KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣5️⃣

*RAMLA*

Hoton ya ɗan fara gewayawa saboda network, har tana shirin fita daga wajen sai kawai ta ga ya buɗe, abin da ta gani ne ya yi mugun kiɗima ƙwaƙwalwarta, ta zaro idanu ƙirjinta yana wano irin luguden bugu. Hannunta ya fara karkarwa tana cikin wannan ɗimuwar hoto na gaba ya buɗe bata ma sai wayar ta suɓuce daga hannunta ta faɗi ba, sai da ta ji ƙara faɗuwarta sai dai ta kasa motsi bare ta ɗakko wayar wani abu take ji tamkar kamun dila tun daga tsakiyar tafin ƙafarta har tsakiyar kanta, dimmm gabaɗaya ta ji kanta ya yi kamar dai ta daina gane komai bare fahimtar komai, ji ta yi duniyarta ta tsaya cak!.

Ta furta

" Hasiya, Hasiya, Hasiya, Abban Humaira" Ta furta cikin furucin da babu sauti, iya bakinta ne ya motsa amma ita kanta da ta yj furucin bata ji sautin ba.

Tsaye ta yi ƙoƙarin tashi daga kan kujerar da take zaune, amma tana tsayawa ƙafafunta sula kasa ɗaukan ɗawainiyar jikinta, karkarwa kawai take, ga wani nauyi da zafi da zuciyarta take ta rasa wane kakar tunani za ta yi ji ma take tamkar ta samu taɓin hankali ganin ƙwaƙwalwarta ta kasa aiwatar da komai don kamar ƙwaƙwalwar ta tsaya da aikin da take yi ne!. Ganin tsayuwar ta gagare ta bare har ta iya cira ƙafarta ta fara tafiya hakan ya sa ta koma ta zauna dakyar ta samu cewa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji,un!!!" Ta zauna haɗe da dafe kanta da hannu biyu, har yanzu hotonsu yana kan ƙwayar idanunta sun kasa ɓata daga idon zuciyarta, tana jin ana batun cin amana amma dai wannan wanda aka yi mata tana jin ya fita daban daga cikin cin amanar da ake yi.

Kamar an tsikare ta ta saki riƙon da ts yi wa kanta, ta saka hannu biyu ta bugi kanta a fili tana furta

"Ramla ki tashi daga wannan mummunan baccin da ya haifar miki da mafarki mafi muni" Ta faɗa tana mai jijjiga kanta, da sauri ta ɗakko wayarta daga lan kafet ɗin ta ƙara duba hotunan a tunaninta ko za ta ga babu komai idanunta ne suka nuna mata a mafarkin da take tunani tana yi amma sai ta gansu rangaɗaɗau suna nan, murmushin da yake mata wahalar gani a fuskar Abban Humaira gashi nan shimfiɗe a fuskarsa, yana yi wa matar abokinsa shi, yana yi wa tsohuwar matar abokinsa wacce ya mutu ya bari wani kallo wanda ba za ta iya iyakance shekarun da ta ɗauka rabon da ya yi mata kallon nan.

Har lokacin gani take ba gaskiya bane, ko dai idanunta ne shaiɗan yakr canja fuskar mutanen jikin hoton yake ɗora fuskar Abban Humaira da Hasiya.

Wani ɓangare na zuciyarta ya ce

'Ramla, Ramla, Ramla, sau nawa na kira ki, idan bacci kike ya kamata ki falka, idan kuma gyangyaɗi ne ki wartsake ki buɗe idanunki da ƙwaƙwalwarki wataƙila ki gane abin da kika daɗe baki gane ba kuma baki fahimta dangane da mijin fa kike aure ba!. ' Tsayawa ta yj tana sauraren maganganun da sashen zuciyarta yake mata linzami da ta saurare su, idanu ta ƙwalalo tana jin bugun zuciyarta yana tafiya da sauri da sauri.

Zuciyarta ta ci gaba da kissima mata cewa

'A rayuwa ya kamata kowane ɗan adam mace ko na miji a ce ya tsaya ya gama karanta haɗe da nazartar hahayyar mutane da suke kewaye da shi, musamman abokin zama miji ko mata da sauran abokan mu,amala ƙawaye abokai da sauransu. Yana da kyau ka yarda da mutum amma yarda ba yana nufin ka masa amincewar da ko da ha,intarka ya yi ba za ka ga laifinsa ba kuma ba za ka yarda cewar shi yake maka abin ba, kullum kana ganin zai gyara ko kuma ba haka ya yi niyya ba bayan kuma mutane sun wuce tunanin duk inda tunaninki yake!.

Ramla kin amince da mijinki irin amintakar da ba kowace mace ba ce za ta yi wa namiji, kin masa wata irin yarda da har yau kike wasi-wasi da shakkun zai iya aikata miki wani abu, kar ki manta kin yi wa mijinki sadaukarwa irin sadaukarwar da ba na jin duk duniya zai samu macen da za ta masa ba, ya kamata a ce ya san darajarki da ba zai bari ko wani ne ya taɓa miki mutuncinki zai tsawatar am a shi kansa bai daina taɓa kima da mutuncinki ba, barw har ya dakatar da wani daga taɓa wannan mutuncin ba. A koma fannin hoton da kika gani yanxu, shin ya kamantu Abdulsalam ya kalli Hasiya da ido na soyayya? Tabbas hakan ba haram bane amma ana barin halal don kunya, kuma cin amana yana da girman da idan aka maka shi ba ya gogewa daga zuciyarka sai dai ka bar abin kawai da zummar ya wuce'

Jin xuciyarta tana mata saƙa da warwarar da hankalinta takr ji ba zai iya ɗauka ba. Sauka ta yi daba whatsapp ɗin ta kamo sunan Asma,u ta doka mata kira, sai dai an yi rashin sa,a domin tun lokacin da Asma,u ta ajiye wayar bata dawo kusa da wayar ba, don haka har kiran ya katse ba a ɗaga ba.

A fili Ramla ta ce

"Kenan dai daman zoben da Aslamiyya ta kawo gidan nan, har na nunawa Abban Humaira, kenan daj shi ne dai asalin zoban da ya kawo gidan nan har yake min tijara saboda ya duba bai gani ba, har ya yi yunƙurin sakina, ashe dai Hasiya ya ba zoben ashe tun lokacin suna tare, ashe suna soyayya ni suke rainawa hankali suka mayar da ni ƙaramar ƴar iska, tabbas Abban Humaira ya ha,inceni da ya bari nale ta mu,amala da wacce yake soyayya da ita take ganina a raine tabbas ta ga makwancina, da har na aika mata zoben ta karɓa, kenan suna tare matsayin masoya shi ee ranar da ta zo gidan nan na rakata wajensa su gaisa amma yake basarwa?

Wata zuciyar ta ce

"Idan kin tuna a ranar da ta zo gidan nan, Aslam ya ce miki ya ga Abbansu ya ɗauki wata a mota amma saboda yarda irin taki kika ce ba mace ya gani ba, tabbas tun da lokacin suna tare to Hasiya ce ya ɗauka a motar, lallai ɗan adam butulu ne, Hasiya bata min adalci ba, har ta zo gidana ta fita mijina ya ɗauketa a mota ni ina cikin gidan na bata yarda da amana a raina!'

Ji ta yi zuciyarta na barazana tarwatsewa da sauri tunanin ambaton Allah ya faɗo mata a take ta fara faɗin

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wakhluf li kairan minha, ya rabby baka jarabtar bawa baka ɗora masa abin da ba zai iya ba ya Allah ka bani ikon juriya da zuciyar ɗaukan wannan jarabawar da ta shigo min" ,Sai a lokacin ne ta ji wani kuka ya taho mata, kuka mai ƙarfi wanda yake ɗauke da abubuwa da dama domin ba iya wannn abin da ta gani kukan ya ƙunsa ba har da wasu abubuwan wanda ta yi a baya, duk da domin Allah ta yi komai amma dai yau idanunta suna son kokawa a kan abubuwa da dama shi ya sa ba za ta hana su zubar da hawayen ba kuma ko don ta ji daɗi a ranta ta samu salama a zuciyarta, don shi kuka mutum ya yi shi ma rahma ne a gare shi.

Ta jima zaune tana kukan mai sauti kanta a kan gwiwarta, kafin ƙaran kiran da aka yi wa wayarta ya katse mata. Ɗagowa ta yi idanunta gabaɗaya sun yi ja, ta duba wayar ta ga sunan Asma'u, hannunta har karkarwa yake ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta kawai sai ta fashewa Asma,u da kuka.

Asma'u ta ce

"Subhanallahi, innalillahi wa inna ilaihi raji,un mene ne ya faru Ramlar Abdulsalam?" ,Ta tambaya hankalinta a tashe, wannan sunan da ta kira shi ya sanya wani kukan ƙwace min domin ta sosa min wani giɓi da ya daɗe yana min matuƙar ƙaiƙayi ta tuna min da wace ce ni, ta tuna min wane ne Abdulsalam a gareni kuma wace alaƙa ce ta haɗa mu sannan ya muka tsinci kanmu a matsayin ma,aurata mene ne abubuwan da suka faru wanda mutane suka sani da wanda basu sani ba a take kaina ya sara, ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo min shekarun baya lokacin ina gidanmu ban ma san wane ne Abdulsalam ba.

*ASALIN LABARI*

Inna Mairamu da Malam Ali me fenti su ne mahaifan Ramla, wacce ita ce babbar ƴar da Allah ya basu, kafin daga baya Amal, da Safiya. Mahaifin ta talaka ne amma mai zuciyar yi, shi ne me unguwa, gidansu gidan tarbiyar da sanin darajar mutane.

Tun da suka taso suna yara sun taso suna ganin iyayansu suna zaman lafiya da girmama juna, kasancewar mahaifinsu me ƙaramin ƙarfi sai Mahaifiyrsu Inna Mairamu take sanar siyar da abinci a gidan da wannan suke samu suna rufawa kai asiri.

Ramla ta taso da son karatu arabi da boko hakan ya sa ta ci burin yin karatun boko me zurfi. Tun da ta taso mahaifiyarta tana zaunar da ita tana karantar da ita lamarin rayuwa tare da nuna mata amfani da muhimmmancin taimako. Da nuna mata komai na duniya samamme ne kuma ƙararre wanda ka bayar shi ne naka.

Lokacin da ta kammaka karatun sakandire, a lokacin ne maza suka mata caaaa kasancewarta kyakkyawa kuma me tarbiya. Sai dai saboda ita ba aure ne a gabanta ba take dakatar da duk wani namiji da ya kawo kansa gare ta.

Abdulsalam shi da Zahraddin abokai ne wanda suka haɗu a makarantar primary kasancewar ajin su ɗaya, kuma a unguwa ma maƙotan juna suke da gidan kawun Abdulsalam ɗin wanda tun da iyayan Abdulsalam suka rasu sanadiyyar haɗarin mota ya dawo da riƙonsa hannunsa da yake asali a ƙauye yake, ya kawo shi ya saka shi a makaranta.

Kullum tare suke tadiya makaranta su dawo tare, sannan islamiya ma idan ɗaya ya shirya sai ya biyawa ɗaya su tafi tare.

A lokacin da suke dab da kammala primary a sannn ne ciwon ajali ya kama kawun Abdulsalam, inda bai jima ba, rai ya yi halinsa. Matar kawunsa daman bata taɓa haihuwa ba haka kawun nasa ma ita kaɗaice matarsa shi Allah bai bashi haihuwa ba. Bayan mutuwar mijinta ko takaba bata gama ba ta haɗa ya nata ya nata bayan bakwai ta yi tafiyarta tun da daman gidan haya ne suka kama. Abdulsalam tun da aka yi mutuwar ya koma gidan su Zahraddin da kwana, idan aka tashi daga zaɓan makoki sai ya bi Zahraddin su kwana tare a gidan, baban Zahraddin bai taɓa hana shi ba haka ma mahaifiyar Zahraddin ɗin don ita tausayin yaron take ba uwa ba uba gashi wanda ya zame masa jigon ma ya bar duniya!.

Bayan an yi bakwai baban Zahraddin ya tafi da Abdulsalam ƙauyan da aka ɗakko shi, ko da ya je kakan Abdulsalam girma ya kama shi, komai sai ana masa, ganin babu wanda zai tallafin yaron hakan ya sa ya karɓi riƙon Abdulsalam ɗin da izinin kakan nasa, haka ya dawo da shi gidansa suka ringa murna shi da Zahraddin don dama da kuka aka raba su.

Haka suka ci gaba da karatu daga ƙaramar sakandire, komai nasu tare ita ma mahaifiyar Zahraddin kasancewar bata da mugunta sai ta riƙe shi tamkar ita ta haife shi bata nuna musu bambanci. Zahraddin yana mugun ƙaunar Abdulsalam, ko mai ya samu sai ya raba ya bashi, shi ma kuma Abdulsalam ɗin yana kwatantawa hakan ne ya ƙara ƙarfafa abokantakarsu, sannan kuma ƴan uwantaka.

Kwanci tashi har suka kammala karatun sakandire suka fara makarantar gaba da sakandire suna dab da kammalawa. A lokacin ne, a lokacin ne mutuwa ta yi gaggawar ɗauke mahaifin Zahraddin, sun yi kuka tuƙuru da su da mahaifiyarsu. Bayan rasuwarsa Zahraddin bai bar gidan ba, haka suke ƴar buga -buga su samo abin da za a ci a gidan, duk da Zahraddin ya fi shi ƙoƙartawa shi Abdulsalam ya fiya son jiki.

Da taimakon sana,ar da mahaifiyar Zahraddin take da ƴar buga bugar da suke suka kammala karatu.

Sai dai aiki ya yi wahala bayan sun karɓi takardun su. Zahraddin ya kama aikin ƙarfi, sannan ya je ya koyi sana,ar yin takalman hannu, shi kuma Abdulsalam ya zauna zaman jiran sai ya samu aikin gwamnati a cewarsa ba zai sha wahala ya yi karatu ba sannan ya zo ya ɓige da aikin wahala. Zahraddin kuwa haka yakr fafutuka yana aikin da ya samu na kuɗi, da kuma ɗinka takalaman duk da ba wani jari gare shi ba amma yana ɗinka kala huɗu biyar wani lokacin har goma ya kai kasuwa ya siyar.

A lokacin da suke tsaka da samartakar, kayan gwanjon da Zahraddin yake siya da takalman da yake yi haka zai siya musu tare, sanann takalmin ma ya musu iri ɗaya, duk da haka Abdulsalam sai ya nuna wani abun na Zahraddin ya ce yana so haka zai haƙura ya bar masa saboda ƙaunar da yake masa.

Akwai wata me awara da suke zuwa wajenta siyan awara a bayan layinsu take sunanta Hasiya. Sun saba idan sun je ana ta wasa da dariya, sai dai daga Zahraddin her Abdulsalam basu san cewa ɗayansu ya kamu da son budurwar ba.

Shi Zahraddin yana da burin aure yana ganin idan ya yi auren albarkacin iyali ma ya samu aikin daga baya, saɓanin Abdulsalam da yake ganin duk budurwar da zai yi sai dai su yi soyayya saboda shi a nashi ƙudurin sai ya samu aiki ya zama mai kuɗi zai yi aure, gashi da son mata wuyarta ya ɗora ido a kan mace tuni zai ce ta kwanta masa a zuciyarsa.

Ranar da Zahraddin ya ƙudurci sanarwa da Hasiya cewar yana sonta, a ranar da Abdulsalam ya tafi ƙauyansu wajen kakansa ne, ko da ya je mata da batub soyayya ta amince da shi don dama yana birgeta akwai ɗaukan wanka yana da tsafta.

Bayan kwana biyu Abdulsalam ya dawo daga tafiya, yana rayawa a ransa zai kai ƙoƙon bararsa wajen Hasiya, da daddare suna zaune a ɗakinsu suna taɓa hira, Zahraddin ya ce

"Ɗan uwa na samo mata fa, ni wallahi na ga wajen zuwa, in sha Allah aurenta zan yi"

Abdulsalam ya ce

"Dan Allah fa wace ce wannan?"

,Zahraddin ya ce

"Ba zan faɗa maka ba, amma dai ka santa, sai dai in nuna maka ita'

Abdulsalam ya yi dariya ya.ce

"Nima akwaiw wacce nake hari amma tun da dai baka faɗa min taka ba nima ba zan faɗa maka zan nuna maka ita, amma sai na sanar da ita tukunna"

Zahraddin ya ce

"Ikon Allah, to ai ni na faɗa mata, kuma kai da son ƴan matanja ma na san ba wai da aure za ka ce kana son ko wace ce ba ma, amma ni kuma da aure nake son tawa, don haka ni ba zan ce wajen wata ma in ganta ba ta zaci da ni za a haɗa baki a yaudare ta"

Abdulsalam ya ce.

"Ka san ni dai sai na yi kuɗi zan yi aure, idan na samu aikin gwamnati bana so matata da ƴaƴana su sha wahalar talauci"

Zahraddin ya ce

"Ni dai zan nema da karfina aikin gwamnatin wuya yake idan rabo ne watarana za mu samu"

Haka suka ci gaba da tattaunawa, washe gari bayan sallar isha,i za su fita, zuwa wajen Hasiya duk da Zahraddin bai faɗa masa wace ce ba sai Abdulsalam ya ce idan dun je wajen budurwar Zahraddin shi ma za a raka shi ya nemi iri a wajen budurwarsa, su duka sun yi gayu cikin yadinsu mai sauƙin kuɗi, suna buɗaɗa ƙamshi suka tafi, sai dai ta unguwar su Hasiya suka bi.

Hasiya kasancewar sun yi waya ta san da zuwansu ta gama suya da wuri daman kaɗan ma ta yi awarar ranar. Ko da suka taho wajen daga gefen kafin su ƙarasa gidansu Hasiya suka tsaya ya buga mata waya sanann ta ce su ƙaraso.

Ƙarasowarsu ya yi daidai da fitowarta daga gida, Abdulsalam wanda da farko da suka biyo layin zatonsa wucewa za su yi sai dai da ya fahimci abin da yake faruwa ransa in ya yi dubu ya ɓaci, tun da Hasiya ta fito tana wani kare fuska alamar kunya, ta gaishe da su dakyar ya amsa kuma bai saki fuska ko nuna farinciki a kan kawo shi da ɗan uwansa kuma abokinsa Zahraddin ya yi wajen wacce yake so.

Tun kafin su gama hirar ma ya ce gida zai tafi kansa ciwo yake, a hanya, yana tafiya dakyar yake ganin gabansa, yana tafiya yana saƙa mugun abu a ransa yana cewa

"Wato da gangan ka je ka ce kana sonta, har kana ikirarin za ka aure ta, wato dai kana so ka ja da ni, to wallahi na ɗaukawa kaina alƙawarin sai na auri Hasiya ko ba jima ko ba daɗe tun da har zuciyata ta kissima minj tana sonta, ban taɓa son wani abu na rasa wani ya samu ba, don haka ni babu ruwana da wata alaƙar da take tsakaninmu, ko kana raye idan ka saki Hasiya sai na aure ta ai ba uwarmu ɗaya ba kuma ba ubanmu ɗaya ba da kai!"

*HAJIYA NAJA,ATU*

Tana cikin safa da marwar nan, ta ji ta kasa jure ambaton sunan wata da mijinta yake yi don haka da sauri ta juyo tana zuwa ta kai hannu ta buge ƙafarsa, ya ɗan motsa amma bai tashi ba, ya sake bugun ƙafarsa ya runtse idanunsa ya buɗe, dishi-dishi ya fara ganinta, kafin ya buɗe idanun warai a kanta cikin muryar bacci me nauyin da ya kama shi ya ɗan murza idanu ya ce

"Naja'atu" Rai ta haɗe kamar bata taɓa dariya ba.

Maimakon ta amsa kiran da ya mata sai ta ce

"Alhaji wace ce Falmi" Gabansa ne ya buga da ƙarfi, ya tsura mata idanu tamkar wanda yake so ya gano inda ta dan mai wannan sunan, sai dai gabansa ya cigaba da bugawa ne lokacin da ya fara tunanin ko dai wani ne ya faɗa mata cewar ya ganshi a wajen Falmi ɗin da ya je kwanaki ko kuma ranar da suka koma da direbansa, wataƙila ma an faɗa mata wani abu a kansa da Falmi ɗin wato an masa ƙarya. Wani gumi ne ya tsatstsafo masa, ya shiga ƙoƙarin tashi zaune, Hajiya kuma ta ji wata irin faɗuwar gaba ganin bai amsa mata ba kuma kamar duk ya ruɗe.

Sai da ya tashi ya ce

"Wace ce kuma me wannan sunan, ni ban sana wata me suna irin wannan ba" Shiru ta yi tana nazartar maganarsa, sai dai zuciyarta ta rabu gida biyu, ɗaya tana faɗa mata gaskiya yake faɗa mata, ɗaya kuma tana kokwanto a kan hakan.

Ta kalle shi ta ce

"Alhaji ya za ka mayar da ni ban san me nake ba shin ka manta da alkawarin da ka min cewa ba za ka min kishiya ba da ni kaɗai za ka rayu, amma yanxu a mafarki na ji kana cewa kana son falmi!" Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin

"Mafarki ai ba gaskiya bane, mutum yana iya yin mafarkin abin da bai sani ba" Shiru ta yi tana nazari sai kuma ta ji hankalinta ya kwanta da bai san ma wace ce ba ashe shaiɗan ne ya kissama masa mafarkin.

Shi kuma a nashi ɓangaren tana ta tunanin lallai Falmi tana son shigowa rayuwarsa tun da gashi har tana zuwa a mafarkinsa kuma yana furta mata kalmar so. Shi zuwa yanzu ma yana hango badaƙalar da Hajiyar za ta yi in aka ce zai yi aure tun da dai ba zai ajiye umarnin uwarsa ya bi na wata ƙatuwa ba.

Cike da wata murya mai kamar bada umarni ta ce

"Inaso ne a yau ba sai gobe ba, Ruma ta bar gidan nan, tana nan ta kwaso kayanta ta dawo gidan nan, ni da kunnena na ji iya da mahaifiyarta suna maganar cewar aurenta ya mutu tana gama idda kai za ta aura!" Da mamaki yake kallonta duk da ya yi mamakin kalmar aure da ya ji ta ambata amma mamakinsa ya fi yawa da ya ga tana bashi umarni tamkar dai ita ce uwarsa Goggo.

Ya gyara zama a tsakiyar gadon ya kalli cikin idanunta ya ce

"Yanzu lamarin har ya kai ki kalleni ki ce kina so ƴar uwata ta bar gidan nan a yau ba sai gobe ba!" Ranta i ya yi dubu ya ɓaci a take zuciyarta ta hasala ta fara tuno irin alwashin da ta ci a gaban Ruma cewar za ta bar gidan na, idanunta suka fara hango mata irin rawar kai da kuma salon tafiya da girgiza jikin da Rumar take yi don ta ja hankalinsa ya aure ta, amma yanzu yana so ya nunawa mutane ita ba kowan kowa bace idan har Ruma bata bar gidan ba, wannan kuma ba ma maganar da hankali zai ɗauka bace domin ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa!.

*** [8/24, 8:10 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH