KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿1️⃣5️⃣

*HASIYA*

Wani sanyin AC haɗe da ƙamshin turarensa ne suka yi wa hancin ta masauki lokacin da ta zauna a motar, rufe murfin ta yi suka zubawa juna ido ya ce

"Kin shiga ɓangaren ki da za ki zauna kin gani kuwa?" Hararar wasa ta jefa masa ta ce

"Haba dai kai ma da wani abu ni yanzu ina ni ina wannan aikin ai ba dai Hasiya ba wallahi" Ta faɗa tana tuntsurewa da dariya, shi ma taya ta ya yi kafin ya dakatar da dariyar ya ce

"To ai kin kusa dawowa ma baki ɗaya, kwana nawa ne maye ya yj amarya ya cinye kayansa" Ta sanya tafin hannu tana mai rufe bakinta alamar ɓoye dariyar ta ta ce

"Kai ko? Na ga alama baka ma tunanin yadda Ramla za ta ji maganar nan, kawai sha,aninka kake" Kallon naki wasa ne ya mata ya ce

"Haramun zan aika ne? Ai ni a nawa tunanin ƙarin aure ba laifi bane tun da halaltaccen abu ne, kuma ko da son ran matar gida ko babu son ranta dole haka za ta haƙura domin ni dai a nawa ganin mace ba ta isa hanani cika burin rayuwata ba sai dai da zaɓa zaman gidana ko kuwa duk abin da ta ga shi ne mafitar ta ya rage nata" Ta ɗan yi jim tana nazarinsa ta ce

"Ramlar?"

Ya yi wata ƴar budurwar dariya ya ce

"Ƙwarai ma kuwa, shin Ramla ita ta yi kanta?"

Kai ta girgixa ta ce

"Ramla fa tana da haƙuri, ni dai zan shiga gidanta ne...

Katse ta ya yi da faɗin

"Shin daman Ramla tana da gida? Za ki shiga gidanta ko za ki shiga gidana" Ta ɗan wayince ta ce

"Gidanka to" Ya murmusa ya ce

"To ni dai na san mace ba ta da gida, don gidana babu ko bulo ɗaya na Ramla bare a kira shi da gidanta, sai dai ko in zan mata kara a kira shi da gidan auren ta" Kai kawai Hasiya ta karkaɗa masa alamar gamsuwa amma dai tana ɗan wasi-wasi furucinsa a ƙalla yadda ta sha jin wasu daga cikin irin halaccin da Ramla ta yi wa Abdulsalam ɗina wajen Zahraddin bai kyautu a ce yana irin furucin nan a bayan idanunta ba, saboda tana ganin zai yi wuya ya yi a gaban idanunta.

Ɗan jingina ta yi da jikin kujerar ta ce

"Mu je dare yana yi" Ya tada motar yana faɗin

"To gimbiya Hassy mai mulkin zuciyata" Ƴar dariya ta yi tana mamakin furucinsa har lokacin, sai dai wata xuciyar ta ce

'To ke mene ne naki don ya yi wannan maganar, ke dai ba kanki kika sani ba, ai ki godewa Allah ma da yake mata hakan, kin ga baki da haufi ko fargabar matsayinta a wajensa da har za kike taraddadin yadda zamanku zai kasance idan kin shiga gidan, kar yake girmamata yana fifita ta a matsayinta na uwar gida'

Ja ya yi suka tafi suna da hira abinsu.

A ɓangaren Aslam kuwa tun da ya hangi motar ya ga shigar wata cikin motar duk da bai gane wace ce ba sai zuciyarsa take ayyana masa ina Mamarsa za su je da daren nan? Amma kuma yana mamakin mai ya sa Mamar ba ta shiga motar a cikin gidan ba sai da ta fito waje, yana ta saƙe -saƙe ya taho don zuwa ya tambaye ta inda za su je ko ba lafiya ba amma yana tahowa kafin ma ya ƙaraso an ja motar an tafi. Hakan ya sa ya juya ya koma masallacin ya yi alwala ya koma aka yi jam,in da shi ya fito ya koma gidan yana so idan ya je ya tambayi sauran ƴan uwansa inda Mamar suka tafi iya da Abban.

Abba yana tafiya suna ta hira, tana jaddada mata so yake kar bikin ya wuce sati biyu ko uku a lokacin da ya yi wannan furucin ta zaro idanu ta ce

"Da wuri haka?" Hankalinsa yana ga tuƙi ya ce

"A warinki ne yake wuri, amma ni a wurina hakan ya yi min nisa sosai, saboda na ƙosa, kuma na matsu in ganki kin zama mallakina, gani nake tamkar wanda wani zai ƙwace min ke"

Wani kallo ta masa tana jin dama a ce shi ɗin ita kaɗaice matarsa, ita kaɗaice za ta mallake shi ba tare da suna kama-kama na rabon kwana da wata mace ba, ba tare da wata tana yi masa kallon ita ma matarsa ba ce sai dai kash addu,a ta riga fata domin Ramla tana kiransa matsayin miji!.

Ta ɗan nisa ta ce

"Ka sa a ranka ni mallakin ka ce babu wani wanda zai raba ni da kai, kawai dai kwanakin da ka faɗa ne sun yj min kaɗan"

Ya ɗan juyo ya kalle ta ya juya ya ci gaba da tuƙin yana faɗin

"Mai ya sa? Baki shirya mallaka ta a kwana kusa ba ne? "

Tana kallon titi ta ce

"Ba haka bane ni kaina zuciyata cike take da ɗokin ganin mun mallaki juna, sai dai hanzari ba gudu ba ka san a halin da ake ciki yanxu ina da buƙatar abubuwan hidimar bikin, tun daga kayan ɗaki da sauran abubuwan, musamman ka san mu mata muna da waji abu in har kina da kishiya to a ƙalla ba aksar ba ko da baki mallaki abin da take da shi ba to ki mallaki gwargwadon halin da kike da shi, duk da na san bani da kuɗin da zan mallaki kayan ɗakin da Ramla take da su, ba ma wannan ba ta kowace siga ta kowane fanni Ramla ta min fintinkau din da ba zan yi kishin komai da ita ba sai dai na mijin da muke aure, saboda ni bani da kuɗi sannan mahaifiyata bata da ƙarfi kuma bani da wata hanyar da zan samu kuɗin uwa uba mahaifinta ƙasa ta daɗe da rufe idanunsa" Ta faɗa tana saka hannu biyu ta rufe fuska tana sakin kukan ƙarya.

Wani irin tausayinta ne ya tsarga masa, har ya yi saurin gangarawa gefen titi ya tsayar da motar ya juya ya mayar da hankalinsa kanta ya ce

"Hasiya ki daina kuka don Allah, nima za ki iya sakani kukan, ki kwantar da hankalinki, ni zan zame miki bangon jingina, na ɗauki alƙwarin zan miki komai idan na ce komai ina nufin komai, ni zan zuba miki kayan ɗakin da duk wasu abubuwan da za ki buƙata, sannan ki saka a ranki hidimar bikin budurwa shi za a yi a bikinki don sai mun yi ƙara,i kuma komai ni zan yi hidimarsa duk wani abu da kike buƙata nine nan zan miki shi" Idanun ta goge ta sunkuyar da kai ta ce

"Na gode Allah da ya bani kai, kuma ina datan ya bani kai ma,ana ya nuna min ranar da zan mallakeka matsayin miji, Allah ƙarawa nemanka albarka"

Yana jin daɗin addu,ar da ta masa duk da Ramla ba ta bar eani giɓi na komai da mace xa ta yi wa ɗa namiji ba ta fannoni da dama, ba ta rage shi da komai ba sai ma shi da yake ragar ta da abubuwa da dama yana tauye mata haƙƙoƙinta, sannan addu,ar ma idan ta masa ya buɗr baki ya amsa ma kamar dai wata alfarma ya yi wa Ramla sai gashi yanzu yana jin tamkar Hasiya ta fi kowa iya furta lafazin addu,a hakan ya sa ya ce

"Kar ki damu, ai itama Ramla komai ni ne nan na siya mata lokacin da aka yi ginin da za mu tare, kema kuma yanxu tun da za ki zo dole na siya miki komai" Ya faɗa yana kallonta ta shiga wasa da yatsunta ya ce

"Shikenan" Kai ta gyaɗa masa, tana rayawa a zuciyarta cewar

',Lallai wannan damin da na tsinta a kale ba ƙaramin dami bane, daman ina tunanin yadda zan mallaki abin da zan yo gogayya da Ramla ashe dai mijin da zan aura sunan shi ƙare kukanka, tun da gashi zai share min hawaye'

Ya katse mata tunani da faɗin

"To ɗago ki kalleni mana" Ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido tare da sakarwa juna murmushi.

Tada motar ya yi, tare da ɗan fara tafiya har dai ya samu ya haura titi, sun biya ya yi mata siyayyar kayan makulashe kafin ya kaita gida a nan ma sun jima suna magana sannan suka yj sallama ba don sun so ba suka rabu, ta kwashe ledojin har wanda Ramla ta bata ta shiga gidan yana cewa ta miƙa masa gaisuwa wajen Dada.

Sai da ya ga shigewarta ya ja motar ya bar wajen yana ta sakin murmushi tamkar dai wanda aka yi wa wani babban albishir.

A ɓangaren Hasiya tana shiga gidan da sallama, Dada har da fitowa daga ɗaki tana mata sannu da zuwa, tare da karɓar leda guda ɗaya tana faɗin

"Wato dai har da tsaraba gaskiya dai Abdulsalam yana ji da ke" Da dariya ta ƙyalƙyale suka shige ɗakin inda su Zainaba suke kallo.

Ta samu wuri ta zauna a ƙasa tana faɗin

"Wash Allahna" Zainaba ta ce

"Aunty gidan biki kika tafi" Hasiya ta ce

"A,a gidan su Aslamiyya na je" Nasira ta ce

"Aunty ina su Humaira, ai daman kin je da mu"

Tana fito da rufaida yogurt da ice cream daga ledar ta ce

"Wataran ma je tare"

Dada ta yi karaf ta ce

"Mene ne na wannan tamabaya ai in dai mun a da rai da lafiya kun kusa ƙaura ma gabaɗaya" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki tsire guda ɗaya cikin wanda Hasiya ta buɗe yana ta tururi ta kai baki tana taunawa. Su duka biyun suka musu kallon rashin fahimta kasancewar ba su san wainar da ake toyawa ba kawai dai suna ganinsa yana zuwa amma ba su san cewar auren Auntyn nasu ba.

Zainaba ta ce

"Kamar ya Dada?"

Dada ta ce

"Ku da uwarku za ta tare a can ai da ku za ta tafi"

Nasira tana riƙe da cokalin da za ta sha ice cream ɗin da Hasiya ta miƙa mata ta ce

"Tarewa kuma Dada Wace irin tarewa?" Dada ta ce

"Tarewa dai ta aure, ai Abban Humaira nr ya ce zai auri Auntyn naku saboda ya riƙe ku tare da ɗaukan ɗawainiyarku" Zainaba ta ce

"Yeeee za mu koma gidan ƴan gayu gida mai kyau"

Nasira ta ce

"Haba dai mijin Mama Ramlar? Kai Aunty gaskiya kar ki auri Abba,kenan fa kishiyarta za ki zama Allah bai kamata ba...

Ba ta ƙarasa ba Dada ta ce

"To uwar ƴan sanin ya kamata, sai ta zama kishiyar tata, idan ma ba ta zama kishiyarta ba ai wata ta zama kishiyarta tun da ko bai aure ta ba zai auri wata, kuma ai saboda ɗaukan ɗawainiyarku zai aure ta"

Nasira ta ce

"Amma Dada yanxu ma ba yana ɗaukan ɗawainiyar tamu ba, ni dai a shawarata wallahi daman Aunty kar ta aure... Hasiya ta ce

"To uwar ƴan iyayi, uban waye ya nemi shawararki? Aure babu fashi, kina faɗa ne saboda kishin ubanki da yake can kwance a kushewarsa, ni kuma aurena babu fashi, ko shi uban naki dama ce bai samu ba da a ce ya samu damar ƙara aure da yanxu na san mu biyu ne ni da wata za mu masa takaba"

Zainaba ta ce

"Ni dai zuwa zan yi wallahi ga cin daɗi gashi ake kai mutum makaranta a mota a ɗakko shi" Ta faɗa tana cusa nama bakinta"

Tsam Nasira ta miƙe tana jin babu daɗi ta nufi hanyar ɗaki, Dada ta ce

"Miƙo min cokalin mu mu shanye ke kya ci baƙin halin" Cokalin hannun nata ta ajiye ta shige ɗaki.

Dada sai faɗa take a ƙarshe ta haƙura suke cin kayan daɗi sai da suka gama Hasiya ta janyo ledar da Ramla ta bata ta buɗe ta ɗakko turmin atamfa ta ce

"Dada ga wannan in ji Ramla ta ce a baki" Dada ta karɓa ta ce

"Ai kuwa sai ƙamshin turare take, tun da ba ta san ma abin da yake tsakaninku da mijinta ba shi ya sa ta bani da ta sani ba lallai ta ban ba kuma ko da ban nima ba lallai na yi amfani da shi ba saboda zargin kar a ƙulla min wani mugun abun a toh" Hasiya da take fito da turaruka da humra masu ƙamshi ta ce

"Wallahi kuwa"

Zainaba wacce take tattare ledoji da robobin da suka gama amfani ta ce

"Turarukan nan sun cika falon nan da ƙamshi" Haka suka gama ganin komai, Ramla ta kwashe ta je ta ajiye ta ɗauki zoben nan da ta cire da za ta tafi gidan Ramla ta saka a hannunta.

A ɓangaren Aslam ana idar da sallah ya nufi gida, yana zuwa ya samu su Humaira suna karatub qur,ani ganin bai ga Mama ba ya ce

"Yaya Humaira ina Mama ta tafi?" Humaira sai da ta dire ayar da take karantawa daman ya mata tambayar ta ɗago ta ce

"Ina za ta je da dare kuma, tana ɗakinta ta ce kanta ne ta ji ya fara ciwo shi ya sa ma ba ta fito ana karatun da ita ba" Bai ba Humaira amsa ba ya juya ya fito ya nufi part ɗin Mama yana wasi-wasin maganar Humaira don a tunaninsa kawai ta faɗa ne tun da ya san ya ga shigarta mota sun fita da Abba.

Yana shiga falon ƙamshin turaren wuta ya ziyarci ƙofofin hancinsa, ya duba ya ga burner ce a jone an zuba tureren wutar ƙamshi yana tashi.

Bedroom ya nufa ya ƙwanƙwasa a hankali, kamar daga sama ya tsinkayi muryarta tana bada umarnin a shigo, tsaiiii ya yi kafin ya yi sallama ya tura ƙofar yana shiga ya ganta ta jingina da gado hannunta a goshinta.

Ya ƙarasa bakin gadon ya zauna ya ce

"Mama daman kina nan?" Tambayar ta zo mata wani iri ta cire hannunta daga goshinta ta ce

"Ina nan mana ina zan je ko wani abu ne?"

Ya ce

"Humaira ta ce kina ciwon kai"

Ta ce

"Eh amma na sha magani kuma da sauƙi" Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba ta kalle shi ta ga alamar kamar yana so ya ce wani abu ta ce

"Aslam mene ne akwai wani abu ne? Ko wani abu kake buƙata" Ya girgiza kai ya ce

"A,a Mama, daman ɗazu ne na fito daga masallaci zan sake alwala da alwalata ta karye, shi ne na hangi motar Abba, kuma fa na ganki kin shiga motar kun tafi amma kuma yanxu na ganki a gida, ko dai muna cikin sallar Abban ya xo ya ajiye ki, tun da na ga motar da ya fita da ita ɗin ba ta nan har yanzu" Idanu ta zura masa tana ɗan mamakin kalamansa duk da shekararsa goma amma ta san ba shi da ƙarya bare ya faɗi abin da bai gani ba, amma sai ta ɓoye mamakin ta ce

"Anya kuwa? Ko dai idanun naka ya zama na tsofaffi?" Ta faɗa cike da zolaya ya ce

"Wallahi Mama da gaske ido raɗau yake, kuma ba ganki kin shiga"

Mama Ramla ta ce

"To bari na tabbatar maka da cewar idanunka sun tsufa saboda ni dai ka ganni ko nan da get ban je ba, don haka na san dai wataƙila abban naka da wani ne suma tafi "

Ya kalle ta ya ce

"To Mama in ba ke ba ce wace ce? Amma tabbas mace ce na gani" Ta masa kallon ƙurilla ta ce

"Kai ba na son shashanci, wa zai ɗauka a mota kuma? Kawai dai da yake daga nesa kake ganinsa za ka iya ganin kamar mace",Ba ya son yin jayayya da ita da yake ta koyar da su babu kyau yaro yake jayyya da babba ko da kuwa yaron shi ne da gaskiya saboda yin jayyyar yana nuni da ƙaryata magana ne, kuma babu dacewa ga yaro ya ƙaryata babba hakan rashin tarbiya ne!.

Ganin ya yi shiru ta san va zai ƙara cewa komai a kan maganar ba, ta ce

"Tashi ku je ku yi karatun idan kun gama ku ci abinci saboda ni ba zan ci komai ba, idan an jima na ji kan nawa ya saka duka, sai na samu wani abun marar nauyi na sha" Amsa masa ta yi ya tashi ya fita ya rufo mata ƙofar, zamewa ta yi daga jinginar da ta yi a jikin allon gadon ta kwanta tare da ɗora kanta bisa filo ta rufe idanunra, sai dai ƙwaƙwalwarta tana mata wasi-wasi a kan maganar da Aslam ya faɗa.

A zuciyarta ta ce

"To shi kuwa wa zai ɗauka da daddaren nan?Gaskiya babu ma wata mace da zai ɗauka a mota, kawai dai idanun Aslam ne suka masa nuni da cewa mace ta shiga motar, wataƙila ma shi kaɗai ya fita a motar ko dai wani ya ɗauka amma jinsin namiji ba mace ba, duk da ban san dalilinsa na fita da daren nan ba'

Wani ɓangare na zuciyarta ya ce

'Wani uzurin ne ya fita da shi mana'

Wata zuciyarta ta sake bijiro mata da tunanin

',Ko dai wajen wata ya tafi hira'Wani tuƙuƙin kishinsa ya tsaye mata a ƙirjinta ta yi saurin kawar da tunanin tare da furtawa a fili cewa

"Idan ma wajen macen ya tafi hirar mene ne naki a ciki? Mutumin da bai damu da ke ba, bai damu ki yi farinciki ko akasin sa ba a kan me za ki damu kanki da shi?" Juyi ta yi tana tausar xuciyarta a kan halayyar mijin nata, kamar daga sama ta ji ƙaran buɗe get gaɗe da shigowar motar cikin gidan ajiyar zuciya ta sauke ta yi lifet kamar mai bacci don ko kaɗan ba ta taɓa kawowa cewar Hasiya ce ya ɗauka a motar ba.

Hasiya da ta yi shirin kwanciya ta ɗakko wayarta ta hau whatsapp ta ɗagawa Karima ƙawarta hannu ta yi sa a tana online kuwa nan hira ta ɓarke tsakaninsu tana ba ta labarin yadda komai ya faru yau a fitar ta da Abdulsalam.

Karima ta mata voice ta ce

"Lallai ƙawata kin samu sake, irin wannan kama zuciyar bazawari, wato har da kayan ɗaki zai yi miki, gaskiya yana ji da ke"

Hasiya ta ce

"Ai sai kin ji abubuwan da yake faɗa wallahi har cewa ya yi za a yi hidimar biki tamkar auren budurci"

Karima ta ce

"Lallai Ramla ta shiryawa zuwanki, domin a yadda na fahimta in ba ta yi wasa ba Abdulsalam yana iya yin waje da ita"

Hasiya ta ce

"Ai kam na ga alama, amma ni ba na son na shiga gidanta da nufin fitar da ita, na fi so mu zauna zaman kishi mu ga ko za ta ƙwaci kanta" Karima ta turo emoji na dariya da hawaye ta ce

"Sai da ke mutuniyata"

Hasiya ta ce

"Sai ma kin ga wasu turaruka da humra masu ƙamshi, kin ga ta bani lasisin in shafawa mijinta idan zai zo yake shaƙar ƙamshin turaren da ita ce ta bani shi"

*Ina masu son kaya masu inganci, muna siyar da lace* , *atamfa, mayafai takalma jaka, kayan yara laffaya, kayan kicin dogayen riguna* , *jallabiyar yara da manya, abaya maganin mata maganin sanyi kayan jariri, zannuwan gado da sauransu duk mai son kaya ya tuntuɓi ne, ni maman afrah ina aikawa mutum kaya a* *duk inda yake na gode* ***** [8/5, 6:17 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH