin ne a raye. Hannu ya sa a aljihu ya ciro kuɗi dubu goma ya ce Ramla ta ba Hasiyar ta siyawa yara wani abu, godiya Hasiya ta masa cikin girmamawa tana haɗawa da addu,a sosai Ramla ta ji daɗin kyautar kuɗin da ya bata a ƙalla dai ko ba komai ya kula yaran abokin nashi tun da ya ce a siya musu wani abu.
Ramla ce a baya Hasiya tana biye da ita, Hasiya ta juya ta yi masa bye-bye haɗe da kashe masa ido ɗaya, shi ma hannun ya ɗaga mata yana kuma mata alama da hannu cewar shi zai mayar da ita gida.
*** [7/29, 5:31 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH