BOOK 1
🅿1️⃣6️⃣
*NURIYYA*
Tun da aka fito sallar azzahar a makarantar take ta jin yunwa, ana gama sallar ɗalibai suka fara cin abinci, wasu tun kafin a fito sallar aka kawo musu abincin wasu kuma bayan an idar da sallar aka kawo musu. Tana zaune ta rakuɓe tana kallonsu shige da ficen ɗalibai da kuma yadda kowa yake sabbar gabanshi.
Har aka kusan komawa sallah, amma shiru ba ta samu abinci ba, daman daga gidansu Ammar ne take samu amma gidan mahaifinta ma babu ita a lissafi ta ci ko ba ta ci ba babu ruwan kowa da ita damkar dai wacce suka ajiye dabba ko dabba ai ana ciyar da ita bare mutum!.
Wasu da suke cin abinci ne ta ji ɗaya daga cikinsu ta ce
"Allah na gode ma Mamata ta mana ɗanwake daman da za mu taho makaranta na ce ta mana ɗanwake" Ta faɗa lokacin da ta buɗe kular abincin ta ga mene ne a ciki.
Ɗayar ma ta ce
"Ni kuwa dambu na ce kin ga kuwa shi aka mana" Su duka suka saka dariya, Nuriyya da take zaune ta waiwaya ta kalle su, a zuciyarta ta ce
'Ni kuwa bani da Mama, ko mai ya sa Mamana ta mutu ta barni?' Ta faɗa hawaye yana zubo mata daga idanunta ta sanya hannu ta share, amma wasu suka sake zubowa, wannan karon ba ta goge ba.
Wani sashen na zuciyarta ya ce
'Ke ai Ya Ammar da Kaka ne iyayenki' Kai ta gyaɗa kamar wanda aka tambaye ta wani abu.
Jin muryar malaminsu yana faɗin
"Saura minti goma a koma a ji, kowa ya yi sauri ya kammala abin da yake, lokaci yana cika idan aka kaɗan ƙararrawa na samu mutum a waje jikinsa zai faɗa masa sauran bayanin" Nuriyya jin wannn bayanin tsam ta miƙe za ta tafi aji, tun da ita babu abin da take a zaune take, sannan babu wanda zai yarda ta ci masa abinci, daman daga gidansu Ammar take daka rai tun da daga can take samu amma kuma yau gashi shiru, hakan ya sa ta sanyawa ranta dangana.
Ajinsu ta nufa, tana tafiya tana jin duk ƙamshin miya da abinci ya cika mata hanci, tana dab da shiga ajin ta goge idanunta, tare da juyowa ta nufi inda ake ajiye musu ruwa, ta je ta sha ruwan tana cikin sha cikin ta ji ya ƙulle, ruwan ta ajiye ta juya za ta tafi, kamar an ce ta wauwaya ta kalli hanyar ƙofar shigowa makarantar, Kaka ta hango riƙe da baƙar leda da kwano a ciki.
Wani irin daɗi ne ya cika mata zuciya, da gudu ta nufi Kaka, tana murnar ganinta, ita ma Kakar bakinta ya ƙi rufuwa, Nuriyya tana zuwa ta rungume Kaka tare da ƙanƙame ta. Kaka cike da wasa ta ce
"Ni kar ki kayar da ni"
Nuriyya ta saka ruƙon da ta mata ta kama hannunta ta ce
"Kuma ƴan makaranta dariya za su miki Kaka in kika faɗi" Ta faɗa tana dariya Kaka ma dariya take ta ce
"Nima ina faɗuwa zan saka hannuna in taɗe ƙafarki ki faɗi, kin ga ai sai a mana dariyar tare" Su duka suka ƙyalƙyale da dariya.
Kaka ta gaishe da malamin nasu ta ce masa abinci ta kawo mata, kasancewar sun saba da Kaka ya ce Nuriyya ta karɓi abinci ta yi sauri ta je ta ci kar lokacin komawa ya yi. Kaka ta miƙa mata ledar tana cewa
"Iccen girkin ne ɗanye, dakyar na samu na dafa abincin, shi ya sa ban kawo miki da wuri ba ki yi haƙuri kin ni Nuryn Ammar" ,Nuriyya wacce gabaɗaya murna ta cika mata ranta, ita ba wai iya murnar cin abincin ne kaɗai ba, har da kawowar a rayuwa tana jin daɗi ta ga an mata abin da aka yi wa kowa, wato kamar dai yadda aka kawowa kowa abinci ita ma an kawo mata, ko da dai ta yi rashin uwa, kuma uban ma duk da tana raye da shi da babu duk ɗaya tun da ba ya taɓa share mata hawaye bai damu da ita ba, amma a ƙalla tana da masu sonta masu kula da ita hakan zai hana ƴan makaranta yi mata gori.
Kai ta gyaɗawa Kaka ta ce
"Ba dai kin kawo min ba, na gode Allah saka da gidan aljanna" Ta faɗa cikih sanyin murya.
Kaka ta ce
"Amin Nury, amma ba godiya" Dariya ta yi ta juya da sauri ta nufi inda ake cin abinci, ita kuma Kaka ta juya ta fita daga makarantar.
A hanya tana tafiya tana tuna Nuriyya da yadda take abu tamkar wata mai manyan shekaru, a zuciyarta ta ce
'Nury in ba ƙaddara ba da yanayin rayuwa, ai da mu bamu isa ma mu ciyar da ke ba, sai dai ke ki taimakemu da kayan abincin ma, amma yanayin yadda rayuwarki take kin taso cikin maraici da rashin kulawar mahaifi, duk da a kullum ina taraddadi kuma har yau a raina ban yarda cewar mahaifinki da gangan ya yi watsi da ke ba, ni na san sai dai in wata maƙarƙashiyar aka yi aka raba tsakaninku saboda kowa ya san irin son da mahaifinki yake miki tun kina tsumman goyo, sai dai yanzu da alama kaidin mace ya yi tasiri wajen datse wannan kyakkyawar alaƙar, wajen rarrabe soyayyar zukatan da suka kwaɗaitu da son juna amma dai na san akwai ranar ƙin dillanci tun da babu abin da yake tabbata daɗi ko wuya! ' Ta faɗa a zuciyarta daga inda take tana iya hango gidan su Nuriyya kafin ta yi kwana ta shige layinsu.
Nuriyya tana samun wuri ta zauna wata ɗaliba ta ce
"Yelalo Nuriyya Rufa'i tsohuwa ce take kawo mata abinci kullum" Ta faɗa cike da tsokana. Shiru Nuriyya ta yi ta ajiye pure water da ta fito da shi a ledar ta fito da abincin ta ɗago ta kalli yarinyar da ba ta fi sa,arta ba ta ce
"Ai dai da tsoho da wanda ba tsoho ba su duka mutane ne, kuma wanda ba tsoho ba shi ma wataran zai zama tsoho, kuma idan kika ƙara tsokanata Malam zan je in faɗawa" Ɗiff yarinyar ta yi ba ta sake cewa komai ba saboda ta san idan aka je wajen Malam jikinta ne xai faɗa mata sauran bayanin.
Ko da aka tashe su, gidan Kaka ta fara zuwa ta kai kwanon, har lokacin Ammar bai dawo ba, Kaka tana ta tsokanarta da faɗin
"Kin kawo ladan gidana ai, tun da nan kika fara zuwa"
Nuriyya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce
"A ƙofar gida na ajiye ladana, ina fita zan ɗauka in kai gida in kai shi ɗakina" Kaka ma dariya ta yi, ta ce
"Ki zauna ki ci abinci"
Nuriyya ta ce
"Na ƙoshi ai ba na jin yunwa" Ta faɗa tana fita ta nufi gidansu.
Tana dab da shiga ɗakinta ta ji muryar Hajiya Hauwa ta katse ta da faɗin
"Ke uwar shegen yawon barbaɗa"
Nuriyya da tsawar ta tsorata ta har zabura ta yi kasancewar ta yi maganar ne a zafafe cikin kausasa harshe .
Nuriyya ta ce ... "Daga makaranta nake" Cike da doka mata harara ta ce.
"Abin da ya fi daga makaranta kike, jiya ma ba koroki aka yi ba, ubanki ne ya gina musu makarantar da za su barki ki je baki biya kuɗin wata ba, kin dai saka yagaggun kayanki kin fita don a ce makaranta kika tafi, kin je yawon shashanci kin dawo mana gida, yarinya ƙarama da ke baki tafasa ba za ki koma, a iya ƴan shekarunki kin san hanyar zuwa wajen maza kusufa-kusufa" Kai Nuriyya ta sunkuyar tana jin yadda take bala,i kamar za ta fasa gidan.
Nuriyya cikin sanyin murya ta ce
"Ni babu inda na je makaranta na je, Yaya Ammar ne ya biya kuɗi.... A mugun tsawace ta katse mata magana tana faɗin.
"Shi Ammar ɗin waliyyi ne da zai ke biyawa mace kuɗi yana ɗaukan ɗawainiyarta ba tare da yana fanshewa ba, yaro ƙarami da shi ya san ya yaudare ki kema da yake zani ce ta tarar da muje mu sai ki bada kai bori ya hau" Ta faɗa tana saka hannu ta dungurewa Nuriyya goshi, Nuriyya da ba fahimtar abin da take faɗa ta yi ba ta ce..
"Wallahi ya biya mun kuɗin, Malam ko dukana bai yi ba kuma ba a koreni ba" Hannu ta saka cike da mugunta ta kwaɗawa Nuriyya mari, da sauri Nuriyya ta dafe kunci saboda marin ya je mata a bazata, ta ɗago dafe da kunci tana kallonta da idanunta da suka ciko da ƙwalla.
Ta nuna ta da yatsa ta ce
"Ina roƙon Allah ya bani tsawon rai in ga girmanki don na san hamshaƙiyar ƴar bariki ce za a yi a nan, dole sai kin yj karuwanci Nuriyya" Nuriyya ba ta san ma,anar karuwanci ba sai dai yanayin yadda ta ga matar mahaifin nata ta ci alwashi ta san ba abun kirki ba ne, uwa uba ta san ba ta sonta.
Tana fama faɗar hakan ta juya ta tafi tana faɗin
"Baƙar annoba mai baƙin hali, wannan yarinyar ina ga ma ba Alhaji bane ya haife ta wataƙila ma uwar ta a waje ta yi cikin ta shigo da shi!"
Nuriyya ɗaki ta shiga, tana shiga ta kwanta a ƙasa ta yi rubda ciki, ta kifa kanta ta fashe da kuka. Ta jima tana kukan kafin da ta yi ta gaji ta tashi ta cire kayan makarantar tana mai ɗaga wandon ta kalli yagar jiki ta rausayar da kai tana jin tausayin kanta, linkewa ta yi ta ajiye ta saka wasu.
Ƙaran saukar tsintsiya ta ji dummm a bayanta tana juyowa ta yi ido huɗu da Hajiya da take huci kamar ta yi tseren gudu ta ce
"Ai ba zama za ki yi ba, fitoea za ki yi ki share gidan nan har wajen get, idan kuma kika sake kika tsaya wasa wallahi sai jikin ki ya faɗa miki"
Cike da ladabi ta ce
"To" Harararta ta yi ta ce
"Naki ya rage" Ta faɗa tana juyawa ta bar ƙofar ɗakin.
Nuriyya fitowa ta yi ɗauke da tsintsiyar a hannunta ta fara ƙarewa harabar wajen kallo ganin masu aiki sun share wajen tasss babu wata alamar datti kawai Hajiya ta yi haka ne don ta ƙuntata mata ta saka ta wahala ba don ta yi sharar ba.
Sai da da share har get ɗin, kasancewar wajen yana da girma tana gamawa dakyar ta miƙe tsaye saboda tsanain gajiya da kuma sagewa da bayanta ya yi.
Ta gama ana kiran magriba, haka ta je ta yi alwala ta taho xa ta shiga ɗakin ta tsinkayi Hajiya tana faɗin
"Kar ki shiga wannan ɗakin har sai lokacin kwanciya"Kai ta gyaɗa mata.
Cike da zafin rai ta ce
"Baki da baki?"
Nuriyya ta ce
"To" Ta faɗa tana juyowa ta fasa shiga ɗakin, ɗankwalinta ta ware ta yafa ta yi sallar a ƙasa a ƙofar ɗaki, tana idarwa ta saci hanya ta tafi gidan Kaka.
Tana shawowa kwana ta hangi Ammar tsaye a ƙofar gida, da gudu ta tafi kasancewar ya bata baya tana zuwa ta yi salle ta ɗane shi, a zuciyarsa yana mamakin wanda ya masa haka sai dai ya san babu wanda zai masa hakan sai wacce yake tsaye a wurin dominta.
Baki ya buɗe ya ce
"Ko da ban sani ba Nury ce" Ta ƙyalƙyale da dariya tana sauka ta dawo gabansa ta tsaya ta ce
"Ya aka yi ka sani?"
Ya ce
"To ai na san ke ce kawai za ki min haka sannan daman zaman jiranki nake".
Suna riƙe da hannun juna suka shiga gidan Kaka
Kaka ta amsa sallamar tana cewa
"Ga zara ga wata, wato an samo ta kenan"
Ya zauna a tabarma yana faɗin
"Dama fa ba ɓata ta yi ba Kaka kawai dai tunanina ko ba za ya fito yau ba"
Kaka ta ce
"Gashi kuwa ta fito ai daman ba a hana ta fitowa"
Nuriyya ta gaishe da Kaka, Kaka ta amsa tana janyo baƙar ledar gabanta ta miƙawa Nuriyya ta ce
"Gashi in ji yayanki" Da hannu biyu ta karɓa tana godiya duk da ba ta san mene ne a ciki ba, tana buɗe ledar yadin makaranta ne a ciki sai pant guda biyu, tana karɓa ta fashe da kuka ta faɗa jikin Kaka saboda tsabar farinciki.
*ALHAJI MUHAMAD*
Bayan ya kammala komai ya nufi ɓangaren Goggo a can ya tarar da ita za ta ci abinci Amira ta jera mata a kan kafet. Bayan ya gaishe ta ta ce ya sakko su ci abincin da yake shi ko ta kan dining ɗin fa aka jera abincin bai bi ba, shi ya sa ma bai ci ba, gabaɗaya zuciyarsa tana ga tunanin wacce direbansa ya kaɗe yana ta tunani sai dai ba wani tunani ne ba illa tunanin a wane hali take tun da yana ganin su ne silar ciwon nata.
Suna cin abincin suna ɗan taɓa hira har suka kammala duk da bai wani ci sosai ba, fura ce ya sha da ɗan dama wacce aka saka ƙanƙara haɗe da kwakwa. Bayan sun gama Amira ta kwashe kwanukan.
Goggo ta yi gyaran murya ta ce
"Muhammad wai ya batun alƙawarinmu da kai ina maganar ta kwana ne?" Ya yi saurin kallonta don shi kwata-kwata ma maganar ta kwanta masa, sai yanxu da Kaka ta tambaya ne ya tuna da batun ƙarin aure.
Shiru ya yi na wasu daƙiƙu sai kuma ya ce
"Goggo a tayani dai fa addu,a" Ƙaran shigowar saƙo wayarsa ne ya dakatar da shi daga maganar da yake, kasancewar wayar tana hannunsa ya buɗe saƙon an yi rubutu kamar haka
" _Har abada zuciyata ba za ta gaji da dakon sonka ba, har sai ranar da ta ga ta mallake ka matsayin abokin rayuwa sannan za ta haƙura, idan kuma saɓanin haka ne ya faru to tabbas zan rayuwa da tabo mafi muni a cikin zuciyata!"_
Wani irin ɗaurewa kansa ya yi shi ya ma rasa wane kalar tunani zai yi, har yau ya rasa wace ce wannnna da take damunsa a waya sai ya amince ya karɓi soyayyarta.
Maganar Goggo ta katse shi da faɗin
"Addu,a daman ai ana yi, kuma va za a daina ba sai ranar da numfashi ya bar gangar jiki, amma a ƙalla sai mutum idan yana addu,a da neman zaɓin Allah a kan abu to yana da kyau ya fuskanci abun, don idan har abin ma ba alkairi bane da kanshi zai ji abin ya fice masa a rai' Kai ya gyaɗa alamar gaskatawa da magabarta ta ce
"Yanzu dai inaso ka samo matar aure... Banko ƙofar da aka yi shi ya hana Goggo ƙarasa maganarta, Hajiya Naja,atu ce ta shigo ko ƙofar ba ta rufe ba sannan basu samu arxikin yin sallama ba tana shigowa Goggo ta ce
"Haba Naja ya za ki shigo mana ko sallama babu?"
Hajiya ta yatsina fuska ta ce
"Muhammad wajenka na zo" Bata jira cewarsa ba ta ɗora da faɗin
"Wato yanzu a gidan nan ma bani da ikon mallakarka ni kaɗai sai kana raba mana lokaci ni da Goggonka? Haka kawai ko da ba ɓangarena za ka je ba a ƙalla ai ka zauna a ɓangaranka" Ransa ne ya ji ya yi mugun ɓaci a kan furucin ta tabbas yana mutuwar sonta irin son da yake jin idan aka cire mahaifansa to tabbas itace xa ta xo a mataki na uku, duk da bai haihu ya rayu da yaran ba tun da wanda ta haifa mutuwa ya yi, bai san ya shaƙuwar ƴaƴansa a zuciyarsa ba amma a jikinsa yakr ji kamar ko ƴaƴansa ba za su samu matsayin son da yake mata a zuciyarsa ba. Amma duk da wannan matsayin da take da shi a wajensa, hakan ba zai sa ya bata damar ciwa mahaifiyarsa fuska ko da a bayan idanunta ne bare a gaban idanunta.
Goggo wasu ƙwallar taƙaici ne suka ciko idanunta ta yi saurin ƙoƙarin mayar da su, Allah ya taimake ta suka koma, ya fara rayawa a ranta cewar
"Shin ƴa mace za ta iya fito na fito da mahaifiyar mijinta? Bayan uwa ita ta ɗauko cikin ɗanta wata tara, ta sha wahalar naƙuda ta zo ta shayar da shi, har ya kai ga matakin mallakar hankalin kansa, amma matar da ya haɗu da ita bakinsa fal da haƙora ita ce za ta yi kishin ko sa,in sa a kan mahaifiya an ya an yi duba na tsanaki a lamarin'
Muhammad ya miƙe tsaye yana ƙanƙance idanu ya ce cikin furuci da yake nuna yana jin ɗacin abin da ta faɗa
"Najaaaaa, ki gaggauta sauya furucinki daga kan lamarina da mahaifiyata, shin da kin damu da ni? Bibiyarki fa nake tamkar raƙumi da akala, binki nake sau da ƙafa irin bin da kaɗan ne daga cikin mata suke bin maza sau da ƙafa irin bin da nake miki, zuciyata umarninki take bi, sai dai ke ba nine a gabanki ba sabgar gabanki ce wacce bata da wani alfanu shi ne saboda na zo wajen mahaifiyata muna hira ina jin daɗi a raina shi ma kike baƙin ciki? Ke kin isa ki haɗa kanki wajen gogayya da mahaifiyar da ta haifeni.?Wllahi wallahi ki yi min komai amma a kan mahaifiyata ina iya yanke igiyoyina uku a kanki kuma ko da zan samu taɓin hankali saboda ciwo rabuwa da ke!" Ya yi furucin cikin ƙaraji.
Hajiya Naja ta kama ƙugu da hannu biyu, ta damƙe leɓanta na ƙasa da da haƙorinta na sama ta ce
"Eh lallai duniya juyi-juyi kwaɗo ya faɗa a ruwan zafi, ni kake faɗawa wannan kalaman?" Ta faɗa tana taku ta zo daf da shi.
Goggo tsaye ta miƙe ganin abin yana ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa ta dakatar da shi daga maganar da ya guntso a bakinsa zai fesar ta hanyar ɗaga masa hannu alamar ya saurara, ta ce
"Yanxu Muhammad a gabana? Har kana ikirarin yin saki? Abin da Allah ya halasta yinsa ba don yana so ba abin da Allah ba ya ƙauna?"
Hajiya Naja,atu da take jin tamkar ta samo wani ƙaton katako ta sheme Goggo saboda tsabar haushinta da take ji, ta ce
"Hankalinki ya kwanta, daman ai kin ce za ki ɗauki mataki, ashe dai wannn ne matakin da kika ci alwashin ɗauka, wato shiga tsakanina da mijina to ai sai hankalinki ya kwanta kamar tsumma a randa tun da mun samu saɓani"
Alhaji Muhammad ya buɗe baki zai yj magana sai dai tunawar da ya yj Goggo ta dakatar da shi
Goggo ta ƙarasa gabanta za ta dafa kafaɗarta amma ta ja baya, Goggo ta sauke hannunta daga ƙoƙarin dafa ta ɗin ta ce
"Naja, mijinki nali ne har abada, ni kuma matsayin ɗa yake a wajena, inaso ki sani uwa guda ɗaya ce tak a duniya, kuma ba a taɓa canjat... Naja,atu ta ce
"Haba Goggo na san dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi wato ki ce za a canja mace uwa ba a canja ta, to ki sani kamar yadda ba za ki canju ba haka nima zai dawwama da ni sai mutuwa babu canji kuma babu ƙari" Zuciyarsa zafi take a duk lokacin da Naja,atu take shuka masa rashin mutunci ko da yana jin ciwon haka a ɓangaren zuciyarsa to ta wano sashen sa an samu bambanci ma,ana zai ji ko kaɗan ba ya jin haushin ta, ko da a lokacin ya ji ciwo to daga baya zai daina ganin laifinta, amma yau fuskarta ma ta masa baƙiƙƙirin saboda ɓata ran mahaifiyarsa da ta yi wannan abu ya rage matsayinta da darajarta da yake gani a zuciyarsa ya ce
'Lallai Naja,atu da alama baki san yadda sanin darajar mata da za ta yi wa mahaifiyar mijinta yana da tasiri ƙwarai a wajen zamantakewa, yana ƙara danƙin kauna da matsayi a wajen miji, amma wuƙanta uwar miji babu abin da yake sakawa illa iyaka mace ta ficewa namijin a rai'
Goggo ta yj murmushi mai ciwo ta ce
",Haba Naja wa zai ja da ikon Allah...
"To tun da ƴan hana ruwa gudu suna nan, gashi ƙaurowa gidan da kika yi bai isheki ba sai....Wani wawan mari da Alhajin ya ɗauke fuskar Hajiya Naja,atu da shi, ji ta yi wani fauuuuu tunaninta ma fatar fuskar ce ta ɗaye daga fuskar, sai da ta ɗan buɗe idonta don yana wanka mata marin tunaninta ma Goggon ce domin iya tunaninta a rayuwarta ba ta taɓa zaton ko da a mafarki Alhaji Muhammad zai kaiwa ko da karen da take kiwo ne a gidanta ba zai mara ba saboda matsayi da soyayyar da yake mata amma yau dai ta ga soyayya iya soyayya.
Ta nuna kanta da yatsa ta ce
"Ni ka mara? Kana cikin hayyacinka kuwa? A kan wannan ka mareni?" Yanzu saboda na faɗawz mahaifiyarka maganar da bata taka kara ta karye ba, har na ci hukuncin mar...
Muryar Goggo ce ta katse shi da ta ce
"Muhammadu a gabana? Shin abu ne mai kyau ka saka hannu ka mari mace? Macen ma matarka ta sunna, shin baka san shi kansa mari ma bau kyau ba, saboda manzo S.A.W ya ce kada a mari fuska" Kai ya sunkuyar Hajiya kuma ta ce
"Wallahi babu macen da ta isa ta min bariki duk girmanta ko da gemunta yana jan ƙasa, bariki alalar gero ce bayan kin gama zuga shi ya mare ni za ki z... Hannu ya ɗaga a karo na biyu hannun yana dab da isa kumarun ta Goggo ta riƙe masa hannun gam, Hajiya Naja ta fashe da kuka ta juta a fusace rai a matuƙar ɓace ta baro sashen Goggo.
Goggo ta hau shi da faɗa, Amira da Mero da suke laɓe suna ganin dirama yau an mari matar gwal suka tuntsure da dariya marar sauti, suka miƙa hannu suka tafa da juna amma tafawar wacce ko kaɗan ba a ji sautinta ba.
Goggo ta inda take shiga, ba ta nan take fita ba, sai da ta gama masa faɗan shi dai tana ta bata baki, haƙuri kuwa ta bata wanda shi kanshi bai san adadinsa ba.
Sai da ya ga ta sakko tana masa nasiha an kan haƙuri a zamantakewa sannan ya ji daɗi a ransa, ya mata sallama ya baro sashenta.
Yana fitowa a daidai nan Hajiya Naja'atu ta fito daga sashenta riƙe da ƙatuwar akwati shaƙe da kayanta, tunaninta zai taho da sauri ya shiga bata haƙuri ya durƙusa mata ya karɓi akwatin ya mayar amma sai ta ga saɓanin hakan, lokacin da ya fito ta juyo suka haɗa ido alamar ya ganta sarai, amma sai ta ga ya saka gabansa inda ya dosa wato ɓangarensa ko kallo ba ta ishe shi ba, mamaki haɗe da mugun al,ajabin da ya kasa barin birnin zuciyarta ne ya mata dabaibayi.
***
[8/8, 6:55 PM] null: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH