BOOK 1
🅿2️⃣2️⃣
*ABDULSALAM*
Sun daɗe suna zuba soyayya a waya, Hasiya sai shagwaɓa take zabga masa, gabaɗaya ji yake duniya banu wata mace da take da babban gurbi a zuciyarsa sama da ita, zuciyarsa ta raja,a a kan ƙaunarta da kuɓa yarda ya zauna da ita matsayin matarsa!.
Sai da ya yi da gaske ta bar shi ya koma gidan, don cewa ta yi tun da ya fito sai ya ƙaraso ta ganshi shi kuma ganin sun jima suna waya lokaci ya ja ya ce yana jin kunyar Dada.
Sallamar da suka yi kafin ya ajiye wayar ya ce
",Ki tsara min kalamai masu daɗi, masu tafiya da zuciya wanda zan karanta idan zan yi bacci"
Hasiya ta ce
"An gama ranka shi daɗe!"
Abba ya ce
"To gimbiyata Hassy"
Yana murmushi ya tada motar tare da karya kwana bayan ya yi revarse ya kama hanyar komawa gida, a zuciyarsa yana fatan Ramla ta bar ɗakinsa don yana ji a ransa yanxu lokacin Hasiya ne da za su zuba soyayya musamman da ya gama gano cewar ba wai haɗa baki ta yi da Ramla ba soyayya take masa ta tsakani da Allah!.
Yana zuwa ya yi horn mai gadi ya wangale masa get, ya shigo da motar, ya.samu waje ya yi parking, ya kashe motar tare da ƙoƙarin buɗewa kafin ma ya buɗe direbansa da yake zaune kan bencin mai gadin ya taso da sauri cike da girmamawa ya buɗe masa ƙofar, wayarsa ya ɗakko ya fito daga motar, ya nufi hanyar shigewa cikin gida.
A ɓangaren Ramla jin an buɗe get ɗin ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, don sai lokacin ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi saboda gabaɗaya ta gagara nutsuwa da fitar tashi amma jin ya dawo ta ji ta samu salama.
Ƙofar ɗakin ya turo ya shigo, ganinta ya kawar da dukkan annurin da yake shimfiɗe a fuskarsa, don ya so yana xuwa ba zai same ta a ɗakin ba kawai ya buɗe data su ɗora da soyayyarsu shi da amaryarsa Hasiya. Rai ya haɗe yana wani kawar da kai gefe tamkar wanda ya ga kashi, ɗan kawar da idonta gefe ta yi a zuciyarta ta ce
'Ya na ga fuskarsa ta canja da ya kalle ni, ko dai ba ya ƙaunar ganina ne a ɗakin nashi?'
Abba kuwa kamar ma bata ɗakin haka ya yi, tana nan zaune ba ta ce uffan ba shi ma haka ne a nashi ɓangaren, har ya gama shirin kwanciya ya zo ya hau gadon ya janyo wayarsa wacce yake ganin ta fi Ramla muhimmanci a wajensa a halin yanzu.
Ta sauke ajiyar zuciya har sai da ya ji saukar sautin a dodon kunnensa, baki ya taɓe ya juya baya, ta yi gyaran murya ta yi ta ce
"Abban Humaira har ka dawo?"
Kamar ma ba zai bata amsa ba sai zuwa jimawa can a shelaƙe ya ce
"Eh" Ta ƙaraso kusa da shi ta kwanta tana miƙa hannunta mai cike da laushin fata ta ɗora a saman kafaɗarsa, ji ya yi tamkar ta ɗora masa gwarwashin wuta, bai daina danna wayarsa ba amma dai saƙon abokinsa ya shiga dubawa, ta sake matsawa ta lafe a jikinsa ya ɗan yi ƙaramin tsaki ya ce
"Wai mene ne Ramla?" Tambayar ta xo mata a bazata, kuma abin ya mata ciwo, saboda yanayin yadda ya mata furucin tamkar dai ba matarsa ta sunna ba sai ka ce wata karuwarsa, a ganinta ko karuwarsa ai ba zai yi wa wannan hantarar ba. Hannunra ta janye daga kafaɗarsa, ta yunƙura ta tashi, ta zura ƙafafunta ƙasa ta sauke daga kan gadon ta ce
"Na tafi ɗakina" A tunanina zai ɗan nuna damuwar cewar bata ji daɗin abin da ya msta ba, amma ga mamakinta sai ya ce
"Idan kin fita ki rufo min ƙofar" Ta ɗan ƙanƙance idanu, ba ta ce komai ba ta juya ta fita daga ɗakin tare da rufo masa ƙofar, da har wata zuciyar ta ce ta bar masa ƙofar a buɗe, amma dai ta daure ta rufe masa ta fito daga ɓangaren nasa ta nufi nata ɓangaren.
Tana tafiya tana saƙe-saƙe, har ta ƙarasa ɗakinta tana shiga ta rufe ƙofar, ta janyo ƙaramar lokar mudubi ta jefa zoben a ciki. Ta tsaya a gaban madubin hannuwanta a naɗe a ƙirjinta tana ƙarewa kanta kallo a madubin.
Kyakkyawa ce ita ajin farko duk da ba ta da farin fata, sai dai fatarta tana da kyau matuƙa, tana da doguwar fuska da yalwar gashi, uwa uba tana da dama da ƙasa, cikaken dirin da kowace mace za ta yi taƙama da shi, duk da ba za ta ce ta haɗa komai da komai ba, saboda ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Fuskarta da take ɗauke da manyan idanu, ƙaramin baki wanda yake da baki da ja tamkar ta shafa jambaki, tana da dogon hanci matsakaci.
Yanayin yadda ƙirjinta yake tamkar bata taɓa shayarwa ba, uwa uba bata da wata ƙiba mai muni sai da ba za a kira ta ramammiya ba, babu wanda zai ganta ya ce ta haifi yaranta, uku duk da Humaira ce babba Aslam da Aslamiyya ƴan biyu ne, saboda yanyin kyan jiki da take da shi.
Hancin ta ta kai jikinta tun kafin ta kai hancin ƙamshin kulakca, humra haɗe da kabbasan da take turara kayanta da shi, ban da kabbasan fesawa da sauran turarukanta, duk inda ta shiga kafin ka ganta ƙamshin ta ya maka sallama, duk da bata fiya saka turare mai karfi in za ta fita ba saboda gujewa faɗawa halakar wasu mazan su ji ƙamshinta.
A fili ta furta
"Mai ya rage min a halittar da mace za ta birge namiji? Mai ya sa bana birge shi, mai ya sa duk iya ƙoƙarina na ganin na faranta ran mijina na tsaftace masa ganinsa daga matan da suke haramun a wajensa amma shi ba ya gani su ɗin su shaiɗan yake masa jagoranci ya kalle su, su suke birge shi, mai ya sa ba ya sauke nauyin haƙƙin auratayya a tsakanina da shi matsayinmu na ma,aurata duk da na san ya warke daga wannan tsohuwar cutar da ta addabe shi a baya?" Idanunta ta lumshe ta kai tsawon minti huɗu a haka tana tuna wane ne mijinta, tana tuna ya ta ɗauke shi a rayuwarta, tana tuna girma da muhimmancin da ta ɗauki aure da irin burikan da ta ci tun tana bidurwa wajen ganin ta farantawa duk wanda ya same ta matsayin matar sunna, sai dai babu zato da tsammani Abdulsalam duk ya yi fatali fa wannan manyan burikan nata, ya sanya duniyarta yin wani irin zafin da sai wanda aka yi wa abin da aka mata ne zai ji.
A zuciyarta ta ce
'A rayuwata na tsani wulakanci, na ƙi jinin wulakanci, in yi ko a mini, amma Abdulsalam ya mayar da ni ba kowan kowa ba a wajensa, mai ya sa wasu mazan suke da son kansu?' Idanunta ta buɗe tana jin suna mata raɗaɗi kamar yaji, ta fara takawa zuwa gadonta, ranta fal da tunanuka iri -iri ta hau gadon tana faɗa a fili
"Da a ce ina da kishiya da zan iya tunanin ko shiga tsakaninmu aka yi, duk da ina da kyautata zato a kan mutane, sannan duk da na san halin mijina"
A ɓangaren Abba kuwa, Mama Ramla tana fita sai ya ji tamkar an yakice masa wata ƙaya mai tsini, don ji ya yi wata iska tana shigarsa ta ko ina, ya barbaje a tsakiyar gadon ya yi ɗai-ɗai yana shiga account ɗin Hasiya, ya samu ta jero masa wasu kalamai na soyayya da muradi masu daɗin gaske sai dai tsaftattattu ne ba wai kalmomin da suka saɓa shari,a ba.
Ya gama karantawa ya tura mata emojis na soyayya kafin ya ɗora da faɗin
"Kin kasheni da kalmominki Hassy tah, tabbas a cikin mata akwai mata, akwai kuma muna mata, ke ban ware ba na yarda har da mata -maza" Ta tura emoji na rufe fuska alamar kunya ya tura mata emoji na bugawar zuciya ta ce
"Ni a wane sahu nake?"
Ya gyara kwanciya ya rubuta
"A sahun farko na mata, ke ai ta daban ce a cikin mata, akwai matan da basu ma san yadda za su yi lafazi mai daɗi ga miji ba, ke wata ko magana bata iya ba, bare wata soyayya amma ke kin haɗa komai shi ya sa na matsu na auro ki ko na yi bankwana da sahun gwauraye!"
A zuciyarta ta ce
',An zo wurin' Saboda daman tana son ta samu damar da za ta ji sirrinsa tsakaninsa da Ramla don ta san irin shigowar da za ta yi yanxu kuma cikin hikima ta samu abin da take so duk da ta lura yana da wayo amma kuma tun da shi namiji kamar ƙaramin yaro yake dole mace za ta iya yin ƴan dabaru na mata ta samu abin da take so.
Duk da ta lura da a ce Ramla tana da wani matsayi a wajensa da a wannan lokacin da suke charting yana tare da Ramla da ba za su yi ba, kenan Ramlar bosho ce a wajensa wato akwai ya babu kakar wajen uba.
Maimakon a matsayinta na ƴa mace ta yi iya yinta wajen daƙile duk wani sirrinsa da matarsa da zai faɗa mata, saboda faɗin bahaushe yai taka gobe ta ɗan uwanka, kuma abin da aka yi wa wani kaima watarana kana iya tsintar kanka a ciki, duk da hausawa suna cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, amma a wanann zamanin ciwon ƴa macen sai ya zamana yawanci ƴar uwarta mace ce take saka mata.
Ta ce
"Amma ai da baka da aure shi ne za ka yi wannan furucin" A sannn ne ya gane ya kusa sakin layo saboda ya fahimci son Hasiya ya sanya ya yi katoɓara shi da yana so ta gama ganewa ta gama yarda cewar shi yana da sanin darajar iyalinsa, ba ya son ta samu wata ɓarakar da za ta fahimci zaman da yake da matarsa bare har ta bijirewa aurensa, hakan ya sa ya ce
"Ba haka nake nufi ba, kin san kowace mace da irin baiwarta ba wai na ce matata ta gida bata da rawar da take takawa ba" Ranta ta ji ya ɓavi da ya yabi Ramla bata san cewar duk bula bace, kamar ya san tunanin da take ya ce
"Ai matsayinki ya ɗara na kowa" Kamar ya zuba mata ƙanƙara a zuciyarta haka ta ji, hakan ua sa ta tura masa wata sticker ta soyayya, yana ganin haka ya kira ta bidiyo call ta ɗauka suka ci gaba da hirarsu, sai da suka raba dare suna hira kafin suka yi sallama ya ajiye wayar bacci ya yi awon gaba da shi.
Hasiya kuma tana ganin tun kafin ta zo gidan ta fara janye hankalin Abba daga kan matarsa tun da gashi ta ita yake yi ba ta Ramla ba, kafin ta shiga gidan a yi wacce za a yi.
Washe gari da yamma Ramla tana zaune a falonta, ta kamo sunan Hasiya don ta faɗa mata maganar zoben nan da Aslamiyya ta zo da shi, amma ta ji call waiting. Hakan ya sa ta ajiye wayar bayan kamar minti goma ta sake kira amma har lokacin call waiting ota tana so ne zoben ya bar hannunta saboda ko kaɗan idan ta kalli zoben tana jin wasi-wasi kamar daj zuciyarta bata gama yarda da zoben ba, sai dai son da take yi wa Abba ba zai bari ta ƙaryata maganarsa ba.
Jim kaɗan ta ɗauki wayar ta shiga kiran Abba, kamar haɗin baki shi ma ta ji call waiting ta ɗan yi jim sai dai ko kaɗan zuciyarta bata kawo mata cewar wai da juna suke waya ba kawai ta ɗauki hakan a akasi ne!.
Bayan kamar minti takwas kiran Hasiya ya shigo, ta ɗauka suka gaisa, Hasiya tana jin wani haushi da kishin Ramla ya cika mata ciko don maganat da suke yi ma don dole ne, amma ji take kamar ta haɗiyo zuciya ta mutu, a matsayinta na wacce za ta aurewa Ramla miji amma tana jin kishi, ina ga ita Ramla da za a aurewa mijin fa?.
Bayan sun gaisa Ramla ta ce
"Na kira ai na ji waiting"
,Hasiya ta ce
"Eh muna waya da Karima ne" Ramla ta ce
."Ayya" Hasiya ta cire wayar daga kunenta ta dokawa wayar harara tamkar Ramla tana ganinta a zuciyarta ta ce
',Da mijinki nake waya, ko ma in ce mijinmu, don saura ƙiris'
Ramla ta ji yadda Hasiya take bata amsa ba yadda suka saba magana ba, hakan ya sa ta takaita maganar da faɗin
"Daman Aslamiyya ta xo da wani zobe, shi ne ta ce naki ne ta taho da shi"
Hasiya ta ce
"Ayya eh nawa ne, nima Karima ta zo min da shi daga Niger wani zuwa da ta yi to da yake ma a ajiye yake ban fiya sanyawa ba"
Ramla ta ce
",To shikenan ba damuwa zan ba direba ya kawo miki"
Hasiya ta ce
",Ok na gode" Tana faɗar hakan ta yanke kiran, Ramla ta ciro wayar daga kunneta tana bin wayar da kallo.
Hasiya kuwa tana kashe wayar ta doka tsaki ta ce
"Ba dole ki maido min zobena ba, tun da mijinki ne ya siya min ya bami ba ke koka siya min ba"
Ramla tana tashi ta shiga ɗaki ta ɗakko zoben ta ƙulle a leda ta ba direba ta ce ya je ya kai wa Hasiya, ya karɓa cike da girmamawa ya tafi ya kai.
Yau ya rage saura sati ɗaya bikin Hasiya da Abba, ana ta shirye-shirye don tuni ya je ya gaisa da magabatan Hasiya kuma an bashi ita. Ɓangaren ta daman babu wani abu da yake buƙata kaya kawai za a saka, kuma sun masa lissafi ya bayar da kuɗin komai da komai, ga kayan lefe da ya rakata suka siyo, komai tamkar budurwa haka ya mata duk sun tatiƙi rabonsu ita da Dada da Karima.
Duk wani abu da ake yi a bikin budurwa shi za a yi a bikin Hasiya da Abba, daga kan kamu dinner da sauransu, sun yi ɗinkunan fitar biki, kamar ba gobe haka shi ma Abban ya yi kaya har wanda zai saka a ɗaurin aure. Amma duk bidirin nan da ake yi bai faɗawa Mama Ramla ba, bare ya bata ko da naira biyar don kyautatawa zai ƙara aure kamar yadda wasu mazan suke ba matansu idan za su ƙara aure.
A yadda ya tsara sai ranar da aka ɗaura auren zai sanar da ita kawai ya fi so komai ya yi shi a ɓoye, amma abokinsa Alhaji Abdullahi ya ce gwara dai ya bari ko ana saura kwana uku ne ya faɗa mata.
Yau saura kwana biyar ɗaurin aure, yau suka yi za su je hoto, sun je wurin hoton sun saka kaya kala uku suka canja, suna yin hoton, sun riƙe hannun juna tana murmushi yana mata wani irin kallo kaf hotunan da suka ɗauka babu wanda ya yi matuƙar kyau sama da shi.
Ko da ya ajiye ta, gida ya wuce lokacin ana kiran magriba, kayansa bai fito da su daga mota ba, yana shiga ya yi alwala ya tafi masallaci ya bar wayarsa tana caji a falonsa.
Ramla da ta shigo falon nasa, ta ji tashin ƙaran wayar alamar ana kira, ko kallon wayar ba ta yi ba har ta wuce sai kuma kamar wanda aka ce ta je wajen ta nufi wajen bisa son ganin wane ne mai kiran duk da ba halayyarta xe binciken wayar miji ba...
*** [8/19, 8:14 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH