KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿1️⃣3️⃣

*HASIYA*

Da suka koma falon Ramla suna zaune suna ɗan taɓa hira, jefi-jefi a ɓangare guda kuma suna ta chart da Abdulsalam suna musayar kalaman ƙauna. Ita Ramla tana zaune basho ba ta san wainar da ake toyawa ba, da yake ita tana waccan kujerar ita ma tana waccan, ba ta san cewar charting take da mijinta a gabanta a cikin gidanta, hausawa suka ce rashin sani ya fi darr duhu!.

Ganin ya fiya mayar da hankali a kan wayar saɓanin maganganun da suke Mama Ramla cikin wasa ta ce

"Ni kam wai charting kike ne? Ko dai an fara kula manema ne tun da kin yi idda" Gaban Hasiya ne ya buga da ƙarfi, don sosai maganar ta bata tsoro har take tunanin kar dai Ramlar ta fahimci da mijinta suke magana. Da ɗan sauri ta ajiye wayar tana ƙirƙirar murmushi yaƙe ta ce

"Ah haba dai! Kema da wani abu ni yanzu ai aurr ba ya ma cikin lissafina, bare har na kula maza ni fa a takaice ma yanzu gani nake idan zan kula wani kamar dai amanar Zahraddin zan ci, ke ni fa na gwammace in rayu ma babu aure don na gama aure a duniya daga kan Abbien su Nasira" Ta faɗa tana ƙirƙirar ƙwallar ƙarya, wani irin karaya zuciyar Ramla ta yi tana tuna zafi da raɗaɗin mutuwar miji da take ji ana faɗa tun da ba ta taɓa tsintar kanta cikin wannan hali ko yanayin ba, hakan ya sa cike da tausayawa ta ce

"Allah sarki ki yi haƙuri duk mai rai ai dama mamaci ne kowa lokacinsa yake jira, mu ci gaba da masa addu,ar saduwa da rahmar ubangiji, ke kuma ki daure ki cire wannan ra,ayin watarana idan damuwar ta ragu sai ki yi aure tun da ai baki wuce auren ba" Kai ta shiga girgizawa hawaye ya sirnano daga idanunta, da sauri Mama Ramla ta taso daga kujerarta ta zo gaban Hasiya, hannunta ta kai ta kamo nata, tana rarrashin ta, haɗe da faɗa mata kalamai masu ratsa zuciya na nasiha.

A ɓangaren Abdulsalam wanda ya koma ɗakinsa ya hau gado ya yi ɗai-ɗai yana kwance reran, ya ɗaga ƙafafunsa sama ya jingina a jikin bango, yana charting da masoyiyarsa Hasiya, yana jin tamkar ita kaɗaice duk duniya a cikin mata da ta fi kowacce iya kalami da kuma soyayya. A daidai gaɓar ne ya ga ta sauka daga whatsapp ɗin, wanda a can falon Ramla lokacin da ta mata furucin da ta ajiye wayar, shi ne da hasken wayar ya ɗauke sai ya mata saƙo ya ga ya yi layi ɗaya alamar ta sauka.

Ransa ne ya ji ya ɓaci da aka katse masa wannan yanayin mai daɗi. Ganin an ɗauki ɗan lokaci ba ta hau ba, sai ya yanke shawarar ya mata plashin, ya san idan ta ga plashing ɗin za ta gane yana nufin ta hau online.

Tun da da suna charting ta kwatanta masa irin zaman da suke yi da Ramla, wato kowacce tana kujerarta da ban sun ba juna tazara hakan ya sa ya yanke shawarar kiranta tun da ya san Ramla ba za ta ga kiran ba.

A daidai lokacin da ya kira, a daidai lokacin da Ramla ta dawo kusa da ita ne take lallashinta, a wannan lokacin ne kiran ya shigo, Hasiya da gabaɗaya daman ba a daidai take jinta ba tun furucin Ramla da ta ce mata ko magana take da manema. Jin wayarta ta ɗauki ƙara, kuma daman tana saka ran zai iya kiranta a yadda hirar da suke ta ɗauki zafi, suna ji tamkar ido da ido ne suke hirar ba wai ta waya ba, ta san zai iya gwada kiran duba da yadda ta sanar masa irin tazarar da take tsakaninta da Ramla.

Hasiya da sauri ta warce hannunta ɗaya, daga hannun Ramla da ta kama hannun duka biyu, tana zaune daga gefenta, tana wartar hannun ta yi saurin ɗaga wayar ta kifa, wato ta kifa fuskar a kan kujera.

Ramla cike da mamaki ta ce

"Hasiya....

*UMMA MAGAJIYA*

Duk yadda ta yi ta fahimtar da Goggo lamarin da take so ta fahimta ba ta fahimta ɗin ba, hakan ya sa ta daure ba ta faɗa mata manufarta ba sai dai ta sanyana ranta akwai lokaci domin kafin dai Ruma ta kammala takaba to komai ta san zai daidaita, duk da ta san ta ce mata ba za a ɗauki dogon lokaci ba zai ƙara auren, amma dai ta san ba za a yi auren ba tare da an sanar mata ba hakan zai sa a lokacin da za a ƙara tuntuɓarta da maganar auren ta shugar da maganar Ruma.

Ranar dai haka ta baro gidan da ɓacin rai ga haushin Goggo kamar ta karta, ta kasa gane ko dai fahimta ne ba ta yi ba.

Lokacin da ta dawo gidan, Ruma ta dafa abinci ita da yara sun ci, sai dai cikinta ya kaɗa a yadda ta ga Umma ta dawo gidan, kamar dai babu alamun nasara a lamarin. Wani yawu ta haɗiye muduk, wanda ta ji haɗiyewarsa kamar wanda ta gaɗiyi ƙaton dutsi a zuciyarta ta ce

'Kar dai in yi saki na dafe, ya aka yi ita Umma da ta ban ƙwarin gwiwar kashe auren tana bani tabbacin zan auri Yaya Muhammad ɗin, amma in ganta ta dawo jiki sanyi ƙalau'

Umma sai da ta zauna a kan tabarta, ta saka hannu ya sharce gumin goshinta, ta ce

"Wash Allah"

Ruma da gabanta yake faɗuwa ta ce

"Umma ya na ganki haka? Ya ake ciki?"

Umma a faɗa ce ta ce

"Haba Ruma daga dawowa ta, ba kya bari in fatsar da gajiyar ba ma, za ki fara jero min tambayoyi kamar a ɗakin jarabawa"

Shiru ne ya ratsa wajen, su Umar suna ɗaki suna wasa.

Ruma ta ce

"Umma ko dai Goggon ba ta gida" Banza ta mata ta tashi ta nufi randa sai da ta je ta sha ruws ta dawo, ta nufi tukunya ta zubo abinci saboda tsabar takaicin rashin dacen abin da ta je dominsa shi ya sa ko abinci ba ta ci a can ba ta kamo hanya da rana gaɗau-gaɗau ta dawo.

Ta cinye abincin tass ta ce

"Rumasa'u na je na same ta, amma ta inda nake mata bayani ba ta nan take fahimta ba, a ƙarshe dai ba ta fahimci cewar ga abin da nake son ƙullawa ba tsakaninki da Muhammad ɗin"

Ruma ta ce

"Haba Umma ai sai ki faɗa mata yanxu idan ta sama masa wata fa, ke fa kika bani tabbas ɗin zan aure shi"

Umma ta ce

"Kina da wutar ciki wallahi, ai aure in dai ba a yi ba sai dai ɗayanku ne ba ya numfashi matuƙar kuna raye kamar an yi aure an gama, na bata dama ne dai, saboda kar ta ga daga xuwana gidan na faɗa mata mutuwar aure kuma in zo da maganar haɗin aure, hakan zai sa ta zargi wani abu, amma kafin dai ki yi idda cikin hikima zan ke aika ki gidan nata, har hankalinta ya kai kanki idan kuma hankalin nata bai faɗa mata gaskiya ba sai na fito mata a mutum, wato na warware mata na mata magana da harshen hausa ɓaro-ɓaro yadda za ta fahimta" Ajiyar zuciya Runa ta sauke, duk da tana ɗan jin taraddadi saboda a tunaninta Umma za ta dawo da dahir ɗin maganar cewa tana kammala idda babu makawa za a ɗaura auren amma sai aka samu akasi.

*ALHAJI MUHAMMAD*

Ganin wani kallo da take yi masa ya sanya shi shan jinin jikinsa cike da takaici ta ce

"Wannan wace irin rayuwa ce, haka kawai ka faɗar min da gaba"

Yana kallon ta ya ce

"Ashe dai kina sona, ji yadda hankalinki ya tashi da kika ji na ce wayyo Allah cikin muryar da take alamta akwai abin da yake faruwa"Tsabar takaici ka sa magana ta yi, yana ta faɗa mata cewar kwalliyar ta ya xo ya gani domin tun daga ɗakinsa ya hangi fitowarta hakan ta sa ya zo ya gani idan ma siyar masa za a yi ya amince zai ga kwalliyar. Banza ta yi masa ko ta kansa ba ta bi ba, sai da ta cire kayan ta karkaf ta saka rigar bacci doguwa mai ƙaramin hannu ta ce

"Na sha faɗa maka ƙudurina, amma kai na kasa gane wane irin mutum ne da baka fahimta ko kuma kana sane kawai rainin hankali ne" Hannunsa ya makale a ƙirjinsa yana bin ta da kallo shi ko faɗa take yi ma ba ganewa yake yi ba illa iyaka dai yana jin ɓacin rai idan tana faɗa masa maganganu sai dai ba a ɗaukan lokaci yake mantawa.

Ya ce "Ni dai ba wannan na tambayeki ba, kaya ne kin riga kin cire har fa cewa na yi zan biya, shin bakya ganin kallonki ko kallon shigarki halalina ne? Amma na cw zan biya, duk da haka baki min lamuni ba to mai kike so in fahimta kuma?"

"Ka fahimci ba na sahun macen da zan taɓa faranta maka, ni fa tun da na gama jin labarin maza kai ni babu namijin da zan yi komai don na faranta masa ko na birge shi, har kullum ina tunani tare da hangen hanyoyi masu yawa don in daƙile duk wani abu da za ka ga farinsa a tattare da ni"

Taku ɗaya biyu ya yi ya juya bayansa ya ce

"Naja'atu ko dai soyayyarmu ta rikiɗa ta koma ƙiyayya ne bani da labari?"

Ba ta bashi amsa ba sai da ta je ta kama ƙofar banɗaki ta juyo ta kalle shi a wulakance ta ce

"Shafa ka ji" Tana faɗar hakan ta buɗe ta shige ta banko ƙofar da ƙarfi, ransa in ya yi dubu ya ɓaci bai taɓa jin abin da Naja'atu take masa tozarci ba ne sai yau. Ya jima a tsaye amma ba ta fito ba kuma babu alamar ma za ta fito, ransa ya ringa ƙunci da zugi hakan ya sa ya juya cikin sanyin jiki ya buɗe ƙofa ya fito daga ɗakin.

Dakyar ya kawo kansa ɓangarensa yana ta saƙe-saƙe da zancen zucin da tambayoyi masu yawa suke bijiro masa dangane da zamantakewar auratayyarsu.

*NURIYYA*

Tana shiga ɗakinta ta karkaɗe zanin da take shimfiɗawa wanda shi ma Ammar ne ya siya mata kasancewar ta faɗa masa a kan tiles take kwana shi ne ya siyo ya bata take shimfiɗawa ta kwanta a ka.

Tana kwantawa bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. Washe gari kasancewar lahdi babu makarantar boko sai islamiya, hakan ya sa ta tashi tana zaune cikin ta yana ta ƙugi. Banɗakinta ta shiga ta yi wanka da ruwa saboda babi sabulun wanka a banɗakin sannan kuma store ɗin da ake ajiyewa ba ta da damar ta shiga bare har ta ɗauka daɗin daɗawa ba ta da ƴancin da za ta tambaya a bata.

Har ta fito daga wankan take jin jikinta yana mata ƙaiƙayi so take kawai ta yi wankan da sabulu rigarta ta mayar ta fito ta yi can inda ake wanki ta shige duddubawa ta samu sauran sabulun wanki ta taho da gudu ta faɗa ɗakin nata gudun kar Hajiya ta ganta ko wani cikin ma,aikatan gidan ƴan gulma da neman wuri su faɗa mata, ya san muddin hakan ra kasance to kashin ta ya bushe gashi dai sabulun ba amfani za a yi da shi ba sai dai a jefar amma saboda kar ta amfana sai an mata hulunci da za ta ji daman sati guda ta yi ba ta zubawa jikinta ruwa ba.

Tana shiga banɗaki ta yi wankan ta da sabulun, tana cikin yi ma ya karye kasancewar ya zama ƙarami, amma haka ta fito da shi ta ɓoye a cikin kayan ta.

Kayan makarantar ta ɗakko, ta saka, bayan ta saka take leƙa tsakanin ƙafafunta, har sai da ta hangi pant ɗin ta wanda shi ma ya yi tsufa, dama guda biyu ne take da sauran duk sun yage guda biyun ma Ammar ne ya siyo mata. Hijabin ma da ta saka wuyan ya yi yawa saboda yagewa da ya yi, lokacin ƙarfe takwas da rabi, tana fitowa tana tafi saɗaf-saɗaf, wata uwar tsawa da Hajiya Hauwa ta doka mata sai da takalmin hannunta da ta maƙale saboda kar a ji takun tafiyarta, ya suɓuce ya faɗi a take jikinta ya ɗauki ɓari saboda cikin tsawa ta ce

"Keeee!"Juyowa ta yi jikinta yana karkarwa da sauri ta durƙusa gwiwoyinta a ƙasa ta ce

"Ina kwana" Tana aika mata mugun kallon tsananin tsana ta ce

"A gidan uwaki na kwana, shegiya mai baƙar aniya,da don ubanki baki je kin gaisheni ba sai yanzu da na ganki ne munafuka" Kai kawai take jijjjigawa tamkar mala,ikan mutuwarta haka take kallon Hajiya tana mugun tsoronta saboda ba ta jin daɗi ko kaɗan a hannunta.

Jin ta sake sakar mata wata tsawar tana tambayarta sai yanzu za ta gaishe ta ta ce

"Kin ce kar in ke shiga ɓangarenki, kar in je in kai miki baƙin halina ɗaki" Harara take aika mata don daman ita da kanta ta hanata saboda ba ta ƙaunar ganinta amma ta tambaye ta dalilin ne saboda kawai ta tsorata ta.

Cike da nuna tsana ta ce

"To a kan mai zan barki kike shiga min ɗaki, halinki da kika yi gadon wajen tsohuwarki ki je ki kwasa mini" Kanta a ƙasa hawaye yana zuba ta tsani ta ji Hajiya tana cewa mahaifiyarta mai baƙin hali, duk da kasancewarta yarinya amma tana jin ciwon abun, musamman da ta san mahaifiyarta ta mutu.

Maganarta ce ta katse mata tunani da faɗin

"Ke uwar ƴan karatu da neman ilimi, da sassafen wannan har kin saka wannna tsumman kayan makarantar taki mai kama da na almajirai, saboda baƙar ƙwawa jiya ma sai da aka koro ki amma shi ne don naci kika shirya za ki je, Allah sa yau ma a miki dukan tsiyar a koro ki, idan kin gaji ai dole ki haƙura"

Kai ta ɗago fuskarta da ɗan guntun hawayen ta ce

"Ya Ammar ya ce zai biya min" Cike da harararta ta ce

"Uwar ƴan roƙo da cusa kai babu kwarjini, shi wannan ɗan a nacen wahalalle kullum shi yake taimakonki, to ai duk abin da yake miki ba a kyauta yake miki ba"

Nuriyya ta ce

"Wallahi kyauta yake min, ai bani da kudin da zai min rance"

Da wafa dariya ta sheƙe har sai da Nuriyya ta zuba mata idanu, lokaci ɗaya ta daina dariyar ta haɗe rai ta ce

"Sakaryar banza an faɗa miki da kuɗi za ki biya shi, ai akwai lokacin da aai fanshe wataƙila yana jira ki ƙara tasowa sannan shi ma ya ƙara girma yadda zai ji daɗin nomar shuka da ya yi wa ban ruwa" Nuriyya duk ba ta gane kalaman ba kawai da idanu ta bita, ganin tana kallonta ta kai hannu ta dungure mata goshi tare da saka hannun ta riƙe mata kumatu da ƙarfi har sai da ta saki ƙara sannan ta sakar mata, ta sake kai ƙafarta ta haure Nuriyya sai gashi ta ɓingere gefe daga durƙuson da ta yi a kan gwiwarta. Juyawa ta yi ta tafi ta barta a wajen, Nuriyya ta tashi tana hawaye ta saka takalmin ta ta fita daga gidan.

Tana tafiya tana share hawaye da gefen hijabin ta, har ta je gidan su Ammar. Tana shiga ta ga ɗakinsa a buɗe can ta nufa ta tsaya a ƙofa ta yi sallama ya amsa ya ce ta shigo, tana shiga ya kalli idanunta ya ce

"Nuri kuka kika yi?"Wani hawayen ne da ba ta san zai zubo ba ya zubo ta goge, tare da gyaɗa masa kai.

Hannunta ya kama suka shiga gidan, Kaka ta shiga lallashin ta, koko da waina aka ba ta ta shiga ci tana gamawa ta ce

"Ya Ammar kuɗin makarantar"

Ya yi dariya ya ce

",Ni bani da kuɗi" Da kuka ta fashe, Kaka tana cewa

"Ke rabu da shi wasa yake miki, ai tun wajen ƙarfe bakwai ya je ya kaiwa malamin naku kuɗin" Da dariya ta fashe cike da murna

Ammar ya ce

"Ana dariya ana kuka"

Kaka ma ta yi dariya, ya ce

"Tun da lokacin makaranta ya yi ki tashi ki wuce, kar ki makara a miki bulala, nima zuwa zan yi in tafi talla, saboda gobe nima zan je makarantar boko"

Tsaye ta miƙe ya taka mata zuwa ƙofar gida ta ce ya raka ta ƙofar makaranta, da yake babu nisa duk a unguwar ne, haka ya tafi suna zance tana cewa

"Kullum Hajiya sai ta ce wai duk abin da kake siya min bashi ne za ka fanshe" Shi ma dai ba gane abin da ake nufi ba ya yi ya ce

"Ni dai kyauta nake miki ba bashi ba" Ya ɗora da faɗin

"Ji yadda wuyan hijabinki ya yage da tun wuri ne na kai an ɗinke miki" Ta saka hannu daga cikin hijabin ta riƙe saitin wajen ta ce

"Sai in ke riƙewa da hannu kafin a ɗinke, daman ƴan ajin suke ta xolayata" Ya ce

"Ki rabu da su kansu suke faɗawa koma mene ne"

Ta ce

"Sai a ɗinke min har wandon, shi ma ya yage kuma ana ganin pant ɗina daga yagar, gashi pant ɗin ma ya yi tsufa" Cike da tausayi yake kallonta duk da shi ma maraya ne har yau kuma bai gama ɗanɗanar ɗaci da raɗaɗin maraici ba, amma dai yana tausayinta tun da ita ba da da mai tallafa mata ko nuna damuwa ko kulawa a gare ta bayan mahaifinta yana raye, sai dai shi da Kakarsa ne kawai take samun hakan daga wajensu, saɓanin shi da yake da Kakarsa da yake ganin ta maye mishi gurbin iyaye!.

*** [8/2, 6:40 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH