KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣1️⃣

*HASIYA*

Ta tsorata matuƙa da da kalamansa, dakyar ta samu ta saita kanta sai dai ta yi ƙoƙarin yin typin ta tambaye shi ya mata bayani dalla-dalla sai dai hakan ba samu ba sanadin yadda jikinta yake karkarwa hakan ya sanya ta kasa rubuta komai, da sauri ta shiga masa voice call, shi kuma yana ƙoƙarin ɗauka sai kiran ya katse, a ɓangarenta ita ta katse kiran amma kuma va tare da ta san ta danna ba hakan ya sanya garin ta sake masa voice call sai ta danna video call.

Ɗagawa ya yi, hakan ya yi daidai da dawowar Ramla cikin ɗakinsa nasa, kasancewar fuskar wayar tana fuskantar ƙofa ne, muraran ta hango Ramla ta shigo ɗauke da ƙaramin kofi a kan ƙaramin plate. Abdulsalam da dawowarta ta masa bazata ya yi saurin kife wayar a kan gado, ba tare da ya katse kiran ba, bai san cewar Hasiya ta datze kiran tun da ta hango Ramla don ita bata ma yi tunanin bidiyo ta kira shi ba, sai da ta hango shi kafint a furta wani abu ta ga Ramla shi ya sa ta katse kiran.

Ramla ta lura bidiyo call yake domin idanunta sun sauka a kan screen ɗin wayarsa, amma ganin ya kife wayar sa ta nuna bata ma san yana yi ba. Ƙaramin tebur ta janyo ta ɗora masa shayin, tana shirin zama ya ce

"Ki ɗakko min spoon bana son shan shayi yau da tea spoon" Kallon mamaki ta masa amma ya haɗe rai, hannu ta kai ta ɗauke tea spoon ɗin ta juya ta fita daga ɗakin tana mamakin wannn sabon salon wai kiran sallah da usur.

A ɓangaren Hasiya tana kashe wayar ta ajiye ta a kusa da ita ta dafe ƙirji, shigowar Dada ɗakin ya dakatar da ita saboda furucin ta na faɗin

"Hasiya lafiya kuwa? Ya na ganki kamar wacce aka ƙwato daga bakin kura gabaɗaya a firgice kike, ko wani abu ne ya faru?" Hasiya ta ɗago goshinta da ya jiƙe da gumi ta ce

"Dada komai fa ya faru"

Dada gabanta yana faɗuwa ta ce

",Ba dai ya fasa aurenki ba Hasiya?" Ta faɗa tana dafe ƙirji da hannu biyu kamar an sanar da ita mutuwar wani makusancinta.

Hasiya ta ce

"Dada ba wai maganar ya fada bane, batu ne a kan Ramla" Dada ta yi saurin sauke hannuwanta daga saman ƙirjinta da ta dafe tana jifanta da wani kallo tare da yin ƙaramin tsaki ta ce

"Aikin banza,.aikin ɓur in ji tusa, to ke kuwa wane dare ne jemage bai gani ba sai ko daren mutuwarsa, yanzu Hasiya kin shirin shiga gidan mace fafatawa zaman kishi da ita amma har kike barin wani abu a kanta yana saka zuciyarki bugawa, har kike ruɗewa, shin Abdulsalam don Ramla kaɗaia aka yi shi ne? Ki sa a ranki tun fil azal daman akwai aure tsakaninku an samu jinkiti ne kawai, ban da ƙaddarar auren Zahraddin da kuma haihuwar su Nasira wataƙila ma da ke Abdulsalam ɗin zai fara aure, kuma na san da a ce ke ya aura ma ba zai yi marmarin sake kallon wata mace a matsayin mata ba, don kin fi wannan matar tashi sau dubu sai dai ta faɗa miki dogon hanci da diri"

Hasiya ta ɗan runtse ido ta buɗe su a kan Dada ta ce

"Dada ke kin sanni tayar keke nake bani da gaba bare baya, kuma ni hadari malafar duniya ce, kuɓa Ramla bata isa ta ɗaɗani da ƙasa ba don a yadda na saka rai zan auri mijinta kuma na ƙwallafa rai a shiga gidansa, na gwammace duk wata alaƙa ta rushe a tsakaninmu, amma duk batun ba wannan bane ina zoben da Abdulsalam ya bani"

Dada ta ce

"Wannan me ɗankaren kyan yana sheƙi?"

Kai Hasiya ta gyaɗa alamar eh, ta ce

"To zoben ne Abdulsalam ya gani a wajenta" Dada ta zaro idanu ta ce

"Kina nufin naki zoben ko kuma ita ma siya mata ya yi, ko tare ya siya muku, ko kuwa nakin ne ta san yadda ta yi ya je hannunta saboda ta je a yi mata wani mugun abu a zoben ta kawo ki saka a hannunki komai ya wargaje, fahimtar da ni na kasa gane komai"

Hasiya ta ce

"Dada nima dai ban sani ba, amma dai tabbas zoben ne duk da ban san ta yadda aka yi ya je hannunta ba, amma nidai zoben ba ya hannuna, bari na tabbatar shi ne" Ta tashi da sauri ta duba inda ta ajiye amma bata gani ba ta shiga bincike Dada tana tsaye riƙe da ƙugu aka duba zobe ko sama ko ƙasa amma babu shi babu alamarsa.

Hasiya ta ce

"Wallahi zoben ne, mai hakan yake nufi"

Dada bata yi magana ba ta ɗan tsaya nazari tana riƙe da haɓa ta ce

"Da walakin goro a miya, to an yanka ta tashi, wato dai zuwa ƴaƴan Ramla gidan nan yau ba alkairi bane, anya ba aiko su ta yi su ɗauki zoben ba? To Allah sa ma dai ba wani barbaɗe-barbaɗen suka yi a gidan ba kika taka" Gaban Hasiya ya buga tana jin wata faɗuwar gaba saboda tunanin kar Ramla ta girgiɗe auren daular da take fatan yj ta shimfiɗa sabuwar rayuwa!.

Idanunta a waje ta ce

"Dada Ramla bata yi kama da mata masu bibiyar malamai ko bokaye ba" Dada ta galla mata harara ta ce

"Inyeee to tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, an faɗa miki ana gane mugu a fuska ne, ko an faɗa miki idan za ta je faɗa miki za ta yi, " Kai ta girgiza. Alamar a,a amma dai tana shakku a kan maganar sai dai ruɗun da ta tsinci kanta a ciki ya dagula mata lissafi maganar Dada ta katse mata tunani da ta ce

"Wataƙila ma ba mutum ne ya zo ya ɗauki zoben ba" Idanu ta zaro cike da mamaki ta ce

"Kamar ya Dada?" Dada ta ce

"Ko bokan nata ne ya aiko aljani ya ɗauka, ke ki rabu da mutum fa mugun icce ne, hummm ki ji tsoron Allah, ki ji tsoron sharrin mutum" Duk batun nan da suke wayarta tana ƙara kuma Abdulsalam ne yake ta kira sai dai ta kasa ɗagawa ma ga ruɗun da take ciki ga kuma tunanin ko dai ma bashi ne yake kiran ba Ramla ce ta kwace wayar take kiranta, duk da ta san shi ba kanwar lasa bane kuma ta san daga yanayin rayuwarsa Ramla ce take karɓar gashin ƙuma a zaman auren ta san shi ba namijin da mace za ta juya bane daga yanayinsa, amma dai baka fahimtar baccin makaho!.

Kamar za ta yi kuka ta ce

"Dada gabaɗaya kin sakani a ruɗu kar dai mafarkina na auren Abdulsalam ba zai cika ba, na ɗora rai a kan zan yi sabuwar rayuwar jin daɗi a gidan daula ba a gidan talauci ba kamar yadda na yi a baya"

Dada ta ce

"Sha kuruminki ai aure kamar an yi an gama, kawai dai ki ɗauki wayarki ki ji kiran da yake miki"

Hasiya ta kai kallonta kan wayar, Dada ta ce

"Ki ɗauka komai ta fanjama fanjam, rigima uban wa ta kashe"

Hasiya ta ce

"Ni dai ban so Ramla ta san maganar auren nan yanzu ba wallahi, ba haka na tsara ba" Dada ta harare ta ta ce

"Wallahi kika ce tsoron kishiya za ki saka a ranki idan ta ga lagonki kin shiga uku, kashi ma sai ya fiki kyan gani"

Hasiya ta ce

"Ba za ki gane ba ne Dada"

Tsaki Dada ta yi.

Abdulsalam tun fitar Ramla da ya ɗauki wayar ya ga Hasiya ta sauka daga online yake kiranta, saboda ya sanar da ita cewar ga yadda aka yi zoben ya zo hannun Ramla don ya lura kamar ta ɗan ji tsoro.

Amma yana kira bata ɗaga ba, ganin kiran da yake mata ya fi a ƙirga bata ɗaga ba hakan ya sa ya fara saƙe-saƙe cewar kar dai Hasiya ta janye airensa duk da ya san da wuya wai gurguwa da auren nesa, amma dai tun da ya gane cewar ba wai wata maƙarƙashiya ce suke shirya masa ba wato ba wai soyayyar ƙarya take masa ba suka haɗa kai da Ramla har ta bata zoben, hakan ya sa ya ji duk wata fargaba ta kau a zuciyarsa. Sosai abi ya ɗaga masa hankali da ta ƙi ɗaga kiran bai san cewa ita ma suna can ita da Dada suna cikin nasu ruɗun ba, a zuciyarsa ya yanke shawarar ya tashi ya fita ya je gidan Dada a wannan daren ya samu Hasiya, in ya so idan ma batun auren ta janye ya bata haƙuri ya sa Dada ta taya shi bata haƙuri don a yadda yake ji yanxu a kan Hasiya da a ce ya rasa aurenta gwara komai ma ya faru.

Tsaye ya miƙe ya ɗauki wayarsa tare da key ɗin motar, Ramla ta turo ƙofa ta shigo, ganinsa a tsaye da mukulli da waya a hannunsa alama ce da ta nuna mata cewar fita zai yi, cike da mamaki ta ce

"Ina kuma za ka je Allah sa dai lafiya?" Wani haushinta ya ji ya turnuƙe shi, tun da yana ganin duk ita ce silar damuwar da yake ciki, da a ce bata zo da batun zoben ba da yana cikin annashuwa da soyayya, tun da a lokacin da ta zo masa da batun ma suna cikin charting shi da Hasiya amma yanzu koɓai ya rikice ta ɓata komai tun da gashi yana ta kiran Hasiyar shi kansa bai san iya adadin kiran da ya msta ba amma bata ɗaga ba, bayan ya san tana tare da wayar.

A taƙaice ya ce

"Lafiya" Ta ƙarasa gaban teburin ta saka spoon ɗin a cikin kofin shayin, ta ce

"Ikon Allah, amma shayin da ka saka na haɗa maka fa ai zii huce" Ba tare da ya kai kallonsa gare ta ba ya ce

"Na fasa sha" Ganin gabaɗaya fuskarsa babu annuri yana bata amsa kamar ya haɗiyi gatari ta ce

"Amma ka san ba sha za ka yi ba ka sa na je na haɗo maka" Cike da gajiyawa da maganarta ya ce

"Ramla kayan shayin nan ji na saya da kuɗina, sannan ke kuma zamana kike, kin ga kuwa tun da dai zaman aure kike a ƙarƙashina ko sau dubu zan ce ki haɗa min shayin kuma na ce na fasa sha ban ga dalilin ki na yin ƙorafin daman ba sha zan yi ba na ce ki haɗa" Yana faɗar hakan ya fara takawa yana nufar hanyar ƙofa.

Ramla ta ce

",Har yau kana nan a kan halayanka wanda baka taɓa.canjasu, ko don ƴaƴanka ya kamata a ce a cikin gidan nan muna zaman aure irin na ma,aurata, ba a ce a kowane gidan aure babu saɓani ba, amma a ƙalla a samu zaman lafiya da fahimtar juna, a samu soyayya da jin ƙai a tsakanin ma,aurata, yara su taso suna ganin walwala da farinciki a tsakanin iyayansu, wannan zai ba yaran damar fuskantar rayuwa, su san cewar zaman aure ana ɗabi,a mai kyau su ma hakan ya zame musu abin koyi idan sun yi nasu auren, amma a ce komai faɗa komai izza komai rashin fahimta, yanzu mene ne abin cewar kawai saboda ina zaman aure ko sau dubu za ka sakani in haɗo shayin ba zan yi ƙorafi ba, shi fa zaman aure ba wai zaman kurku bane da za a ce mace bata da ƴanci don kawai a ƙarƙashin wani take, ubangiji ya sanya namiji matsayin jagora ne a cikin gida don a samu shugaba a gidan, mace ta san cewar namiji shi ne zai bata umarni ta bi ba wai an baku shugabancinnne don ku nuna izza ko tauye haƙƙin macen ba, ai ubangiji da ya haɗa ma,aurata sai ya sanya mawaddatan wa rahma, wato soyayya da jin ƙai a tsakanin ma,auratan sannan ya ce su tufafi ne a gareku, kuma tufafi ne a gare su... Daga bakin ƙofar da yake ya bata baya ya ɗaga mata hannu yana faɗin

"Ya isa haka Ramla, baki san damuwar da nake ciki ba, ke har abada baki san abin da za ki faɗawa miji ba, ke kullum kanki kika sani, sai wani batun a zauna lafiya yara su ga ana zaman lafiya ana fuskantar juna ana wanene menene shi kaɗai kika iya, mata da yawa sun san yadda za su yi magana da miji amma ban da ke, ke kamar ke kika fi kowa sanin ya kamata, don haka ni ina da abin da ya fi wannan kalaman naki muhimmanci" Yana faɗar haka ya ja ƙofar zai fita hakan ya yi daidai da faɗowar zoban hannunsa na wajen Hasiya, ita da shi suka kai kallonsu a tare kan zoben, shi ya ɗan razana saboda tunanin kalaman da zai ce tun da ta ga zai fita a gefe ɗaya kuma daman ta zarge shi a kan zoben, sannan kuma da ya ɗauka ina zai kai? Ya san wannn tambayar ce za ta yi mata dirar mikiya a zuciyarta.

Cike da ƙarfin hali yana haɗe rai tamkar bai taɓa dariya ba ya ce

, ",Ina sauri ma har na manta da wannan ƙarfen a riƙe a hannuna, ki ɗauki ki ba yaran nan su mayar mata idan za su je ko kuma idan ta zo ko kin je ki bata ni bana son yayime-yayimen kayan mutane a gidana" Kafin ta furta wani abu ya fice daga ɗakin tare da banko mata ƙofar.

Ɗif jinta da ganinta ya ɗauke na ɗan wasu sakanni, a lokacin da ta yi arba da zoben da ya faɗo daga hannunsa, sai dai tambayoyin da suka fara mata arangama a zuciyarta tuni Abdulsalam ya yi mata fatali da su ta hanyar furucin da ya yi, a take ta ji ta neme su ta rasa.

A nan ya barta tsaye sai dai ta kasa saƙe-saƙen ma don ba yau ne karo na farko ba da zai yi abu kafin ta yi yunƙurin zarginta ko furta wani abu a kan abun tuni zai yi amfani da kalamansa masu kaifi ya danƙwafar da nata tunanin ko zargi a kan abun, sai dai har yau ta kasa fahimta, wataƙila son da take masa ne ya yi awon gaba da komai ta yadda ba ta gane komai da kuma tsananin yarda da ta yi da shi tana ganin kamar ba zai cuce ta ba. Ƙaran buɗe get ɗin gidan ne ya dawo da ita daga ɗan guntun tunanin tana jin lokacin da mai gadin ya rufe get ɗin bayan ya fita da motar.

Ta kalli zoben ta ƙarasa ta ɗauka, tana sake ƙare masa kallo, har lokacin dai tana jin zuciyarta kamar tana rawa a kan maganar amma dai wani ɓangare na zuciyarta ya ce

'Kin ga alamar bashi da dangantaka ma da zoben ko a jikinsa ya bar shi a nan inda fa faɗi, daman bai san ma yana hannunsa ba, sannan da kunnenki kin ji ya ce miki ba ya son kayan mutane a gidansa, sannan kuma kin san dai kafin mutuwar Zahraddin ma ba wani jituwa Abban Humaira yake da shi ba bare kuma Hasiya, ranar nan da ya zo a gabanki dakyar ya amsa gaisuwarta' Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke ta koma ta zauna a bakin gadon ta kalli shayin da ya sa ta haɗa masa, sai dai tunaninta ɗaya shi ne ina zai je sannan mene ne damuwar da ya ce yana da ita bayan ta san da ta tambaye shi lafiya zai fita a wannan lokacin ya ce mata lafiyaa.

A ɓangaren Abba, yana fitowa daga gidan ya fara tafiya, kasancewar gudu yake saboda gabaɗaya a kiɗime yake da rashin daukan kiransa da Hasiya ta ƙi yi, bai fi minti huɗu da fara tafiya ba kiran ya shigo wayarsa, wani uban birki da ya ja taimakonsa da Allah ya yi ma, babu abin hawa a bayansa kasancewar layin shiru, tsayar da motar ya yi domin yana kallon wayar ya ga ita ce, yana tsayawa da sauri ya kai hannu kafin ya ɗaga kiran ya katse yana shirin kiranta wani kiran da shigo yana ɗauka ya ce

",Haba Hassytah, mene ne hakan mai ta sa kikason saka zuciyarta cikin ɗimuwa ne? Mai ya sa za ki nesanta da ita a daidai lokacin da take cike da son kasancewa da ke" ,Wani murmushi ne ya suɓucewa Hasiya jin kalamansa hakan yana tabbatar mata da cewar duk runtsi da wuya Abdulsalam yana tare da ita, Dada wacce take tsaye ta kafe Hasiya da ido ganin ta murmusa ita ma Dada murmusawar ta yi don tunaninta ma ko wani albishir ɗin wasu kuɗaɗe masu nauyi ya mata.

Ta sanyaya murya ta ce

",Duk ka sa na ruɗe da batun zoben ne, hankalina yana ga duba shi, in tabbatar shi ne, wannan dalilin ne ya sa ban ɗaga kiran ba" ,Ajiyar zuciya ya sauke ita kanta ta ji sautin hakan ya ce

"Amma sai ki bar ni a damuwa, yanzu kin sa gani na na fito ina cikin tuƙi ma na tsaya don wajenki na taho saboda hankalina ya kasa kwanciya, abin da ya sa ma ban ɗaga kiran ina tuƙi ba gudun kar ki faɗa min wata maganar da za ta sa motar ta kuɓuce min"

Hasiya ta ce

"Wai da gaske ko wasa ka fito"

Ya ce

"Wallahi da gaske Hasiya" Ta yi shiru tana tunanin ashe har matsayin nata ya kai don bata ɗaga kiransa ba ya baro cikin iyalinsa a wannan lokacin saboda ita, kai ta jijjiga tana tunanin lallai Abdulsalam ya wuce duk inda take zato a soyayyarta.

Ta murmusa ta ce

",Ina zoben?" Lokacin ma Dada ta bar ɗakin.

Ya ce

"Yana wajen Ramla"

Ta ce

",Mai ya sa ka bata?"

Ya ce

",Kin santa da kishi, tun da kuma na ɓatar da tunaninta ta hanyar nuna zoban ba na wajena bane kamar yadda take zargi, a tunanina da in maido miki shi yanzu saboda ba ƙaramin ƙawata min hannunki zoban yake ba in ya so sai in ce mata ban ma san inda yake ba, to kuma sai aka yi rashin sa,a ya faɗo daga hannuna a ƙoƙarina na buɗe ƙofa ya faɗo da na ga ta gani shi ne fa na bar shi ina cewa ban ma san yana hannuna ba" Hasiya ta tuntsure da dariya ta ce

"Kai ko" Shi ma dariyar ya yi ya ce

"Ni me?" Suka ƙyalƙyale da dariya a a tare.

*HAJIYA NAJA,ATU*

Kamar za ta tashi sama haka ta fito tana haɗa hanya, Mama Magajiya da Ruma da suke cike da farinciki babu zato da tsammani suka ganta kamar an jefo ta, Mama Magajiya cike da wayincewa don bata taɓa tunanin Hajiya Naja,atu ta ji maganganun da suke tattaunawa ba.

Cike da tsantsar rashjn mutunci ta kalle su ta ce

"Mai na ji kuna cewa?" Mama Magajiya ta murmusa ta ce

"A ina kuma?" Hajiya ta ce

"Kar ku mayar da karuwa ƴar iska mana, ya ina tambaya kina tambayata" Ruma wacce take jinta kanta ɗaya da Hajiya Naja,atu a ganinta in aka bi ta wani fannin ma ta fi Hajiyar matsayin tun da tana dab da taka matsayi biyu ne a gidan, matsayin ƙanwa ga mai gidan sannan amaryarsa ta ce

"To da karuwa wace ce in ba ƴar iska ba, tun da har ta kai matakin da za a kira ta da karuwa ai kuwa ni a ganina ma babu wacce ta cancanci a kirata da ƴar iska sama da karuwar" Hajiya Naja'atu ta ce

"Ke ƙaramar alhaki, ƙaramar ƴar iska ina zuwa kanki yanzu da uwarki zan yi tukunna" Mama Magaji ta dafe baki ta ce

"Naja da ni kike cewa za ki yi, kin manta ni ƙanwar sirikarki ce Goggo" ,Tuno da mugun haushin Goggo da take ji ya sa ta yatsina fuska ta ce

"Sunan makaranta ne hakan? Ko kuwa filin sukuwar dawakai ne haka" Salati Mama Magajiya ta ɗauka tamkar an yi wani gagatumin abu ta ce

"Sunan uwar mijin naki ce filin sukuwar dokuna Naja? Baki san bin na gaba bin Allah ba... Hannu ta ɗaga mata a fusace ta ce

"Ke Magajiya bari ki ji in faɗa miki, duk wani munafurci da kutungwilar da kuka shiryo zuwa gidan nan na gama jinsa, ban da ma.ɓatan basira har ina wannan ƴar taki take da kalar macen da za ta yi tunanin Alhaji zai iya kallonta a matsayin mace? To bari ku ji in faɗa muku ku ja tsumman ƙafafunku ku bar gidan nan kafin na saka a fitar da ku, ni nan ni kaɗai zai rayu da ni kuma wallahi idan har kuka kuskura raina ya kai ƙololuwar ɓaci sai na haramta muku shigowa gidan nan gabaɗaya ma" Daga Mama har Ruma sai suka samu kansu da kallon gidan, kafin su dawo da kallon su kan Hajiya Naja,atu Mama ta ce

"Lallai Naja wato Ruma ce bata da kamar mata? Ke har kina da bakin magana, Ruma juya ta ganki kema kin isa abar kallo ga kowane ɗa namiji ba ga mijin nata kaɗai ba" Ruma ta juyo bayanta ta yi taku ɗaya biyu tana karkaɗa mazaunai, ta ƙara juyawa Mama ta ce

"Ruma cikakkiyar mace ce, kuma tun da ke baki da kunya za ki san ke ce gidan nan zai haramta a gareki, amma Ruma kamar ta shigo gidan nan ta gama ne" Ruma ta ce

"Mama ai faɗa ma ɓata baki ne" Hajiya Naja'atu a ƙufule ta warci akwatin hannun Ruma ta hankaɗa akwatin gefe ta sanya ƙafa ta taka akwatin da ƙarfi Mama ta sanya hannu ƙiiii ta janyo rigar Hajiya Naja'atu, Hajiya Naja,atu ta ɗaga hannu ta wanke fuskar Mama Magajiya da mari, Mama ta dafe kunci tana sakin rigar Hajiya tare da sakin wani uban ihu, Ruma ta doka tsalle ta shaƙo wuyan Hajiya Naja'atu tana kai mata wani uban naushi a baki, Hajiya ta saki wani ƙara, Goggo wacce ƙaran TV ya hana ta jin maganganun da ake yi sannan kuma da ɗan tazara daga inda suke zuwa ɓangaren nata, sai dai ihun da Mama ta saki da wanda Hajiya ta saki ya ankarar da ita akwai abin da yae faruwa, ta shiga ƙwalawa Amira kira Amira wacce take wanke banɗakin Goggo ta fito da sauri ta zo don amsa kiran Goggo.

Goggo ta ce

",Amira fita ki duba na ji ana hayaniya da ihu, ko dai wasu ne suka zo neman taimako mai gadi ya hana su shigowa ake tababa, ki ce na ce ya barsu su shigo, ai shi arziƙi Allah ya baka ne kaima sai ka bayar taimakon mutane wanda basu da shi yana da kyau, saboda kaima baka da tabbas ɗin za ka gama rayuwarka da arziƙin akwai samu kuma akwai rashi, duk ɗimbin dukiyarka watarana tana iya gushewa, sannan shi talaka hakan ba yana nufinnzai dawwama a talauci ba, watarana Allah yana iya azurtashi don komai yana da lokaci!" Kai Amira ta jinjina alamar gamsuwa tana son Goggo saboda ta san mai take yi kuma tana da hangen nesa.

Fitowa ta yi daga nesa ta hangi ana wani abu mai kama da dambe, idanu ta ƙura musu ana ta tumurtu tsakanin Hajiya Naja,atu da wacce bata gama gane wace ce ba, Amira ta fara tafiya a hankali tana addu,ar kowace ce yadda ta shaƙi Hajiya Naja Allah sa ta nakaɗa mata na jaki. Ranta fari ƙal kamar ta yi tsalle saboda murna.

Hajiya hannu ta kai ta riƙo kafaɗar Ruma, Usman da Umar da suka ga ana faɗa da mahaifiyarsu, suka cire takalmi suke dukan Hajiya Naja, Mama Magajiya ta kama ƙafar Hajiya Naja'atu, Hajiya jin an warci ƙafarta ana ƙoƙarin raba ta da ƙasa ta shiga kurma ihu amma sai da Mama ta kaita ƙasa, Sai sannan Amira ta taho da sauri tana rafka salati, ta juya da gudu tana kwalawa Goggo kira, Goggo wacce ta jiyo kiran Amira da sauri ta taso tana gyara ɗaurin zani don ta tabbata ba lafiya ba.

Goggo ta fito tana faɗin

"Lafiya?" Amira ta ce

"Ana ƙaramin yaƙi, wallahi Hajiya ce da Mama Magajiya ake faɗa" Da sauri ta biyo bayanta tana mamaki tana sauri tana haɗa hanya har suka ƙaraso, tana zuwa ta ce

"Ruma mene ne halan, Magiya ya da girmanki za ake wannan aiki" Ruma ta saka Hajiya tana haki Hajiya Naja,atu ta miƙe tsaye ta ɗauki ɗankwalinta da ya faɗi tana ɗaurawa tana faɗin

"Wallahi kun yi kaɗan ku shigo gidana ku nemi raina min hankali, duk wanda kuka gani a gidan nan ni na so ya shigo ya zauna "Ta kai ƙarshen maganar tana yi wa Goggon kallon ɗaya saura kwata. Goggo da ta gane manufarta da jam,un da ta yi na faɗin duk wanda aka gani a gidan ta san tana nufin har da ita kenan, bata ce komai ba illa faɗin

"Magajiya mai ya kawo wannan hargitsin ne don Allah" Mama Magajiya ta share zufa, ta fara ƙirƙirar kukan ƙarya ta ce ..

",Yarinyar nan Naja saboda ta san ba ni na haifi Muhammad ba, amma na ɗauka ai ana kiran mijin iya baba, tunanina da ni da ke duk ɗaya muke amma ta wanke idanunta ta ci min mutunci ta uwa ta uba ta farfaɗa min maganganu har da kifeni da wani mari saboda kawai ta tsinci muna maganar da bata fahimci inda maganar ta dosa... Kafin ta kai aya Hajiya Naja'atu ta ce

"Wato ni saboda bani da galihu shi ne ba za ki tambayeni ba, saboda son kai kike tambayar ƴar uwarki abin da fake faruwa, don a nuna min ƙoƙon asali" Goggo wacce ta ga ƙwalla ta taru a cikin idanun Hajiya Naja,atu da alama ta daku ga wajen gefen bakinta da ya yi suntum gabaɗaya inda Ruma ta mare ta ya kumbura.

Goggo ta ce

"Wai mai ya sa Naja baki da fahimta ne? Ko ma wa na fara tambaya ai ba zai yiwu a ce na tambayi mutum biyu a lokaci guda ba, sannan in kika yi haƙuri kema zan zo kanki sannn ma ai Magajiyanita ce babba ita ya dace na fara tuntuɓa ni fa ƴa na ɗaukeki ke ce dai kika kasa sakin jiki da ni" Baki ta taɓe ta kawar da kai gefe tana aikawa Ruma harara, Ruma ma hararar ta aika mata.

Ruma ta ce

"Goggo kawai fa daga gani mun shigo da akwati shi ne ta tare mana hanya wai sai mun koma"

Hajiya Naja'atu ta ce

"Ke kin isa ki min sharri, ko uwar taki ma da ta ƙi faɗar gaskiya ai don bata da gaskiya ne za ta ce wai kuna maganar da ban san inda ta dosa ba, ni babu wanda nake tsoro kuma gaskiya a duk inda ta zo dole in faɗa" Goggo ta ce

"Naja ɓangarenki ne kawai kike da ikon cewa sai wanda kika ga dama zai shiga amma ba huruminki bane ki ce ƴan uwana ba za su zo gidan da nake ba kuma mallakin ɗana!"

Hajiya ta hayayyaƙo da faɗin

."Ai sun san abin da na ji suna faɗa, wai Ruma ce za ta yi idda ta auri mijina wallahi ashe wanda ya mutu yake cikin kabari ma zai yi fatalwa ya falko in har haka ta faru!" Goggo ta kalle su da rashin fahimta, tun da ta ga Naja,atun ko gizau bata yi wajen furta maganar ba, da alama dai an yi maganar.

Ruma kuwa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa don ita daɗi ma ta ji an furta maganar da take son a fasa ƙwan kowa ma ya sani don a yadda take ji yanzu ko Alhajin tana iya tunkara da maganar don ba za ta tsaya kallon ruwa kwaɗo ya mata ƙafa ba, ba za ta tsaya tana ni tana gani ya je ya auro wata ba bayan ita tana nan tana fama da dakon jiran gama idda ya aure ta.

Mama Magajiya kuwa kunya ce ta lulluɓeta tun da dai ba ta haka ta so furtawa ƴar uwar tata wannan maganar ba ta so ta sanar da ita amma hakan ma faɗuwa ta zo daidai da zama don haka zaman ya kamata a yi.

Goggo ta kalli akwatin Ruma da take gefe yashe a inda Hajiya ta jefar ɗazu ta ce

"Ban gane ba," Mama Magajiya ta ce

"To wai ita Najar nan wa ta fi ne da bakwa son a yi zancen mata kishiya, kowane namiji ai mijin mace huɗu ne" Goggo rasa bakin magana ma ta yi don ko ana ha maza ha mata ba za ta taɓa bari Muhammad ya auri Ruma ba, ita da take son ya samu mace kintsatstsiya mace managarciya idan har aka aura masa Ruma ai ba a rabo da bukar ba an haifi Habu tun da dai kanwar suk ja ce ita da Hajiya Naja ƙwaryar sama ce da ta ƙasa domin zani ce ta tarar da mu je mu!.

*NURIYYA*

Ta ji daɗi sosai daɗin da har sai da ta fashe da kuka, Kaka take buga bayanta a inda Ammar ya shiga share hawayen tausayin maraicin Nuriyya tabbas duk maraya abin tausayi ne musamman wanda bashi da galihu ko wanda zai tallafa masa.

Sai da Kaka ta lallashe ta sannan ta haƙura da kukan, Ammar ya ce

"Nury da gulma kike yanzu kayan makarantar kike wa kuka ko pant ɗin" Ta zumbura baki tana kallonsa ta ce

"Ledar da aka saka kayan a ciki"

Kaka ta ce

"Shikenan kuwa kin gama magana" Su duka suka ƙyalƙyale da dariya.

Nuriyya ta ɗaga hannuwanta duka biyu sama ta ce

"Allah ka ba Ya Ammar kuɗi, ka bashi gida ƙato da mota ƙatuwa" Kaka ta ce

"Amin Nury"

Nuriyya ta ce

"Ya Ammar kai baka amsa ba"

Ya ce

"Ni ai a zuciyata na amsa"

Nuriyya ta ce

"Ka san saboda mai na maka addu,a? Ko sallah na yi ina maka addu,a, malamin islamiyarmu ya ce muke yi wa iyayenmu addu,a Allah ya buɗe musu, ni kuma kai ne kake siya min abin da Babana ba ya siya min" Kaka ta ji tausayin yarinyar ya kamata matuƙa ta ce

"Nury ai tun da aka haife ki baban naki yake siya miki kaya, yanzu ma ai matsayin babanki yake kuma yana buƙatar addu,arki, shi ma akwai ranar da zai siya miki" Ta yi shiru bata yi magana ba akamar mai nazari, zuwa can ta ce

"Idan na saka kayan nan kyau zan yi, daman ina addu,a Allah ya ban kayan makaranta in daina saka yagagge ƴan makaranta suna min dariya, gashi Ya Ammar ya siya min"

Kaka ta ce

"Ki bari dai a ɗinka miki ko yadin za ki saka babu ɗinki" Ta faɗa cike da tsokana...

Na yi ciwon idon shi ya sa kuka ji ni shiru amma ynz Alhamdulillah

*** [8/18, 5:51 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH