BOOK 1
🅿2️⃣3️⃣
*HAJIYA NAJA,ATU*
Ta kalli Ruma kallo itin na gargaɗi ta ɗaga yatsa ta kaɗa shi a saitin fuskar Ruma ta ce
"Hawainiyarki ta kiyayi ramata, bakin rijiya ba wajen makaho ba ne... Mama Magajiya ta katse mata hanzari da faɗin
"Ai kuwa sai dai makahon ya tunjima cikin rijiyar don wallahi sai ya yi wasan a bakin rijiyar" Hajiya Naja,atu ta ce
"Wallahi sai dai kuwa ya faɗa ɗin, wannan ai kalen dangi ne da kuma nemawa kai jafa,i don na san duk wacce ta yi gigin auren mijina jafa,i ta jawa kanta, don ma sai na san ni bani da kishiya a duniya"
Gabaɗaya sai wajen ya kacame da cece kuce tsakaninsu, ana ta hayya hayya Goggo tana rabiyar cacar bamin da ake amma Mama Magajiya ta kasa kama girmanta ta yi shiru don ita tana ganin Hajiya bata da kamar da za ta dakatar da cikar burinsu.
Dakyar Goggo ta janye Ruma da Mama Magajiya suka yi ɓangarenta, Amira tana riƙe da akwatin.
Hajiya Naja,atu ta gaji da hayagagar masifa ta yi hanyar ɓangarenta fuuuu tana cin alwashin cewar Ruma bata isa ta kwana a wannan gidan ba matuƙar dai numfashi yana yawo a gangar jikinta.
Goggo suna shiga falo bayan Amira ta ajiye akwatin ta fita Goggo ta kalli Mama Magajiya da ta zauna a kan kujeta tana cire mayafi ta ajiye a kan kujera, su Umar kuwa sun fara wasa abinsu. Ruma ta zauna ɗare-ɗare a kujera ta harɗe ƙafafu ita ala dole ta zo gidan uwa kuma sirika sannan gidan mijinta tun da a yadda ta haɗo kayan bata da niyyar komawa ma ta zo kenan har ta gama idda ta rangaɗa sabon auren da ma gidan!.
Goggo cike da ɓacin rai ta ce
"Yanzu Magajiya ban da dai zubar da girma ina ke ina faɗa da wannan yarinyar Naja, matar da ko kaɗan babu wanda take ragawa bata da kunya kwata-kwata yanzu da ta ɗaga hannu ta mareki mene ne amfanin hakan, ko ba komai fa uwa kike a wajen Muhammad kin ga kenan sirika kike a wajen... Mama Magajiya tana taɓe baki ta ce ...
"A,a wallahi Allah kiyasheni aikin da na sani, ni ina ni ina zama sirikar yarinyar da ta zabga min mari, ai wallahi haihata-haihata" Rasa ma bakin magana Goggo ta yi saboda abin ta fara wuce gona da iri.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"Gaskiya ya kamata ki gyara, ki kama girmanki... Mama Magajiya ta dakatar da Goggo daga maganar da take ta hanyar haɗe rai ta ce
.."Ni fa Goggo ban gane miki ba, yanxu ni da yarinyar nan ta mara ni za kike ganin laifina? Idan har kin ɗaukeni ƴar uwa wallahi ni a tunanina da kika ji batun marin nan waya za ki dokawa Muhammad ki sanar da shi cewa matarsa ta kauɗe ƙanwarki da mari, ya yi maza ya dawo gida, yana zuwa gida ki bashi takarda da biro ki ce ya rubuta mata saki, amma shi ne baki yi duk wannan abu uwan ba har kina da bakin ganin laifina, wato ga Magajiya kuka mai daɗin hawa"
Ruma ta ce
"Ai wallahi ba don tana vanin ta fini jiki ba da sai na mata shegen dukan da sai ta kwanta a asibiti tun da ta mari uwata"
Mama Magajiya ta karkace murya ta sanyaya tare da karkata kai ta ce
"Allah sarki Ruma ai hakan ma kin kwatan ta, yanzu va gashi nan tana yawo da kumburarran baki ba"
Goggo ta ce
"Ni wallahi rasa mai ma zance na yi, Allah ya kyauta, amma dai shi saki ko ubangiji ba ya son shi, kawai ya halatta yinsa ne saboda kawo maslaha idan har yinsa shi ne maslaha" Banza Mama Magajiya ta mata don ita ba haka ta so ba ƙanin miji ya fi miji kyau, ta so a ce Goggo ta saka a saki Hajiya Naja,atu ta yadda ƴarta Ruma za ta sakata ta wala ba tare da wata ƴa mace ta kawo mata wargi ba, amma duk da hakan a juri zuwa rafi ta san watarana tulun zai fashe!.
Tana ta yj wa Ruma faɗan cewar ai Hajiya Naja yaya ce a wajenta tun da matar yayanta ce. Mama zuwa can ta yi yaƙi da ɓacin ranta ta washe baki ta ce
"Mun yi kuskure dukanmu" Ta faɗa tana son shigo da maganar da ta kawo ta.
Goggo ta ce
"Allah kiyaye gaba"
Mama ta ce
"Goggo daman batun mutuwar auren ƴarki ne, kin san muna zaune a gida daga ni sai ita sai yara, shi ne ta ce ita wajen Goggonta za ta koma da zama ni sai na zauna da yaran, wai take kama miki ƴan aikace aikace abinka da Ruma kin santa akwai son aiki akwai taimakawa babba" Goggo ta yi shiru tana jin batun har Mamar ta gama jawabinta, tana ta tunanin yarinyar da ta baro gidan miji ta bar aikin ladan gidan miji ita ce za ta zo ta zauna ta mata aiki bayan tana da masu mata komai ta ce
"Allah sarki Ruma ai da kin yi zamanki a gida ma, ni akwai masu tayani aiki bana so ki wahalar da kanki" Ruma da Mama suka kalli juna, ita Goggo tun da ta ji batun idda da auren ɗanta ta san wata maƙarƙashiyar ce bare yanzu yadda suka yi faɗa da Hajiya Naja,atu to ko da ta zauna za a ringa ɗauki ba daɗi ne!.
Mama ta yi saurin faɗin
"Ai ba wai sai da tayin aikin ba shi mutum ai daɗin zama gare shi" ,Goggo bata so ta nuna wani abu da zai danganci ta ƙi zaman Ruma duk da ta san hakan zai iya zama wani abu da ban amma dai naka naka ne duk da ƴan magana sun ce daɗin zama sai bare!. kuma ita ba za ta ƙi ƴar zumunta ba.
Ta kalli Ruma ta ce
"To ba komai Allah zaunar da mu lafiya, tana ganin lokacin da Mama da Ruma suka kalli juna suka murmusa alamar nasara, daman ta san da wata a ƙasa amma dai ita tana ɓoye ainihin abin da ta gani don bata da saurin yankewa mutum hukunci.
Nan Mama ta wuni sai da yamma suka kwasa ita da yaran bayan Goggo ta haɗa mata kayan abincin da ta ce bata da shi, direba ya kaisu ita da su Umar ɗin gida, lokacin da za su tafi da Ruma ta rako su wajen mota suka keɓe dama ita Goggo daga ƙofar part ɗinta ta tsaya.
Ruma ta ce
"Umar da Usman ku zauna da Mama zan zo in tafi da ku, wannan gidan za mu dawo da zama nan ba da daɗewa ba, har Mamar"Yara suna ta murna bayan sun shiga mota Mama ta ce
"To Ruma gashi nan dai kin dawo gidan nan da zama, kike cin gayu idan kika san zai zo ɓangaren Goggo ki ringa magana cikin jan hankali yadda da kansa zai san kin dace da shi ya yarda zai aure ki!" Ruma ta murmusa ta ce
"Ai kar ki ji komai Mama ai wallahi idan na samu kan mutumin nan, Maja take ko Naja wallahi ta yi kika da kanta don sai na mayar da ita tamkar an shuka dusa a zuciyarsa" Hannu suka miƙa suka tafa suna ƙyaƙalewa da dariya. Da haka suka yi sallama direba ya ja motar bayan sun shiga mai gadi ya wangale musu get suka fice!.
Hajiya Naja,atu tana daga saitin window a sama tana kallon duk abin da yake faruwa, tana ganin lokacin da suke ta tattunawa suna dariyar har tafa hannuwan da suka yi, da kuma fitarsu a mota hakan ya sa ta ƙara tabbatarwa kenan dai zaman Ruma ya tabbata a gidan, wannan dalilin ya sa ta sanya a ranta cewar sai ta yi wata maƙarƙashiyar wajen daƙile duk wani zaman ta a gidan duk da ta san da wuya wai gurguwa da auren nesa a ce ma wai zai yiwu mijinta da yake sonta ida tilo a zuciyarsa ya mata alkawarin zama da ita kaɗai har abada, a ce wata ƙazama bazawara zai aure ta amma duk da ta san abin ba mai yiwuwa bane sai ta nunaw Mama da Ruma da kuɓa ita wacce ta ɗaure musu tsantsa wato Goggo ta nuna musu iyakarsu ta nuna musu tana da matsayi a wajen mai gidan.
Kadan aka samu a hada da hƙr
*** [8/22, 6:06 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH