BOOK 1
🅿1️⃣4️⃣
Ya dai Hasiya" Ta tambaya tana kallonta, amma dai ita ba ta ga wanda yake kiran ba abu ɗaya ta sani shi ne kira ya shigo wayar.
Hasiya wacce ta ji gabaɗaya ta rasa ma mai za ta yi, gabanta yana faɗuwa sai da ta lura Ramla ba ta ga sunan mai kiran ba, sannan ta ce
"Gabana ne ya faɗi da kiran nan ya shigo, idanuna sai suka min gizo da sunan Abbieyn su Nasira" Ta faɗa tana fashewa da kukan tsantsar kissa.
Wani irin tausayinta ne ya dirarwa Mama Ramla a take ta ji tata zuciyar ta karaya, tana sanya kanta a zuwan da ita ce wataƙila ta ji fiye da hakan, idanunta ne suka yi raurau cikin rauni da sanyin murya ta ce
"Ki yi haƙuri Hasiya, komai kin san muƙaddarj ne a rayuwar mutum babu wani abu da zai faru face da sanin mahalicci abin da Abbien su Nasira ya fi buƙata shi ne addu,a sannan ki yi fatan ubangiji ya sake haɗa rayuwarku ke da shi a cikin aljanna"
Hasiya jin tarkoh da ta naɗa ya kama tsuntsu a zuciyarta ta ce
'Hummm ko kaɗan baki da tunani kina da saurin yarda da amincewa da mutum, ai Zahraddini iya rayuwar duniya kaɗai muka yi da shi kuma daga nan mun rufe babin domin a lahira sai dai na rayuwa da Abdulsalam a aljanna saboda shi ne mijin da nake son na rayuwa da shi a can, tun da gidan talaka a aljanna ma ba zai kai na me kuɗi ba, duk da gidan talaka a aljannar ya fi duniya da abin da yake cikin ta, sannan va wai ana nufin me kuɗin a duniya shi ne mai kuɗi a aljanna ba, sannan talakan duniya shi ne talakan aljanna gwargwadon yawan ladanka gwargwadon matsayin muhallinka amma dai ni a nawa ganin na yarda da maganar da bahaushe yake cewa juma,ar da za ta yi kyau daga laraba ake gane ta'
A fili kuma ta saka hannu ta goge idanunta ta ɗan ja hanci ta lumshe idanunta ta buɗe irin ita kaɗai ta san ɗaci da ƙuncin da zuciyarta take ciki na rashin mijinta, sannan ta ce
"Ba komai Ramla, in sha Allah zan ke masa addu,a ai Zahraddin mutum ne da za a so sake rayuwa da shi a karo na biyu wato rayuwa a aljanna, kar ki damu yanzun ma kawai gizon da idanuna suka min ne sai na ji hankalina ya tashi"
Ramla ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Ki yi haƙuri"
Kai ta gyaɗa mata.
Ta ɗan jima tana mata ƴar nasiha, har yaran suka yi sallamar dawowa daga makaranta cike da murna haɗe da ladabi suka gaishe da ita, suna tambayarta su Nasira, ta ce suna lafiya ta baro sun tafi makaranta.
A ɓangaran Abdulsalam ya ji haushin rashin hawanta online bayan kira da ya mata, sai dai ko kaɗan bai danganta hakan da jin haushin ta ba, ya san babu dalilin da zai sa ta yi masa hakan ya fi alaƙanta hakan da cewa Ramla ce ta ɗauke mata hankali da surutun banza har ta kai ga ta hana ta bashi nata lokacin. Wayar ya ajiye yana doka tsaki ya fili ya ce
"Babu abin da na tsana illa mutum ya katse min jin daɗina, ko kaɗan bana son a ce ina tsaka da kurɓar romon soyayya wani ya datse min wannn damar" Ya faɗa yana sake jan tsaki a karo na biyu a zuciyarsa yana faɗin
'To ko dai Ramla ta fahimci abin da yake tsakanina da Hasiya ne, ta fara amfani da wannna damar a matsayin kissar da za ta dakatar mana da jin daɗin hirarmu ta soyayya?' Ya faɗa yana yin nazarin zarginsa, sai dai kafin ya gano bakin zaren wata zuciyar ta ce
'Kai ma dai da wani abu kake, kamar baka san halin Ramla ba, yadda take kishinka, da a ce ta san da wannan abin da yake faruwa tsakaninka da Hasiya da tuni ta yi wa Hasiyar korar kare ma saboda kishi, kawai dai sai dai wani abu ba wannan ba' Hannunta ya saka ya murtsuka idanunsa.
Yana nan yana jiran tsammani, ya ɗauki wayar ya sake hawa whatsapp ɗin, amma ya ga dai har lokacin ba ta nan, ji ya yi tamkar ya tashi ya kama hanyar part ɗin Ramla ya je ya taho da Hasiyar a gaban Ramlar ko ma mai zai faru ta famjama famfam kawai.
A can ɓangaren Hasiya da Ramla ta gama mata nasihar sai ta tashi ta koma mazauninta, suna cikin bakan ne yaran suka dawo, da suka fita daga falon, Hasiya ta ɗauki wayarta ta koma whatsapp ɗin.
Lokacin ma yana cikin account ɗinta ai kuwa ya hangota online, wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana jin wata nutsuwa da kwanciyar hankali tana ratsa shi domin kuwa da ya ganta online ɗin nan sai ya ji tamkar a kusa da shi ya ganta a zahiri.
Ta ce
"Ramla ce ta min shishshigi shi ya sa ka jini shiru, kaɗan ya rage ta ga sunanka lokacin da kake kira" Emoji ya turo mata na zaro ido ya ce
"mai ya kai wayarki hannunta?"
Ta ce masa
"Wani munafurcin ta dai wai lallashina ta zo yj?" Ta ce tana kwashe yadda suka yi ta faɗa masa.
Ya rubuta mata
"Mu bar maganar ma ƙarasa idan kin koma gida, ina fitowa daga sallar magriba zan kai ki gida, ki zauna cikin shiri" Amsa masa tana kashe datar ta ajiye wayar.
Ana kiran magriba Ramla ta ce su yi sallah sai su ci abinci" Hasiya ta ce za ta yi sallar dai amma ba za ta tsaya cin abinci ba gida take son tafiya.
Ko da ta shiga banɗakin Ramla ta yi alwala ta tsaya tana ƙarewa banɗakin kallo tana hango nata banɗakin irinsa wanda zai zama mallakin ta nan ba da daɗewa ba.
A ɓangaren Abba fitowarsa daga ɓangarensa don zuwa masallaci, ya ga Aslam ya fito yana jiransa, su kuma su Aslamiyya da Humaira suna sallar a ɗakinsu.
Suna zuwa da suka yo sallar magriba, gabaɗaya hankalinsa yana kan komawa gidan, tsaye ya miƙe ya fito daga masallacin, Aslam ya biyo bayansa ya fara tafiya ya tsinci muryarsa yana faɗin
"Abba" Dakatawa ya yi tare da juyowa ya amsa Yana zuwa ya ce
"Abba ya na ga za ka tafi gida? Ba sai an yi isha'i za mu tafi ba?" A fili ya ce
"Inason shiga banɗaki ne" Jin hakan sai ya ce
"Ni bari na koma" Abba ya ce
"Ko dai mu tafi gidan" Kai ya jijjiga alamar a,a ya juya ya koma masallacin.
Abba a fili ya ce
"Wannan yaron yana son kawo min cikas" Ya faɗa yana ɗab ɗaga ƙafa ya koma cikin gidan, yana zuwa ya yi wa mai gadi umarnin ya buɗe masa ƙofa, direba ya taho cike da girmamawa tunaninsa shi zai tuƙa Abba, amma Abban ya dakatar da shi, ya shiga motar ya tada a zuciyarsa ya ce
',Duk wani abu da zai shiga tsakanina da keɓewa da Hassy ba so nake yi ba, a ƙalla zan zo mu kasance mu biyu daga ni sai a ita a duniyar lobayya'
Ya ja motar ya fita daga harabar gidan, mai gadi ya mayar da ƙofar ya rufe.
A ɓangaren Hasiya, tana zaune suna taɓa hira jefi-jefi amma hankalinta yana ga wayarta, Ramla ta ji ƙaran buɗe get tare da fitar mota tana mamakin wanda ya fita saboda ta san lokacin mai gidan yana madallaci sannan tana mamakin abin da zai fitar da shi a daidai lokacin wannan. Basarwa ta yi tare da kawar da tunanin. Hasiya wayarta ce ta yi ƙara alamar shigowar saƙo, ta ɗan saci kallon Ramla ganin hankalinta yana kan TV ta buɗe saƙon ta karanta abin da aka rubuta kamar haka
" _Ina mota ina jiranki"_
Tana ganin hakan ta ɗan wayince ta ce
"Bari na tashi na tafi, na ga Dada ta fara min filashin" Ramla ta ce
"Wato ba za ki ci abincin namu ba dai ko?" Ta tambaya tana murmusawa, itama murmusawar ta yi ta cr
"Hankalina ne duk ya yi gida, amma duk ranar da na dawo zan ci" Ta faɗa tana miƙewa ta ɗauki jakarta, Ramla ta ce
"Ina zuwa" Ta faɗa tana shigewa ɗakinta jimawa kaɗan ta fito ɗauki da ledar viva ta miƙawa Hasiya tana faɗin
"Wannan saƙon Dada ne kayan ƙamshin kuma naki ne" Karɓa ta yi tana gode mata a fili da nuna jin daɗinta a zuciyarta ta ce
'Wai ke nan mai gwaninta, to nan ba da jimawa ba Dada za ta fi ƙarfin kyautar wannan kayan naki har ni ɗin ma' Ta faɗa ba tare da ta san ma mene ne a ciki ba.
Ramla ta yi-ta yi ta sanya direba ya kaita amma firr Hasiya ta ce ta bar shi ba komai za ta tafi a napep. Haka ta haƙura ta ƙyale ta, tun da ta ga ta kafe a kan maganar bayan wannan ne karo na farko da ta taɓa ƙin yarfa direba ya kaita gidan, ita kuma Ramla sai ta yi zaton ko don tana ganin Zahraddin ya rasu tun da shi ne ginshiƙin dangantakarsu. Haka ta bata haƙuri cewar mai gidan ya fita da sun yi sallama amma ta ce babu komai ma tun da sun gaisa.
Har sai da ta buɗe get ɗin ta fita sannan Ramla ta koma cikin gidan.
Tana fitowa ta hanga -ta hanga bata ga motar ba, tana shirin kiransa ta ga kiransa ya shigo, ɗauka ya yi tare da kara wayar a kunne kafin ta yi magana ya ce
"Ki taho gaba kaɗan" Da to ta amsa masa don ta ma hangi motar ta shi a ɗan nesa da gidan.
Sai da ta kusa ƙarasawa wajen motar ta ja tunga ta tsaya ta doka masa waya ya ɗauka yana faɗin
"Na hango ki fa ki taho"
Ta wani shagwaɓe murya tana faɗin
"Ni dai na gaji ka dawo da baya" Wata dariya ya saki yana faɗin
"Da girman kujerarki gimbiya Hassy" Ya faɗa yana mai kashe wayar ya dawo da baya har sai da ya zo daidai inda take tsaye ya tsaya yana shirin fitowa ya buɗe mata ƙofar ta dakatar da shi da faɗin
"Na hutar da kai" Zamansa ya gyara yana yin ƴar dariya, ta kama murfin motar ta buɗe a daidai nan Aslam wanda fitar iska ta karya masa alwala(Tusa) Ya fito daga cikib masallacin zai sake alwala, idanunsa suka sauka a kan motar Abbansa lokacin ta buɗe a kan idanunsa ta shiga.
Duk da daga ɗan nesa fa masallacin ne motar take amma hakan bai hana shi gane motar mahaifinsa ba.
*ALHAJI MUHAMMAD*
Misalin ƙarfe biyar fa rabi na yamma, zaune yake a bayan mota direba yana jansa, bayan layin gidansa ta nan suka biyo, miƙowar da direban zai yi zuwa shan kwanar da za ta sada su da layin gidan nasa, wata tana matashiyar mace tana tafiya, cikin rashij sani da kuma tsautsayi da Allah ya aiko, direban ba tare da ya sani ba ya bige ta, faɗuwa ta yi duk da ba wani sosai ya bige ta ba. Wani uban birki ya ja suna kwasar salati shi da Alhaji, wanda motar tana tsayawa ya yi saurin fitowa daga ciki ko ƙofar bai rufe ba, lokacin har mutane sun taho ana hayya-hayya. Zaune ta tashi tana riƙe da ƙafarta wajen saitin gwiwarta, tana ta girgiza kai alamar ita kaɗai ta san mai take ji.
Matashiya ce wacce ba za ta wuce shekara talatin ba. Sanye take da blue black ɗin laffaya mai manyan fulawoyi, ta naɗa ta sosai ta naɗu tamkar wanda daman an yi laffayar ne saboda ita saboda tsabar yadda ta yi matuƙar dacewa da ita!.
Da Alhaji da direba a kusan tare suka ƙaraso suna mata sannu, mutanen da suka zo ma ganin abin da ta faru kowa yana faɗin albarkacin bakinsa, wasu suna faɗin laifin direban ne wasu kuma sun faɗin ita ce da laifi.
Direban ne ya ce
"Sannu baiwar Allah, dan Allah ki yafe min" Ba ta ɗago ba ta ce
"Ba komai " Kana jin muryarta ka san magana ce irin ta ƙarfin hali, ma,ana tana cikin jin zafin ciwo.
Alhaji cike da tausayawa ya ce
"Baiwar Allah ki yi haƙuri, sannan ki tashi mu je asibiti a duba ki" Ya faɗa cike da tausayawar ganin gashi dai an mata laifi don shi kansa ya san direban ne da laifi amma kuma gashi tana faɗin ba komai, bayan ya san da wasu ne sai dai su hau yin masifa. Manyan fararen idanunta da baƙin cikin idanun ya yi wa farin idanun kyau wajen haɗuwarsu ta ɗago ta sauke a kan fuskar da ta ji kalmar mai furta kalmar cikin kamala da sanin ya kamata, kana jin mamallakin muryar ka san mutum ne mai cike da ilimi.
Idanunsu ne suka sarƙe da na juna, jin zafin da ƙafarta ta mata wani zugi, hakan ya sa ba ta ma san ta lumshe idanunta ba, amma cike da ƙarfin hali ta buɗe bakinta dakyar ta furta
Ba komai, daman can Allah ya rubuta faruwar hakan a cikin littafina tare da alƙaluman ƙaddarata, don haka ni ƙaddara na ɗauka Allah ne ya aiko ba sai kun kaini asibiti ba" Tun da ta fara magana Alhaji Muhammad yake kallon laɓɓanta magana take cike da girmama ɗan adam da sanin darajarsa, yana wannan mamakin ya ji wani ya ce
"Ah haba dai ke kuwa, ai dole a biya ki ciwon da aka ji miki, daga ganin yadda kike yamutsa fuska an san kawai ƙarfin hali ne"
Ba ta ce ƙala ba ta tashi tsaye tana jin kamar dai ƙafar za ta bar gangar jikinta saboda yadda take wani bala'in zugi.
Tana tsayawa jiri ya kwashe ta, ta tafi luuuu da sauri direban da wani suka yi saurin riƙe ta. Alhaji Muhammad ya ce
"Ku saka ta a mota mu je asibiti"
Maganar wata mata ce ta katse musu maganar ta hanyar da take faɗin
"Kar wanda ya saka min ƴar uwa a mota, saninku na yi ko kuwa daman lun shirya hakan ne don ku guje min da ƴar uwa"
Direban ya ce
"Tsautsayi ne fa"
Matar ta ce
"Komai ai tsautsayi za a ce" Ita kuma wacce aka kaɗe ɗin tana ƙoƙarin buɗe idanunta da suke lumshewa kasancewar wani irin jiri da take ji wanda da farko ba ta ji ba.
Matar da ta zo wajen ta ce
"Ku ban ita" Ta faɗa tana miƙa hannu ta rungumota, kasancewar ta rinjaye ta da yake jikinta ya saki sai ta kusan faɗuwa, Alhaji da yake kusa da su ya yi sauri tare ta, yana faɗin
"Ke kaɗai ba za ki iya riƙe ta ba, ki shiga mu je a kaita asibiti a duba lafiyarta" Ɗagowa ta yi ta kalli Alhaji za ta masa rashin mutunci amma tana kallonsa ta ji wani kwarjininsa ya dirar mata. Ta ja bakinta ta yi shiru tana roƙar wata mata ta kama mata ita su je su kaita gida,. Sai da suka fara tafiya suna tallafe da ita sannan ta juyo ta ce
"Mun yafe zuwa asibitin naku za mu kaita muma muna da motar ai" Daga haka ta juya ba tare da ta ce komai ba, Alhaji ya kalli direba, direban ya sunkuyar da kai.
Hannu ya saka a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa masa, karɓa ya yi yana mai masa alama da ya je ya basu, da ɗan sauri ya take musu baya.
A daidai wani gida ya same su suna shirin shiga gidan, amma da ta bata matar ta ɓata rai ba ta karɓa ba. Sai gani ya yi tana jijjiga wacce aka kaɗe ɗin amma daga ta buɗe idanun sai ta lumshe.
Ta ce
"Falmi ki buɗe idanunki don Allah ki tashi" Amma shiru, matar ta tallafi falmi ɗin ita kaɗai, ita kuma ƴar uwar ta yi sauri ta shige gidan, sai gashi an buɗe mata get tana fitowa da mota daga cikin gidan tana fitowa ta buɗe ta fito matar ta taimaka mata suka saka ta a baya, ta ja, ta bar wajen bayan mai gadi ya maida ƙofar ya rufe.
Alhaji yana nan tsaye ta zo ta gifta su a mugun guje, yana ta mamakin yadda matar ta ki su taimaka musu.
Ba don ya so ba ya koma cikin motar jikinsa sanyi kalau, yana mamkin yadda da farko wacce aka kaɗe ɗin bai zaci har za ta suma ba ko.
Direban cike da girmamawa ya zagaya ya ja, yana ta ba Alhajin haƙurin abin da ya faru. Alhaji ya ce
"Na yarda Allah ne ya aiko" Iya wannan ya faɗa suka ci gaba da tafiya. Alhaji Muhammad ya jingina da kujera yana jin yadda hannunsa yake kamshin turare mai wani ƙamshi, ya fara tunanin inda ya samo ƙamshin a hannunsa tun da ya sha bamban da wanda yake jikinsa a take ya tuna riƙe Falmi da ya yi lokacin tana hannun ƴar uwarta da ta kusa faɗuwa...
*** [8/3, 5:25 PM] null: ***
*KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH