KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿1️⃣9️⃣

*HAJIYA NAJA,ATU*

Tun daga wannan rana sai ya zaman tamkar maƙiyan juna ita da Goggo saboda ji ta yi ta tsani Goggo tun da har Alhaji zai zaɓe ta fiye da ita a tunaninta son da yake mata zai fifita ta fiye da mahaifiyarsa bata san cewa uban kuturu ma ya yi kaɗan bare na makaho.

Goggo kuwa ta tattara tsumman rayuwaer Hajiyar ta ba bango ajiyarta tun da ta ga ita bata gaji arziƙin sanin darajar manya ba.Duƙufa ta yi a kan addu,ar Allah ya kawowa ɗanta mafita, ya kawo masa wacce za ta share masa hawayensa ta kula da shi ko ya samu nutsuwar aiwatar da komai cikin salama.

A tsakaninta da zaɓantakewa da Alhaji bata sauya zani ba, don tana nan a kan bakanta na ƙin sake haihuwa sai bayan shekara goma, shi ya sa inplan ɗinta da ta sa ko tunanin cirewa ma bata yi, uwa uba haƙƙinsa na auratayya ko girmamawa a matsayinsa na mijinta duk ta yi watsi da su.

A ɓangaren Alhaji kuwa har yanzu yana jin sonta yana nan daƙare a birnin zuciyarsa, kuma yana nan kan bakansa na ƙin ƙara mata kishiya dan son ransa sai dai don biyayyar mahaifiyarsa.

Yau kimanin kwana biyar da direbansa ya kaɗe Falmi kuma tun daga ranar bai sake ganinta ba sai dai a zuciyarsa yana yawan tuna ta, ama ba irin tunawa na soyayya ba kawai dai yana tunawa da ita lokaci zuwa lokaci ne don kaɗewar da aka yi mata, yana tunanin ya kamata a ce an duba ta idan ya tuna cewar ba shi ne ya kaɗe ta ba direbansa ne sai ya fara tunanin to ta yaya zai je ya ce ya zo dubata sannan yadda ya ga wacce ta ɗauke ta a tsaitsaye take sai ya ji ba zai juri cin mutunci ko cin fuska ba.

Zaune yake a falo yau ya kama asabar babu zuwa office, wayarsa ce ta yi ƙara ko da ya ga baƙuwar lamba bai ɗaga ba saboda ya san bai wuce wannan mai kiran nashi da sunan tana son ta aure shi ta share masa hawaye, kallon kiran ya yi har sai da ya katse ya doka ƙaramin tsaki a zuciyarsa ya ce

'Ni in dai don ki auren ki share min hawaye ne gwara ki barni in dawwama hawayena yana zuba'

Ranar litinin ya dawo wurin aiki shi da direbansa za su wuce ta layin gidan su Falmi kamar yadda ya ji sunan da aka kira ta, har sun zo daidai inda aka kaɗe ta yana kallon gidan a zuciyarsa yana faɗin

'Ko ta samu sauƙi? Ko kuwa tana nan babu lafiya'Ya faɗa yana tuno lokacin da aka shiga kafaɗarsa aka ɗaga ta. Kamar daga sama ya tsinci muryar direban yana faɗin

"Alhaji wurin nan ne tsautsayi ya faru ranar nan ko ya jikin nata" Alhaji kamar direban ya san tunanin da yake tun da tun ranar basu biyo layin ba sai yau, Alhaji ya ce

"Tabbas a nan ne" Direban ya ce

"Ko dai mu tsaya a duba ta Alhaji" Ya faɗa saboda ya san halin uban gidan nashi bashi da girman kai shi ya sa yake tunkararsa da kowace magana idan buƙatar hakan ta taso.

Alhaji ya ce

"To ba damuwa, daman a ƙa'ida tun da mu muka yi mata sila ai mu ne da ɗawainiyar ta, to matar nan ce ta hana" ,Samun wuri direban ya yj ya faka motar ya buɗe ya fito yana duddubawa ko zai samu yaro ya masa sallama amma bai ga kowa ba, ƙofar gidan ya nufa ya ƙwanƙwasa get ɗin, matar nan ce dai ta ranar nan ta buɗe ƙofar da alamar ma kamar fita za ta yi, tana buɗewa ta kalle shi sama da ƙasa don ita bata ma shaida shi ba ta ce

"Ya dai malam lafiya kake ƙwanƙwasa mana ƙofa?" ,Ya ce

"Barka da yamma daman nine wanda tsautsayi ya faɗa mjn ranar nan na kaɗe wata a nan layin shi ne na ce bari na ji ya jikinta"

Rai ta haɗe ta ce

"To sai aka yi yaya, ni ai bana buƙatar dubiyarka kuma ban da dai ka raina min hankali yau ne za ka... Maganar ta ta katse ne fitowar Falmi tana faɗin

"Wai aunty ke da wa ne kike ta ɗaga murya?" Wacce aka kira da Aunty ta ce

"Wanda ya kaɗe ki ne da ganganci"

Alhaji da yake cikin mota duk yana ganin abin da yake faruwa, tun da Falmi ta fito ya ƙura mata ido yana son gano ta warke ko da saura sai dai yanayin shigar jikinta kaɗai zai tabbatar maka ta warke sanye take da laffaya ruwan goro hannunta riƙe da ƙaramar jaka da alama ma fita za su yi babu alamar jinya ko wani abu Alhaji Muhammad bai san lokacin da a fili ya ce

"Alhamdulillah!" Sai bayan ya yi furucin ya juya hagu da dama a cikin motar yana son gani ko waninya ji abin da ya ce, sai lokacin ya tuna ashe shi kaɗai ne a motar.

Yana jin maganarta cikin sanyin hali da daɗin kalaman furucinta ta ce

"Allah sarki, haba Aunty ganganci kuma ai tsautsayi ne...

A zafafe ta ce

"Ke ni rufe min baki, ke da zuciyarki tamkar ƙanƙara haka take kan sanyi yadda kika san ba jinin gidanmu ba a ce mutum kai sai haƙuri ina dalili" Shiri ta yi jin ta hayayyaƙo mata ta ja bakinta ta yi shiru.

Alhaji sai ya ji gabaɗaya tausayinta ya kama shi direban ya ce

"Allah ƙara tsare gaba a yi haƙuri dai" Falmi ta ce

"Amin don alfarmar annabin rahma S.A.W"

Auntyn ta ta ce

"Haƙuri kaya ne naɗa gammo ka ɗauka" Falmi duk dai ta ji bata ji daɗin abin da aka yi wa direban ba, tahowa ya yi ya buɗe motar ya shiga yana faɗin

"Alhaji... Kafin ya ƙarasa Alhaji ya dakatar da shi da faɗin

"A kan kunnena aka yi komai" Direban yana shirin jan motar Alhaji ya dakatar da shi hakan ya sa bai tada ba, su Falmi ne suka zo dab da motar ta shi za su wuce da alama ma makota za su shiga, ƙofar ya buɗe ya fito yana faɗin

"Barkan ku dai" Falmi ce ta ce

"Barka da yamma ina yini" Ya amsa yana faɗin

"Ya sauƙin jiki" Ta ce

"Alhamdulillah"

Alhaji ya ce

"Allah sawaqe ki mana afuwa bamu zo dubiya ba sai yau"

Tana ɗan wasa da gefen laffayar jikinta ta ce

"Lah ba komai na warke ma, " Ta faɗa tana ɗago dara-daran fararen idanunta masu yalwar gashi ido ta sauke a cikin idanunsa, shi ma kallon nata ya yi har yana jin tamkar kar ya sauke idanunsa daga kallonta don haƙiƙa kallon da yake yi wa kyakkyawar fuskarta sai ya ji ba ya so ya daina. Kiran sunanta da Auntyn ta ta yi tana tsaye ƙofar gidan da yake fuskantar inda Alhajin yake a ce

"Aunty Fanna gani nan zuwa fa" Ta faɗa tana cewa

"No gode sai an jima" Ta faɗa tana tafiya ba tare da ta jira cewar Alhaji Muhammad ba.

Tana zuwa Aunty Fanna ta ce

"Kin zauna kina biya daɗin bakin mutanen can, baki san halinsu ba, da a ce tsautsayi ya zo da kaɗewar da aka yi miki da sai dai a yanke miki ƙafa kina kallo iyaka su bada haƙuri" Bata ce uffan ba ta shige gidan Aunty Fanna ta tae mata baya.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Alhaji ya sauke, ya shiga motar tare da ba direban umarni, ya ja suka tafi , idanunsa kafe a kan gidan da suka shige, ya ma kasa gane dalilin da ya sa ya ji kamar dai su dawwama da ita lokacin da take masa magana, komai nata abin birgewa ba kamar yayar tata da ko magana bata yi wa mutane ba ta wuce.

Ranar haka ya kwana yana tunaninta, abu kaɗai sai yake tuno da furucinta yana murmushi ganin abin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ya ce a zuciyarsa

"Na kasa gane kaina mai nake nufi ne?"

Bayan kwana biyu Alhaji ya dawo daga office ranar shi ya tuƙa kansa a shirin da ya yi yana so ya biyo ta wajen gidan su Falmi, amma ba ya so su biyo da direbansa hakan ya sa ko da ya biyo yana addu,ar Allah sa ya hangota ko da daga nesa ne, shi kansa bai san dalili ba amma ba ya alaƙanta hakan da so domin ya san kaf cikin matan ba bu wacce yake so sama da Naja,atunsa duk da bata ɗauke shi a bakin komai ba.

Adduarsa ta karɓu domin kuwa tun daga nesa ya hango ta nufi hanyar gidan da alama daga wani wajen take,ɗan ƙara gudun motar ya yi ganin tana ƙoƙarij tura get ɗin sai kawai ya yi mata horn, Falmi jin an yi wani iron horn ta waiwaya ta ga ashe dai a dab da ita ne ake yi, cikin sanyin jiki ta juya za ta shige a karo na biyu ya sake yi ganin za ta tafi ya yi saurin fitowa daga motar tana ganinsa ta murmusa ta tako shi ma kakowar ya yi bakinsa ya ƙi daina murmushi tana zuwa ta ce

"Barka da yamma" Ta faɗa tana ɗan rusunawa ji ya yi yau ta fi kullum birge shi take yi.Amsawa ya yi bayan ta jingina bayansa da jikin mota ya ce

"Ke yawo gare ki ko" Ta yi murmushi gefen kumatun ta ya loɓa ta ce

"Ba daga yawo nake ba aikena aka yi ne" Ya ɗan yi shiru sai ya ce

"Dama wucewa zan yi na hango ki shi ne na tsaya mu gaisa" Ta yi murmushi ta ce

"Na gode"

Ya ce

"Mene ne sunanki Ta ce

"Sunana Fatima ana kirana Falmi, mu ƴan asalin garin Maiduguri ne, aure ne ya kawo Auntynah nan shi ne nake zaune a gidanta" Kai ya gyaɗa cike da gamsuwa, gabaɗaya.wajen ya haɗe da wani irin ƙamshi ya ce

"Zan wuce sai kwana biyu" Cike da ladabi ta ce amsa masa da faɗin

"Allah ya kiyaye hanya" Ya ce

",Amin" Ya faɗa yana buɗe murfin motar ya shiga ya tada tana tsaye ya ja ta ɗaga masa hannu, maimakon ya ɗaga mata hannu sai ya yi horn. Yana tuƙi yana ta nishaɗi shi kaɗai, shi kansa ya rasa dalilin da ya sa yau ya dakatar da direbansa ya fita shi kaɗai don kawai ya biyo ta layin ya ga Falmi, bai san dalilin da ya sa yake ji idan tana magana kamar kar ta dajna saboda zaƙin da muryarta take ɗauke da shi gashi cikin nutsuwa take yi.

Har ya ƙaraso get ɗin gabaɗaya tuƙi yake cikin annashuwa.

Sai da mai gadi ya wangale masa get sannan ne ya fara tunanin mai ya sa bai karɓi lambarta ba. Wani sashe na zuciyarsa ya ce

',Mai kuma za ka yi da lambarta?' Wani ɓangaren na zuciyarta ya ce

',Kawai muke gaisawa"

A ɓangaren Magajiya yau kimanin sati da sakin Rumasa'u yau tun asuba Ruma take rusa mata kuka ta ce

"Wallahi Mama nidai na gaji ya za a yi tsawon sati guda kina mini hanya-hanya kin saka na kashe aurena yanzu kuma kin kasa samo min mafita" Mama Magajiya ta doka tsaki ta ce

",Shin Ruwa uwata ce ke? Ko ke kika haifeni a kan me za ki dameni ai na ce aure babu fashi, don haka ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa wuyarta ki gama idda tuni za a ɗaura miki aure da Yayanki Muhammad mu koma mu rayu a daula" Ta juya ta kalli Umar da Usman da suke bacci cikinsu ya yi lakwaf saboda yunwar da suka kwanta da ita jiya ta ce

"Mama muna zaune cikin rufin asiri bamu rasa ci da sha ba, kin sa mun dawo duk ɗan kuɗin hannuna ya ƙare, jiya garin kwaki muka ci da rana da dare babu garin tuwo ga shinkafa ta ƙare"

Mama Magajiya a fusace ta ce

"Ruma wallahi ki kiyaye ni bana son iskancin banza da wofi, abincina iya cikina nake dafawa amma kuka ƙaru rai uku to ba dole komai ya ƙare ba, sannan daman kayan abincina sun kusa ƙarewa, kawai da asuba kike rafka min kuka kamar gidan mutuwa" Banza Ruma ta yi, zuwa jimawa Mama ta ce

",An jima ki shirya ki je gidan naki" ,Idanu ta zaro ta ce

, ,"Gidana kuma wane gidan nawa?"

Mama ta ce

"Gidan Muhammad ɗin mana tun da kina dab da ɗora karagar mulkinki a cikin gidan ai dole a kira gidan da gidanki" Wani murmushi ne ya suɓucewa Ruma ta ji zuciyarta wasai.

Mama Magajiya ta ce

"Ki haɗa kayanki yau mu je in raka ki, gwara ki tare a can idan kina kusa yana ganinki ai sai soyayyar ta fi ƙulluwa" Wani tsalle ta doka ta dafa kafaɗar Mama Magajiya ta ce

"Allah dai ya biya Mama ai kayan daɗin ma ta waya zan ke turo miki" ,Dariya Mama Magajiya ta yi ta ce

"Ai gidan nan za mu koma ƙwanmu da ƙwarƙwatarmu"

Wajen sha ɗaya na safe suka shirya su duka, suka tari napep Ruma ce ta ranta kuɗi a wajen ƙawarta don ko na napep ɗin basu da shi. A bakin get aka ajiye su, Ruma tana riƙe da katuwar akwati, Mama Magajiya tana riƙe da wata ƙaramar jaka da Ruma ta xuba takalmanta a ciki.

Sun shigo suna yi wa mai gadi kallon tara saura kwata, suka wuce ko gaisuwarsa Mama Magajiya bata amsa ba, a daidai ɗakin baƙi suna tafiya za su tafi ɓangaren Goggo Ruma ta ja ta tsaya ta ɗaga kai tana ƙarewa gidan kallo ta lailayo ashariya ta yi ta ce

"Har na hangoni a matsayin matar gidan nan"

Usman ya ce

"Gaskiya idan muka dawo gidan nan da zama mun zama ƴan gata"

Mama Magajiya ta ce

"Ai gata iya gata ma yaro"

Ruma ta ajiye akwatin ta kama ƙugu ta ce

"Mama har na hangoni mub jero da Yaya Muhammad matsayin mijina, wallahi wannan zoƙoƙuwar matar tashi mai kamar fara sai ta zama bora a gidan nan"

Mama Magajiya ta ce

",Ai kina gama idda za a ɗaura muku aure abinku tuwona maina, ku mu je mu ƙarasa ɓangaren Goggon"

Hajiya Naja'atu da take cikin ɗakin baƙi ta je uzurinta ya kaita tana dube-dube, duk wannan maganganun da su Mama Magajiya suke a kan kunenta" Wata ashar mai maiƙo ta narka tana kamo hanyar fitowa a fusace a fili tana faɗin

"Ma ga uban da zai barki ko sakan ɗaya ki yi a gidan nan da kuka kwaso ƙafafu da shegiyar akwati mai warin talauci kuka taho min gida, a kan sawunku za ku koma kuma za ji nuna min wace ce mai kamar fara!!!"

*** [8/11, 7:55 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH