KIBIYA A IDO

BOOK 1

by @mamanafrah3028

🅿2️⃣6️⃣

*HAJIYA NAJA,ATU*

Cike da mamaki take kallonsa ta ce

",Wai kana nufin ba za ka ce ta tafi ba?" Ya kalle ta sai kuma ya yi shiru don har yanxu bai daina ƙaunarta ba.

Ya ce

"Zan san yadda za a yi amma zan yi nazari"

Ko ta kansa bata bi ba ta tashi fuuuuu ta baro ɓangaren nasa ta nufi nata ranta a matuƙar ɓace don idan har ba zai yi abin da take so ba bata ga amfanin zama a ɗakin nasa ba duk da idan ta zauna ma ba lallai ta tsinana masa wata tsiyar ba.

A ɓangaren Alhaji kwanciya ya yi yana mai lumshe idanunsa, kalmomin da Hajiya Naja,atu ta ce ya furta zuwa ga Falmi suka shiga dawo masa, a take ya shiga tariyo mafarkin da ya yi idanu ya lumshe yana jin wani nishaɗi.

Washe gari da ya shirya bayan ya karya zai tafi wajen aiki, ya fito don zuwa gaishe da Goggo ko ta kan ɓangaren Hajiya Naja,atu bai bi ba, tun daga nesa ya hangi Ruma sanye da wasu riga da wando sun kama jikinta, abun da ya bashi mamaki tun da ta hango shi ta fara tafiya tana doso inda yake cikin wani irin salon tafiya tana jijjiga jiki, lamarin da ya sanya ya ɗauke kai da sauri ya shiga kallon gefe guda.

Bai ƙarasa ƙofar da za ta sada shi da ɓangaren Goggo ba suka haɗu ta yi wani fari da ido ta ce

"Yaya barka da asuba" Bai kalle ta ba ya ce

"Lafiya Alhamdulillah, mu je ki rakani wani waje" Wani daɗi ya ziyarci zuciyar Ruma.

Ya juya ya fasa shiga ɓangaren Goggon ya fara tafiya Ruma tana take masa baya. Wajen ajiye motoci suka nufi a zuciyarta ta ce

'Wataƙila zai nemi wani abun ne a wajena bai san cewa ni ba wai ƴar duniya bace kawai neman ya aure ni ne ya sa nake wannan abubuwan don ya gani ya ƙyasa ina gama idda ya yi wuff da ni, daga nan duk abin da yake ko zan masa' Ta faɗa a zuciyarta tana ƙara sauya tafiya, tana addu,ar Allah kawo tsautsayin da Hajiya Naja,atu za ta gansu in ya so idan bindiga zuciyarta za ta yi sai dai ta yi.

Ko da suka zo ya tsaya a bakin motar yana ƙoƙarin buɗewa, direba ya taho da sauri amma yana zuwa sai Alhajin ya dakatar da shi, da cewa

"Karka damu mi zan yi driving ɗin" Amsa masa ya yi cikin girmamawa yana mai komawa da baya, Ruma kuwa aka yi wz direban wani kallon ƙasƙanci tana nuna masa itama ta isa tun da gashi mai gidansa ns zai jata a mota tare za su fita, a ganinta wannan ba ƙaramin capacity bane a wajenta.

Saboda tsabar tana ganin ta samu sake, don a tunaninta tarkonta ne ya kama tsuntsu. Tsaye ta yi a gefen ƙofar mai zaman banza tana jiran ya zagayo ya buɗr mata tun da itama tana ganin yanzu ne za ta sheƙe ayarta ta yi yadda take so har ta fara tunanin yadda za ta ringa cin banza wato take zo masa da buƙatu tana karɓar kuɗaɗe masu nauyi a hannunsa.

Ganin ya buɗe ta samawa kanta salama ta kai hannu ta buɗe ta shiga tare da rufe ƙofar. A daidai lokacin da ya buɗe ƙofar motar a wannan lokacin Hajiya Naja,atu ta je za ta rufe labulen windown bedroom ɗinta, cikin rashin sa,a ta hango shigarsa mota sannan ta ga Ruma ita ma ta buɗe ta shiga, gabanta ya faɗi wani malolon baƙinciki da takaici ya mata tsayuwar mashi a maƙoshi!.

Idanu ta zaro bata san ma lokacin da ta sakin wani zagi me maiƙo ba, labulen ta saki ta taho a sukwane, sai dai kafin ta zo har mai gadi ya wangale musu get sun fice. Kafin ta sakko daga saman, ta baro ɓangarenta ta fito harabar gidan, tana zuwa sai ƙurarsu ta gani, mai gadi da yake gaishe ta ko ƙurar da ta ɗakkoshi bata kalla ba.

Dawowa ta yj ranta a ɓace tana masifa tana faɗin

"Lallai namiji, namiji ne yanzu kenan Ruma ta yi amfani da gwallinta da iyayi na jan hankali ta ɗauke masa hankali har ya kasa tafiya wurin aiki ya ɗauke ta a mota suka fita, ni da nake so ya bata kudin napep ya ce ta tattara ya nata ya nata ta bar gidan amma shi ne ya ɗauke ta a motarsa ya jata da kansa don ya ja min rai i tukunna ma gidan uban wa suka tafi?"

Alhaji Muhammad ko da ya fita bai yi wa Ruma magana ba ita ma ta ja bakinta ta yi shiru sai dai ta kasa zama waje ɗaya, sai wani motsi take tana wani karkacewa kamar wata karkatacciyar kuka mai daɗin hawa.

Duk abin da take don ta ja hankalinsa yana lura da ita amma sai ya yi kamar ma bai gani ba. Jim kaɗan ta maƙale murya ta ce

"Yaya Muhammad ina muka nufa" Ya waiwayo ya kalle ta ta yi wani farrr da ido har sai da baƙin idanun ya ɗauke. Kaɗan murmushi ya kuɓuce masa amma ya danne ya ce

"Idan ba makauniya bace ke ai za ki gani" Sororo ta yi don yanayin yadda ya yi maganar ya nuna cewa kamar dai a dake ya yi wato ba wai yana ƙyasa wani abu ne dangane da jan hankalin da take masa ba.

Kamar a mafarki ta ga ya nufi hanyar umguwar gidan Mama Magajiya, da farko ta ji wani zummm zuciyarta ta fara zillo amma daga baya da ta yi wani tunani zuciyarta ta mata saƙa kamar haka

'Wataƙila fa tafiyar da kike ce ta ɗauki hankalinsa shi ne zai ɗauke ki ku je wajen Mamar ya mata bayanin yana son aurenki, tun da kin ga ke ba budurwa bace da zai nemi izinin aurenki ba tare da kin sani ba' ,Wani murmushin gefen baki ne ya suɓuce mata ta ɗauke siririn mayafin da yake kafaɗarta wanda ba zai yo girman ɗankwalin abaya ba ta ɗora a kanta tana wani rurrufe fuska.

Mama Magajiya da ta leƙo daga windown ɗakinta tana leƙen waje so take ta duba ko mai shagon layin nasu ya fito ta aiki su Umar su siyo mata suga, don jiya Goggo har da kuɗi ta bata. Sai dai hango kyakkyawar mota ta tsaya a ƙofar gidanta, ta saki baki tana ganin motar har mamallakin motar ya buɗe ƙofar, a daidai na ne ta tuna inda ta san motar wato a gidan ɗan ƴar uwarta wato Alhaji Muhammad. wani daɗi ne ya ziyarce ta kamar ta doka tsalle, don tunaninta Goggo ce ta turo shi a kan maganar ya nemi auren Ruma.

Kafin ta gama wannan tunanin ta ga Ruma ta buɗe ta fito, shi ma ya fito. Da sauri ta saki labule don akwai buƙatar ta kintsa saboda rigar jikinta, duk da ɗanta ne amma kuma yanxu tun da zai taka matsayin suruki a wajenta dole ta fara takatsantsan!...

Hijabinta ta ɗauka zumbulele ta saka ta zauna a ɗakinta a kan katifa, sai washe baki take tana wangale shi, ita ala dole buri zai cika.

Ta ɗaga hannu sama ta miƙa godiya ga Allah da ya kawo musu wannan damar, har ta fara hango ta a matsayin surukar ɗan ƴat uwar tata da kuma ƙauranta can gidan da zama su shiga sabuwar rayuwa.

Ruma ce a gaba shi a baya, sai ta ji ya mata kwarjinin da ba za ta iya juya mazaunan yana bayanta ba, tun da daman ana wankin tukunya ne don tuwon gobe, wato tana duk abubuwan da take yi ne don ya aure ta, tun da kuma gashi ta samu zai nemi aurenta ba sai ta wahalar da kanta ba.

Da sallama ta shiga gidan, Mama ta amsa mata tana cewa

"Wa nake ji kamar Ruma mutanen hutun gidan Goggo?" Su Umar kuma suka fito da gudu suka rungume ta.

Alhaji Muhammad ya yi sallama, Mama ta fito daga ɗaki tana faɗin

"Ah lallai gidan namu yau ya ɗauki manyan baƙin safe" Murmushi ya yi cike da girmamawa, ta haɗe rai tana kallon Ruma ta tsiri faɗa tana cewa

",Ruma wannan wace irin shiga ce kika yi? Ina atamfofinki ko leshi ina hijabi ko babban mayafi, da kika zo kika saka wando da riga duk sun kama jikin ki" Ta faɗa cike da ƙarajin faɗa tana son nunawa Muhammad cewar Ruma ba halinta bane saka kayan irin wannsn tun da yanzu zai aure ta kuma ta san mutum ne na gari, bai san cewa ita Mamar ita ce da bakinta ta sanar da Ruma cewar take bayyana surar jikinta saboda ya ce yana sonta, bayan a matsayinta na mahaifiya a gare ta kamata ya yi ta zama garkuwa a gare ta kuma tsanin hawa madubin dubawa.

Haƙuri Ruma ta hau ba Mama ta shige bedroom ta sako hijabi a kan kayan, lokacin har ya shigo falo suna gaisawa da Mama, su Umar suna tsakar gida. Ɗakin ta koma ta zauna tana jiran tsammani, so takr ma ta kira kawayenta ta fara musu ƙaryar za ta zama matar manya!.

Mama tana murmusawa ta ce

"Muhammad in ce dai Goggo ce ta aiko ka ka sameni?" Ta faɗa ganin ya kasa magana kamar daj yana jin nauyinta ne.

Kai ya girgiza yana cewa

"A,a ba ita bace ita bata san ma mun taho nan ba" Wani fashewa kan Mama ya yi tana jin kanta ya mata wani gingirimgim, don wannan ya nuna za su wucewa sa,a kar ma Hajiya Naja,atu take cewa an yi auren haɗi an mata kutse a gidan miji tun da idan har Goggo ce ta kwaɗaita masa auren Ruma ai cewa za a yi haɗa su aka yi amma sai ta ji daɗi da shi ya kawo kansa wato shi ya ga Ruma ya ƙyasa ya zo sanarwar yana kamu idan ta gama idda shi ya sa ma suka taho tare.

Mama ta ce

"Ma sha Allah, gwara da kai ne ka kawo kanka ba ita ta turo ka ba" Kasancewar ya san dai jiya Naja,atu tana ta masa wasu batutuwa a kan Ruma da mahaifiyarta, sai dai bai ma dauki abin da gaske bane, tunaninsa kawai so take ta kori Ruma daga gidan, duba da irin shigar da ya ga ta yi jiya da kuma wacce ya ga ta yi yau, ya san ba kowace mace ba ce za ta bar wata ƴa mace wacce ba munarramar mijinta ba take mata wata shigar rashin kunya a gidan miji.

Ya ce

"Ni na kawo kaina, daman na kawo Ruma gidan ne a matsayina na yayanta, kuma na kawo miki kashenta saboda jiya da dare ma da ta ganni take ta wasu abubuwa da hankali ba zai dauka ba, kuma ni kin ga ba muharramin ta bane da za take irin abubuwan nan a ganin ko a gaban muharramin ta take yi bai kamata ba, yanxu ɓa na fito da niyyar shiga ɓangaren Goggo muka haɗu da ita tana tafiya, da kayan nan na jikinta da kike mata faɗa, shi ya sa ma ko Goggo ban sanarwa ba na ɗakko ta na kawo ta saboda ni ba zan lamunce take yin haka na, shi ya sa ma na ɗakko ta Goggo ma bata sani ba na kawo ta gida!!!" Mama Magani wani gumi ne tun daga cikin rigarta ya fara tsatstsafo mata a jikinta kafin gabaɗaya goshinta ya jiƙe da gumin.

Ruma wacce take zaune a kan katifa jin wani batu ta miƙe tsaye cike da tashin hankalin ta ga samu da rashi!.

Mama ta haɗiye wani yawu muduk, ta ma kasa magana, ji take tamkar ta samu kujerar tsakar gida wacce mata suke zama ta rafka masa a kansa kansa. Amma haka ta ɗan wayince ta ce

"Ai wannan yarinya an yi yarinyar wofi ce, a kan me za take wannan abubuwan, ni ban san yaushe ta zama haka ba ko ƙawaye ne suke zugata oho, daman na kaita gidan Goggon ne don a samu canji"

Alhaji ya ce

,"Ai kawai ta zauna a gida zan aiko kayan nata" Ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ciwo dubu ashirin ya bata, ya ƙwalawa Ruma kira, Ruma ta fito tana jin wani haushinsa, tana fitowa ya miƙe tsaye ya nuna ta da yatsa ya ce

,"Kar in sake ganinki da wannan shigar, sannan idan kin yi idda kin fitar da miji a fara sanar da ni in yi binciken in gano wane ne" Yana gama faɗar hakan ya juya ya yi wa Mama Magajiya sallama ta amsa tana saka masa albarkar dole, fitowa ya yi ya saka takalminsa su Usman suna masa Allah kiyayr hanya ya amsa ya fita, yana fitowa ya shiga mota ya tada motar ya ja ya tafi!.

A ɓangaren Hajiya Naja,atu kuwa tana shirin yin ɓangarenta ta hango Goggo ta fito tana kiran sunan Ruma dakatawa ta yi da tafiya ta juyo ta yi taku biyu ta kalli Goggo tana sakin wani murmushin raini ta ce

"Goggo an tashi kenan, barka da safiya, wai baƙuwarki kike tambaya? Ai tuni na nuna mata ƙarfin ikona a kan mijina na saka ya kwashe ta da safen nan ya tafi ya mayar da ita inda ta fito!" Tana faɗar haka ta juya ta yi tafiyarta

Goggo ta bi bayanta da kallo sai dai kalaman sun sosa ranta, tana ganin kenan har Muhammad zai bi umarnin matarsa ya ɗauke ƴar zumunta daga gidan ba tare da ta sani ba. Rashin ganin Ruma ya nuna mata akwai ƙamshin gaskiya hakan ya sa ta nufi wajen mai gadi ta shiga tambayarsa ba,asi ai kuwa ya tabbatar mata da cewar Ruma dai da mai gidan suka fita!.

Ɓangarenta ta nufa domin zuwa ta kira shi ya kora mata bayani.

Hajiya Naja,atu kuwa tana shiga ta ɗakko mayafi ta fito ta saka direba ya ɗauke ta a wata motar suka fita, ranta sai suya yake tamkar ana gasa ƙuli-ƙuli a ruwan mai.

Sai dai ita tunaninta ɗaya shi ne Ruma ta janye hankalinsa ne da wannan ɗabi,ar rashin kunyar da take tafiya ta kaɗa jiki ta kuma dai ta ji jiya ma Ruma tana batun sai dai idan babu lafiya jikin namiji. Tana ta tunanin inda zai kai ta sai dai sanin halin mijinta na cewar ba ya zina hakan ya sa ba za ta yi tunanin wani waje ya je ya kai Rumar don su keɓance ba, ta fi tunanin gidan su Rumar suka tafi, sannan mafi zarginta shi ne neman auren Ruma ya je tun da ita a tunanin ta birgensan da Ruma ne ta yi har ya ɗauke ta a mota suka fita tare.

Lokacin da motar ta tsaya a ƙofar gidan Mama Magajiya, ta fito tana yi wa gidan kallon ƙasƙanci, ta duba wajen ta ga sawun mota duk da bata gama yarda cewar ba sawun motar mijinta bane, hango Umar da Usman sun taho za su shiga gidan ta tambaye su Alhaji ya zo, amma su ma saboda sun ga abin da ya faru jiya tsakanin Mama, Ruma da kuma Hajiya Naja,atu sai suka ƙyaleta basu bata amsa ba. Sai da ta tambaya cikin tsawa sannan Umar ya bata amsa da cewa ya zo ya tafi.

Ko sallama babu ta shiga gidan tana ta faɗar baƙaƙen maganganu, Mama Magajiya da Ruma wanda daman a wuya suke da lamarin suka hau mayar da martani, sai da suka gama yi wa juna tatas sannan ta fito tana ta zage-zage ta shiga mota direba ya ja suka tafi.

Alhaji daga gidan su Ruma ta layin gidan su Falmi ya biyo, yana ta addu,ar Allah ya sa ya ganta, idanunsa kafe a get din gidan nasu amma shiru bai ganta ba, yana dab da wucewa kamar wanda aka ce ya ɗaga idanunsa ya ganta ta fito, da sauri ya dan sauka hanya ya yi horn tana ɗagowa ta ga mota, ya fito yana kallonta ta tako ta zo gabansa ta gaishe shi tana ɗan sunkuyar da kai ganin yana ta kallonta, nan ya shiga ce mata wurin aiki zai je ya tafi, ya bata wayarsa ta saka masa lambar wayarta, sannan ya sanar da ita zai kira ta ya gabatar mata da wata munimmiyar magana, ta gyaɗa kai ya mata sallama ya shiga morar ya ja ya nufi gida domin zuea ga ɗauki jakar wurin aikinsa ya tafi.

Shi kansa ya gaza gane kansa a kan yarinyar, yana kasa mallakar kansa idan yana tunaninta. In ban daj dai ƙaddara ma gani yake ko a mafarki aka ce zai so wata ɗiya mace zai ƙaryata amma sai gashi abu a zahiri yana faruwa da shi.

Yana zuwa ya yi horn mai gadi ya buɗe, ya shigo da motar ta nufi ɓangarensa ya ɗakko jakarsa, yana fitowa ya hango Goggo ta fito daga part ɗinta ranta a ɓace, ba komai yake mata ciwo ba idan ta tuna wai Hajiya Naja,atu ce ta saka shi ya ɗauki Ruma ya mayar gidansu, duk da dai itama ba daɗin zaman Rumar za ta ji a gidan ba amma naka -naka ne daɗin zama sai bare.

Bata san cewar shi da kansa ya dauke ta ya mayar da ita ba, saboda tserewa kaidinta na mace da kuma kaidin shaidan, irin yadda take bayyana sura garw shi da wasu abubuwan da take yi kar shaidan ya yaƙe shi gwara ma maganin kar a yi kar a fara.

Sosai ya shiga tashin hankali ganin ran mahaifiyar tashi a ɓace shi kuma ya yi hakan ne kasancewar akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da mahaifiyarsa idan ya mata bayani za ya fahimce shi ashe daj akwai ƙura!.

Tahowa ya yi suka haɗu cike da ladabi ya ce

"Goggo ina kwana barka da safiya" Goggo wacce ba ta ma san Ruma har ta yj wanka ta yi kwalliya ta fito ɗaukan hankalin mai gidan don ta sace zuciyarsa.

Goggo ta ce

"Muhammad yanzu ina raye, ina cikin gidan nan har matarka za ta baka umarnin ka fita da ƴar ƴat uwata daga gidan nan ka bi umarninta, ko shawarta ta ba za ka yi ba?" Wannan maganar ta yj daidai da horn da aka yj mai gadi ya wangale get su duka suka juya suna bin motar da kallo shi sai lokacin ma ya lura motar bata nan. Ko gama parking direban bai yi ba Hajiya ta buɗe ta fito a fusace duk zaton ta maganar auren ce suka yi.

Tana zuwa ya ce

"Daga ina kike? Yaushe kika bani umarnin fitar da Ruma daga gidan nan"

Kamar jira take daman ta fara jin haushin mijin nata saboda ta lura ya canja mata kwana nan.

Cike da gadara ta ce

"Ni na ga damar fita, gidan su Ruma na je na kora mata kashedi ita da uwarta a kanka, kuma da kake batun umani ai jiya da dare na je sasshenka na faɗa maka"

Ran Goggo ya ɓaci babu wanda ya fita jin takaicin juya ɗanta da matarsa take yi, har tsaurin idanunta ya kai ta je gidan ƴar uwarta ta musu cin mutunci ba don Ruma bata da hali ba da tana kammala idda za a daura musu aure ta ga tsiya. Cike da ɓacin rai ta ce

"Wai duk a kan kar ya auri Rumasa,u kike wannan baloƙoƙon? Saboda kar a miki kishiya?"

Ta kama ƙugu ta ce

"Ai ni bani da kishiya a duniya!" Muhammad ya shaƙa yana so ya wanke mata fuska da mari saboda faɗi in faɗan ka take da mahaifiyarsa, sai dai bin umarmi ta na hana shi yin mari kwanaki da ya mari Naja,atun ya sa bai kai hannun ba.

Goggo ta haɗe rai ta ce

"Muhammad na baka na da kwana uku ka fito da wacce za ka aura, ba wai fito da matar ne na baka kwana uku ba, ranar ce za a ɗaura maka aure! Idan kuma baka da wacce za ka aura inaso ka sani a ranar da zai cika kwana uku za a daura maka aure da duk wacce na yi ra,ayi"

Cike da bin umarni ya ce

"Allah ya nuna mana Goggo an gama farar uwa me farar aniya!"

Baki a hangame Hajiya Naja,atu take kallon Goggo ya juya ta kalli Alhaji Muhammad da ya bi umarnin babu ko nuna damuwa ko jin nauyin tana wurin, sannan bata ga alamun wasa ba daga gare shi ko daga wajen Goggo ba, tana hangen rashin nasararta na cin dukiyar gadon mijin nata sannan ko ma wace ce kenan za ta zo ta haihu ita tana nan zaune!

Gidan ne gabaɗaya ya fara juya mata, a take ta nemi ji da ganinta ta tasa, bata ankara ba ta ji ta tafi luuuuu ai kuwa yiffff ta faɗi, ba ta san i da take ba.

*** [8/25, 6:42 PM] Baiwar Allah: *KIBIYA A IDO* NA

MAMAN AFRAH