KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣0️⃣

ABDULSALAM

Duk da ya ruɗe da ganin zoben amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama, sai ya dage ya danne wannan fargabar duk da ba tsoro yake yi ba Ramla ta san halim da ake ciki, amma dai ya yi mamakin yadda zoben ya zo hannunta idan har ba Hasiya ce ta bata shi ba a ina za ta samu?.

Cike da rainin hankali ya ce

"Ramla mene ne hakan? Mene ne wannan za ki ɗakko wani ƙarfe ki ɗora min shi a kan cinya?" Tana masa kallon lallai idan da ranka ka sha kallo ta ce

"Wannan ne ƙarfe? Idanunka basa ganin shi a zobe ne ko yaya? Ko za ka ce baka gane zoben nan ba, idan har ka manta ni da ban manta ba bari na tuna maka, shi ne dai xoben da a kansa a wata ranar da ba zan manta ba ka bini har ɗakina kana min faɗan in fito maka da abin da na je ɗakinka na ɗauka bayan ka san sata va ɗabi,a ta bace, baka gushe ba har sai da ka shiga watso min kayana saboda kana ganin zoben ɓoyewa na yi daga ƙarshe da ka koma ɗakin saboda muhimmancin zoben, ko in ce saboa muhimmancin wacce za ka mallakawa zoben sai da ka yi yinƙurin rubuta mini takardar saki!" A daidai gaɓar na da sauri ya ɗago ya sauke idanunsa a kanta don shi har ga Allah bai ma san ta ga takardar ba, tun da ya fara ƙoƙarin rubuta takardar ya hangi zoben wannn dalilin ya sa ya fasa.

Ta ɗora da faɗin

"Abdulsalam ka manta wace ce Ramla a gareka ne? Ka manta irin soyayya da ƙaunar da na nuna maka fisabilillahi, ka manta irin sadaukarwar da na yi a gareka amma a ce a kan wani zoben da za ka baiwa wata ƴa mace ni har za ka iya rabuwa da ni? A zatona ko wuƙa aka saka maka a wuya ba za ka iya sakina ba za ka ce mutuwa ce kaɗai za ta raba mu ashe dai kai ba haka bane a zuciyark... Ganin tana son gano lagonsa tun da har yake sauraronta hakan ya sa ya katse ta fa faɗin

"Ya isa haka Ramla, a kan batub me kike yi ne, kina ta batun zobe -zobe ni ban ma gane inda maganarki ta dosa ba, kuma da kike batun saki shin na sake kin? Ai ko da kin ga takardar da na yi yunƙurin hakan wataƙila na tuna wace ce ke ɗin har na fasa hakan shi fa shaiɗan a koyaushe burinsa ya shiga tsakanin ma,aurata" Ganin ya hayayyaƙo mata ya sa ta ja bakinta ta ɗinki, duk da ita yanzu fargabarta shin wannan zoben da ta zo tuhumarsa da shi zobensa ne da ta gani kwanaki, ko kuwa ba shi bane idan har shi ne mai ya kai shi gidan su Hasiya, kuma mai ya sa yaran basu danganta kowa da zoben ba suka ce na Hasiya ne, idan har zobensa ne kuma a wajen Hasiya mai hakan yake nufi?.Wata zuciyar ta ce

'Babu inda ake bada zobe sai wajen da aka ƙulla soyayya'

Ganin ta ɗan yi shiru ta zura masa ido ya sa ya ɗan sha jinin jikinsa amma duk da hakan bai bata wata ƙofa da za ta gano rashin gaskiyarsa ba, shi a nashi tunanin abu ɗaya yake jira ya samu ƙwarin gwiwar kare kansa ta kowace hanya, wato yana son ya san cewar wannan zoben Hasiya ce ta bata kuma ta faɗa mata abin da yake tsakaninsu?

Wani ɓangare na zuviyarsa ya ce

'Da wuya wai gurguwa da auren nesa, babu ta yadda za a yi Hasiya ta faɗa mata tsakaninku fa sannan uwa uba kai da kanka ka gamsu cewar Hasiya da gaske take sonka kuma take son ta aureka, idan har ta karɓi soyayyarka ne don ta haɗa baki da matarka Ramla da tuni ka gano tsantsar rashin gaskiya a tare da ita'

Daga wani ɓangaren kuma zuciyar ta ce

"Abdulsalam ka san wace ce mace kuwa anya? Ka san su waye mata, to idan baka sani ba ka sani yawanci ku maza ku ne kuke wa wasu matan kallon basu san abun da suke yi ba, ba su da dogon tunani ko kuka musu kallon basu da wayo musamman idan kuka haɗa da kanku maza amma wata macen ta fi wani namiji nazari da tunani kuma akwai abin da mata za su haɗe maka kai baka isa ka gane inda suka saka gaba ba, mace da kake ji da gani shu,uma ce, sannan shaiɗan da kansa idan ya hangi taron mata tsoron shi yake saboda kaidin wasu matan yana da tsanani matuƙa' Wannan ɗan jijjiɓin kalamai masu jan hankali da zuciyarsa ta rattabo masa su ne suka saka ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar da ita kanta Ramla sai da ta ji saukar ajiyar zuciyar, da sauri ta kalle shi ita ma ya yi saurin kawar da kansa gefe yana ɓoye abin da yake kan fuskarsa don ba komai ne damuwarsa da tashin hankali ba idan har Hasiya rufarsa ta yi ba za ta iya aurensa ba ta yi hakan ne don ta taya ƴar uwarta mace Ramla nuna masa shi maci amana ne to tabbas yana cikon damuwa, zuciyarsa za ta iya bugawa idan Hasiya yaudararsa ta yi don ya gama yarda cewar zai aure ta ya rayu da ita kamar yadda ya daɗe yana dakon zonta tsawon shekaru sai yanzu da ya sakankance zai mallake ta, ta nuna masa arewa ba kudu bace!.

Wata zuciyar ta ce masa

"Sun haɗa maka maƙarƙashiya ne shi ya sa suka yi amfani da zoben nan domin su ƙara gane gudun ruwanka su ƙara tabbatar maka kai makaryaci ne idan ka ce ba zobenka bane, kuma ka san dai Ramla ta ga zoben a ranar da ka shigo da shi tun da har ta faɗa maka cewar a kan zoben ka yi yunƙurin sakin ta, wataƙila ko charting ɗin da kake da Hasiya yanzu duk yana cikin abubuwan da za su yi amfani da shi su kama ka, ko su bari sai ka je hira kuma zaune cikin mota Ramla ta zo su maka ɗiban albarka a ƙarshe ka yi ba wan ba ƙanin, wato ba Hasiya ba Ramla'

Muryarta ta katse matsa dogonnzancen zucin da yake ta ce

"Ka yi shiru ka barni kamar an shuka dusa" Ya juyo ya ce

"Ni fa ban san ma wannan wane zobe bane, shi zoben da kike magana a kansa tun a ranar na fita da shi daga gidan" Ta ƙanƙance ido ta ce

"Ka kaishi ina?" Ya zaro ido cike da ƙarfin hali ya ce

"Ya kike min wasu tambayoyi kamar wata uwata ne Ramla, inda na kai zoben ma sai na faɗa miki" Zuwa yanzu zuciyarta bugawa take da mugun ƙarfi domin cike take da fargabar cewar zarginta zai zama gaskiya.

Cike da raunin zuciya ta tashi daga kan gadon, baya ta bashi ta maƙala hannuwanta a ƙirjinta, ta yj taku ɗaya biyu ta ja ta tsaya, ta ɗaga kanta sama ta sauke a kan silin, hawaye masu zafi suka surnano mata, ba komai ne ginshiƙin hakan ba sai tunowa da ta yi da sadaukarwar da ta yi wa Abdulsalam a baya, idan ta cire gabaɗaya irin abubuwan da ta masa na halacci ta ajiye a gefe wannan sadaukarwar da ta tuna guda ɗaya ita ce har yau idan ta tuna sai ta ji bata yi wa kanta adalci ba, babban abin da yake sakawa ta ji hakan sai yadda soyayya ƙauna, haɗe da sadaukarwa. Ta runtse idanunta hawayen masu zafi suka zubo.

Duk da ba ganin fuskarta yake yi ba ya san tsantsar damuwa ce a fuskar, sai dai ba zai nuna mata ya karaya ba a kan cikar burinsa, shi yanzu abu ɗaya yake son ji shi ne a ina ta samu zoben, matukar ya tabbatar da cewa ba Hasiya ce ta bata ba to zai yi ƙoƙarin ganin ya linketa a baibai ba tare da ta fahimci ainihin gaskiyar lamarin ba.

A ɗan hasale ya ce

"Kin zo da zobe kina ta jan maganganu, bayan ni ban ma san inda kika samo zoben ba, kin san dai ba wai ina tsoron ta mutu bare ta yi rai ba, matsawar akwai wani abu dangane da zoben da na faɗa, bari ki ji in faɗa miki wannan zoben da kika gani, wata budurwa ce na yi, yarinyar ƴar candy ce wato ta gama secondry school shi ne ta ce na kawo mata zobe, shi ne na saya na bata daga baya ma da na gane bata da tarbiya na watsar da lamarinta" Ya faɗa da nufin ta warware masa biri har wutsiyarsa.

Ɗiff ta yi, da farko ta ji matuƙar haushi da ta gane ya yi haka ne a kan wata yarinya ƙarama, yarinyar da a haihuwar kaji ma zai iya haifarta, musamman idan ta tuna a kan ƙaramar yarinyar ne zai sake ta. Amma dai sai ta ji da dama dama wai KIBIYA A IDO, a maimakon a.ce zarginta ne ya zama gaskiya wato wata alaƙa ce tsakaninsa da Hasiya.

Hannu ta sanya ta share hawayenta, wani irin daɗi ya cika masa zuciya, ta juyo ta ce

"Amma wannan zoben na Hasiya ne" Saboda tsabar ɗan duniya ne shi ya ɗan yatsina fuska ya ce

"Wace ce Hasiya?" Ta kalle shi da mamaki fal fuskarta ta ce

"Hasiyar ce baka sani ba?" Ya ɗan yi jim kamar mai tunani ya ce

"Kin san Allah na manta ina dai jin kamar na san sunan" Ita abin ma sai ya bata dariya tana darawa ta ce

"Wai Hasiyar ka manta lallai Abban Humaira, to Hasiya dai matar Zahraddin Allah jikan rai" Ya ce

,"Oh kin ga ta kwanta min kin san ni ba damuwa na yi da sabgar mutane ba, to ke mai ya kawo zobenta hannunki?" Ya faɗa yana mai tsura mata ido ta ce

"Aslamiyya ce ta kawo shi gidan nan" Ta faɗa tana kwashe yadda aka yi zoben ya zo hannnunta ta faɗa masa. Ya sauke ajiyr zuciya ya ce

"To ke da, da kika zargi cewar zoben da na shigo da shi kwanaki ne, ni mai zai haɗa ni da su wata Hasiya har zan je gidansu na jefar da zobe" A zuciyarsa ya ce

'Wasu matan suna da ƙaramar ƙwaƙwalwa har ta yarda da bayanina, ba tare sa dogon nazari ko bincike ba, wasu kam akwai saurin yarda'

Ramla ta ce

"Kawai dai na ga iri ɗaya ne da wanda ka kawo kwanakin" Yana basarwa ya ce

"Kawai dai iri ɗaya ne"Ya faɗa yana cewa ta samo masa shayin, da to ta amsa masa ta fita, tana fita ya yi hau whatsapp suka ci gaba da charting shi da Hasiya, bai faɗa mata maganar zobe ba sai kawai ya ɗauki hoton ya tura mata tana gani ta tura emoji ta zaro ido ta ce

"Wani ne ka sake saya?"

Ya ce

",Ba wani siya wannan nakin ne dai" Ta ce

",Ban gane ba a ina ka ganshi?" Ya ce

"Wallahi a wurin Ramla... Hasiya da take kwance a katifa jin abin da ya ce da sauri ta tashi zaune tana jin gabanta yana bugawa da ƙarfi.

***

[8/17, 5:24 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH