BOOK 1
🅿2️⃣4️⃣
*RUMA*
Tana sakin wani makirin murmushi ta bi get ɗin da mai gadin ta rufe, ita kaɗai ta san irin daɗin da take ciki don ta hango nasararta ta auren mai gidan, idanunta ta zubawa ɓangaran Alhaji Muhammad idanu ta jima tana kallon saman tana hango irin rayuwar auren da za su yi ita da shi, a katafaren ginin nashi ta saki wani murmushin mai ƙayatarwa tana wani ɗan jijjiga kai irin na samun nasara. Duk abin da take Hajiya Naja,atu tana kallonta cike da tsantsar tsana don idan ma ta kalli Ruma yana jin wani takaici idan ta tuna wai tana shirin jera kafaɗa da ita duk da ta san hakan ba mai yiwuwa bane amma dai ta san rainin wayon ya yi yawa, Ruma da mahaifiyarta sun ga makwancinta tun da har suna tunani irin wannn a kanta.
Ruma tun da ta ɗauke idanunta daga kallon ɓangaren Alhaji Muhammad ta fara wata irin tafiya, tana kaɗa mazaunai haɗe da girgiza ƙirji, a zuciyarta ta ce
'Gwara na fara gwada itin tafiyar da zan ke yi a cikin gidan nan domin yin wuff da zuciyar Yaya Muhammad, domin cikar muradina na aurensa, tun da na san kowane namiji mai jini a jika, mai cikakkiyar lafiya tabbas akwai abin da zai birgeshi a jikin ɗiya mace, yana da kyau a gareni in san yadda zan aiwatar da takuna a cikin gidan nan, da kuma yin amfani da matakan tsaro wato abubuwan da za su ja hankalinsa su ne matakan tsarona a wannan gidan!' Ta faɗa cigaba da tafiya, sai dai tafiyar a hankali take yi cikin yanga da kissa.
Ran Hajiya Naja,atu in ya yi dubu ya ɓaci, tana ganin yanayin tafiyar da Ruma take a take ta ji wani ƙululun baƙinciki ya tokare mata a ƙirji!. Abu ɗaya ne ya zo mada a zuciyarta shi ne wannan tafiyar da Ruma take yi saboda mijinta take yi, duk da ta san lokacin ba ya gidan kuma a nata tunanin ko da zai ga Ruma ba zai kawo komai ba wato ba zai ji wani shauƙi dangane da Rumar ba, amma haushin da take ji guda ɗaya ne shi ne, wai ita za a yi wa bariki alalar gero saboda an rainata ita dangin miji sakainar kashi za su yi wa rainin hankali. A fusace ta fara sakkowa daga matakalar benen, tamkar an jefo ta haka ta sakko ƙasan falon nata, ta samu Mero tana goge kujeru, wani kallo ta yi wa Meron ta ɗauke kai, don sai ta ji duk wata ƴa mace ma haushi take bata, Mero kuwa da sauri ta ɗauke kanta a ranta tana fatan Allah kawo ranar da Alhaji zai rangaɗowa uwar ɗakin nata kishiya wacce za ta shigar da ita hankalinta, ko ta dawo hayyacinta.
Fuuuu ta fito ta nufi hanyar da za su haɗu da Ruma, Ruma da take tafiya ta hango Hajiya ta taho ran nan a ɓace kamar an sanar da ita mutuwa, bata canja tafiyar da take ba haka nan bata dakata da abin da take yi ba, wannan ya ƙara fusata Hajiya. Tana zuwa gaban Ruma ta ja ta tsaya, kasancewar ta shiga gaban Ruma sai Ruma ta dakata da tafiya ta zugaw Hajiya idanun ganin tana jijjigar jiki kamar mai shirin dambe.
Ruma ta ce
"Hajjaju ya kika tare min hanya, ko da magana ne?" Ta faɗa tana kallon Hajiyar don yanzu jinta take kansu ɗaya da ita daidai take da zamaninta.
Hajiya a maimakon ta ba Ruma amsar tambayarta sai ta jefo mata tata tambayar ta ce
"Mai ya hana ki tafiya inda kika fito?" Ruma ta mata kallon lallai kina da sauran aiki ta ce
"Ra,ayi kukan jaki"
Hajiya ta ce
" A shawara muhimmiya da kin bi tsohuwarki kun koma gida, idan kin yi idda wataƙila ki samu miji daidai ke wato ɗan Allah baku mu samu mai zuwa maula gidan masu kuɗi, amma zamanki a gidan nan ɓatawa kanki lokaci za ki yi"
Ruma ta yi shewa ta ce
"To in dai kin yarda da kalaman da kike faɗa, mene ne naki na damuwa da zamana ko tafiyata? Ɗazu muka gama ɗaukan ƴan kallo shin wannan bai isheki izina ba? Ko halin dai kike so mu sake rabawa ne?" Cike da mamaki Hajiya take bin Ruma da kallo ganin tana jin wani falli tana ganin kanta itama wata ce, ƙwafa ta yi tana bin ilahirin jikin Ruma da kallo ta ce
"Lallai wuyanki ya isa yanka, to inaso ki sani bakin rijiya ba wajen makaho bane kamar yadda na faɗa miki da safe, amma tun da kina ganin za ki gagara da ni ga wajen nan, inaso ki sani ko tsirara za kike yawo a gidan nan mijina ba za ji ishe ki kallo ba" Ruma ta kalli Hajiya ta tuntsure da dariya tana tuno yadda aka ce Alhajin ko haƙƙinsa Hajiyar sai ta ga dama take bashi ta ce
"Ban da dai tsirarar na tabbata indai yana da cikakkiyar lafiya, ko da kayana a jikina zai gane akwai bambanci tsakanin ruwa da ruwan lemo" Tana faɗar hakan ta juya ta fara tafiya ɓangaren Goggo sai da ta ɗan yi tafiya kamar taku goma ta ɗan sunkuya ta kaɗa mazaunai ta ɗan ɗaga murya ta ce
"Allah bani mijin wata in yi wuf da shi, in sa ta zama hoto a wajensa" Tana faɗar hakan ta yi saurin shigewa ɓangaren Goggo.
Hajiya ta yi mugun jin haushin abin da Ruma ta mata, ta yi kamar minti biyu a wajen ta doka uban tsaki tana ƙudurta a ranta cewar dole ne ma Ruma ta san inda dare ya mata.
Hanyar ɓangarenta ta nufa tana ta sauri, ta matsu mai gidan ya dawo ta faɗa masa tana son Ruma ta koma gidan tsohuwarta, tun da ta san faɗar maganarta gare shi kamar yankan wuƙa yake, duk ta ji ta damu ba ma komai ne damuwar ba sama da kar dai maganar ta zama gaskiya ya zamana gadon da take hari za ta samu na mai gidan ya zama mallakinsu da Ruma duk da ta san babu ma batun wai zai aure ta.
Tana komawa ɓangarenta ta ɗauki wayarta, a kan gado ta zauna daga bakin gadon, ta kamo sunan Mahaifiyarta, tana ɗagawa ko gaisawa basu yi ba ta ce
"Mom kin san wani sabon salo kiran sallah da usur" Ta faɗa tana kwashe komai ta faɗa mata, Mom ta narko ashar mai maiƙo ta luƙa ta ce
"Wai ke har kina da lokacin sauraron ƙauyawan dangib nan nasa? To ni mo uwar da ta haife shi sa da dama ai canja ta za a yi ta yi ƙauyanci da yawa a kirata da surukarki, ita yanzu shegiyar tana ina?"
Hajiya Naja,atu ta ce
"Tana ɓangaren Goggon, Mom har fa wata tafiya take tana karkaɗa mazaunai, wai ni bazawara za ta zo gidana yin idda ta gama ta auri... Bata ƙarasa faɗa ba Mom ta ce
"Dalla rufewa mutane baki, kar na ƙara jin kina wannan maganar ai sai ki jawa kanki raini, to ni ai gani nake a rayuwa kon ci baya idan har aka miki kishiya, ko da mai aji ce kuwa bare kuma wannan da bata wuce mai miki hidima ba, ki ma daina wanann mafarkin"
Hajiya ta ce
"Nima kawai dai abin da suka yi ɗin ne yake ɓata mun rai am a ai na san babu ma yiwuwa a wannan lamarin"
Mom ta ce
"To ki ma daina wannan tunanin, idan ya dawo sai ki sa ya bata kuɗin napep ta san inda dare ya mata"
Hajiya Naja,atu ta ce
"Daman ai wuyarta ya dawon" Sun dan tattauna daga bisani suka yi sallama.
Ruma tana komawa ɓangaren Goggo ta same ta tana karatub qur,ani, ɗakin da ta kai kayanta ta wuce wanda yake daga can gefen yana kallon ɗakin Goggon, tana shuga ta rufo ta hau gado ta yi wata irin shewa, ta ɗakko wayarta ta kamo sunan Haulatu ta kira.
Haulatu suna zaune da mai gidanta suna hira, mai cike da nuna soyayya da ƙaunar juna, duk da wani lokacin mijin nata butsu ne, amma kuma ta gwammace ta zauna da shi a kan ta fito daga gidanta, ita idan ma ta tuna maganar Mama abin yana ɗaure mata kai, tun da ta ji labarin mutuwar auren Ruma ranta in ya yi dubu ya ɓaci, kiran da ya shigo wayarta ne ya saka ta ajiye gyaran zogalen da take yi ta ɗakko wayar tana dubawa ta ga sunan Ruma ta kara a kunne tana faɗin
"Assalamu alaikum ƴar uwa rabin jiki" ,Ruma ta amsa daga ɗayan ɓangaren don sai ta ji yau bata ma jin haushin ƴar uwar tata, tun da yanzu tana ganin Allah ne ya mata gyaɗar dogo da ta rabu da aurenta gashi yanzu za ta yi auren cikar buri!.
Ruma ta ce
"Albashirinki"
Haulatu ta ce
"Goro fari tasss kuma ƙato"
Ruma ta ce
"Yau na koma gidan Goggo da zama" Haulatu ji ta yi ranta ya ɓaci da wannan maganar, tun da ta san daio zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, wato ta koma gidan ne da wata manufa.
A taƙaice ta ce
"Ma sha Allah"
Ran Ruma ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, tana jin inama tana da wata ƴar uwar ba wai Haulati ce ƴar uwarta kaɗai ba, ƴar uwar da za suke kashewa suna binnewa, ƴar uwar da za ta goyi bayanta a kowane lokaci. ta ce
"Wato ma sha Allah kaɗai xa ki ce, anya Haulatu ni fa sai in ke ganin kamar baƙinciki kike min, a kan me zan kira ki da babban albishir amma ki wofantar da maganar, tunanina za ki nuna farinciki sosai fiye da zato amma sai ki nuna halin ko in kula"
Haulatu ta sauke ajiyar zuciya ta kalli inda mijinta yake, ita tana da sirri bata ƙaunar abin da mijinta zai san sirrin gidansu, sirrinsu naau ne na su kaɗai, ita bata uarda da tattauna matsalar gjdansu ba.
Ta ce
"Haba Ruma mene ne a cikin ido ban da ruwa, na san dai iya gani iya ƙylaewa kum... .
Wani uban tsaki da Ruma ta doka ne ya sanya Haulatun yin shiru Ruma ta ce
"Haulatu ki yi rayuwarki in yi tawa, duk ranar da Yaya Muhammad ya min alkawarin aure ko Allah sanya alheri karki min" Tana faɗar hakan ta kashe wayar,, Haulatu ta yi ƙoƙarin bin kiran amma yaƙi tafiya saboda babu kuɗi a cikin wayar, ta haƙura tana saurin ƙaƙalo murmushi gudun kar ya harbo jirginta, bata san shi idan da sabo har ya saba da matsalar mahaifiyarta, duk da tana ɓoyewa amma akwai lkcn da yake fahimta.
Ruma tana nan a ɗakin sai da ta ji Goggo tana waya da Alhajin sannan ta tashi ta faɗa banɗakin cikin ɗaki ta yi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga da ta bi jikinta ta banka uban turare, ta fito ta zauna a falo bakin nan sai sheƙin lip stick yake, lokacin Goggo ta shiga ɗakinta.
Alhaji Muhammad ko da ya dawo ɓangarensa ya nufa, har ya yi wanka, ya shirya, ya yi alwalar magriba. Lokacin da ya dawo daga masallacin magriba ɓangaren Goggo ya nufa don ya sanar da ita dawowarsa.
Yana shigowa ya ga girmawar wata ta shiga ɗaki ta rufo, bai gama gane wace ce ba, ya zauna a falon yana mayar da idanunsa kan TV.
Ruma kuwa da take zaune tana kallo baya ta yi sallah, kamar daga sama ta ga an buɗe ƙofa, bayan an ƙwanƙwasa, muryarsa da ta ji ya yi sallama hakan ya sa a 360 ta nufi ɗakin nata, tana zuwa ta sake shafa powder da turare ta fito. Yana zaune zaman jiran fitowar Goggo don ya san wataƙila tana zaune a ɗaki tana lazimu, sai ya ga Ruma ta taho, tun da ta fito daga ɗakin take rangwaɗa tana wata tafiya, shi kallo ɗaya ma ya mata ya ɗauke kai ya mayar kan TV.
Tana zuwa ta siranta muryarta haɗe da tsuke baki, ta ce
"Yaya ina wuni barka da dare" Ya ce
"Ruma lafiya ƙalau ke ce a gidan yau" Kai ta gyaɗa, ta faki idanunsa ta ga hankalinsa ma ba a kanta yake ba, ta ɗan sake maƙe murya ta ce
"Yaya" Jin ta sake kiransa sai ya zaci tana buƙatar hankalinsa ne hakan ya sa ya juyo, yana juyowa ta saki wani uban farfari da idanunta, shi abin har ya so bashi dariya, yana shirin magana Goggo ta fito, Goggo tana fitowa ta yi arba da Ruma sanye da wata riga da baya daxe mace ta saka ba sai a gaban muharramanta.
Ko da ta zauna Muhammad ya gaishe ta bayan ya zamo daga kan kujerar, ta amsa ya koma ya zauna. Goggo ta kalli Ruma ta ce
"Rumasa,u bamu waje za mu yi magana da yayan naki kin ji" Wani daɗi ya cika ta, tunaninta ko Goggo za ta gabatar masa da gudurinsu, ita kuma Goggo ta yi hakan ne saboda ganin irin rigar jikin Ruma har ta fara tunanin ita Rumar ko kunya ma bata ji, tana ganin ko ita ai ta ji kunyar ta ganta a haka bare kuma Yayanta Muhammad.
Tana shiga ɗakin cike da Murna ta yi tsalle ta haura kan gado tana ganin ai kawai tana gama idda da mijinta a hannu.
Bayan ta shiga ɗaki take sanar da shi dawowarta gidan da zama, saj dai shi ba zai so zamanta a gidan ba lura da ya yi da rawer da kanta yake kuma daman ya san tana da rawar kai.
Sun ɗan jima suna hira, har aka kira sallar isha,i ya fito don zuwa masallaci. Bayan ya dawo ya je ya ci abincin da Mero ta jera masa a dining, ɗanwake da miyar ƙwai, ya ci sosai saboda ya yi masa daɗi ga laushi da santsi. Sai dai motsi kaɗan sai Falmj ta faɗo masa a rai. Yana gamawa ya shiga ɗaki, ruwa ya sake watsawa ya hau kan gado bayan ya yi shirin kwanciya, tunanin Falmi ne damfare a zuciyarsa, hoton fuskarta yana masa gizo a idanun zuciyarsa, lokacin tana murmushi. Juyi ya yi yana lumshe idanunsa, zuwa yanzu yana son ya gano wani abu a ƙoƙon ransa duk da ya kasa gane mene ne, amma abin yana masa shige da kalmar nan da ake kira SO.
Yana wannan tunanin bacci mai daɗi ya yi awon gaba da shi. A cikin bacci ya ga Falmi ta turo ƙofar ta shigo bakinta da sallama cikin muryarta mai daɗin sauraro. Ya amsa mata ta noƙe a bakin ƙofar tana faɗar sai ya tashi zaune zai amsa sallamar bata so ya amsa a kwance, kansa ya samu da bin umarninta, don yanzu gani yake kamar komai ta ce zai iya zame mata raƙumi da akala. Tun da zuciyarsa ta fara addabarsa da azababban tunaninta, shikenan sai yake jin bai damu da Hajiya Naja,atu sosai kamar yadda ya damu da ita da ba, sannan da ya je ɓangarenta ta masa wannann wulakancin da ta saba gwara ya zauna yake ta zancen zuci da Falmi.
A hankali ta tako cikij tafiyarta mai birgeshi, sanye take da kayan bacci masu taushi blue black rigar mai ƙaramin hannu, tana zuwa bakin gadon ta zauna ta kai hannunta saman fuskarsa ta shafo fuskar tana faɗin
"Kullum ƙara min kyau kake, zan so na rayu da kai a nan duniya, da kuma aljanna!" A daidai wannan gaɓar da yake wannan mafarkin mai daɗin, sanyin AC yana kaɗa shi, a lokacin ne kuma Hajiya Naja,atu da ta tashi daga nannauyan baccin da ya ɗauketa don ba magriba ba isha,i tun da suka gama waya da Mom ta ringa hamma bata san lokacin da bacci ya yi gaba da ita ba, mafarkin Ruma ne ya falkar da ita, inda take ganin Ruma sanye da rigar amare Alhaji Muhammad riƙe da hannunta suna cikin farinciki, wannan mafarkin ne ya falkar da ita cikin ɗimuwa ta tashi zaune ta haɗa wani uban gumi.
Babu wata addu,a sai wani uban ashar da ta yi tana faɗin
",Wallahi ƙarya kike yarinya daga ke har uwarki" Ta faɗa tana sakkowa daga gadon, ganin agogo ya sa ta yi mamakin baccin sa ta yi, maimakon ta yi sallah haka ta fito ta nufi ɓangaren mai gidan.
Har haki take wajen hawa saman benen, saboda tsabar yadda zuciyarta take bugawa, don ta fara tunanin kar dai mafarkin ya zama gaskiya. Ƙofar ta buɗe ta shiga ganinsa yana bacci, sai dai lokacin da ta kai, cikin ɗaki ta tsinkayi ya yi magana, sai dai bata ji abin da ya furta ba, amma dai da ta ƙarasa gaban gadon ta ga tabbas bacci yake hakan ya bata tabbas ɗin mafarki ne yake.
Zaunawa ta yi a bakin gadon hakan ya yi daidai sa furucin da ya yi ya ce
"Falmi!". ,Yatsina fuska ta yi tare da ƙanƙance idanu, ƙwaƙwalwarta tana mata safa da marwa cewar sunan mene ne ya kira don ita bata ma gane cewar sunan mace ne ya kira ba, abu ɗaya ta sani ta san in ban da Goggo babu wata mace mai tasiri a rayuwarsa sai ita. Hannu ta ɗaga za ta kai kan ƙafarsa ta tashe shi, don zuwa ta yi ta rattaba masa shiga hanci da ƙudundunen da su Ruma suke shirin yi mata, ko ma ta ce suka yi mata, ta faɗa masa a cikin daren nan yau ba sai gobe ba Ruma za ta tafi ta bar gidan!.
Tana dab da taɓa kafaɗarsa maganar da ta sake yi a baccin ta sanya gabanta mugun bugawa da ƙarfi, lokaci guda ta ji ji da ganinta sun ɗauke na wucin gadi, wani tashin hankali ta ji ya mata dirar mikiya na furucinsa da ya ce
"Falmi, ina sonki Falmi" Ji ta yi tamkar ƙaramar hauka ta same ta, ita a duniya bayan ita ma bata taɓa zaton bakin Muhammad zai iya furta kalmar so ga wata halitta mace.
A zuciyarta ta ce
"Ya aka yi na bar jaki nake dukan taiki? A ina ya samu wannan mai sunan, wace ce ita? Wace mai ƙarar kwanance? Kenan ba iya Ruma ce take shirin gogayya da matsayina ba, lallai namiji ɗan bala,i ne, ni zai sincewa zani a kasuwa ni zai yi wa alƙwarin ƴan nepa!',Ta faɗi hakan a zuciyarta, da sauri ta miƙe daga bakin gadon da ta yi wa kanta masauki hannunta da ta kai za ta tashe shi ta fasa ma taɓa shi, wani irin haushinsa ta ji ya kama ta, sama da marwa take yi a ɗakin tana tunanin ta inda za ta fara don Allah ne kaɗai ya san ƙaramin yaƙin da za a yi!!!.
*RAMLA*
Tana zuwa wurin wayar kiran yana katsewa don haka, bata tsaya karanta sunan wanda ya yj missed call ɗin ba. Juyawa ta yj ta yi abin da za ta yi ta baro ɓangaren nasa ta nufi nata ɓangaren.
Washe gari da yamma, tana zaune suna charting da ƙawarta Asma,u, Asma,un ta ce
"Ramla wallahi jiya na zo wucewa napep na ga wani kamar Abdulsalam da wata a gaban motarsa" Ramla ta karanta saƙon gabanta yana dukan tara-tara duk da ta san halin mijinta na son mata da kuma kallon mata da yake da shi amma a duk lokacin da ta ji wata ƴa mace ta kusanci inda fake sai ta ji gabanta ya faɗi, hakan ya sa ta rubutawa Asma,u saƙo kamar hakan
"Asma,u anya kuwa, kuma kema ai kama kika ce ba wai kin ce shi ɗin bane"
Asma,u ta ce
"Ai tun da har kika ga na faɗa miki to bana son na tabbatar miki tun da bani da wata hujja da zan kafa miki, amma ni ina da yaƙinin shi ne!" Maganar ta ɗaurw mata kai, ita duk da dai ba a son kishiya amma a nata hangen nesan sai take ganin a matsayinsa na wanda wasu suke kira mahaifi kuma allon kwaikwayonsu, kamata ya yi ya nutsu ya san inda yake masa ciwo ko don ƴaƴansa, tun da ba zai kyautu a ce ka tashi kana ganin mahaifinka a wata irin rayuwa ba.
A zuciyarta ta ce
'!Ina tsoron watarana Abban Humaira ƙawayen su Humaira sunzo gidan nan yake binsu da mayen kallon nan da yake bin baƙina da shi, tabbas za a yi abin kunya ni tsorona ma kar ƙawayen suke yi da su a bayan idonsu'
Ramla ta ce
"To amma wa zai shigar motarsa, ya ina nan zaune ina zaman aure da shi yana waje yana cin amanata?"
Asma,u ta turo emoji na zare ido ta rubuta mata saƙon kamar haka
"Na ce miki na ganshi yana aikata wani abu ne? Kawai na ce miki na ganshi da wata a mota"
Ramla ta yi voice ta ce
"Haba Asma,u akwai wacce xai ɗauka da take muharramarsa ne? Ai ni a ganina yadda mace take kamun kanta a gidan aure shi ma namiji ya kame kansa idan ya fita ko da a ce zai so mace tun da shi mata huɗu aka halatta masa sai ya je don soyayyar gaskiya ta aure amma a ganina cin amana ne namiji ta ɗauki wata a mota matarsa tana gida "
Asma,u ta ce
"Koma mene ne idan akwai ƙamshin gaskiya watarana gaskiya za ta yi halinta"
A daidai wannan lokacin da suke wannan maganar, gabaɗaya zuciyar Ramla ta mata wani irin nauyi tamkar an ɗora mata ƙaton dutsi.
A lokacin kuma a wannan lokacin Haaiya tana zaune suna charting da ƙawarta Karima, suna tsara yadda komai zai tafi a biki. Hasiya ta tura mata gabaɗaya hotunan da suka yi jiya ita da shi, buɗar bakin ta ta ce
"Kai, kai, kai, kai, taɓɗi, ƙawata irin wannan uban tsantsara kyau haka, lallai ga zarah ga wata, kun yj matuƙar dacewa da juna, ji wani kallo da yake jifanki da shi tamkar zai haɗiye ki" Hasiya ta tuntsure da dariya ta danne voice ta fara magana kamar haka
"Ke dai bari, ai wallahi ban taɓa sanin mun yi matuƙar dacewa da juna ni da Abdulsalam ba sai da muka yi hoton nan ke a wajen hoton ma mutane sai yaba dacewar mu suke, hatta mai hoton cewa yake haɗin ya dace wai zaren kalar yadin ne, don har kyauta Abdulsalam ya masa"
Karima ta ce
"Taɓ a ce dai matarsa ta ga hotunan nan"
,Hasiya ta ce
"Ai na san wataƙila a take ta yi gawa, don ba za ta jure ba, ga kiɗimar ganina da shi ga kuma kiɗimar kyan da muka yi"
Karima ta ce
",Wataƙila zuciyarta ta buga"
Hasiya ta ce
",Hummm daga ganin wannn sai ta hau bugun zuciya, ta jira shigata gidan dai, ta ganmu tif sa taya ni da shi muna zuba soyayya ina zuba shagwaɓa" Gabaɗaya suka turawa juna emojis ta dariyar nan mai tuntsurawa.
Karima ta ce
"Ko dai tura mata hotunan za a yi, to yanzu duka fa saura kwana shida ai gwara ta fara gani"
Hasiya ta ce
"Ai ya ce sai kwana uku zai faɗa mata"
Karima ta ce
",To ke ba sai ki faɗa mata ba" Dariya ta yi ta ce
"Da ƙarfin halin nawa ya yi yawa"
Karima ta ce
"Ga shawara, ba kuna da number juna ba, ai kawai ki zaɓi wanda ya fi birgeki ki ɗora a status ta gani, kin ga idan ta je masa da maganar ma ko da ya tuhumeki sai ki faɗa masa cewa shaf kin manta cewa tana ganin status ɗinki"
,Hasiya ta ce
"Ni fa tun da na fara soyayya da mijinta ma na yi blocking ɗinta a ganin status ɗina, ko na ɗora bata gani"
Karima ta ce
"Wallahi ki buɗe shegiya ta gani kawai a wuce wajen"
Hasiya ta ce
"Allah ko ƙawata?"
,Karima ta ce
"!Ke dalla haka za ki je ki zuba mata ido ba kissa da kisisina? Ai dole ki fara ƙona mata rai tun yanzu ta san tana dab da samun abokiyar zama, Abdulsalam ɗin ba ita kaɗai ba ce mallakinsa, kuma shi idan ya tuntuɓe ki da maganar sai ki shagwaɓe masa ki nuna baki ma san ta gani ba"
Hasiya ta ce
"Kin kawo shawara kam" Tana faɗar hakan da sauri ra shiga status privacy ta cire sunan Ramla a waɗanda basa ganin status ɗinta, tana cirewa ta shiga wajen ɗora status ta shiga gallary, tana shiga ta ringa scrolling na hotunan, har dai ta je kan guda biyu da suka fi tafiya da zuciyarta sannan duk macen da ta ga wannan hoton ko da a ce mijinta ne da matarsa ta sunna wato kishiyarta sai zuciyarta ta sosu bare kuma wannan ba a kai ga ɗaura auren ba sannan babu zato da tsammani. Guda ɗaya Hasiya tana zaune a kan kujera shi kuma ya ɗan ranƙwafo tana kallon fuskarta itama shi take kallo wato sun kalli juna. Hoto na biyu a tsaye suke hannunau sarƙe da na juna ta lumshe idanunta yana kallon fuskarta cike da so da ƙauna. Duka biyu ta ɗora na farko ta rubuta a jikin hoton ",Allah tabbatar mana da alkairi nawan, a hoto na biyu ta rubuta "Haƙiƙa na yj dace mun yj matuƙar dacewa da juna" ,Tana ɗorawa ta faɗawa Karima cewar ta ɗora kuma ta ga Ramla a online da ta duba.
Ramla kuma, suna magana da Asma,u sai Asma,un ta ce mata tana zuwa ta sauka daga online ɗin.
Tana sauka itama ta fita saga account ɗin Asma,un tun da daman maganar da suke yi ne ya sa bata amsa wasu saƙonnin. Tana fitowa ta buɗe wani saƙo ta bada amsa, ta fito ta shiga ɓangaren status tana shiga sunan Hasiya da ta gani ya ɗauki hankalinta, saboda ita dai ta san bata ganin status ɗin Hasiya, don haka ta miƙa yatsanta don buɗewa ta ga mene ne ta ɗora....
*Masu kirana da masu yi min mgn, cewar shiru ba a yi posting ba, daman a sati bana yi alhamis da juma,a duka sauran ranakun ina yi sai dai idan wani uzuri ne ya taso min, wanda suke missing page ki shiga *channel ɗina ta link ɗin da yake ƙasa, idan kina channel ana turawa za ki gani don a can nake fara turawa ma ngd*
*** [8/23, 7:43 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA
MAMAN AFRAH