BOOK 1
🅿1️⃣7️⃣
*HAJIYA NAJA'ATU*
Galala take tsaye baki sake hannu riƙe da akwati, zuciyarta tana gudun famfalaƙi, na tsananin mamaki da al'jabin abin da mijinta Muhammad ya mata a matsayinta na fitila kuma tilo a birnin zuciyarsa.
Ƙara gyara tsayuwa ta yi har lokacin bata dawo daga suman mamakin da take ɗauke da shi ba. Hannunta ta saka ta doki goshinta tana mai jijjiga kanta da mugun ƙarfi saboda a tunaninta dai abin nan da ya faru ba a zahiri bane, ta fi tunanin mafarki ne, duk da ko a mafarki bata taɓa zaton akwai wata rana da za ta fito ta gabas ta faɗa a yamma amma Alhaji Muhammad ya yi halin ko in kula da ita a fili ta furta
"Shin mafarki nake ko a zahiri ne? Mutumin da ko raina ne ya ɓaci abinci ma kasa ci yake, mutum da idan ya ga annurin fuskata ya kau zai gaza zaune ta kasa tsaye amma yau shi ne ya wanke fuskata da mari a kan uwarsa, sannan ya gannj a fusace rai a ɓace na fito da himilin kaya zan yi yaji amma ko a kwalar rigarsa, ni Naja na shiga uku" Ta faɗa tana jin gabanta yana difdifdif alamar bugawa.
Har ta fara jan akwarin a hankali amma sai ta fasa dama ta fito da ita ne domin ta san muddin ta fito ya ganta da akwati gaba ɗaya zai susuce hankalinsa ya tashi ya shiga lallashinta tana mata manyan kyautuka da alƙawarurruka masu tsoka, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa take tarkar hala kaya idan ta yi fushi amma daga ya ga ta nufi drower zai riga ta zuwa ya kasa ya tsare yana ta mata magiya, amma yau dai ruwa ya ƙarewa ɗan kada!.
Waiwaye ta tsaya yi sai da ta tabbatar babu wani mahluƙin da ya taho daga ɓangaren Goggo, sannan babu wani da ya ganta, ta yi dogon wuya wajen hango hanyar bakin get ko mai gadi ya ga wannan lamari, amma cikin ikon Allah ko ina kamar an yi shara. Waige-waigen harabar wajen ta shiga yi don kar wasu ƴan tsurku daga cikin ma,aikatan gidan su ganta. a zucuyarta ta ce
'Na so Alhaji ya zubar fa gwiwoyinsa a ƙasa yana bani haƙuri da lallashina yadda labari zai kai kunnen waccan kucakar uwar tasa amma sai aka samu alkasin lissafi ya tafi ya barni ko kallo ban ishe shi ' Ta faɗa tana mai canja akalar tafiyar tata zuwa komawa ɓangarenta tun da ta lura babu wani wanda ya ganta.
Tana zuwa ta shiga da akwatin daga ciki, ta tafi ɗakinta lokacin tana ta dokawa mahaifiyarta kira, sai dai ba a dauki kiran ba.
Tana shiga ɗakin lokacin kiran na biyu yana neman katsewa aka ɗaga, Mom wacce ta kame a kan kujera tana cin dubulan zaƙinsa yana kai mata har ƙwaƙwalwa ta kara wayar a kunne tana faɗin
"Ta gaban goshin miji... Ba ta kai ƙarshen maganar ba, kukan da Hajiya Naja'atu ta saka ya dakatar da ita haɗe da sanya gabanta bugawa da ƙarfi bata san lokacin da ta tashi ta xauna dakaka ba, cike da jin tashin hankali ta ce
"Mugun ji mugun gani Allah rabamu da mummunar ƙaddara, Naja,atu ba dai wani abu ne ya same ki ba"
Naja'atu cike da muryar kukan da sai da ta ji muryar Mom ya kufce mata ta ce
"Mom Alhaji ne ya... Mom ba ta jira ta ji ƙarashen zancen ba ta ji wani daɗi ya mata dirar mikiya a cikin ranta don a tunaninta Hajiya Naja'atu cewa za ta yi Alhajin ne ya mutu, hakan ya sa take ganin za su fara cin duniyarsu da tsinken tsire wato tun da bashi da ɗa bashi da jika ai gadonsa dole Naja'atu za ta samu kaso mafi tsoka.
Hajiya da bata gane abin da Mom ta fahimta ba hakan ya sa ta ji wani sabon kukan ya taho don idan har ta tuna cewa yau Alhaji Muhammad ne ya saka hannunsa ya kwashe fuskarta da mari sai ta ji duk ta tsani kanta ma.
Cike da son fahimtar da Mom ta ce
"Mom na ji kina wani batun da ban gane inda kika dosa ba, ni fa yau da hannun hagun na tashi domin Alhaji ne ya falleni da wani gigitaccen mari... Mom idanu ta zaro ba ta san lokacin da ta yi cilli da dubulan ɗin hannunta ba ta miƙe tsaye tana faɗin
"Mari fa kika ce Naja'atu? Giya ya sha ko burkutu?"
Hajiya ta ce
",Rasss yake wallahi daga faɗawa wannan baƙauyar uwar tashi magana shi ne har ya samu ƙarfin gwiwar marina" Hajiya ta kawo wasu ashar masu maiƙo guda uku a jere ta luƙa ta ce
"Mahaukacin ina ne shi, halan ya fara shaye-shaye, Naja'atu mutumin nan ko dai daman ƙarya yake shirga miki ba sonki yake yi ba? Amma ta yaya zai ɗaga yatsu biyar ya sauke miki?" Shiru ta yi tana sheshshekar kuka ita kuma Mom tana ta bala,i da cewar sai ta masa wankin babban bargo.
Hajiya ta ce
"Mom ba wannn ne abin da zai baki mamaki ba kin ga akwatina can a falo kayana na cika a ciki ta ɗauka zan bar masa gidansa...Mom ta ce
"Kul kar ma ki fara wannan mafarkin, idan kika bar gidan wannan ina muka kama, ni na rasa wannan masifa uwar miji ta zama kishiyarka wannn wane irin bala,i ne"
Hajiya ta ce
"Mom nima fa daman ba tafiya zan yi ba, na yi haka ne don na wana shi in ja masa rai in tada masa hankali amma wallahi kallo ɗaya ya yi min ya wuce ɓangarensa hakan ya nuna da tafiyata da zamana duk uwar ubansu ɗaya"
Mom ta ce
",Inyeee lallai wannan mutumin sai an taka masa birki, anya ba uwar ce ta shiga ta fita ga duba da irin makahon son da yake miki?"
Hajiya ta ce
.",Na zargi hakan nima, don har yanxu ban gama dawowa hayyacina daga duniyar mamakin da ya shayat da ni ba, abin takaicin ma a gabanta sannan a karo na biyu ma sai da ya sake ɗaga hannun zai mare ni wai sai ita ce ta riƙe masa hannunta tana wani faɗan munfurci"
Mom ta ce
"Rabu da shegiya guntun tuwon dawa da miyar kuka, wato ta samu ta kuɓuto daga ƙauye kan mage ya waye tana cin shinkafa da jar miya har take da damar da za ta yi wa rayuwarki kutse, ke da kike wayayya ƴar birni" Ta faɗa tana cigaba da kwashewa Goggo albarka, sun jima suna tattaunawa inda Mom ta ce
"Ki yi zamanki a ɗakinki idan ma so take ta ga ta fitar da ke ta sama masa wata a ƙauye, saboda na lura baƙinciki take saboda ke kaɗai yake so kuma ya ce ba zai ƙara aure ba, wannan dalilin ne ya hana rayuwarta sakat ga uwa uba rashin jikan da ta ƙwallafa rai"
Hajiya ta ce
"Ai sai dai ta mutu don wannan tsinken hana haihuwar na hannuna yana gama expire zan je na sake saka sabo, idan ba shekara goma ce ta zagayo ba zan ga uban da zai sakani in sake haihuwa, wallahi idan suka taɓani ma in ce ba zan haihun ba in ga ta tsiya"
Mom ta goyi da bayan ƙudurinta daga ƙarshe suka yi sallama tana batun za ta zo gidan, ta sauke musu ruwa bala,i da masifa, inda suna gama wayar Hajiya ta ci alwashin sai da damƙa masa kashinsa a hannu idan ana kwana ana tashi!.
Wayar ta ɗora a kan gado, ta fito falon ta ja akwatin ƙiii ta mayar ɗaki, saboda takaicin da yake nuƙurƙusar zuciyarta ma ba ta mayar da kayan drower ba a akwatin ta barsu.
A ɓangaren Alhaji kuwa lokacin da ya ƙarasa ɓangarensa ya haura sama, don shi har lokacin zuciyarsa zafi take na maganganun da Hajiya ta faɗawa mahaifiyarsa, tabbas ya san yana son Naja'atu kuma yana ƙaunarsa amma ko kusa ba za a haɗa matsayinta da na mahaifiyarsa ba, wacce ta zame masa bango abin jingina wacce ta tsaye masa ta hanyar amfani da aljihu da addu,arta har ya kai matsayi da matakin da yake takawa a yau!. Uwa uba ita ce ta sha wahala har ya dira a duniya ta ina za a haɗa matsayin Goggonsa da wata Naja'atu wannan ma gani yake kamar saɓo ne.
Bayan ya kwanta yana jin ƙamshin turaren nan da yaka jikinsa tamkar wanda bai yi wanka ba, ya rasa wannan wane irin turare ne mai kama jiki, duk da ya san yana da turaruka masu ƙamshi da zama a jiki amma wannan ma yana da matuƙar ƙamshi da daɗin shaƙa. Hannunsa duka biyun ya ɗago yana kallo ya mayar da idanunsa kan hannun da ya mari Naja'atu da shi zuciyarsa ta masa nauyin da yake jin ya yi wani abu mai girma na farko shi ba namiji ne mai ɗabi,ar dukan mace ba, amma yau zuciya ta kai shi ga aikata hakan, abu na biyu yadda hannun ya mari fuskar Naja'atunsa wacce yake matuƙar ƙauna, sannan ya san hanin da ma,aiki S.A.W ya yi a kan yin mari.
Juyawa ya yi ya ja bargo ya kwanta, yana mantar da tunanin Hajiyar don idan ya tuna abin da ta ce a kan Goggon sai ya ji ko kaɗan bai yi da na sanin abin da ya mata ba. Ya yi addu,a ya shafa bacci ya yi awon gaba da shi, falkawar da ya yi da asuba ya yi alwala ya nufi masallaci.
*RAMLA*
Washe gari da yamma tana zaune tana taɓa charting kiran Hasiya ya shigo wayarta, murmushi ɗauke a fuskarta ta ɗaga tana faɗin
"Assalamu alaikum"
Daga can ɓangaren Hasiya ta amsa, tana faɗin
"Barka da yamma ya gida fa yaranmu" Ramla ta amsa mata tana tamabayar su Nasira da Dada ta amsa da kowa yana lafiya.
Bayan gaisuwa shiru ya ɗan biyu baya Ramla ta ce
"An je gida lafiya?" Ta amsa da
"Lafiya ƙalaw, ai jiya sai da na hayo saman layinku sosai na samu napep dakyar na samu" Ramla ta ce
"Subhanallahi, ai daman sai da na ce miki direba ya kaiki amma kika ƙi"
Hasiya ta ce
"Karki damu ai ba komai ba na so ne na ɗora miki nauyi" Sun ɗan taɓa hira a takaice don yanzu Ramla ta lura tun daga mutuwar mijin Hasiyar, ta rage sakin jiki da ita sai ta danganta hakan da mutuwar ce wataƙila har yanzu bata gama sakin ta ba.
Sallama suka yi Ramla ta ci gaba da abin da take yi, a inda Hasiya ta ja ƙaramin tsaki a fili ta ce
"Daman zatona za ki min zancen mijinmu, don ba zan ce mijinki ba tun da ni ɗin ma yana dab da zama mallakina kamar yadda yake halaliyarki, na rasa ina ya shiga ina ta kiranshi shiru duk hankalina ya gaza kwanciya, amma da na kira sai na ji na kasa tambayarki daman zan tambaya ne cikin hikima, wato in ce ina baban su Humai kuwa fatan duk kuna lafiya a gaishe min da su. Na san idan na faɗi haka za ki iya faɗa min inda yake ta hanyar cewa yana lafiya ba ya nan ma ya fita sai dai da na yi tunanin mun kusa haɗa zaman kishi na san daga baya za ki iya ganin na raina miki hankali tun da har ina tambayarki shi yana matsayin mijinki kuma na san zan aure shi, zuciya ma tana iya zuga ki cewar ni na fara cewa ina son shi!" Ta faɗa tana miƙewa a doguwar kujera ta ajiye wayar haɗe da rufe idanunta tamkar mai bacci, ƙaran da wayarta ta ɗauka ne ta sanya ta buɗe idanun tana dubawa kuwa ta ga sunanshi ɓaro-ɓaro a kan screen ɗauka ta yi tana mai karawa a kunne ta ce
"Tun daɗewa nake ta faman kiranka amma baka ɗauka ba, duk hankalina ya tashi" Gyara zama ya yi a kujerar office ɗinsa ya ce
"Muna meeting ne wayar tana silent sai yanzu da muka fito na ga missed call ɗinki"
Fuska ta shawaɓe ta ce
"Duk na tsorata tunanin ba lafiya ba" Ya yi ƴar dariya ya ce
"Ko awa ɗaya ba mu yi da.yin waya ba fa"
Ta ce
"To ai ni yanzu kunnuwana sun saba da jin muryarka a koyaushe don haka ba na so ka yi nisa da ni"
Ya yi ƴar dariyar soyayya ya ce
"Kwantar da hankalin ki in sha Allahu nan da wasu ƴan kwanaki da ba za su rufa sati biyu ko uku ba za mu kasance a inuwa ɗaya wato tif da taya, don ba lallai ma a yi sati uku ba" Wani ɗan ihun murna ne ya suɓuce mata ta yi saurin rufe bakinta cike da kunya don bata zaci ihun zai fito ba, ta ƙosa Abdulsalam ya zama mallakin ta. Dariya shi ma ya yi suka yi sallama don ya ce yana shirin tafiya gida ne.
Bayan kwana uku su Humaira suka damu Mama Ramla a kan suna son zuwa gidan su Nasira, ta ce su bari ranar da babu makaranta sai su je. Haka aka yi kuwa sai suka tafi friday bayan masallaci direba ya kai su, saboda asabar fa lahdi ma suna da islamiya haka ma su Nasira ɗin. Ko da Ramla ta samu Abba da maganar a fili cikin halin ko in kula ya ce
"To tun da suna son yin zumunci ni ai ba na hana su ba" A zuciyarsa kuma ya ce
'Yara in dai har ganinsu kuke son yi sai kun gaji da ganinsu tun da sun kusa ƙaurowa kuke rayuwa tare, makaranta tare cin abinci tare komai da komai ma tare'
Daman Ramla ta sanar da Hasiya kuma ta nuna ta ji daɗi, tana maraba da zuwansu duk da yanzu kishin yaran take ji a ranta, saboda tana taraddadin kar idan an yi auren suke gorantawa ƴaƴanta ba ma wannan ba kawai tana kishin yaran tun da ubansu ya ce zai aure ta. Shi da kansa ya kira ta a waya ya ce yau tana da manyan baƙi ƴaƴanta za su zo gaishe ta ta nuna masa ta ji daɗin hakan a fili kuwa ta taɓe baki.
Ko da suka zo da yamma ta yi shirin fita zuwa gidan su ƙawarta Karima ta cewa Abban za ta je ta duba ta bata jin daɗi, ya ce zai zo ya kaita amma fir ta ƙi ta ce saboda su Humaira kawai ya bari. Bayan ta shirya ta fita, ta bar zobenta wanda Abba ya bata a kan madubi da ta cire tana gwada wasu zobunan sarka sai ta manta bata mayar ba, Zainaba da Aslamiya suna ɗakin bayan fitar ta, Zainaba ta ɗauki zoben ta gwada tana cewa ya mata kyau duk da ya mata yawa kuwa. Aslamiyya ma ta karɓa ta gwada a babban yatsan hannunta, suna cikin haka Dada ta ƙwala musu kira suka fito da gudu, ko kaɗan Aslamiyya ta manta ba ta cire wannan zoben ba. Kafin ma Hasiya ta dawo direba ya je ya ɗakkosu ana kiran magriba.
Suna shiga sallah suka nufi za su yi, Aslamiyya za ta yi alwala ta ga zoben ta tuna, da ta fito ta je falon ta ce
"Aslam ka ga zoben nan Zainaba ta ban na gwada na Auntynsu ne fa, amma shaff na manta ban ajiye ba na taho da shi, sai yanzu na gani da zan yi alwala, ka gani ya ɗan min yawa ma duk da babban yatsa na saka" Mama Ramla tana jin haka ta ce .."Ku dai Allah ya shirya ku, yanzu zoben ne kuka ɗakko mata sai kun jefar mata? Kawo nan a ajiye kar ku ɓatar mata" Tana dariya ta ce
"Gashi Mama" Ta faɗa tana ɗorawa Mama Ramla a tafin hannun da ta miƙo mata. Tana ɗauke hannunta idanun Mama suka sauka a kan zoben idanu ta ƙanƙance kafin ta zaro idon, ƙirjinta ya bada sautin rasss a take hannun nata ya fara karkarwa da har sai da zoben ya suɓuce ta faɗi ƙasa....
*** [8/9, 7:22 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH