BOOK 1
🅿1️⃣8️⃣
*RAMLA*
Hannunta yana karkarwa ta kai za ta ɗakko zoben daga faɗuwar da ya yi a saman kafet ɗin, Allah kaɗai ya san irin yanayin fargaba da tashin hankali da ya saukar mata a zuciyarta muryar Aslamiyya ce ta katse ta da ta ce
"Mama hannunki karkarwa yake" Ta faɗa tana riga Mamar tata kai hannu ta ɗakko zoben ta miƙa mata, Mama Ramla da take jin zuciyarta tana wani dik-dik-dik ta yi saurin danne abin da take ji ɗin cike da ƙarfin hali ta ce
"Ban san ma ya aka yi hannun nawa yake karkarwar ba" Ta faɗa tana miƙewa tsaye sai ta ji gabaɗaya ƙafafunta sun sage tamkar ma wacce dila ya kamawa ƙafafu, amma haka ta dage ta tsaya a kan ƙafafun nata ba tare da ta bar wani abun da zai sa yaran su fahimci komai ba.
Aslamiyya tana damƙa mata zoben ta yi saurin barin wurin, domin a yadda take jin zuciyarta barin wajen da yaran suke shi kaɗai ne mafita, ji take tana son ta kaɗaice saboda tana buƙatar kaɗaicewar domin yin nazarin zulumin da take ciki.
Ɗakinta ta nufa, tana zuwa ta buɗe ƙofar tare da mayar da ƙofar ta rufe, jingina ta yi a jikin ƙofar, tana jingine da bayanta a jikin ƙofar ta ɗaga zoben tana ƙare masa kallo a fili ta furta
"Shi ne, wallahi kamar shi, amma idan har shi ne ya aka yi zoben ya je hannun Hasiya tun da Aslamiyya ta ce nata ne?"
Wani ɓangare na zuciyarta ya ce
'Ke kuwa shin ba a iri ɗaya? Ai ba Abdulsalam kaɗai ne aka yi wa zoben ba da a ce shi ya zana zoben da hannunsa aka ƙera masa, kuma zoben yana da wata alama ta harafin da za ki shaida cewar nasan ne shi ne za ki tuhumi mai ya kai zoben Hannun Hasiyar, amma zoben nan kina iya ganin guda ɗari irinsa' Shiru ya gifta a tsakanin maganganun da suke kai kawo daga zuciyarta da kuma wanda suke zuwa da dawowa a kan laɓɓanta.
A hankali ta fara taku zuwa tsakiyar ɗakin har lokacin tana riƙenda zoben, sannan wasi-wasin yana nan a zuciyarta sai dai ko kaɗan zuciyarta ta ƙi aminta da cewar zoben ne saboda abin akwai ɗaure kai.
Safa da marwa take a tsakar ɗakin ta furta
"Ta yaya zoben Abban Humaira zai je hannun Hasiya? Haba shaiɗan mai ya sa kai kullum baki da aiki sai saka wasi -wasi a ƙirajen mutane?" Ta sauke ajiyar zuciya.
Ranta wata irin suya yake mata, duk da har yanzu zargi ne a zuciyarta ba wa tana da tabbas ɗin cewar zoben Abban bane.
Jin an kira isha,i ta tashi ta gabatar da sallah saboda ba za ta iya zuwa ma wajen yaran su yi ba, lokacin da ta kai goshinta ƙasa ta shiga faɗawa ubangiji damuwarta. Da ta idar ta koma bakin gadon ta zauna.
Tana zaune a bakin gado tana ta wasi-wasi, shigowar Humaira ta ce
"Mama mu je mu ci abinci" Ta ɗan lumshe idanu ta buɗe tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce
"Ki je gani nan zuwa" Humairar ta ɗan kafe ta da ido ganin Mama ba ta bata damar furta wani abun ba don haɗe fuska ta yi ba yabo ba fallasa saboda ta san halin Humaira da fahimtar hali ko damuwar da mutum yake ciki, Humaira ma ganin hakan ta juya ta fita tare da rufo mata ƙofar.
Ajiyar zuciya ta sake saukewa, ta ware tafin hannunta wanda ta rufe hannun lokacin da Humaira ta shigo ta jimƙe. Tashi ta yi ta je gaban madubi ta janyo ƴar ƙaramar loka ta saka zoben a ciki, saboda ba ta son ko kaɗan yaran su san halin da ake ciki amma dai sai ta tuntuɓe sho ta ga da irin kalaman da zai yi amfani wajen kare kansa.
Saboda babu wani mutunci ko kima ga iyayen da suke sa'insa a gaban ƴaƴansu idan matsala ta faru a tsakaninsu, a cikin hikima kuma a bayan idon yaran ake warwarewa ba tare da sun ga wata ɓaraka a tsakanin iyayen ba.
Da sallama ta shiga ta same su a kan dining Aslam yana zaune yana game, ta aro walwala ta ɗora a fuskarta tare da ɓoye asalin fuskarta da take lulluɓe da damuwa, kaso mafi yawa a cikin damuwar tata a kan batun zoben bai wuce irin yadda Abban Humaira ya nuna mata bata da wani muhimmanci ko kima a idanunsa ba ya ci mata fuska, a ƙarshe a ɗakinsa ta ga takardar da ya yi yunƙurin rubuta mata saki a ranar da abin ya faru, kenan ko ma wa ya ba zoben nan tana da matsayi mafi girma a wajensa, matsayin da ita duk kasancewarsu tsawon shekaru bata same shi ba tun da gashi a rana ɗaya saboda waccan ɗin zai iya rubuta mata saki, ba tare da ya duba ta a matsayinta na abokiyar rayuwarsa ba, matsayinta na wacce ta masa halacci ba matsayinta na uwar ƴaƴa a gare shi ko bai mata halacci don kanta ba ya kamata a ce ya mata halacci don ƴaƴanta tun da bahaushe ya ce ana barin halal don kunya.
Tun da ta shigo falon ta same su sai ta ga babu Abbansu, kuma ta san an yi sallar isha'i ya dawo, ta san ba zai wuce ɗakinsa ba, ita ta rasa shi wane irin mutum ne da bai cika ba iyali lokacinsu ba, ba zai zauna ana hira ana raha da iyali ba. Sai da ta ja kujera ta zauna cike da wasa ta ce
"Ko duk kun ci abinci ni ce kaɗai kuka bari in ci nawa?" Aslamiyya ta ce
"Haba Mama wa zai iya cin abinci bakya nan" Aslam ma tasowa ya yi ya ce
"Mama ni yau a baki ma za ki bani" Dariya ta yi tana kallonsa har ya zo ya ja kujera ya zauna, ta sanya hannu ta dafa kafaɗarsa ta ce
"Ƴan biyuna yau kuma ɓacin ne ya motsa?" Ta faɗa tana ɗan karkata kai tana kallonsa kai ya gyaɗa, yana yi wa Aslamiyya gwalo, sauke ta yi daga kan tata kujerar ta shiga buga ƙafa tana faɗin
"Mama kin ganshi ko yana min gwalo" Humaira ce ta ƙyalƙyale da dariya ta ce
"Wolalo ba za a bata abinci a baki ba an fi son Aslam"
Takowa ta yi ta zo gaban Mama ta kifa kanta a kan kafaɗar Mamar tana kukan ɓaci Mama ta dafa ta da ɗayan hannun ta ce
"Kyale su, sai na baki a baki kin ci kin ƙoshi sannan zan bashi sauran" Ɗagowa ta yj ta yi tsalle ta ce
"Yeee" Gabaɗaya suka kwashe da dariya, tashi Mama ta yi zuwa ɗakin Abban domin ta kira shi su ci abincin.
Tana dab da shiga ɗakin ta ji dirin magana alamar kamar yana magana, hannunta riƙe da handle ɗin ƙofar tana son buɗewa ta ji ya ce
"To yanzu ya kike so a yi uhummm" Gaban Mama Ramla ne ya doka da ƙarfi don ta ji tabbas da mace yake waya tunanin zoben nan ne ya faɗo mata a rai a take ta ji tashin hankalinta ya ruɓanya da da suna magana da yaran har ta sha,afa da damuwar tata amma yanzu ya sosa mata mikin, kunnenta ta kara a jikin ƙofar duk da laɓe ba halinta bane, sai ta ji ya ce
"To ki yi haƙuri kin ji, kaina bisa wuyana" Shiru ta ji ya yi alamar ana magana daga ɗayan ɓangaran jim kaɗan ta ji ya ce
"Idan baki haƙura ba ko abinci ba zan ci ba" Hannun ƙofar Mama Ramla ta saki ta riƙe haɓa da hannu ɗaya a zuciyarta ta ce
'An bar jaki ana dukan taiki, ni ban san mai wasu mazan suke son su zama ba matarka ta sunna bata da damar ganin fara,a da walwalarka, bata da damar ku zauna ku tattauna matsalolin zamantakewarku, bare ka ji damuwarta, wasu matan na gida da zarar sun shiga gidan aure batun soyayyar nan babu shi sai dai ki gani a novel ko film ko wasu daga cikin matan masu rabo mazajensu suke musu, amma sai namiji ya samu wata a waje yake ƙure malejin kalaman soyayyarsa a wajenta ke ta gida ko oho, kin zama mai gadin gida da rainon ƴaƴa'
Wani kishi ta ji ya tokare ta, da sauri ta murɗa ƙofar ta tura ba tare da ta ƙwanƙwasa ba, har sai da ƙofar ta doku da jikin bango. Abba da ya yi ɗaiɗai a tsakiyar gado yana rungume da filo ɗaya, yana cikin shauƙin soyayya ya ji hankaɗowar ƙofar, zaune ya miƙe babu shiri ya kusa lailayo ashar amma sai idanunsa suka sauka a kan Ramla, yana jin muryar Hasiya tana magana amma ganin Ramla ya kawar masa da nutsuwar da zai gane abin da ta faɗa masa, gefe ya ajiye filo ya sauke wayar daga kaunnensa ya datse kiran, yana muzurai ya hayyaƙo mata da faɗin
"Ramla wane irin shashanci ne wannan?" Ya za ki doko min ƙofa ba ƙwanƙwasawa ba sallama" Takaicin furucinsa na farko ya fi ƙona mata rai, hakan ya sa ta ji zuciyarta ta sake hasala itama ta hayayyaƙo masa cike da zafin kishi ta ce
"Ni kake kira shashasha? Shin igiyar aurenka a kaina har ta baka damar ka kirani da kowane sunan ƙasƙanci? Saboda kawai ina zama a ƙarƙashin inuwar aurenka?" Wayar ya ajiye gefe ya ce
"Oh na fahimta daman takanas kika zo ki ci min mutunci, in ba haka ba daga magana sai cibi ya zama ƙari, kamar daman kina jiran kulle ki ce casss"
Takowa ta yi zuwa tsakiyar ɗakin ta ce
"Abban Humaira na gaji da abubuwan da kake min, ka san dai an daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa"
Ya ƙara hasala da furucin ta ya ce
"Tun da ita ƙasar ta gaji da shanye ruwan ai sai ta burtso shi ko?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye ta masa wani kallo ta ce
"Saboda bamu da galihu irin na sauran iyalai shi ne za ka zo ka yi shame-shame a tsakiyar gado kana waya da wata? Bayan mu iyalinka muna da buƙatarka muna buƙatar lokacinka, shin ka mana adalci? Na ce akwai adalci a cikin wannan abin da ka yi ko kake yi?"
Gabanta ya zo ya tsaya cike da mamakinta ya ce
"Hummm daman ku mata har kullum lissafinku ɗaya ne, duk charting ɗin da mutum zai yi to da wata mace yake, duk wayar da mutum zai yi da wata macen yake, duk fitar da zai yi daga gidan lissafinku wajen wata mace zai je, kin zo kin sameni ina waya da abokin aikina muna maganar a kan abin da ya shafi wajen aiki amma saboda neman dalili kina faɗin da mace nake waya don ki nuna min na yi watsi da ku, shin rashin zuwa cin abinci tare da ku shi ne rashin adalcin ko rashin kulawa ko kuwa shi ne rashin bada lokacin? Idan kika yi aiki da hankali wanda ya nemo abinci ya kawo maka ai ya gama maka komai ba sai ya zauna kun ci tare ba, ko zuwa kiran nawa da kike in za a ci abincin shi ne ya tsaye miki a rai"
Ranta in ya yi dubo ya kai ƙololuwa wajen ɓaci musamman da ya ce wai da namiji yake waya bayan ta san fa mace yake waya ta kalle shi ranta yana ƙuna idanunta suna cikowa da ƙwalla ta ce ..."Waya da namijin ne sai ka kwanta ka rungumi filo? Ko an faɗa maka ban ji abin da kake faɗa a wayar ba... Bata ƙarasa ba ya tari numfashin ta da faɗin
"Ya isheki Ramla kenan laɓe kike min a bakin ƙofa? To tun da hakan ne lissafinki na yi ɗin" Idanunta ta rufe a hankali ta danne zuciyarta ba ta ma ƙara furta komai ba ta juya fuuuu ta baro ɗakin nashi don idan ta zauna tana ci gaba da musayar kalamai da shi to tabbas za ta yi ta ɓacin rai.
Sai da ta tsaya a ɗan korido ta goge idanunta ta saisaita kanta tana ambaton Allah har ta ji ta ɗan samu nutsuwa sannan ta nufi dining ɗin tun kafin ta ƙaraso Aslam ya ce
"Mama muna ta jiranku yunwa fa muke ji, amma sai muka ganni ba tare da Abban ba"
Ta yi dariyar yaƙe tana jan kujera ta zauna ta ce
"Na same shi yana banɗaki ne shi ya sa yanzu ba gani na zo ba "
Aslamiyya ta ce
"Mama ina Abban to" Ta ɗan yi shiru saboda bata so ta ce musu yana zuwa saboda bata san ko zai zo ba, tun da sun yi rabuwar baram-baram.
Cikin ƙarfin hali a fili ta ce
"Yana nan zuwa" Ta faɗa tana fara janyo kwanuka ta shiga zubawa kowa, har shi ɗin ma ta zuba masa duk da bata da tabbas ɗin zuwansa.
Sun fara ci kenan sai gashi ya fito, ya zauna yaran suka fara masa magana ya amsa musu ya ja abincin ya fara ci ba tare da ya kalli ko inda Ramla take ba.
Suka kammala kowa ya tashi, Mama Ramla ta sanya Aslamiyya da Humaira suka kwashe kayan.
Da daddare ta ɗauki zoben nan ta nufi ɗakin Abba don tana son gano dalilin wanzuwar zoben idan wanda take tunani ne.
Ko da ta same shi chart yake, daman lokacin da ta je kiransa maganar cin abincin tana fita sai da ya kira Hasiya suka yi magana yana faɗa mata Ramla ce ta faɗo masa ɗaki babu zato ba tsammani shi ya sa ya kashe.
Zama ta yi a bakin gadon ta ce
"Magana na zo mu yi Abban Humaira"
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce
"Ramla na gaji da wannn gutsuru tsomar naki, yanzu har kin ga fuska a wurina da za...
Maganarsa ta katse ne da Ramla wacce bata ce masa ko uffan ba ta dire masa zoben a kan cinyarsa, bai san lokacin da ya ajiye wayarsa da sauri ya ƙurawa zoben ido wasu kalmomi da bashi da amsar su suka fara masa aringizo a ƙwaƙwalwa a zuciyarsa ya ce
',Ina Ramla ta samo zoben nan? Kar dai Hasiya baki suka haɗa da Ramla duk soyayyar da nake da Hasiya shuka nake a idon makwarwa?"
*** [8/10, 7:35 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH